Showing 21001 words to 24000 words out of 72176 words

Chapter 8 - KAREN BANA complete by ammey laylerh .txt

nashi cikin tafiyar zaratan mazan da idan suna yinta sai ƙasa ta amsa,


A hankali ya murɗa handle ɗin kofar falon ya shiga, zuwa loƙacin babu kowa a falon: sai dinner daya gani a jere akan dining table, wanda dama yasan yana ɗaya daga cikin aikin baby doll ɗin nashi cikin tafiyar sassarfa ya ƙarasa gaban ɗakinsa yana tura ƙofar babban falon nashi..


daddaɗan kamshin da kuma sanyin easyn daya bigeshi ne ya kuma cakuɗa masa tunanin sa nan take cikin wani irin yanayin daya tashi dashi ya sa shi zubewa kan ƙafafun sa yana sakin wata iriyar ajiyar zuciya!


Yafi ƙarfin mintuna goma a wurin kafin kuma yasa ma damar jan ƙafafun sa yanufi toilet, A daddafe yayo wanka ya zira jallabiya falon yanufa, kai tsaye wurin abincin yanufa kaɗan yaɗanci sabo da marar sa dake wani irin azababben ciwo ko ƙofar ɗakin jadda bai kalla ba ya shige ɗakin sa haɗi da jan ƙofar yana rufe wa


__________________




A hankali yake ware idanunsa wanda suka yi jajur dasu, hannu yasa yana dafe kansa, dake Sara masa kaɗan kaɗan , hakanan gaba ɗaya duk bayajin ƙarfi a jikinsa, wanda hakan kuma baya rasa nasaba da ƙarfin maganin daya sha daren jiya , wanda ko sallar asuba ma daƙar yatashi yayi.....cije jajayen laɓɓan yayi cikin ɗan kuzarin daya saura ajikinsa ya sauƙo daga saman gadon nashi..




***Kai tsaye yanufi toilet, tundaga bakin toilet ɗin yasoma rage kayan dake jikinsa, kafin ya faɗa bayin nasa, yana sakarwa kansa shower lumshe luhu luhu eye nashi yayi yana sakin ƙyaƙyƙyawar ajiyar zuciya, wanda hakan ne yasa shi ɗan jin relief.


A haka ya kwashi sama da 15 minutes yana tsaye ruwa na dukan jikinsa, ahaka dai yayi wankan koda ya fito daga toilet ɗin towel ne ɗaure a waist ɗin sa, gaba ɗaya jikinsa ɗauke yake da damshim ruwa, yayinda itama lafiyayyar sumar kansa tayi lub, itama hankali take ɗan digar da ruwa.


Wani mini towel ya ɗauka wanda dashi ya goge kai da kuma jikinsa




Wani tsadadden kuma fitinannen body lotion me ƙamshim gaske ya shiga shafa wa lallausar fatar jikin sa, gaban drawer ɗin sa ya ƙarasa wanda ke jere da kayansa makil; ɓangaren ƙana nan kayansa ya buɗe ya ciro riga da wandon track suit masu masifar ƙyau da tsada, koda yasanya kayan a jikin sa ba ƙaramin ƙyau suka masa ba haɗuwarsa da kwarjinin sa sun sake baiyana , gashin kansa kuwa sai shining yake domin yasha mayuka masu ƙyau da tsada... Wasu white shoes yasanya a ƙafafun sa sannan ya debi wayoyinsa da kuma wata black bag yafice a ɗakin,




A zaune ya tadda ta tana breakfast da wani irin azababben kallo yabita mai kama da zaki sani ɗin nan


"Good Morning sir." Ta faɗa cikin siririyar Muryar ta ko inda take bai kuma kalla ba a gurguje ya zauna, yayi break ɗin ma kafin cikin azama ya fice a falon baki ɗaya, kai tsaye compound ɗin gidan yanufa,....




