Showing 24001 words to 27000 words out of 72176 words
Chapter 9 - KAREN BANA complete by ammey laylerh .txt
 ɗin ƙofar nata tayi tare da mirza ma ƙofar key tana barin key ɗin ajiki, ahankali tashi ga cin abincin ta cikin kwanciyar hankali 
Bayan ta kammala kuma taje toilet tayi brush, saman lafiyayyan gadon ta tafaɗa tayi konciyarta...
*MALEEK*
koda yadawo bai ganta aɗakin ba shoulder ɗinsa yaɗaga alamun baida meshi ba,jallabiyan jikinsa ya zare dare da komawa saman gadon yayi konciyarta  
11 dot yatashi toilet ya shige aƙalla yaɗauka sama da 30 minute bai fito ba,  kana ya fito yashirya kansa cikin  kakansa sky blue denim jacket ya ɗaura saman kakin nasa, kai tsaye wajen shoesrug ɗinsa dake cike da takalma kala kala ya nufa wani haɗaɗɗan white sneakers shoe ya ciro haɗe da sanyawa aƙafarsa,  cikin falon yanufa kai tsaye dining table yanufa ganin an shirya abincin kamar koda yaushe,......Zama yayi yafara ɗiban gara kamar yadda ya saba  har wani kumshe  blue eyes ɗin da yakeyi tsabar abinda yake i nayi mishi daɗi......Still haka yaci gaba da cin abincin sa aƙalla yakusa  ɗaukan 15 yana ƙaryawa!¡!
*Kashim baba*
After like 30 minutes haka suka shirya meeting ɗin gaggawa cikin wani haɗaɗɗan building mai haɗe da wani ƙaton hall acikinsa , coutions ne acikin sa na alfarma wanda hall ɗin yaji kayan more rayuwa, ko ina stainding A/C ne manner a wurin sai sanyayyar ƙamari da kuma fitar numfarfashin jama'ar da wurin ya tara ne ke tashi  
meeting sukayi me sunan meeting  Dan har wajajen sha ɗaya rana sunanta daman kulli da warwara, ahaka har suka sami mafita kana kowa ya kama gabansa.
Relaxing Hajiya kubba tayi akan bed tana juya maganganun da sukayi da  ita da aminiyarta    
Yazama dole  awannan karon nufi to a ainihin  mu lubna domin naga wankin hula na naiman kaimu dare, konace yana naiman kaimu domin Ni tun tuni nadaɗe da gamawa da abu ɗaya saura ɗaya 
Ke kuwa fa? har yanxun ki kasa cimma burinki lubna  gashi abin da muke gudun harya faru anyima MALEEK AURE !  Kuma kinriga da kinsan idan har MALEEK yakusanci matar sa ƙamari na iya far 
Hyyyyyyyy hakan ma ba zai taɓa faruwa ba   taya ya ma zanbar hakan tafaru tafaɗa cikin ƙara ji tana dafe kanta da hannuwanta duka biyun, wanda  takejin tamkar zai rabe gida biyu
*MALEEK*
Kuyi manage da wannan insha Allah xuwa safe zaku sami ƙyaƙƙyawan typing 
Takuce dai ammeyn laylerh ceeeeee
Good NIGHT masoya 💔
My  MOMMEI  Naaaaaaa help me pls basai nafaɗa ba Dan Allah 💅🏻✨
More comments More typing
Eheeeeeeee 
Byyyyyyyyy*🔥❤️KAREN BANA❤️🔥*
NA MARYAM NASEER MIRRAH✨
*Ammey laylerh*
FREE BOOK
Page 2️⃣1️⃣
081-04-49-32-15
*Dedicated to Mommie Naaaaaaa abar  al'fahari Naaaaaaa*
____________-Ke kuwa fa? Har yanxun kinkasa cimma burinki Lubna, gashi abinda muke gudun harya faru anyima MALEEK aure!  Shin taya ta ya ya? Zaki hana tabbatuwar wani al'amari; idan har MALEEK yakusanci  matar da aka AURA mishi  tamkar,
 hyyyyyyyyy bazai taɓa yiyuwa bama  tafaɗa hakan cikin ƙara ji wallahi yayi kaɗan bazan taɓa barin hakan ma tafaru baaaaaa LAURAAA , tafa ɗi hakan tana dafe kanta hannuwanta duka biyun domin jin tamkar  zai rabe mata gida biyu,.....
