Showing 54001 words to 57000 words out of 72176 words
Chapter 19 - KAREN BANA complete by ammey laylerh .txt
 Allah harta koma sai kuka kawai take.
A 36 maleek ya saɓeta a kafaɗarsa yayi cikin mota da ita, ammey ce tayi saurin biyo bayansu itama ta shige cikin motar.
Cikin ƙanƙanin loƙaci maleek ya isa asibiti mafi kusa privete me kyau da tsada inda dama Anan ne jaddan take xuwa awon ta.
 Nurse INDO ADO Mai UNGUWA ce ta amshi haihuwarta emagerncy room tayi da ita, ganin wanda ke tare da ita  sananne ne a kasar ma baki ɗaya, hakan yasa ita da sauran nurse  suka amsheta jiki har mazari yaje, cikin gaggawa suka sóma bata dukkan wani taimakon da suka san zasu iya mata.
Haka aka dinga fama su MALEEK sun kasa tsaye sun kasa zaune, gashi ance musu haihuwar da saura.
Hakan yasa maleek yake ganin kamar ko basu iya aikinsu da ƙyau bane, daƙar ammey ta lallashehi ya barta cikin asibitin, haka jaddah taci gaba da kanta wani irin tukuƙin bala'i ne idan ya faro daga tafin qafarta saiyazo daidai mararta zai cakeee Anan, aikuwa idan ta soma wani irin murɗaɗɗawa da surutan da itama kanta batasan mene take faɗa ba, idan kuma ya lafa mata CENN xuwa jimawa wannan turnuƙun zai kuma dawo mata, gashi ana ta fama amma har wajajen sha biyun dare shiru babu haihuwa babu dalilin ta, hakan yasa jaddah sarewa******
Har take ga kamar itace ba zata iya haihuwar da kanta ba, hakan yasa cikin kuka ta shiga roƙar nurse INDO ADO ɗin dake tsaye akan, akan kawai su taimaka su mata tiyata, nan suka shiga bata baki suma suna qara kwantar mata da hankali, suna faɗin ta kusa saura qiris...
wajajen qarfe ɗaya da rabi loqacin duka nurse basa wurinta sai iya INDO ADO ceeee itama barci ɓarawo ya soma kwasarta hakan yasa jaddah kuwa tayi wuff ta diro a gadon nan, ta saɗaɗo ga azabar ciwon mara da ciki amma haka ya fito wurin da ammey ke zaune, tana zuwa ta zube tana kuka tana faɗin "ammey nasan baxan iya haihuwar nan da kaina ba pls acenzan asibiti muje Amin CS  kawai na huta, ana haka  nurse INDO ADO ta ƙaraso wajen, bayan ta farka bata ganta bane, hakan yasata fitowa wajensu a guje, ta  kuma meda jaddah.
shi kuwa maleek bama ya wurin yana a cikin motarsa ya ɗauka tasbaha yana faman yima Annabi salati, kan Allah ya saukaƙama wannan baiwar Allah tashi.
Wajen ƙarfe uku da mintuna arba'in, naƙuda gadan gadan ta kuma tasar ma jaddah, haka suka shiga fafatawa a  filin yaƙin mata, cen tace ma nurse INDO ADO ɗin zatayi kashi, inda dama akwai wani qaton foo na musamman domin irin haka nan akace ta sauƙo tazo tahau, haka ta ƙaraci nishinta amma ko ƙyamass ta gaza yin kashin Nan.
Tana komawa gadon kuwa nurse INDO ADO mai unguwa  zira hannu, sai kawai ta ji kai ya taho, hakan yasa tace ta ware ƙafafunta ga kai nan tahowa, Nan tasa ta fara nishi, tun tanayi da qarfinta har qarfin nata ya kusan qarewa, qiran sallar farko tare da dirowar santaleken  baby boy  ɗin nan ya faɗo duniya, Nan kuwa baby ya  zankata ma su ammey qiran salla na biyu,  nan ta yanke cibiya tare da gyara babyn da uwar babyn, badai raki ba Dan wurin yasar jini ma ansha daru, inda wata nurse INDO ADO  ta fara mata, tayi sau uku tace ya isa.
Nan kuwa wata gabjejiyar nurse ɗin tace ta bari ta qara mata koda so biyu ne, ai kuwa jaddah tana kyalla id0 ta hango hannuwan wannan nurse yayi biyun na nurse INDO ADO...
nan kuwa tace bal bata san zance ba,. Haka nurse INDO ADO da ƙyar ta qarisa mata yasar jinin.
