Showing 39001 words to 42000 words out of 72176 words
Chapter 14 - KAREN BANA complete by ammey laylerh .txt
 yayi ƙoƙarin zuwa gaban  fridge  ya buɗe ya ɗauko ruwa mai tsananin sanyi yana zuwa ya yayyafawa maryam abduljalaal tare da jaddahn.
 ajiyar Habebty ta sauƙe tare da ƙara rumtse idanunta fatan ta  da burin ta bai wuce ace yau mafarkin Nan nata ya tsaya iya nan ba tanason yaukam suyi magana acikin mafarkin da tasaba na ƴar nata, saidai kuma jin ƴar hayaniyar su ammey da suke hamdalar ganin ta buɗe idanunta ce yasa taji wani tukuƙin bala'i tsaya mata arai.
Sai kuma ta buɗe idanun nata wanda suka kaɗa sukayi jazur dasu, ganin dai tabbas ta buɗe idanun nata ne kuma ta kuma ganin wanda ko tantama babu gudan jinin tace yasa a sukwane tayi kan jaddah tana farɗeta daga  cikin jikin ummey tana rungumeta tsammm acikin jikinta, sai kuma hawaye sharrrr suka shiga sauƙa asaman fuskarta,...sai kuma ta  fara magana cikin sheshsheƙar kukan dayaci qarfin ta.
"Me yasa? Me yasa kuka rabani da gudan jinina? Mafi soyuwa acikin duniyata mene mai muku?!!! dana cancanci wannan muguwar sakayyar daga gareku kodan kawai s0n wani cik0n muradi naku marar tabbas marar ɗorawa!¡!"
"An ha'inceni anci amanata anrabani da duk wani sukuni na rayuwa shin dukk akan abin duniya ne kuke wannan abunnnn; bayan kunsan idan akan abin duniyar ne be shafeni ba! Bayan kuna da tabbacin cewar ba daga gidan tsiya na fito ba..."
"Muna da tarin dukiyar da kaff ahalinmu na MADINAH babu wanda yasan iyakar  arzuƙin da iyayenmu suke dashi. kuma nasan ku ɗin ba akan komi kukamin hakan ba kuka rabani da rayuwata saidan kurayu da arziƙi iya kar ku! Meya hakan mene kuka aikata kenan?"
________
Gaba ɗaya jama'ar falon babu wanda ya iya furta komai face idanuwa da suka bita shi, ummey kuwa kusan mutuwar zaune tayi dan ganin wannan bahagon al'amari dake shirin faruwa dasu, jin Muryar matar kuma shine yaƙara rikita ta tare dasa mata wani irin tsoro mai tsananin gaske.
Ammey kuwa cikin ƙarfin hali ta matso kusan da FRIEND tare da ɗora hannun ta saman shoulder ɗin friend ɗin, jin hannun mutum kuma saman shoulder nata ne kuma yasa ta ɗago kanta domin ganin waye ya riƙe ta haka, cakk kuma ta dakata tas0n zancen da takes0n furtawa, ganin AYSHA MALEEK IBN MALEEK ce dafe da kafaɗarta hawaye shaɓe shaɓe saman kyakkyawar fuskarta, cikin wani irin sanyi da ammey ta tsinci kanta aciki ta farawa aminiyar Tata ta gani kasheni amma ADA CENN shekaru masu ɗan dama wanda aloƙacin tana ɗauke da cikin dake jikinta na jaddan wanda tayi ma ƙawar Tata alƙawarin zata sanya mata sunanta indai mace ta haifa za kuma taba MALEEK aurenta wanda loƙacin yana ɗan shekara goma sha biyu, amma sama ta ka kowannensu ya manta, da ɗan uwansa babu dalilin komi amma kowa yanajin kewar girman abotar dake tsakanin su.idan kuma suka zurfafa da tunanin junansu sai suji kansu yaɗaure da tsanin azabar ciwo tamkar zaya rabe musu gida biyu......