*NIGHT*
Cikin kasala yake murza steering  motar nashi domin ya gaji sosae, ya daɗe baiyi aiki irin nayau ba, 
goma da rabi dot yakutso   hancin motar nashi cikin tsakiyar compound ɗin gidan, get man ɗinsu haɗe da sauran guard sara mishi , kota kansu baibi ba ya kutsa kansa xuwa nashi ɓangaren domin baijin zai iya biyawa ta ɓangaren su ammeyn shi su gaisa  hakan yasa kai tsaye yanufa ɓangaren su....
Cikin wani irin yanayi marar misaltuwa yasa hannu ya  murza handle ɗin ƙofar nasu, 
Ahankali ya maida ƙofar bedroom ɗin ya rufe tare da juyawa ya sauƙe idanunsa akan JADDERH wanda take kwance cikin wasu haɗaɗɗan riga da wando na barci dogaye masu santsi..
gashin kanta wanda ya baje akan fillown yabi da kallo, wata iriyar ajiyar zuciya me ƙarfi yasauƙe tare da ɗan jingina bayansa ajikin ƙofa,...Idanu ya zuba mata yayin da aransa yake jin wani irin matsanancin S0 da kuma shauƙinta na ɗibarsa, ɗan numfasawa yayi ahankali tare da karasowa cikin ɗakin.....
Rashin sanin cewa jaddan barci take yine yasa ya ƙira sunanta cikin wata sassanyar murya, ganin shiru bata motsa bane yasa shi zama abakin gadon ahankali ya ɗan ranƙwafa tare dasa hannunsa ya bude mayafin data rufe fuskarta dashi...tozalin da yayi da ƙyaƙkyawar innocent face ɗinta wanda ke ɗauke da busassu hawaye ne yasa shi sauƙe ajiyar zuciya tare da sakin wani murmushi me ɗauke da ma'anoni daban daban...
Ahankali yakai hannunsa ya shafi gefen fuskanta cikin cikin Muryar sa da tayi ƙasa sosae yace "baby doll" rigima ko yaushe cikin kuka, MALEEK kuwa ganin barcin nata yayi nisa ne yasa ahankali ya kama kafaɗunta tare da ɗan juyo da ita ya zaman suna fuskantar juna..idanunsa suka sauƙe akan ƙirjinta wanda ƙusan rabin breast ɗin ta suka bayyana ta saman rigar dake jikinta sanadin santsin da rigar keda, take kuwa yaji tsiƙar jikinsa ya wani irin zuba yayinda tashin farko yaji wani irin abu na yawo aduka sassan jikin sa, domin wannan shine karon farko daya fara ganinta ahakan, ahankali yasaka hannuwansa yaɗan rungumota sauƙan lallausan fatar jikin ta akan nasa jikinne yayi sanadiyar miƙewar tsiƙar jikinsa, take yaji ƙofofin sadarwa da tunanin sa sun tsaya, yayinda taushi da kuma laushin jikinta suka birkita tunani da lissafin sa loƙaci ɗaya, suka kuma sauƙar masa da nannauyar kasala, idanunsa da suka ɗan soma marairaicewa ya zubawa ƙyakƙyawar fuskarta wacce tayi smooth take kuma shining ɗin kyau, gyara kwanciyar sa yayi tare da ɗan ware idanunsa wanda ya sauya daga normal zuwa sexy emotion.... Tamkar kuma wanda aka zabura yayi saurin miƙewa tsaye yana barin ɗakin baki ɗaya..