Tsabar farin ciki kuwa ammey harda hawayenta, shi kuwa oga maleek sujjada yawa subhanahu wata'ala, wanda ya bashi wannan farin cikin da yasan duk duniya in za'a hadesu babu mai iya bashi, aikuwa ana kammala kimtsa masu jego yayi wuff, ya shige ɗakin yana xuwa baibi takan mutanen cikin ɗakin ba ya haɗe babyn da maman babyn ya rungume su tsammm acikin ƙirjinsa, ya kuma ƙi cikasu ganin rashin kunyar na neman yawane yasa ammey korar shi daga cikin ɗakin.
Nan yashiga ɗaukar babynsa zafafan pics a wayarsa qirar samfurin samsum galaxxy 8 4100.
Kafin kace me har wannan haihuwa ta gama zagaye dangi da ma social media, Inda har mutanen Adamawa Kano sun gama bayyanuwa suma acikin asibitin.
Kasan cewar a jirgine suka zooo su duka inda harda su Malam Abdullahi da ummey.
Nan jaddah aka sami abinda akeso ta maƙalƙale ummey ta hanata koda ganin ɗan be wanda ubansa harya riga ya masa huɗu ba, saidai babu wanda yasan sunan wayene ya masa huɗu bar dashi.
Gaba ɗaya faɗin irin farin cikin da wannan ahali suke ciki faɗa loƙacine, inda kowa ƙoƙarin ganin ya faran tama jaddah rai yake, nan aka basu sallama suka ɗun guma gidan Maleek kai tsaye suka nufa, inda suka yanke shawaran ummey ne zata zauna da ita zaman wanka har arba'in.
Ai kuwa ummey taji daɗin wannan abu da suka mata, domin sun nuna mata har yanxun matsayin ta yana Nan a wurin jaddah na uwa, malam Abdullahi ma yayi murna da hakan.
*********
    Mutane MADINAH ma sun qira video call, inda suka ga santalelen babyn  nasu mai kama da maleek sakk babu abinda ya bari nashi, saima kusan kereshi da yayi wajen hasken fata da kuma ƙyau, duba da cewar uwarsa ba cikakkar Hausa bace  half cast ce ruwa biyuce, hakan yasa babyn ya zarta mahaifinsa a komai da komai.....
Kwana biyu a tsakani mutanen MADINAH suka dira tare da uban kayan barka saukace hauka, aikuwa zokaga yadda ake ruwan kayan barka, ga uban shimilin kayan akwatunan da maleek ya musu ita da babyn, banda wanɗanda suka dinga saya suna ajjewa.
Kai wannan baby yazo duniya a sa'a.
A kuma babbar rana sarki ABDULPHATA OMAR, sarki MALEEK IBN SUFFYAN ma haka suka kawo nasu kayan barkar, inda abinda sarki ABDULPHATA OMAR ya kawo gurgiza zukata da yawa domin jirgin sama guda yaba jikan nasa yace shine jika na farko kuma mafi soyuwa daga ɓangaren matarsa Hajiya maryam abduljalaal yeko,shi  sarki maleek ibn suffyan shima ƙyautar da yawa babyn ta girgiza zukata, inda maleek ne da kansa ya garga ɗeni da kada na gayawa FAN'S abinda ya bashi.
Mai girma maleek kuwa ya bawa NURSE INDO ADO MAI UNGUWA kujerar maka tare da wasu maƙudan kuɗaɗen dani kaina AMMEY LAYLERH bansa nawa bane.
___________
   
Mom sani ita ce mace ta farko acikin FAN'S na KAREN BANA ta tazo wa jaddah barka, tana zama saiga bloody AYSHANTY tazo kamar anjefota, tana muzurai wai danme mom SANI ta gudo ta barta.
Shi kuwa maleek yana daga gefe sai faman murmushi yake musu domin yasan akan meyene suke hakan.
Cen kuma ƙofa ta fara buɗe wa inda OUM SHAHEED, tare da maman Inaya suka diro suma cen saiga masoyiya ✨ Asmitar hydar tare da Aunty Reema suma sun zo barka, a ahhh saiga su teemah shalelen Abba sun bayyana suma.
Ai kuwa nan FAN'S of KAREN BANA suma ƙofa ta buɗe musu💃
Gaba ɗaya KAREN BANA FAN'S groups ne suka zo atare, inda SAPWAN AHMED ya raɓe a bakin ƙofa yana jiran umarni daga MALEEK akan ya masa is0, aikuwa saiga maleek ya taho tare da rungume SAPWAN AHMED, dan shifa maleek baya da tsayayyen abokin daya wuce  JAWAD., Gashi JAWAD baya ma qasar hakan yasa yakes0n su raba farin cikin tare da SAPWAN AHMED🥰.