Ammey ce cikin sanyin da dake ciki ta shiga faɗin "kiyi kuka Maryama idan da abinda yafi kuka yau kiyi shi kiyi  abunki FRIEND domin nafi kowa sanin ancutar da rayuwarki, bansan meye yasa ba ban sani ba bansan abinda ya raba girman abotar dake tsakanin muba MARYAM. kawai na tsinci kaina da mantawa dake da kuma kasa zuwa gareki, duk loƙacin da nayi ƙoƙarin zuwa gareki kuwa inajin tamkar fitar raina!"
" Nayi kuka nayi kuka nayi kukan da bansan adadinsa baaaa MARYAM, meye ya rabamu? Wane ya rabamu? Na kasa gane hakan idan kuwa na zurfafa da tunanin ki ranar ina kwanan hospital ne MARYAM duk miye hakan? Mene dalili?"
Haka dai ammey ta shiga fadar abubuwa tamkar zararriya marar kai MALEEK dake tsaye idanunsa sunyi wani irin farin azaba bama ja bane yayi garen murya,hakan yasa gaba ɗaya jama'ar falon maida hankalinsu kanshi tare da zuba masa na mujiya.....sai kuma mai martaba sarki maleek yayi gyaran muryar shima tare da cewa kowa ya nutsu  suna s0n agama komai da wuri domin yau sukes0n komawa inda suka fito, hakanne yasa kowa ya nutsu bayan ansha ruwa dan kamm sun gaza cin komi ruwan ma ba kowane suka sha ba.
Bayan an nutsu kowa yaga MALEEK ya miƙe tsaye tare da fuskantar dukkan jama'ar fal0n
"SHEKARUN BAYA"
"A cen shekarun baya da suka shuɗe mana, shekaru ne na musamman acikin rayuwarmu dama ahali biyu zuwa uku, ba kowane waɗannan ahalinba face ahankali sarki maleek ibn suffyan da ahalin sarki ABDULPHATA OMAR tare da ahalin mahaifan MARYAM ABDULJALAAL"
 "Tun ina ɗan ƙaramina nasan girman alaqar dake tsakanin waɗannan ahali sarki ABDULPHATA OMAR wanda yake ɗan uwaa a wurin kakana Sarki MALEEK ibn suffyan sun taso cikin s0n junansu,domin su giyar mulkin bata sa sun guji junansu ba kamar yadda wasu mutanen suke yi a tsakanin su!.. wannan abune  yasa alaƙa mai tsanin ƙarfin gaske kulluwa tsakanin mahaifiyata da kuma Amaryar sarki ABDULPHATA OMAR wato MARYAM ABDULJALAAL, aloƙacin da aka kawo ta 9j mahaifiyata ce ta zame mata babbar ƙawa aminyi ƴar uwaa domin bata da kowa anan ɗin, loƙacin da sarki abdulphata ya auro maryam abduljalaal inada shekara goma a duniya  ina kuma tsananin wayo wanda ko mahaifana basu san inada wannan wayon da basira haɗi da baiwar da Ubangiji na yamin ba, aloƙacin da na fara ganin AUNTY MARYAM sunan dana bata kenan, na maƙale mata kawai naji ina kaunar ta sosae inajinta tamkar mahaifiyata ne, kai hakan yasa idan sun ziyarci junansu nakan maƙalewa aunty maryam nayi ta kuka ince Ni saina bita a gurinta zan zauna, fatan dukka baku manta hakan ba?.
Ya faɗi maganar yana kallon ammeyn sa da kuma FRIEND,...kai suka shiga ɗaga masa tamkar wasu ƙadan garu kana shi kuma yaci gaba da faɗin.
