Showing 57001 words to 60000 words out of 72176 words

Chapter 20 - KAREN BANA complete by ammey laylerh .txt

tsofin najadun aboka nankan"


Wata sheɗaniyar dariya su kashim baba suka sheƙe da ita kana suka haɗe baki gaba ɗaya suka ce .
"To shikenan YARO, shege ka fasa amma duk abinda zakayi karka mance da cewar kana yaro da mata mafi soyuwa acikin RAI da RUHINKA!, Kuma sune duniyar ka maleek!."


Cikin zafin zuciya maleek da ƙuna maleek ya shiga faɗin


"Lallai kammm za kuyi dana sani marar ƙarewa! Kana ina mai baku albishir da cewa ina dab da tagaiyara rayuwarku baki ɗan ku.....


Ciki dariyar mugunta da sanin muguntar da suka ɗana masa suka shiga faɗin.


"Kada ka manta fa yanxun ba kai ɗaya bane, kana ba ki biyu bane baku goma bane kuna da yawa, mafi soyuwa kuma ɗan ka ayman, wanda muka seta Ranar mutuwarsa daaaaaa hhhhhhhhhh"
Suka shiga ƙaƙata dariya su duk.
Bai samu zarrar cewa komai ba aka yanke ƙiran kitt daga ɓangaren masu ƙiran.


Hakan yasa maleek komawa jikin rug ɗin office ɗin, tare da jingina jikinsa da kujerar, yana dafe daidai saitin zuciyarsa daya fara jin ta masa wani irin nauyi.
Cikin jin ya gaji ya kuma ƙosa wannan rana zato ya miƙe tsaye a fusace, tare da saka hannunsa na dama ya doka plasma ɗin cikin office ɗin, ai kuwa ji kake taratsatsa ta tarwatse. Gefin leɓensa ya shiga taunewa da qarfin gaske, ya cuta hannunsa zai kuma tarwatsa system nashi ne, Jawad ya shigo cikin office ɗin ganin a halin da maleek ɗin yake a ciki ne, yasa shi saurin dafe kafaɗarsa haɗi da cewa "haba maleek b a man mana ka nutsu, kana karanta innalillahi wa'inna ilaihir raji'un"
Ai kuwa nan dana ya shiga nanata kalmomin da Jawad ya shiga faɗa masa, cikin kudira ta Ubangiji kuwa ya soma jin wata irin nutsuwa na sauƙar masa.
Hannunsa Jawad Ya kama ya zaunar dashi, tare da fuskantar sa kana ya shiga faɗin "yanxun haka na riga da na gama dukkan wani shirin da kace na shirya maka! Sannan akwai ƙalu bale sosai tattare da hakan, amma kada ka damu Ni zanji da komai."
Cikin sanin irin aikin Jawad ɗin agareshi ne yasa ya shiga kaɗa kansa haɗi da cewa " weldone" yana bashi hannu suka kashe..
Nan Jawad ya fice a office ɗin na maleek bayan ya damƙa masa wasu muhimman abubuwa.
Nan shima maleek ya miƙe tare da yin wajeee cikin gaggawa.
Kai tsaye motarsa ya shiga tare da mata key yana janta da wani irin mugun gudu na fitar hankali, gida ya nufa nan danan kuwa ya isa gidan cikin ƙanƙanin loƙaci.
Kota kannnn su jadderh baibi ya shige ɗakinsa cikin wani irin azabar sauri, domin dama yasan tarkon daya haɗa musu shi yasa cikin hamzari, yake komai tun kan burinsa yacimma haƙa.


Idan hankalinsa yayi dubu toya tashi yana son yau ɗin nan ba sai gobe ba kama su kashim baba a hannunsa, cikin sassarfa ya faɗa ɗakinsa tare da shigewa cikin clothes nashi rigar bullet nashi ya ɗauko ya zira ajikinsa tare da wasu shirye shiryen sa, kamar kibtar ido yazo ya gimla su jadderh dake zaune a parlourn fuuuuuuuu ya fice a gidan baki ɗaya, saida ya tabbatar ya gama Bama gidansa da kuma gidansu tsaro na musamman.
Motarsa ya kuma faɗawa tare da janta a 360 yabar gidan. Duk inda na'urar bibiyar dake nuna masa yake bi tare da shima da setawa su Jawad hanya, nan ya fara kurdawa cikin lunguna da saƙuna tun yana cikin garin na Abuja, harya fara barin cikin garin.