Aikuwa zokaga  murna wajen SAPWAN ganin loƙaci ɗaya ya samu shiga a wurin maleek ɗinnnnn...
Hajiya LUBNA
Idan tace zata yi kuka to kuwa tayi qarya domin ta gwada yin kukan, yafi cikin carbi amma ya gaza zuwar mata, hakan yasa cennnnn ƙasan zuciyarta ya kuma kaikasgewa da bushewa.
Inda ta kuma ɗana uban Target ɗin dayafi nada tsanani, 
HAJIYA LAURA 
Loƙacin dataji cewar jaddah ta haihu, ji tayi kamar ta mutu dan baƙin ciki, Ashe bataji komai bama lokacin dataji cewar Sarki ABDULPHATA OMAR jirgin sama guda ya mallakawa ɗan gidan kishiyarta shi kuma ƴarsa ɗan kuma jikansa, jika na farko a wurin sa ai saida takaita ga faduwa ƙasa warwass...
Ahalin malam Abdullahi Rano ma sunyi masa kara wajen zuwa barkar samun qaruwar da sukayi.
*🔥♥️KAREN BANA ♥️🔥*
Na Maryam Naseer mirrah
*Ammey laylerh*
Page 38&39
08104493215
✯D͟A͟Z͟Z͟L͟I͟N͟G͟ S͟✯T͟✯R͟'✯W͟R͟I͟T͟E͟R͟S͟
==================================
________________________
FRIEND kuwa faɗin irin uban kayan data saima babyn  ɓata  baki ne.
Zo kuga yacce jadderh take samun kaya ita da babyn nata, oga maleek kuwa hamm ba'a magana, gaba ɗaya yabi ya kanainaye babyn da maman babyn! Wanda saidai ammey tayi da gaske kana ya shiga taitayinsa, dan da kammm ma hana ɗaukar babyn nashi yayi.
Abbie ma campanynsa na sarrafa auduga sukutum ya  mallaka wa babyn.
        Bayan kwana biyu
Wanda ya kama saura kwana uku suna kenan, duk ƴan uwa na kusa dana nesa kowa yazo ganin wannan babyn mai farin jini, kuma ɗan gatan dangi.
      Ai kuwa gida ya cika ba'a magana su aunty sumayya da aunty yusrah ma duk sunzo Kasan cewar suna manya kuma ba'a nan suke da aure ba!
Ita sumayya tana aure a Lagos yayinda yusrah take da aure a London ƴaƴan Hajiya lubna kenan.
     Tare da aunty hauwa'u  itace babba a ɗakinsu na Hajiya talatu nera tana aure a Kaduna.
Amma fa tun kamin suzo tuni sunga hotunan babyn da maleek ya tuttura musu, wasu kuma suka gani a status nashi da sauran yaran gidan.
       Barin ma auta Zahra  da taci wayanta da hotunan baby, kowa ya gani dole ya yaba.
Pan's ma hotuna duk sunzo muku na sani😄🤣🫰🏻
Ammey kamm tayi ƙememe a ɗakin ta hana maleek sakewa, dan tunda jadderh ta haihu bata taɓa bari sun ƙeɓe da juna ba, 
Masha Allah baby dai kam yayi goshi , kayan Barka ba'a magana aunty sumayya da nata aunty  yusrah da nata, aunty hauwa'u da nata!*****
A babban masallacin dake ƙofar gidan Alhaji taufiq aka raɗa suna, inda aka sanya ma babyn sunan malam Abdullahi.
Aikuwa zo kaga murna wurin wannan bawan Allah, kowa yayi murna da wannan kara da maleek yawa malam Abdullahin! Faɗin tarin farin cikin da suke a ciki ɓata loƙacine.
              Saniya guda aka yanke ranar sunan Abbie kuma ya ɗakko ƙaton rago daga gidan gonarsa irin wanda ake masa kiwo a ƙauye, shima aka yanke, kai gata dai iya gata wannan yaro ya samu inda yanke Za'a na qiran babyn da AYMAN wajen karantawa malam Abdullahin.
  Daga nan aka fara shagalin suna inda suka shirya ƙwarya²walima iya cikin gidan nasu!
Ai kuwa Ranar suna saiga babbar ƙawa kuma ƴar ɗaya tilo Basma Ibrahim ɗin jadderh, ai kuwa kamar suyi hauka bare an daɗi ba'a haɗuba.
