Showing 57001 words to 59518 words out of 59518 words

Chapter 20 - FUSKA BIYU COMPLET BOOK PDF Writing by Halima k. Mashi.txt

maltina. Kusa dashi ta zauna ta mika
mishi maltina, kasha naka in sha nawa. Yace yau
nima naki zan sha. Tace
toh bari na dauko maka wani. Yace bani wannan
ma ya ishe ni. Ta mike bazan baka ba tana
dariya wai ita wasa. Ya gane giya ce ta zuba,
yace yau naga abin
ala'ajabi. Ta zauna, a ina? Kuma me ka gani kai
da baka cika damuwa da lamuran mutane ba,
yace to ai yau nasha mamaki. Wani soja ne cikin
wannan barikin
ya kama matarshi da wani, ta zauna da gaske
kake fada? Yace sosai ma kuma matar aure
kace? Yace Allah matar aure mijinta kuma salihi
ne dan tare muke.
Tace innalillahi, kai wannan tayi asara. Ita ko ina
zata kai zunubi, kina matar aure sannan kina bin
wani? Sojana anya mutane sun san girman
zunubin zina
kuwa? Balle matar aure ga hakkin miji ga na
Mahalicci? Tir da wannan mata. Kallonta yake
cike da mamaki bai san tsawon lokacin da ta
dauka tana
cutarshi ba. Yace kinsani my farida yanzun ji nake
in ni ne wane mataki ya kamata na dauka a
kanta? Kashe ta zanyi ko hukuma zan hada ta
dasu? Tace ai
ba zancen hukuma in yana son ya more mata ko
ya sake ta dama kaga ai in haka ta faru ba aure.
In ya sake ta sai ya barta da Allah ya isar mishi
sannu kan hankali sai Allah ya saka mishi da
mata ta gari. Ita kuma zata ga karshenta. Ya
mike cike da murmushi, shawararmu tazo daya
my farida. ya mika mata takardar sakinta uku,
yace gashi kinga karshenki, sannan tuni Allah ya
min sauyi. Kije Allah ya isa Allah ya isa ban taba
zina ba, nagode Allah da bai bani haihuwa dake
ba. Yayi daki ya bar ta nan cikin mamakin
wannan lamari.
Bansan hidimar da suke yi ba sai dai washegari
naga ya shigo da wasu zaratan sojoji sun fita da
kayan farida sai kangon dakin. Ga zatona sabon
gida ya gina
mata ta tare tun da naga itace matarsa. Sai dai
ganin ko yaushe yana gida na soma zargin ko
sun rabu ne? Wata kulawa yake mana wacce tafi
ta baya. Kullum
yana lallashina ni kam kara botsare masa nake.
Yau dai da muna kwance yace ya min alkawari na
karshe da zasuyi ya dawo zai sallame. Cikin satin
tafiyan wata biyu zasuyi wata haihuwata zai
dawo. Suka tafi dan kwantar da tarzoma tare da
runduna karkashinsa. Ranar tafiyar tamkar kada
ya rabu da 'ya'yansa. Nima ya rungume ni
sannan ya durkusa
gabana wai in yafe masa laifukan da yayi min
wanda ya sani da kuma wanda bai sani ba.
Cewarshi ko ba zai dawi ba, jikina yayi sanyi
nace tunda kace in ka dawo zaka sake ni na yafe
maka. Yace kina sona? Na girgiza kai alamar a'a.
Ya fita sai wata zuciyar ta ce kilan tafiyar kenan.
Sai kuma hankalina ya tashi. Kaduna muka koma
kowa ya sha mamakin ganina da
tsohon ciki ga yarana dake bibiyata ko ina na
shiga. Yanzu nima gaban kowa nuna musu so
nake balle ma da babansu yayi wannan tafiya sai
naga tamkar sun zama marayu. Su rahma da
jamila suna min tsiya kai matar nan da gulma
take, bana son miji bana son miji sai shegen
hadama, har kin kunso wani cikin. ban da
ta cewa wai barawo hannun mata, kowa haka
yayi ta min tsiyar nan ni damuwata ta dame ni
tunanin mijina.
Sai yanzun na yarda da batun su hajjo na cewa
ina son mijina domin yanzu na kasa kuzari ko
yaushe ina kwance da tsohon cikina ina tunanin
mijina tare da
tuno tafarkin rayuwarmu har zuwa yau. Waton
yadda na dauki ya umar ba haka yake ba, ba
mugu bane wancen karan yaki halina ne da yake
zaton ina dashi.
Ko zaman mu na kudu bai taba hanani ci da sha
ba. Kuma yana horani ne in nayi masa laifi.