Cikin tafiyar sassarfa yaka hanyar barin ɗakin nata domin dama baisan abinda ya shigo dashi ba,  "ya rabb" yafaɗa cennnn ƙasan zuciyarsa yanajin tamkar ahana ƙara hura wutar abinda ake ji akansa da tunanin sa, haka yaɗaura ya kama ƙofar falonsa yana faɗawa ciki kai tsaye asalin cikin ɗakin nasa yanufa, yana xuwa baiyi wata wata ba ya faɗa saman lafiyayyan gadon shi  tare da ambaton sunayen Allah kozai samu abinda yake ji ɗin yaɗan ragu, cikin iko na ubangiji kuwa sai gashi yaji dama dama ahanzarce kuwa fa tashi yana faɗa toilet, ruwan shower mai tsananin sanyi yasa karma kansa....wata kakkarar bathrobe ɗin dake gefen sa ya sanya ajikinsa batare kuma daya tsaya ruwan dake ɗiga daga saman kansa xuwa jikinsa ba yayi ficewarsa hakan, pyjamas na barci masu santsi yasanya yayi kwanciyar sa da ƙar barci barawo yayi nasarar sace shi bayan yaɗauka dogon loƙaci yana fama da kansa ......
*JADDERH*
Ƙiran sallar farko ta asbashi ta farka tare da danjin sauyin yanayi tattare da ita sai kuma taga gadon duk yayi squezing  ɗan murmushi kawai tayi, domin ta lura a ƴan kwanakin nan mutumin nata naɗan rage zafi da ita, saidai ko afuska bazata taɓa gangancin barinsa yagane tana sane baaaaa 
"No one like you ya MALEEK"
 
"Saboda komai naka na daban ne sannan kuma babu wani irinka" 
Still wani murmushin ta kuma saki domin tuna wani moment din daya kasa barin brain ɗin ta moment ne mai matuƙar daɗi agareta wanda zataso maimaituwarsa akoda yaushe...
Sai dai tuna azahirin abun kuma kuma  abin ba haka yake ba yasata kimtse kakyakkawar fuskanta  dana jin wani irin abu na ƙoƙarin taso mata mai kama dajin haushi, ahankali kuma tazuro ƙafafunta  tana miƙewa kai tsaye toilet ta wuce tana dauro alwula 
*Ohh my God dan Allah 👏🏻 kumin afwa wllh bana da ishashshen chajine yanzun haka 3 parcen ke gareni amma muhaɗe xuwa dare insha Allah*
*Wannan alƙawarin MIRRAH ✨ neeeeee*
Byyyyyyyy*🔥💔KAREN BANA💔🔥*
 NA MARYAM NASEER MIRRAH✨
*Ammey laylerh*
Page 2️⃣2️⃣
081-04-49-32-15
*DEDICATED TO INDO ADO, MAI UNGUWA🫂🫶🏻*
*JUMA'AT MUBARAQ IN ADVANCE 🫶🏻*
_______Kai tsaye toilet ta wuce tana ɗauro alwula, bayan ta idar da sallan saman gadonta da faɗa tana ta sakin wani irin murmushi da ita kaɗai tasan ma'anarsa, still haryanzun murmushin ne kwance saman kyakkyawar innocent face ɗin ta, ko mai ta tuna ta wani ƙanƙame jikin ta wuri guda tana sakin wata kyakkyawar ajiyar zuciya, idanunta da suke akulle gammm ta buɗe wanda cikinsu suka tara wani irin ruwa ruwan  masu hasken gaske,  "bansan miye nakeji agame dakai ba *YA MALEEK*"
"Amma ko mene nakeji haka! na tabbata wani babban al'amari ne mai girman gaske"
Tayi maganar sounding s0 very commond, relaxing tayi akan gadon nata tana ta saƙa da warwara, ahaka har wani wahalallen barci yayi awon gaba da ita sai faman ajiyar zuciya take saki cikin barcin nata......