{Nasan masu karatu masu manta Basma Ibrahim ba! Ƙawa ɗaya taki da jadderh take da}
5:0pm na yamma su mom Sani dasu  bloody Ashanty su Reema, Oum shaheed, Sis bilkisu AUTARMU, maman inaya, Asmeetar hydar  cutie sumy suka shirya tasu gagarumar walimar suma!.
nima nida ƴan KAREN BANA Pan's muka shirya tamu ƙwarya²walimar muma, muka ce ba za'a barmu a baya ba eheeeeeee,  ai kuwa Pan's sunsha casu.
Irinsu Fatima Aliyu , qanwan taeba maman taeba, fatima lawan60
Maryam Yahaya, samira Eli, Indo Ado, M Y M, maman hannat, Iclass hhhh tsabar rawa saida maleek ya fito ya kashe musu djn, dan yaga basa da alaman dakatawa🥰😄.
    Alhamdulillah suna yayi suna su MALEEK da AYUSH sunsha ƙyau photographer kammmm sunsha ɗaukar pics nasu ba iyaka, inda photographer ɗin ta kasance UMMI MUHD {maman humairatu}
Aikuwa kowa jikinsa ya faɗa masa, sabo da gajiya, ita kanta me jegon a gajiyan take.
***********
Bayan kwana biyu kuma kowa ya kama gabansa, sai iya ummie, kai kace gidan bai taɓa tara kowa ba!
 Haka suka ci gaba da wanka inda ake ma AYUSH tsabtataccen wanka, mai tafe da gyaran jikinta, ummie kamm tace ƙara ta gyara ƴar nata ciki da bai, dan taga da dukkan alamu babu ɗaga ƙafa daga gare maleek ɗin.
Wannan dalili yasa ta baje dukkan wani sirri na gyara domin ta kankaroma da ƴar nata mutuncinta da kuma daraja haɗi da kima, dama kuma su Adda nimra sun basu wasu nau'ikan gyaran na musamman****
      Daga gefe guda ma ga ammey itama tana basu nata gudunmawar,  sosae....
           ^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^
Cikin ƙasaitacciyar takunsa irin ta jarumta yake shiga cikin gidan  nasu, ɓangaren mahaifiyarsa yake nufa kai tsaye,dan dubo lafiyar ta.
Zaune ya sameta kan rug tana riƙe da rabbana arba'in, tsananin farin ciki ne ya ziyar cesa shi yasa ahar kullum yake alfahari da mahaifansa, yake kuma qara godema Allah da yayosu acikin addinin Islama, duk sanda zaka ganta indai bata kitchen, to kuwa zaka sameta da littafin addaoi, ko kuma Alqur'ani mai girma tare da ita.
Zama yayi taga gefen da take zaune, littafin ta ajje gefe haɗi da faɗin "Babana lafiya kuwa?" Kansa ya ɗan shafa wanda hakan ya kusan zame masa ɗabiarsa "yunwaaa" ya faɗi maganar a shagwaɓe Tamkar wani jariri***
Kai kawai ammey ta girgiza tana tashi ta nufi kitchen, ita kanta wani sain lamarin yaron nata mamaki yake bata. 
Lafiyaiyen tuwan ɗanyar shinkafar da tayi miyar kuɓiya ta zubo masa, tare da haɗo masa da kunun gyadar nashi na gado, cikin jin yunwar dake damunsa ya shiga cin abincin, saida yaji ya qoshi kana ya ture kwanan a gabansa, tare da yin hamdala bayan yasha kunun gyadar san.
Sai wajajen qarɓe 9:pm ya nufi gida! Aloƙacin har ummie ta riga tayi barci, hakan yasa maleek yaji wani sahihin farin ciki ya kama shi, ganin ummie tayi barci, yau zai samu ya keɓe da matarsa, tsawon 3weeks kenan amma kullum tana tsare  ummie ta kasa ta tsare.
Cikin tafiyar nan ta ƙasaita haɗi da jin kaiii yake nufar ɗakin jadderhn, ahankali ya tura ƙofar bedroom nata.
Tsaye take a gaban clothes tana ɗaure da towel fari ƙalll da shi  naiman riga mai ɗan kauri, Kasan cewar yau garin  ana ɗan busa sanyi, daga inda yake tsayen ya zube hannayensu cikin aljihun rigarsa, tare da zuba mata mayatattun idanunsa, wanda suka fara tara ruwa acikin su sukayi haske sosai tamkar ruwa ne kwance acikinsu. Sai kuma ya shiga takawa, daidai loƙacin data ciro wata riga da wando masu kauri!, Daidai loƙacin maleek ya qariso kusanta babu zato babu tsammani, kawai tajita jikin mutum ƙamshinsa daya ziyarci hancinta, shine abinda yasa bata tsorata ba.