Daga cennn kuwa ɓangaren su kashim baba gaba ɗaya suna tare Dukansu, gaba ɗaya suma sun gama zama cikin target, domin ko yaushe wannan shegen yaron ka iya kai musu farmaki, shi yasa akoda yaushe suke kewaye da yaransu, gaba ɗaya suka shiga tattaunawa akan yadda za suyi da rayuwar maleek bayan sun gama kashe yaronsa a gaban idonsa, zasuzo suga yadda maleek zai yi bayan sun kashe jaririn yaronsa mafi soyuwa a gaban idansa!.
Hakan yasa suka shirYa sosai wajen farmakar maleek ɗin.


Shi kuwa maleek cikin ƙwarewa yaci gaba dabin diddigin na'urar, haka ya dinga barin cikin garin yana kutsawa jeji, saida yayi tafiya ta fitar hankali kana na'urar ta tsaya cakkk daidai wani ƙaton kango, hakan yasa shi yin wani uban reverse daidai ƙofar mashigar.
Fitowa yayi cikin shirin Kota kwana yake kutsa kansa cikin gidan, nan ya dinga haɗuwa da nasu gaɗin su kashim baba da miyagun bindugu, aikuwa ya shiga sheƙesu tare da ɗebe makayan yana tattare su wuri guda, babu zato babu tsammani kawai su kashim baba sukaji qarar harbin bindaga hakan yasa a gigice suka miƙe, tare da yin settings kowa na abinda yake hannunsa.
Suna Nan tsaye sukaji ƙarar fasa ƙofar da maleek yayi tare da kutso kansa cikin wargajejen forlourn! Me zasu gani maleek ne tsaye hannayensa duka biyun riƙe da manyan bindugu hakan yasa su kashim baba sheƙewa da wata sheiɗaniyar dariya tare da tafa hannayensa, sai kuma yaYi wani irin fito fifitttt, Nan kuwa kan kace me gaba ɗaya yaran su kashim baba suka zagaye forlourn baki ɗaya.sai kuma sukawa maleek ƙawanya suka sashi a tsakiyar su, Nan suka Alhaji Atiku suka shiga ƙaƙatawa maleek dariya, tare da faɗin "Sannu jarumi, wai kai nan JARUMI ko? Hhhhhhhhhh yau qarshen ka yazo kazo a daidai dan yanxun hakan na tabbata yaronka yana kan hanya, da munso saimun kashe shi kana mu tura maka da gawarsa, bayan munyi raping nashi, amma babu komai ko ba komai zakaga yadda za muyi raping na jaririn ɗan ka akan idonka! Kaga kuwa dole ne yayi MUTUWAR AZABA da RAƊAƊIN FAƊEEE"
Hhhhhhhh hhhhhhhh hhhhhhhh sai suka shiga ƙaƙata dariya Dukansu kafin kashim baba ya ratso ta tsakiyar taron tare da nuna maleek da bindiga kana ya shiga faɗin.
"IDANNNNNN🙊🙊🤣🤣🫰🏻🥰


Mai zai faru?
Idan yayi mene kenan?


Allah masani amsar
kunsan tana ina?😉


Tana Nan


*KAREN BANA*
👆👆👆🏻👆👆


🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰
*🔥♥️ KAREN BANA ♥️🔥*
Na Maryam Naseer mirrah
*Ammey laylerh*


Page 4️⃣0️⃣


08104493215


✯D͟A͟Z͟Z͟L͟I͟N͟G͟ S͟✯T͟✯R͟'✯W͟R͟I͟T͟E͟R͟S͟
====================


Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/B5h5bUBTy1SDjMGoQs7Yb1




*IDAN nagama dakai zanbi ahalinka,ɗaya bayan ɗaya na sheƙesu! sannan na aure matarka uwar yaronka ayman, waɗanda na tabbata sune rayuwarka MALEEK!"*


Wata iriyar razanan niyar uwar tsawa maleek ya bugawa Kashim baba, daya nuna kanshi da bindiga,
Wani irin kallo maleek yabi Kashim baba dashi irin dube kan nan, sannan ya naɗe hannayensa a ƙirji ya fara magana cikin dakewa da rashin tsoro
*"KAREN BANA* maganin *ZOMON BANA* sa shiru hana ƙara Hayaƙi NOOOOOh, Inkaji ana ƙi gudu to sa gudu ne bai zoba"
Gaba ɗayansu sun razana da irin tsawar da maleek Ya musu, amma dake suma shegun kansu ne, hakan bai hana Isa tanbuwal ƙarasowa gaban maleek ɗin ba.
Cikin tacewa a rashin M Isa tanbuwal ɗin Ya fara magana " Kai yaro iya bakinka! Kasan su waye kaka bugama tsawa haka?, To kada ka manta Kashim baba shine mijin matarka bayan ka sheƙa duniyar da ba'a dawowa! Sannan gwamnatin da kake taƙama dasu, mune Nan gwamnatin ba kowa baaaaa!"