Awalce yake ware manyan idanunsa wanda suka  sanja kala daga  farare zuwa jajaye, cikin son kawar da duk wani tunani nata da kuma abinda yake ji dangane da ita ya yunƙura cikin karfin hali yatashi zaune  yana dafe kansa da yakejin yamasa wani irin nauyi, akasalance za zuro sawayensa zuwa ƙasa ahankali yake takawa zuwa cikin toilet ɗin nasa  wanka yayi haɗi da  ɗauro alwula yana ficewa a falon nasa, masallacin dake manne da ƙofar gidan nasu ya nufa, shine bai dawo ba sai wajajen ƙarfe tara da rabi na safe  kasancewar yau weekend ce ranan hutu, 
ɓangaren ammeynsa yanufa kai tsaye tare da tura ƙofar palon nata ahankali yasanwo kansa ciki tare da sallama' a bakinsa,....ammey dake cikin kitchen tana shirya breakfast ce ta amsa shalelen yaron nata tana fitowa a kitchen ɗin hannunta riƙe da ɗan madaidaicin kofi sai faman tururi yake, cikin fara'a take amsa gaisuwar yaron nata, tana miƙa mishi kofin dake riƙe a hannunta
Wani lafiyayyan kunun gyaɗa na markaɗaɗɗiyar gyada sai ƙamshim daɗi yake fitarwa,..cike da wani irin farin ciki marar misaltuwa ya amshi lafiyayyan kunun nashi ɗaya daga cikin kujerun falon ya naima yazauna, cikin zafi-zafi yake sipping na kunun nashi hankali kwance har wani lumshe idanuwa yake tsabar garɗi da kuma daɗin da kunun yake da, 
Cikin wata iriyar siriryar muryanta tayi sallama daga bakin ƙofar palon tana sauraran abata izinin shiga "wa'alaikissalam" ammey ta amsa tana faɗin "kishigo mana haba MARYAMA  kullum sainace kishigone kamar wata baƙuwa" ta faɗi hakan tana yarfe hannayen wanda ta wanke kayan lambunta da tayi amfani dashi cikin lafiyayyan girkinta 
Ahankali ta sawo kanta cikin tsakiyar palon hannunta riƙe da wani haɗaɗɗan  basket da kullum take amfani dashi wajen kawo wa ammey breakfast 
"Barka da safiya ammie"
"Barka muntashi lafiya maryama"
"Lafiya alhamdulillah ammie" , tafaɗa hakin tana tura basket ɗin dake riƙe a hannunta sai kuma ta kama wasa da yatsun hannunta 
"Masha Allah Ubangiji yaƙara buɗi ƴaa taa  ya kuma haɗemin kawunanku wuri guda har ranan da zanga ƴaƴanku" kanta ta sunkuyar ƙasa tana cigaba da wasa da hannunta
Shi kuwa ogan acen ƙasan ranshi yake faɗin ai yama kusan haɗewa ammeyna domin nafiki buƙatar hakan sai kuma wani irin murmushin da bai shiryama zuwanshi ba ya subce masa, ummitah dake tsaye daga cikin ɗakin ammeynce ta kafe yayan nata da tsayayyawun idanunta masu kama da nashi, sai kuma akayi katari kamar ance ɗaga kanka, ya kuwa ɗaga yana sauƙe ganinsa akan AUTAR ammeynsa, gira ta ɗaga mishi tare da ɗaga kafaɗunta alamar naga komea, da ido yamata alama da tazo  kafaɗa ta noƙe alamar bata zuwa sai kuma tayi wajen ammeynta a guje tana shigewa jikinta....
"Barka da safiya YA MALEEK" 
Jikin kujerar ya koma yana ƙarayin relax yana sauƙe wata ɓoyayyar ajiyar zuciya da idanu ya bita, ita kuma dama batayi tsammanin amsawar nashi ba dan haka taci gaba da murza hannuwanta,.....kamar kuma daga sama taji sauƙar muryansa wanda a ƴan kwanakin nan take muradin jine ya dawo da ita cikin hayyacinta 
"Lafiya alhamdulillah tare dake" 
Sai kuma ya miƙe tsamm yana nufar ƙofar fita 
"Babana  fita zaka yi bayan kuma ga breakfast  katsa ai kaɗan sama cikin ka ko ɗan wani abu ne!"
"Zan tafi cennn ammey Naaaaa nawan nacen yana jirana ammey " 
Daga ammey har jadda da idanuwa suka bishi da kallo jin wani sabon salo na daban kuma,...shi kuwa ko ajikinsa ya kaɗa kai yafice abinsa.....