Tsammm ya rungumeta cikin jikinsa tare da ɗaura kansa cikin wuyanta, inda yake shaƙar wani daddaɗan ƙamshin tularen out jg mai azabar daɗi.
Ahankali ya tallafi kanta tare da fara yawo da kansa cikin dokin wuyanta, cikin wani irin yana jadda ta juyo gaba ɗayanta tare da faɗawa cikin faffaɗan chest nashi, ahankali yake lalubar bakinta! Tare da faɗin "babe I missed you, with missing you there is no limit" cikin dakewa da kuma kama kanta, ta ɗan zame daka jikinsa tare da juya mar baya, cikin taku ɗaya biyu ya ƙara juyo da ita tare da cewa.
"Do you not miss your husband?" Sai kuma ya haɗe bakinsu wuri guda tare da bata wani irin Italian kisses.
Nn jadda ta shiga ja da baya maleek na biye da ita har takai daidai bakin gadon ta, hannuwansa yasa ya sarƙo waist nata tare shigar ta ita jikinsa sosae yana sauƙe ajiyar zuciya.
"I love you my life" love u too My world" cikin sautin da yayi ƙasa sosai ta furta masa hakan, tare da rumtse idanunta jin wani lafiyayyan kissing nata da yayi daidai🥰
Ummie ce ta farka daga barcin daya ɗan ɗauke ta jin kukan ayman daya farka.
Ɗaukar shi tayi bayan ta ɗan jijjigeshi ganin yaƙi yayi shirune yasa ta nufi ɗakin jadderhn, jin qofar a garƙame ne kuma  yasa tajan burki, tare da knocking na qofar jin qamar ana taɓa qofane yasa jadderh saurin janyewa daga cikin jikin maleek ɗin tare da faɗin "na shiga uku ummie" ƙoƙarin qara riƙota maleek yake hakan yasa ta dira daga kan gadon ba shiri tana faɗawa toilet a guje. Maleek miƙewa yayi tare da ɗan gyagygyara kayan jikinsa yana nufar bakin qofar, kai a ƙasa.
Buɗewa yayi hakan yasa ummie sanyo kanta cikin ɗakin  tare dabin kan gadon da duk ya harmutse, maleek kuwa yayi wuff ya fice a ɗakin baki ɗaya.
Cikin ɗaga murYa tace "saiki fito idan kin gama wankan tsarkin aiiiii......hakan yasa jadderh dake toilet a ɓoye fitowa babu shiri  tana faɗin "Wallahi babu abinda nayi ni ummie" da harara ummein ta bita " idan kuma kina son ɗaukar wani cikin kusa ne bisimillah, tunda ku yaran zamanine ba'a iya muku" ai kuwa nan jadderh ta shiga kuka da shushshura qafa itafa ummie ba haka tace mata ba aiiiiiiii.
**********************
Maleek zaune a cikin wangamemen office nashi, sai faman aiki yake da dukkan alamu typing ne ake yi dan ganan sai faman latsa system nashi yake cikin sauri, kirrrrrrr wayar sa ta ɗauki kukan agaji, janyo wayar yayi ganin numbern dake qiran nasa ne kuma yasaka shi sakin wani murmushi
hakan yasa  babu ɓata loƙaci yayi answering call ɗin, tare dasa wayan a amsa kuwwa.
Daga cennn ɓangaren yaji ance 
"wannan shine qira na ashirin da biyar kenan da muke yi maka, cikin dukka layukanka amma switch off nakejin hakan! Fatan ba kayi hakan bane don ƙauracema qiraye qiraye daga wurinmu"
Baya da  buƙatar tambaya  mai ƙiran don yasan kosu waye
"Baka da ƙima  da darajar da zaka sanya na rufe layukana, ka faɗi dalilin ƙiran"
Dariya yayi daga cen ɓangaren kana  yace
"Kana kasheni da jarumtarka MALEEK, amma ka sani wannan shine kasheɗi na ƙarshe da zamu maka, ka janye  dukkan ƙudirorinka akanmu na ganin lalle sai ka kawo qarshen mu! Idan kaƙi ji kuma to kuwa lalle akwai saurin kuka, a gabanka maleek kukan jini bana ruwa yarooooo"
Maleek bai san loƙacin daya sheƙe da wata uwar dariya ba, kana ya shiga tafa hannayensa,  sannan yace.
"Da dukkan alamu harkun tsorata kenan? Qarya kuke yi Atiku  ina mai tabbatar muku wannan karon, kune za kuyi kukan zuciya da idaniya, saina mayar daku abin kwatance a Nijeriya! Harda