Haka zanyi ta musu kuka har mahaifina yace ya bawa AUNTY MARYAM niiii! Naje na mata hutun aloƙacin ina primary 5 badan mommah taso ba dan aloƙacin ina wurinta da zama baki ɗaya tun daga yayena da tayi;....haka cikin murna Ni kuwa na shiga haɗa kayana abbiena ya kaini har garin Adamawa da kansa al0ƙacin ne na hango wata iriyar s0yayyar da bantaɓa ganinta agun kowa ba face mahaifiyata wato ammeyna kenan!, sai kuma  naji tamkar kada nayi tafiyar saboda wannan tsabtatacciyar soyayyar dana hango acikin idanuwan mahaifiyata akaina, amma kuma yarinta tasa nayi tafiyata Adamawa wurin Aunty maryam, danakejin tamkar akwai raina da rayuwata tare da ita! Naga gata mai sunan gata awurin Aunty maryam domin soyayyar duniya ta ɗauka ta ɗora min duk kuwa da cewar aloƙacin tana ɗauke da nata cikin, Amma hakan baisa ta sauya daga soyayyar da take nunamin ba, haka na fara huta na cikin kwanciyar hankali komi na nema ina samu, idan aka bani abu Tofa saina raba biyu na bawa FRIEND rabin nace mata wannan na MATATACE ko ABOKINA domin ban manta alƙawarin dake tsakanin mahaifan nawa ba;.
Aloƙacin da cikin dake jikin  friend yakai wata takwas aloƙacin ne kuma mahaifina yazo ɗaukana mu tafi wai hutuna yazo ƙare su, akuma loƙacin nima na dire nace babu inda zani"
"Domin naji na kuma gani da idanuna irin makircin da auntyn nawa take a ciki haka naƙi yarda sammm nabi mahaifina Abuja!, Akwana atashi babu wuya wata Ranar juma'a wacce takasance babbar rana kuma baƙar rana agaremu  Aunty maryam ta tashi da nakuda hankali na idan yayi dubu toya tashi haka inaji ina gani aka tafi da Aunty maryam ɗakin haihuwan:.Tasha matuƙar wuya kafin ta haihu aloƙacin dukkan likitocin dake kula da ita suka fita sallar azzuhur"
"Akuma loƙacinne na samu damar kutsa kaina cikin ɗakin haihuwar ina zuwa na tarda ta haihu ta haifi ƴarta mace, na rasa yadda zanyi gashi bata cikin hayyacinta ita domin ma bata san ta haihunba ba kuma tasan maine ta haifa ba! Ganin almakashi dadai sauran kayan haihuwane yasa na ɗauki almakashin nan na yanke cibiyar domin ina ganin yadda ake acikin game na wayar wasan da Aunty maryam ta saimin, kuma dama dukkan wani FATANA da BURINA shine inzama LIKITA! Haka bayan na yanke cibiyar na ɗaukar kyakkyawar babyn auntyna wanda dukkan jikin nata jinine amman banji ƙama ba haka na rungume babyn a ƙirjina a kuma daidai wannan loƙacinne ta fara wani irin kuka, kukan ashe da ashe kukan rabuwa da mahaifiyane Ni bansaniba, kamar wacce aka sauken wahayin da nayi mata huɗu ba hakan yasa na raɗa mata AYSHA!"
"Sunan ammeyna kenan  ina gama mata huɗu bar nan likitocin suna dawowa hakan yasa suka koreni nayi cikin gidan ina kuka, anan aka bayyana cewar amaryar mai martaba sarki ABDULPHATA OMAR ta haihu ta haifi ƴarta mace.
Anan kuma naga mommah Naaaaa Hajiya LUBNA kenan wai dama ɗaukana tazo haka ina kuka ina komai ta kama hannuna zuwa ɓangaren hajiya LAURAH wai zasu gaisa, zaunar dani tayi a daya daga cikin kujerun falon tace na zauna tana zuwa karna yarda na biyota, sammm naji ban gamsu da Wannan dokar nata ba hakan yasaaaaaa
Tofa muje zuwa 
Donji mene ya faru a gaba 
🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰
More comments more typing😌😌😌
Shin mene maleek ya jiyo ?
Menene dalilin sa na kin tafiya yabi mahaifinsa?