"Kitashi kibishi saiki haɗa masa abincin nasa"
Tasan da ita ammeyn take dan haka tsamm ta miƙe tana nufar ƙofar fitar itama...
Tafiya take ahankali da  tarin tunaninnika mabanbanta acikin rai da kuma ruhinta, ahaka hartakawo ɓangaren nasu hannunta ta ɗaura akan handle ɗin ƙofar tana turawa, yana zaune ƙafar nan ɗaya kan ɗaya yana faman latsa wayarsa samfurin ƙirar iPhone 12promax, Jin ƙarar taɓa handle ɗin ta akayi ne yasa shi ɗago da kansa yana kallon bakin ƙofar, kyawawan sawayen daya ganine yasa shi fashimtar itace ta shigo bai ɗauke idanunsa daka kanta ba har tagama shigowa complete nata, akan kyakkyawar fuskarta ya sauƙe ganinsa tare da kafe ta da idanunsa wanda suke ɗauke da wani irin shining na zallar ƙyau da kuma ƙayatarwa , jin kamar idanuwa na yawo akanta ne yasa ta ƙara haɗe jikin ta wuri guda tare da ɗago kai ahankali domin tabbatar da abinda take garzi caraff suka haɗa ido sai kuma yayi saurin sauƙe nashi ƙasa kamar bashine mai satar kallon ta yaci gaba da latsa wayarsa.....
Ƙarasa  shigowa tayi  tana jan filastik ɗin abincin gabanta, ahankali tashiga sarving nashi, shikuma hakan yabashi dama yaci gaba da more wa kallon ta,
"Bismillah food is ready"
 tafaɗa tana yimashi nuni da lafiyayyan delicious ɗin data gama shirya masa, ita kuma tana nufar barin falon domin bashi wuri kamar yadda tasa ba...
Uhummmmm yayi gyaran Murya ɗan juyo tayi dan ganin da ita ne yake ko kuwa, da ido yamata  nuni da tazauna  suyi lunch din tare  ɗan girgiza kanta tayi halamun bataci yaci abunsa kafaɗunsa ya ɗaga irin ko ajikinnan nashi, cokali ya ɗauka yadan debi abincin yana kai loman daya ɗebo bakinsa, sai kuma ya ɗan lumshe idanuwansa yana ƙara daidaita zaman sa, nan kuma ya shiga lodama cikin sa abincinsa hannu baka hannu ƙwarya....saida yaji ehhhh lallai fa ya ƙoshi da gasken gasken  kana yaɗan yagi tushu ya goge bakinsa, kafin kuma yanufi ɗakin sa kai tsaye.
A ɗaya daga cikin sopan da suka ƙawata ɗakin nasa ya zauna yana janyo jakar system ɗinsa waɗansu sucurity yashiga latsawa masu kama da harrufan sunaye, saidai nima bansamu ganin ko wanna sunane yasaba domin kunsan mutumin namu akwai tsaro, haka na hakura nadena leƙe idan da rai da rabo wata rana magani abinda ake gudun kada mugani ɗinnnn....
Cikin nutsuwarsa da Ubangiji yamasa yake latsa keyboard ɗin loptop ɗin nasa   ta inda yashiga bata nan yake fita ba, ataƙaice dai wuni yayi yana sarrafa system ɗin nasa sai wagagen ƙarfe ɗaya da rabi ya tashi akanta, yana barin gidan baki ɗaya,......Shine bai dawo gidanba sai bayan sallar magrib ya shigo gidan, wani irin daddaɗan kamshim dake tashi acikin falonne ya bugu hancinsa hakanne yasashi lumshe ido tare da buɗesu ahankali cikin wata irin murya mae amsa amo da kuma sauƙar da kasala ya furta  "kinas0n kasheni kwanana bai ƙareba JADDERH WHO dana cancanci haka daga gareki" 
"gashi kuma da alamun naga keɗin da gaske bakya fashimta" 
"Amma ya zuwa wannan loƙacin yaci yace kinɗan fashimta ko yayane *MY AYUSH*" ya faɗi hakan yana sakin Gwauron numfashi...."shi yasa nake tsoron baiyana miki abinda ke RAI DA RUHINA AYSHA ABDULPHATA OMAR" 
"da kuma gudun kada ki rainani shi yasa nake taka tsantsan da kaina wajen biyewama zuciya da kuma ruhina wajen tunkararki" amma very soon insha Allah"  sai kuma yayi shiru yana sakin wani irin cool smile  yashiga zance da kuma zuciyarsa,daga nan bankuma sanin abinda yake sakawa a cikin zuciyarsa baaa.....