Maleek ne ya buga masa tsawar data sa ya riqe kansa, sannan ya damƙi gefin rigar saya fara jijjaga shi cikin ihu yace, "Su wa ye ku wanda ya wuce dabbobi! Azzalumai!! Maciya amanar ƙasa!!!, Duk wanda ya qara magana ba tare da izininaba! Na rantse saidai uwarsa ta haifi wani badai shiba."


Ya faɗi hakan yana cilla Isa tanbuwal da qasa,wanda kansa yaje ya bugu da jikin ginin ɗakin.


Ai kuwa duk loƙaci guda suka ja baya,ganin ran ƴan maza ya ɓaci a tsorace suka soma ja baya. Suna zare idanu jin irin uban worning ɗin daya gargaɗesu.

Cikin aro jarumta azama ranshi Kashim baba ya shiga tafa hannuwansa, "da kyau JARUMI Lallai jarumtarka ta daɗe tana burgeni. duk kuwa cewa kana sansani na kewaye da yarana, amma hakan baisa ka girgiza ba. Na gaishe ka UBAN AYMAN! To kasani a yau base GOBE ba Lahira zatayi babban baƙo, MAZA afara aiki"


Ya faɗi hakan yana sakin wani irin munafikin murmushi.


Aikuwa kankace me yaran nan suka yo kan maleek, hakan yasa maleek ja baya ya zama qafarsa, tare da jan wata uwar tunga. Nan sukayo kanshi haiqan da bindugu suka shiga fara harbawa maleek bindugu, aikuwa kankace me gurin ya turniƙe da qaran harsasai. Daidai Nan kuma ƙungiyar rundunar sojojin maleek suka kutso kansu cikin gidan. Aikuwa suma tu daga bakin qofa suka fara nasu aikin suma, kafin su kutso kansu cikin ɗakin Nan aka shiga fafatawa tsakanin yaransu Kashim baba, da rundunar sojojin.


Ganin yadda gaba ɗaya wurin ya turniƙe, kuma gashi sai zubar da yaransu akene. Yasa hankali Ibrahim nera tashi, hakan yasa ƙoƙarin fecewa daga cikin ɗakin.
Saidai bai sani ba yayi shuka a idon makwa domin kuwa maleek yana ankare dashi, kafin yayi woni yunƙuri kuma, maleek yaja rawanin daya naɗa ma kansa.
Tuni jikin Ibrahim nera ya fara mazari gudun abinda kake yazo, amma cikin dakewa yace " kanason wasa da rayuwar ka kenan?, Yaro ka tafi kabar Nan idan harba mutuwar wulaƙancin da yaronka zai yi kakeson gani ba. Kana Kasan Ni Ko waye! Kuma Kasan matsayi na na shugaban ƙasar ku".


Zuciyar maleek ce ta fara tafarfasa jin irin kalaman Ibrahim nera, wai ahakan ko kunyar kansa baiji ba yake ƙiran kansa shugaban ƙasa.


Ba tare daya iya control kansa ba, ya sanya hannu ya finciko shi ya haɗe sifes ɗin dake tsakanin su ta hanyar haɗe jikinsa dana Ibrahim nera, baiyi tsammani ba kawai sai ganinsa yayi a gaban maleek. Yana huci tamkar zaki.


"Me kace?, Kace kai shugaban ƙasa ne? Kai yanxun ko kunyar kanka bakaji ba dan Allah? ku sani ba kowanne hadarine yake ZUWA da ruwa ba.
Kuna buɗe asibiti a mazaunin kyauta wa al'umma! Bayan kuma abin ba haka yake ba. Kuna da woni naku tsarin na daban akan bayin Allahn da basu jiba, basu gani ba. Alhalin kun buɗe asibitocin ne kawai dan kuna auna jinin mutum! Idan yayi daidai da jinin da kuke nema sai ku zuƙema mutum jininsan. Daga qarshe sunan mutum min mattace! Ku kuma kunsa mi abinda kuke soooo Koooooo"


Ya faɗi maganar ƙarshen cikin hargowa da amsa kuwwa.


Shiru Ibrahim nera yayi cikin bugawar zuciya sai rarraba idanu yake, ganin duk yadda hankalin jama'ar wurin ya dawo kansu, Nan ya fara muzurai yana ƙafƙafta idanu, ya TSOHON maye.
Cikin tsananin azabar sukar da zuciyarsa take cikine, naƙin bashi dama akan ya harbe su kashim baba a hannunsa, da aka ƙi bashi damane yasa ya fara magana cikin wani irin ɗacin rai yace.