Ya akai aka sace jinjirar da ko mahaifiyarta bata samu ganinta?😭😭😭😭🙃🙃🌚
Amsar kunsan tana ina
*🔥💔 KAREN BANA 💔🔥*
        👆🏻👆🏻👆🏻👆🏻👆🏻🤠👆🏻👆🏻👆🏻👆🏻👆🏻👆🏻
Muje zuwa by 
✨ *Ammeyn laylerh🫶🏻*
*Allah yaci gaba da haskaka al'amuranmu cikin farin ciki da kwanciyar hankali🤲🏻*
*Allah Ubangiji kaci gaba da shiga cikin Al'amuranmu Allah kaci gaba da shige mana gaba akan komi namu🤲🏻*
*Ina miƙa sauƙin ta'aziyyyata gareki MUB'ASHA IBRAHIM na rashin dan uwaa da kikayi fans kuma members acikin group na KAREN BANA FAN'S group Allah yakai haske ƙabarinsa Ubangiji yasa mutuwa hutuce gareshi🤲🏻🤲🏻😭😌*
Ohh my God
*🔥💔 KAREN BANA 💔🔥*
NA MARYAM NASEER MIRRAH ✨
*Ammey laylerh*
Page 3️⃣1️⃣
08104493215
Yau fejin nakune masoya littafin KAREN BANA 💔
*Haƙika Ina jin daɗin comments naku sosea masoyansa*
INDO ADO
Fatima lawan60
Fatima Aliyu
A'isha Yusuf
qanwan ta'eeba naman ta'eeba
Aunty apple Naaaa
MLS jamilat
Mub'as Ibraheem
Dama wanda alƙalummana bazasuyi amfani wajen rubuta tarin alkairanku gareni baaa,saidai nace ilahu yabar ƙauna har gaban abadan🫶🏻🫶🏻🫶🏻
*❤️🔥It's just that you are close to Ammey Laylerh, she is very kind to you🫶🏻*
________________________¥
_____Kawai naji sammm ban gamsu da wannan dokar nata ba hakan yasa na miƙe nabi bayansu!,na laɓe abayan labulen dakin, inas0n ki kashe ta idan kin tafi bana ƙaunar ganin jinin MARYAM acikin duniyar Nan lubna.
"Wannan kalmace da takusan tarwatsa tunanina, amma ina cikin wannan tashin hankalin maganar ne kuma...kunnuwana suka ƙara jiyo abinda ya kusan tafiya da rai da numfashi na, daga matar da naɗauka mahaifiyata a wancen loƙacin wato Lubna!"
"Idan kikace kisa ai kinyi ɗan ƙaramin abu LAURAH, zan tafi da jinjirar yarinyar zan yarda ita a cikin kurmin jejukan dake ƙauyen Kano, nasan rayuwar yarinyar zaya tagaiyara tazam abin tausayi bayan ita jinin mulki ce gaba da baya!.
Ko kin manta da cewar da nima wannan tsinan nan yaron MALEEK so nayi na kashe ɗan banza, ammah kuma danayi wani tunani nace idan na kashe! shi dole uwarsa ta haifi wani, wannan yasa na sanja tunani ta hanyar raba uwarsa ta mahaifarta baki ɗaya, sannan nazamar da yaron tamkar bawa acikin gidana, sannan shi kuma yaron na cusa masa tsantsar tsanar mahaifiyarsa AYSHA GALADIMA, kana kuma nayi amfani da yaron wajen tarwatsa rayuwarsu da kansu shida shegiyar uwarsa!"
"Miye kike ganin zai faru gaba?" Idan har wannan shawara tawa tayi miki hhhhhhhhh suka sheƙe da wata shegiyar dariya ta tsantsar rashin imani da mugunta"
"Wannan zance nasu da naji,shine farkon shafin ƙaddarar ta tazo ta gitta daga cikin rayuwana, shine dalilin sauyin ra'ayina daga zama LIKITA zuwa SOJA, domin kawo ƙarshen zalumci irin nasu LUBNA da LAURAH.