*JADDAH*
Bayan da idar da sallar magriba ta miƙe tsamm ta nufi falon domin shirya masa dinner  sauri-sauri gudu-gudu dashiga shirya dining table ɗin gudun kada su haɗu domin bata da buƙatar hakan,  saidai kuma inaaaa fatanta bai cikiba, tunima shi yagama ƙarewa ganin nata..
Sanye take cikin wata doguwar riga samfurin ƙirar kampanin Morocco blue black ta naɗe kanta da voil ɗin abayar nata sharp ɗin ta ya fita sosae   , kamshi kawai take zubawa abinta,...
*MALEEK*
Ji yake tamkar ya tafi da gudu ya rungume ta domin kada ta ɓacewa ganinsa sosae ƙamshi dake tashi acikin jikinta ya shiga rikita tunani dama ƙwaƙwalwarsa jikin sane yaɗau tsuma tamkar bai wata cutar,... Cikin tafiyar sassarfa ya ƙarasa shigowa cikin palon, babu zato babu tsammani kawai taji sauƙar hannuwa zagaye faffaɗan kugunta an kuma ɗora haɓa akan kafaɗarta cikin tashin hankali da kuma dubun tsoron da Allah yamata, ta wani irin zabura zata zankaɗa ihu sai kuma ta sauƙe ganinta akan MALEEK, ajiyar zuciya taɗan saki kaɗan tare da ƙoƙarin janye hannuwansa daya zagaye kugunta dashi... saidai kuma samm takasa hakan domin mutum ko gezai baiyi ba bare tasa ran zai sake ta ɗin saima ƙara zagaye ta yayi yashiga hura mata iskar bakinsa ahankali, kici kicin kwace wa tashiga yi amma samm bai bata damar hakan ba saima haɗe bakinsa da nata da yayi  ahankali yashiga giya mata lallausan sajen dake kwance akan kyakkyawar fuskarsa yaɗan shiga goga mata akan gefen fuskarta cikin wata kasalalliyar murya ya ƙira sunanta cikin wani irin salo najan hankali..
   *"AYUSH*" ya ƙirayi sunanta cikin wata irin sillent voice ɗinsa dake bayyana irin zallar feelings ɗinta da yake ciki, sunan da kara na uku kenan daya ambata saitaji bugawar zuciya da  shiga wani irin zubuɗin sunan da takeji, saita kejin kamar wannan ɗin shine ASALIN SUNAN TA ba MARYAM baaaaa 
*JADDAH*
Kuwa jin sauƙar muryarsa cikin kunnuwana ne yasa ta rumtse idanunta da ƙarfi yayinda zuciyarta taci gaba da wani irin buguwa , sai kuma ta saki kukan ta ita kanta batasan na menene ba, cikin cracking voice tace dan Allah kaa saa kee nii  Please ya maleek ta fadi kalmomin ararrabe...sai kuma takifa kanta akan faffaɗan ƙirjinsa ta shiga raira kukanda babu dalilin yinsa tanajin kukan da take yi ayanxun shine mafakarta kuma garkuwarta ..
"Enough JADDERH enough is enough please"
Idaanunta da sukayi raurau  kana suka ƙara cikowa da ruwan hawayenne  ta lumshe jitayi gaba ɗaya zuciyarsa ta karye sai kuma kawaiiiiii taaaaaaa
Tafiya da gwaninka akwai daɗi maganar ciki zata fito fili ahhhhhhhaaaaaa
Ehhhhhhhhhhh mana  
*By ammeyn laylerh*
*KAREN BANA* nakune