Sannan bakaken maganganu da na aikata
maganganu ba laifi bane dan ya gaya min su,
tunda ya gane zaton shi ba haka bane fa? Yana
kyautatamin, yana tausayamin kuma yana nuna
yana sona. Ya umar yana da alheri, sadaka,
kyauta, zumunci da kuma adalci. Na tuna sanda
ya ba farida jari haka ya siyo min gold na daidai
kudin da ya bata yace in ajiye. Na tuno irin
soyayyar da yake min a lokutan da muka kadaita
don auratayya. Nayi juyi na rungume pillow na
saka dayan hannuna ina shafa cikina wanda
muka same shi muna tsaka da soyewa a london.
Ina son cikina, na tuno sanda ya umar zai bar
gida yaso in fada mishi
kalmar so na kasa, in bai dawo ba ba fa? Nan
kuka ya kwace min cikin kukan nake fadin ina son
ka ya umar don Allah ka dawo zan gaya maka
kaji, ina tsananin
sonka.
Na fito daga wanka na koma ban shafa mai ba
na saka kayana ban daura dankwali ba na xari
hijabina .tunanina ya sha kaina tun gun wanka
nake kuka,yau fiye da wata ya umar babu waya
in na kira tashi sai ace min tana rufe, ni kam bai
ta ba min irin wannan tfy ba,na fito falo hajja da
su sayyada suna kallo catun..
Na xari key din mota,dama motocinshi duka ya
xube min keys,ban da tawa, sayyida ta dube ni
anty an biki,anty suke kirana dan sunji hajjo tana
ce min, na kalle ta xo to muje, na dubi sayyid
yaran akwai haquri nace xaka? ya daga kai
alamar eh, nace to xo muje, hajjo tace anty ina
xaku je? nace gun su momy tace to sai kun
dawo, na riqe musu hannu muka fita sayyid yace
anty banbino aje, nace a'a sayyid yace dady mun
je ko?na kalle shi kana san ganin dady ne
babana? ya ce um sayyida tace nima ,sabon
hawaye ne ya xubo min ina yin parking a qofar su
momy ya aliyu tsaye shi da wani suna
magana.sayyid ya ce anty ga uncle suna sauka
gunshi suka nufa ni kam ciki nayi da sauri. na
tasa momy ina kuka tace me ya faru? hankalinta
tashe,cikin kuka nake gaya mata halin da nake
ciki tace min dama yacd mata inda xasu je daji
nd inyi haquri in Allah ya yarda lfy xai dawo, aliyu
ya shigo da yara nan suka yi ta lallashina har na
haqura muka yini sannan muka koa gida.
Yau watanshi 2 cur na xuba ido shiru har dare
wasa wasa har sati duk na fita hayyacina ga ciki
ina gani tsabar tension ne ya sani naqudan dole,
naqudan ma ta jini, tunda EDD dina saura kwana
10, kwana na 3 a asibiti na haihu yaro namiji
qato, sai dai na xubar da jini sai da aka min qarin
jini, aliyu da usman suka bani, an sallame ni duk
da ya bar komai hannun aliyu, cewa nayi baxanyi
taron suna ba, abar ni inji da kaina, da kuma
damuwata, suna kuwa da su abba suka tambaye
ni nace susaka sunan ya umar nasan mun rabu
kenan yanda nake yi suma duk na karya musu
xuciya hankalinsu suka tashi, kai wasa wasa har
muka yi arba'in su aminu ma suna xuwa suna
kwantar min da hankali shine mai kawo min lbrn
halin da suke ciki yace har an qara tura su wata
rundunar sbd abin yaci tura, sai da qar ya
kwantar min da hankali ya kance wai shi suna
waya,inma musa sai hajjo tace kada kiyi musu
anty kin san fa shima soja ne sai ta yuwu
hakanne.
Kwatsam rannan ya aliyu yaxo min da lbrn sun
dawo suna abuja,amma an riqe su sbd xa ayi
muru qarin girma.murnan dana ringa yi har
mamaki tayi ta ba mutane. sai kuma ahanyan su
ta xuwa lagos jirginsu yayi hatsari, mafi yawa sun
mutu,ina xaune ina kallan lbrn CNN da misalin
12,sai ga lbrn da duminshi,wai jirgi mai dauke da
man yan sojojin da xa'ayi ma qarin girma ne ya
fadi,jirgin yata so ne daga lagos xuwa abuja,ai
ban gama jin xance ba na saka ihu,ashe gida
sunji ance kada a gaya min domin hajjo tana
musu waya tace gani nan na fadi sume bata san
me ya faru ba,nan momy ta saka kuka tace shi
kenan wani ya gaya mata,farkawa nayi na ganni
a gadon asibiti kuka nake sosai musamman dana
ga daukachn yan uwana su momy ne ke
lallashina ita da mama,mama tace asma-u ai shi
bai rasu ba, nace ya mutu ba kwasan in sani
ne,lkcn ma su kansu ba sani sukayi ba,jinina
ance ya hau dan haka sukaimin alluran bacci na
samu ya dauke ni xuwa yamma sunji bai mutu ba
suna asibitin sojojh dake can abuja.