Wannan shine abunda baya taɓa gitta wa daga cikin rai da ruhina, wannan abu yasa nayi alƙawarin zamewa wannan jaririya GARKUWA agareta;"
       "Kafin su fito kuwa bayan na tabbata sun gama tattauna komai. nayi saurin komawa saman sopar da mommah ta zaunar dani tamkar babu inda na motsa...saima sautin kukana dayafi na ɗazu yawa da gunji, da banyi niyar bin mommah na ba amma wannan dalili yasa na amince zanbita, zanbita domin kare rayuwar rayuwata AYSHA ABDULPHATA...haka mommah ta jani muka fito ashe Hajiya LAURAH sun haɗa baki da likitocin cikin masarautar ta hanyar siyesu da wasu maƙudan kuɗaɗe, koda muka fito kai tsaye cikin clinic ɗin masarautar muka nufa!" Koda isarmu har sun saka jaririyar acikin kwali, muna shiga aka miƙowa LAURAH kwalin Nan wanda na tabbata jaririyarce acikin wannan kwalin, haka inaji ina gani a gaban id0na! Hajiya LAURAH ta miƙowa mommah wannan kwalin ko sakan ɗaya bamu ƙara acikin masarautar Adamawa ba muka ɗauki hanya, tafiya muke babu ji babu gani haka muka dinga tafiya, munzo daidai wani gari da bansan ko ina bane amma jejin garinne ta faka motar tace na zauna acikin motar tana zuwa ta ɗauki kwalin Nan tayi gaba, tana fita a motar saida na tabbata tayi nisa ni kuma na fito na dinga bin bayanta!....saida muka wuce gonaki uku ta tsaya tana ajiye wannan kwalin Ni kuma ganin ta ajje wannan kwalinne yasa nayi saurin zaro kibiyar da riga na ɗauka tun acikin ɗakin LAURAH, wata jikin ƙatuwar bishiyar gamjin dake kusa da gonar na shiga rubuta cikin sauri domin yazame min shaida wajen gane wannan gurin!" Abinda na rubuta kuwa ba komai bane faceee...
" RAYUWAR AYSHA ABDULPHATA da RAYUWAR MALEEK TAUFIQ WATA RANA ITACE SANADIN KU" 
"Shine na rubuta  ajikin wannan bishiya ta gamji, wanda zanen ya zauna ɗoɗar har kwanan gobe kuwa yana Nan ajikin wannan bishiyar.
haka nayi gudu na koma cikin motar mu har mommah ta taddani zaune kamar dai wancen loƙacin bata fashimci komai ba, haka muka ƙara ɗaukar hanya cikin baiwar kwakwalwar da Allah yamin nake bin hanya da kallo ina gane komai har muka is0 cikin garin wannan ƙauyen inda naka an rubuta *WELCOME TO RANO*"
"RANO ta zauna a tsakar kaina daram zane a ruhina, muna isa Kano muka nufi filin jirgin sama dake dama a jirgin tazo sabo da mugun nufin sune yasa, ta ɗauko matar ƙawarta wanda tace ta barta zatasa Azo a ɗauka mata domin tana da yara a Kanon,muna isa kuwa acenn ma muka tadda yaran Hajiya LAURAH sun zo ɗaukar motar nata!.
Haka muka shiga cikin jirgin ina ji tamkar rai da rayuwana baya tare dani,ahaka jirgin mu ya lula sai garin Abuja"....haka bayan dawowana gida nabar duk wani famarki nawa na zamowa babban dactor na tashi daga dactor zuwa soldier.....ansha fama dani kafin na dawo normal kamar kowa tunda ga wannan rana kuma duk wani burina da target nawa na ɗaurasu akan waɗan Nan mutane biyu, wato LUBNA da LAURAH.