"Bani da loƙacin ɓata laƙacina zanyi biyayya wa shugabana, kawai wajen miƙaka hannunsa ba tare dana sheƙe kuba ku duka, amma da zarar naga abinda raina bai gama kwantamin da wasu abubuwan ba dole saina sheƙeku da hannuwanaaaaaa!" Ya faɗi hakan ne yana wani irin mutsutstsuke hannuwan nashi.


Murya ƙasa ƙasa Ibrahim nera yace " hattara dai yaro bari kaga ƙarɓin shugaban cina"
Hannun yasa ya ciro wayarsa tare da laluba wata NO wacce aka mata sifelin da VP, ya doka ƙiran numbern.
Yana jin an ɗaga numbern cikin zallar iya mugun makirci, ya shiga faɗin " Inason ashiryomin privete jet na musamman tare da masu tsaro, ina tsohon campany na dake sule ja 24 house"
Daga çen ɓangaren kuma mai girma Chief of army ne ya amshe zancen da cewa " Allah mr. President, za kuwa mu shirya hakan kamar yadda ka buƙata ɗin mr. President" ya ƙarasa faɗar hakan yana yanke wayar baki ɗaya.
Cikin woni irin tashin hankalin da ba'a sa masa rana, su kashim baba suke ja da baya. Domin duk abinda aka faɗa ɗin akan kunne su, hakan yasa 380 suka ranta ana kare, ganin kamar mushe zai juye da miji ya.
Nan take maleek ya take musu baya ganin suna ƙoƙarin tserewa ne yasa shi zaro guns ɗinsa , dake maƙale a aljihun wandonsa, Kashim baba ya fara harbi a gwiwa. Hakan yashi sakin wota irin azabar ƙara, nan ya shiga harbinsu gaba ɗaya saida maleek ya tabbatar yaga raunatasu.
Kana yawa sauran rundunar su ta sojojin dasu tattare masu raunin cikin su.
Wata baƙar mota ce Hilux tayi parking daidai wannan tsohon campanyn, wata dojuwar matace ta fito a cikin ta. Inda tun daga kan ƙafafunta har zuwa samanta, babu abinda ake gani gaba ɗaya kayan jikinta baƙaƙe ne, ga liƙaf data ɗora a saman fuskartan, hakan yasa kai tsaye ba zakace ga yanayin ta ba in ka ɗauke tsayi kawai da matar take da. Cikin taka tsantsan take tafiya wani abu saɓe a kafaɗart, wanda yayi kama da riƙon ɗaukar jariri, saida ta tabbatar babu komai kana ta sanwo kanta cikin tsohon campanyn taci gaba da tunkarar cikin gidan
Maleek dake tsugunne daga jikin wata baƙar mota ne ya saki wani irin murmushi, duk kuwa da halin da zuciyar take a ciki, hakan bai hana shi sakin murmushin ba,
Tazo daidai tsakiyar harabar wajen kawai babu zato babu tsammani, taga MALEEK TAUFIQ tsaye a gabanta yana tafa hannayensa tare da nuna ta da guns yana faɗin.


"YOUR UNDER ARREST my Mommah"


Hakan yasa ta sakin abinda yake riƙe a kafaɗartan, cikin wani irin salo maleek ya taro abin tare da rungumesa tsammm a ƙirjinsa.
Ita kuwa gaba ɗaya jikinta ne ya shiga mazari, tare da wani irin tsoro mai tsanani.
Cikin fusata maleek ya ɗago ya zubama matar idanunsa, wanda suka kaɗa sukayi jawur dasu, ya fara magana cikin azabar sukar zuciya abinda yake shirin faruwa koma yace ya farun.
"Ahar kullum ina takaicin lalacewar ƙasata! Yaushe zata gyaru? Yaushe sanji zai zo mana? Kowa ya juya bayansa kansa kawai ya sani! Yana tafiya a kife Ohhhh Allah!. Nayi baƙin ciki da takaicin yau ga ɗaya daga cikin ahali na da laifi dumu² andaɗe ana ruwa ƙasa tana tsotsewa, amma duk da haka baki ankara ba LUBNA!, Waima mene kike nema?".


"Kuɗi?, Mulki?, Duniya? Nasan dole acikin hakan kina da buƙatar ɗaya daga cikin su, koma dukka kike da buƙata ohooo! Matar mahaifin JARUMI SADAUKI MALEEK TAUFIQ tsamo tsamo acikin manyan gawurtattun masu lefukan Nan da aka kama, tana ɗaya daga cikin su!. Shine burinki? Shine alfaharinki ba?".