Su abba sun dugunxuma can ina farkawa na
samu lbr nafa ce saina je aka yi ta lallashina kan
in naje hankalina xai tashi ne sbd ko su an hana
su gani shi.da qar nayi sati tsabar kukana da
rashin cin abinci yasa aka ce su barni inje.da qar
suka barni na shiga gun shi.na sha kuka ganin
yanda kusan duk jikinshi an nannade shi gidanmu
na abuja muka dawo,cikin satin ya soma motsi
na liqe a asibitin nike kuka dashi addu'oi jama'a
sai yi suke masallata har da isalamiyu sbd ya
umar mai jama'a ne ga alheri shi yasa kowa ya
damu da ya fara jin sauqi, sai me? duk damuwa
da kuma hidiman da nake yi dashi sam baya min
walwala ko sakin fuska. da farko na ce ciwo ne
amma da yaji sauqi fa? sai dake min tare da shan
qamshi, watan shi daya aka sallame shi kuma
cikin satin wanda suka yi saura suka samu qarin
girma, harda ya umar a cikin wadamda suka
samu prmt, kowa nata murna abokai sun shirya
dinner mi kam tsoron shige mishi nake, shi kam
yana yine sbd kada na mishi xancen saki.
Bayan duk wadannan bidirin yau na fito wanka
bayan sallar isha'I yara suna gurin hajjo har da
junior. Kwalliya na zauna na soma tsarawa. Yau
kam na dauki aniyar nuna ma ya umar ina
sonshi. Zan gaya mishi baki da baki kuma zai
gani a aikace. Sosai nayi gayu, dakinshi na shiga
abin da ban tabayi ba shine zuwa turaka. Sanda
na shiga yana sanye da gajeren wando fari sol
haka singiletin jikinshi. Yana rubuta wata 'yar
takarda. Ina shiga ya hada rai tamkar yaga
mutuwarshi, yace yawwa gashi. Jikina ya soma
bari nace me zan gani ya umar? Ya dubeni duban
wulakanci abin da kika dade kina so ne na baki.
Kasa na zube gwiwa biyu ka min rai yaya zaka yi
da yarana? Yace ki amsa yaran da dama ba wai
kina son su bane ko dama da kika wulakantasu
me ya same su? Na rike mishi kafa kada kamin
haka. Yanzu ina sonka ina kaunarka. Yace karya
ne ke da kanki kin fada. Bakin da yace ki, ko yace
so karya ne don haka amshi ni tuni na samu
matar aure. Kingama hoton ta nan, ban kalli
hoton ba na amshi takarda na fita ina kuka, na
dauki gyalena tare da key din mota yana zaune
falo nazo wucewa yace au na manta batun karatu
in kina bukata zanfa taimaka. Cikin kuka nace
banaso ka cuce ni ka koya min yadda zan soka a
karshe ka tsunduma ni cikin kogin sanka sannan
ka sake ni, ban yafe ba. Yace haka kika min. Na
tafi na rasa inda zan nufa.
[7:59PM, 17/10/2016] 🌹@lh@ji🌹 A R: Fuska Biyu 2----15
Karshe
Gidansu naje a tsakar gida na saka ihu da gudu
su momy suka fito dasu anty cikin kuka nake
fadin ya umar ne ya sake ni. Saki? Inji momy.
Shiru abba yayi, anty tace me ya hadaku? Nace
ni ban mishi komai ba shine yace wai ba ya sona
yanzun ya samu wata. Momy tace anya bai samu
matsalar kwakwalwa ba hadarin nan? Abba yace
ku shiga daki bari na neme shi a waya. Muna
daki sai kuka nake ba ran ma da nonuwana suka
soma zuba wannan alamace ta junior ya tashi,
nace momy dan Allah ku bashi hakuri ban san me
nayi mishi ba yaace ya sake ni, in ma auren zaiyi
ai ban hana shi ba, momy tace to ya isa haka yi
shiru, abin da kara firgita ni shine duk wayoyinshi
a rufe. Ya kira aliyu ya kai shi gidan ya umar
amma maigadi yace musu ya dauki mota ya fita,
kwana nayi kuka damke da takarda a hannuna.
143-Da safe kam labari ya kai gidanmu. Abba da
alhaji a falo suna tattauna yadda za'ayi. Abba
yace anty amarya ta kira ni suji ko saki nawa ne.
Ta same ni momy tana ta min fadan kukan da
nake ta ce ai yazo ma sai ya kara raina miki
wayo. Gara ma ki daure ki nuna bai dame ki ba.