Haka rayuwa taci gaba da wakana acikin rayuwata amma koda wasa ban taɓa furtawa kowa wannan babban al'amari ba hatta kuwa mahaifiyata!.
haka na ci gaba da bibiyar rayuwar AYSHA ABDULPHATA OMAR ba tare da sanin kowana ba harna gano inda take. saida na tabbatar da inda  take zaune take kuma rayuwa a wajen babu wurine na musamman kana hankali na ya kwanta, saidai koda wasa ban taɓa zuwa ga iyayen Aysha ba kawai dai ina bibiyar rayuwarta, ta inda na tabbata bata da wani! Nakasun rayuwa kamo daga addinin Musulunci da kuma karatun boko, amma ina xuwa gareta da kaina nasha zaunar da ita na koya mata karatu, kusan kullum kuwa ina hanyar Kano ba tare da sanin mahaifana....ana cikin haka jarabawata ta fito inda mahaifina ya naima min gurbin karatu a ƙasar London.
Banso hakan ba domin gani nake tamkar wani abu ka iya cutar da ruhi da rayuwana wato AYSHA ABDULPHATA OMAR, wacce ta koma jaddah a yanxun! Na bibiyi rayuwar AYSHA fiye da tunanin mai tunani"
"Nine na ɗauke nauyin karatun ta tun daga kan primary har secondary nata har ya zuwa poly nata.
Amma sai nace kada malaman makarantar su baiyana cewar wani na daban kawai suce gwamnati ce taɗau nauyin karatun nata....ina daga cennn ƙasar London nake yin duk wannan abubuwan ta hanyar yarana, haka kuma sau dama nakan shirya gagarumar kyauta nabi ta wani salon na daban ya zuwa MALAM ABDULLAHI RANO, tunda na tafi ƙasar London ban ƙara ganin AYUSH!
 ba haka nake daure wa duk kuwa da cewar ba ƙaramin abu bane nayi, duba da cewar tamkar rai da rayuwane aka raba, ina tsananin ƙaunar AYSHA ta yanda nima kaina bansan irin adadin S0yayyarta gareni baaaa!"
"I just know that I love her very much,I have a lot of love for her, I don't know how much,I love AYUSH more than anything I own  in this world I took my parents, AYUSH is the life of MALEEK TAUFIQ completely alone♥️💘"
I give her a kind of S0N S0 and I don't know the end of it I love her forever I love you my wife with all my ❤️"
"Amma haka na daure duk da cewar akwai tsananin wuya da azabtarwa, tun daga wannan loƙacin ban ƙara ganin Aysha ba har sai da na kammala karatuna daga Nan na fara karɓar horaswa ta musamman daga gurin aikina   na soldier tare da kammala komi nawa, daga nan na tattaro na baro ƙasar London baki ɗaiii!.
 A loƙacin ina da shekaru talatin cifff inda na fito da babban matsayin da kowa yayi mamaki,kasan cewar nasa aikin nawa araina sosea fiye da tunanin mai tunani, saidai kashh a loƙacin da nake da ɗoki da mararin gani abu mafi soyuwa acikin rai da ruhina, aloƙacin ne kuma wasu shaiɗanun mutane suka shigo cikin komar hukuma da rayuwata!.
Hakan yasa na ajje batun soyayya ta a gefe domin tunkarar abokan hamayya ta, kwatsam kuma ban tashi auneba naji mata maganar data kusan sanadina magana mafi muni da azabtarwa agareni, loƙacin da mai martaba sarkin maleek yazoma da mahaifina zancen auren da sukeson sumin mai kama dana dole, aloƙacin naji tamkar na kashe kaina na huta ne...kawai domin kuwa na shiga tashin hankali kwarai da gaske, ada naso bijerewa umarnin mahaifina da mai martaba sarki maleek, saboda nasan bazan iya rayuwa da ko wacce mace ba idan ta huce AYSHA ABDULPHATA OMAR, amma haka wani ɓangare na daga cikin zuciyana  ta bani kwarin gwiwa akan hakan, domin gudun ɓatawa mahaifana raii.
idan mai martaba sarki maleek ibn Suffyan bai manta ba a ranar ɗaurin auren ma saida naje na masa mugun kasheɗi akan kada ya sake aɗaura wannan auren!."
Yayi maganar yana kallon mai