Gaba ɗaya jikin ta tamkar babu wani abu mai rai daya saura haka take jin kanta, yaushe? Yaushe?, Yaushe MALEEK yasan tana cikin ƙungiyar su Ibrahim nera? Taya kuma akayi yasan itace ta shigo wurin kai tsaye? Bayan kuma gaba ɗaya jikin ta a rufe yake, koda yatsarta ba'a iya gani.
Amma kai tsaye yace mata.


YOUR UNDER ARREST my Mommah. Shine kalmar daya girgiza DUNIYAR ta.
Hannayensa ya rataye a qirjisa tare da zuba mata runannun idanunsa, sannan yace


"Wannan haka yake amma kisa Ni domin sauƙaƙama wasu! Dole sai an takura ma wosunsu,sai kuma an sadaukar da wani abin ake samun wani, kamar dai haka!"


Ya faɗi hakan yana zaro onka ya kama hannayenta, ya zira mata onkar. Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da faɗin "uhummmm to da kyau JARUMI, amma ka sani kare da da yaga rawar kura cewa yayi da kyau. Ba lallai kasan koni wace ba!, Lalubene kawai acikin duhu kakeyi maleek! Baka da hujjar da zaka sa kotu tayi aiki a kaina.
Cikin wani irin salo maleek ya karyar da wuyansa gefe, tare da faɗin atafin hannayena kike komai Mommah, domin tundaga ranar dana gama sanin ke ko wacece, hakan yasa naci alwasai akanki Mommah, tun ranar da kika ɗauke min RAYUWA ta tun daga ranar nasan asalin ki! Sannan nasan wacece keeeee. Zanso ki hasaso ranar Mommah keda aminiyar haɗin ki Laura!. Dama! damammaki!! Rana! Ranaku!! Loƙaci da loƙuta duk a lissafe suke kuma tafiya suke cikin tsarin ubangiji sammai. Abu mafi haɗarin kuma nine jagoran tafiyar!, Wannan shi ake ƙira da ƙarangiya, kin haƙa ramin da zai rufta dake! Gurnanin zaki kaɗai yakan sa sauran namun su girgiza, ya hana su samun kwanciyar hankali. Hausawa sunyi gaskiya tabbas na yarda KAREN BANA shike maganin ZOMON BANA Mommah. Ya faɗi maganar daidai lokacin da su Jawad suka ƙara SO da sauran masu laifin.
A kuma daidai loƙacinne shel kwafta na sojojin 9j ya dira a tsakiyar babban filin campanyn, nan aka yi gaba dasu Ibrahim nera tare da sauran miyagun yaransu.
*****


ACEN GIDAN MALEEK kuwa.


Idan hankalinsu yayi dubu toya tashi, ummie dake tare da AYMAN suna kwance akan 3ster acikin parlour. Barci ya fara ɗaukar ta sama sama, ita kuwa jadderh tana cikin bedroom ɗin ta tana barci itama.
Ƙawai sai farkawa sukayi sukaga babu ayman babu dalilin sa, da ummie tasha tana barcinne yayi kuka bata ji ba, shine uwarsa ta fito ta ɗaukesa, sai kuma da taga shiru shiru ko motsin jadderh batajine yasa jikinta bata kamar ba ƙalauba.
Hakan yasa ta nufi bedroom ɗin jadderhn, amma me zata ga sai taga wayam babu alamar jariri a tare da jadderhn, hakan yasa ta shiga tashinta koda ta tashin take kuma tambayar ina kuwa AYMAN. Tace mata ai yana wurinta Nan fa hankalisu idan yayi dubu toya tashin jin baya gurin kowanne acikin su, ai kuwa jadderhnku ta taqarqare ta zunduma uban ihun daya ɗau hankalin uban jami'an da maleek ya zuba. A 370 suka shigo cikin parlourn gidan ganin matar ogansu ta dage sai uban kuka take hakan suma ya tashi hankalin su kwarai da gaske. Jin anshigo har cikin gidan an kuma ɗauke AYMAN wanda su kansu haidane yaron shine DUNIYAR ogansu maleek, ai kuwa Nan kowa ya shiga tashin hankali marar iyaka a cikin su, wasunsu harda masu fara hawayen tausayin kansu da kansu.
Cikin tashin hankali marar qarewa ummie ta qira ammey take faɗa mata wannan tashin hankali da suke ciki, ai kuwa itama idan hankalinta yayi million dollars toya tashi, cikin qanqanin loƙaci sai gata a gidan maleek ɗin.


Abinda zaifi baka dariya da tausayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login