A raina nace momy ba zaki gane bane, samun
kamar ya umar zai min wuya. Anty tace su abba
suna kirana shima ya umar din sunci sa'a ya
kunnan wayarshi kuma sunce suna neman shi
yanzun nan. Kizo da sakin saki nawa ne? Fuskata
duk ta kumbura cikin kuka nace bansani ba. Na
dauko takardar kan madubi da zanyi sallah na aje
ta don hannuna ta kwana muka tafi har momy
tana cewa muje zai ga fushina yau. Muna shiga
yana shigowa, wani kyau naga ya kara min
shigar kananan kaya ta kara maida shi matashin
yaro ya zauna. Momy dake zaune kusa dani ta
zungureni ta baya alamar wai in daina kallonshi.
Na sunkuyar da kai can na kara kallonshi sai ya
min gwalo. Abba yace yanzu umar abin da kayi
yayi daidai kenan? Yace me nayi abba? Momy
cikin fada tace ina fa zaka sani, shiyasa nace a
caji kwakwalwarshi. Alhaji yace duk ba haka ba,
yanzu ta kawo takardar saki nawa ne? Na mika
musa. Abba ne ya fara dubawa, tsaki yayi sannan
ya ba alhaji. A raina nace shi kenan uku ya min.
Na kalle shi ina sabon kuka shi kam dariya yake
yi. Alhajin ya mike sun maida mu 'yan iska ne ma
yaran nan. Momy tace saki uku ne ko? Alhaji ya
bata gashi ki gani itama ta mika ma anty amarya
ta fita. Dariya naga anti tana yi ta fita duk sun
bar mu. Na dauki takardar a hannun kujera in da
anty ta ajemin na soma duba ko saki nawa ne?
Sai naga ya rubuta:
144 “Ni Umar faruk na kara nunka igiyoyin
aurenmu, ba saki ba yaji. Ina son matata shin
tana sona?” Na mike ina kallonshi yana min
dariya nima dariyar nakeyi fuskata ga hawaye. Ya
iso gurina ya rungume ni na dan mihsi dukan
shagwaba a kirji nace kai ko? Yace sorry kin son
umar ko? Nace ina sonka sosai. Ta kofar waje
muka fita ba tare da na koma cikin gidan ba
muka je muka bude sabon shafin soyayya da
rayuwa mai dadi.
145 Na fito daga cikin mr biggs ina tare da
yarana, sayyida da sayyid 'yan shekara biyar
suna dauke da kayan kwalama. Junior yana da
saurin girma don ya kamo 'yan uwansa, sai yaron
cikin da nake dauke dashi muka nufi gidan
rahma. A hanya ya umar ya min waya ina dauka
yace kin zama matar general gobe za'a tabbatar
damu, sai ku shiryo kuzo akwai shagulgula.
Murna ba'a magana. Ya umar yana da sa'a duk
cikin wadanda suka samu wannan mukamin ya
umar ne mai karancin shekaru. Gurin dinner ne
mata suka so su minkwace don haka na manne
mishi. Munsha dauka gurin 'yan jaridu da kuma
tambayoyi. Ranar muna kwance wata number sai
kiran min miji ake yaba dauka sai naga yana
kallona. Ana sake kira na dauka muryar mace naji
tana cewa don Allah ka taimaka min ciwon sonka
yana damuna, nace sai dai ya kashe ki, miji nawa
ne ni daya. Yace haba asmy yaya zaki kashe min
kasuwa? Na harare shi na tashi xan fita ya kamo
ni Allah ni naki ne ke daya, da ace ina kula mata
da nayi goma yanzu. Na dube shi bana son
kishiya fa kaji mijina? Zo muyi wata hira mai dadi
ki bar batun kishiya ke kina wadatani baki hanani
abin da zai sa inji sha'awar wata. Kina wadata
ni, zokiji wani story kanwata. Yau asibitoci muka
nufa don kai taimako ga marasa lafiya. Ya umar
kan ware kudi duk wata uku dan taimaka ma
al'ummar annabi. Yace yau zan rakaki asmy nima
ina son samun ladan ziyara. Kai fa ke bada kudin
gurin 'yan HIV, muka soma a bakin gdon wata
mata na tsaya jin tana cewa soja, baiji ba nace
ya umar, farida ta fita hayyacinta ta koma
kwarangwal. Duk wannan kyan babu shi ya gudu,
ta soma kuka tana neman gafara. Yace yau ga
sakamakona kuma kinga yadda Allah yayi dake,
dama kince da sannau zanga yadda Allah zaiyi
dake. Ya fita nima na bishi. Ina dukiyar da ta
tara? Ina iyaye da 'yan uwanta? Duk sunki ta da
ko itace ma shanawa a dangi. Mu kam soyayya
akalar rayuwa, dan iyaye sun miki zabi kada ki ki.
So da yawa yana zama alheri.
Tammat bihamdulillah.
THE END!!!

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login