Soldiers ɗin sa dake zazzaune ne suka mimmike suna ƙamewa ogan nasu ,


joy ne cikin hanzari ya buɗe wa maleek ɗin murfin motar dazai shiga cikin isa da kuma taƙama ya shiga cikin motar yana lallatsa wayar dake hannun sa ƙirar iPhone 12 promax


Cikin 40 minutes suka ƙarisa babbar headquarters Abuja , cikin yanayin na sanin takan aikinsa yanufi ofishin sa kai tsaye, kan ɗaya daga cikin kujerun ofishin nasa ya zauna yana ɗaura ƙafa ɗaya ƙan ɗaya, anan yaci gaba da gudanar da sauran ayyukan sa cikin kwanciyar hankali,




__________________




A ɗaya ɓangaren kuwa anata shirye shiryen zaɓe sabo da yana gab da gaba towa, yayinda wasu daga cikin su ɗauki manya manyan alwasuka na ganin bayan *LIEUTENANT GENERAL MALEEK TAUFIQ*


Saidai kashhhh


Wannan maganar da ƴan azanci sukance kowa ya *ƘONA RUNBUNSA* yasan inda *TOKA TAKE TSADA* to kamar haka abin yake ga LIEUTENANT GENERAL MALEEK taufiq, Shima a wannan karon ashirye yake tsabb domin fuskantar su gaba da gaba, a gwabza *YAƘI*




Can kuma idan muka koma cikin gidansu maleek taufiq hajiya lubna itama ta shirya tsabb domin tarwatsa rayuwar Hajiya Aysha galadima gaba ɗaya.


Ɓangaren Hajiya talatu nera kuwa itama akwai wasu kudirorin dake ƙasan ranta




*** Cikin tafiyar ta mai kama da yanga take tunkarar ɓangaren surukuwar nata, gabbb taji an wani irin mangajeta, saida tayi taga taga kamar zata kai ƙasa sai kuma cikin zafin nama tayi wani irin juyi tana kuwa juyowa ta ɗauke husna da wani azababben marin daya kusan zauta duniya da tunanin husna na wucin gadi




Cikin tsabar fitsara da rashin kunya ta dubi *JADDAH* tana Binta da kallon ƙasa da sama, wani wawan kallo da jaddah ta wurgawa husna ne yasata sakin trolling dake hannun ta babu shiri, tana fashewa da kuka kafin kuma ta ruga a guje zuwa ɓangaren mahaifiyar ta hajiya talatu nera tana risga kuka




Ita kuma jaddah da tayi niyar zuwa wajen ammey yasa ta koma nata ɓangaren tana jin wata irin tafasar zuciya da kuna




Hajiya talatu tana zaune gaban makekiyar plasma ɗin ta tana kallon tashar arewa 24 ce tayi saurin miƙewa tsaye, tana nufar ƴar lelen nata wacce gama wayar su kenan bayan sauƙar ta, a jirgi ta dawo daga wurin karatun ta daga ƙasar America!¡!


Cikin kiɗima Hajiya talatu nera ta kamo hannun ƴar lelen nata tana zaunar da ita kusa da inda take zaune, tana faɗin wanda shegen ne kuma ya taɓamin ke daga shigowar ki ƙasar cikin sheshsheƙar kuka take faɗin momi bansan ko wa ce ce ba momi amma sainake ga kamar matar bro wacce kika tura min pisc ɗin ta ta Whatsapp fa momi;


Cikin wani irin wutar bala'i take cin Hajiya talatu nera tace


bantan ubancan


ita ɗin ƴar uban waye


ubanta waye a Nigeria da har tasama *ZARRAR DUKAN KI*


Tana gaba faɗar haka fuuuuuuuuu ta fice a falon baki ɗaya


Tana mai nufarrrrrr














To be continued in Sha Allah


Xuwa safe






Kuhuta da wannan
Masoya yanxune asalin wasan zai fara a shafi na gaba








🙃🙃🙃 Akwai Tarin cukurku ɗaɗɗiyar Cakwakiya a gaba




*Ƙaddara ƙaddara wata abacee dake dan ƙare a jini da ƙuma ɓargon ko wanne bawa*


*Kuma kowa akwai irin tashi ƙaddara domin rubutaccen al'ƙalamine tundaga rabbil izzati*


*Ko wanne bawa ta nashi kalan ƙaddarar manne a ƙirjinsa*


*Idan har kaga ƙaddarar wani ƙada kayi ma tashi ƙaddsarar dariya domin kai ɗin baka san ya taka zata kasance ba🤗*


*Dan haka ƙaddarar MALEEK da kuma JADDAH a manne take a jinin jikin ko wannen su kuma akwai wani tarin kalubalen da zasu fuskanta nan gaba*

*Rai da rashin su a manne yake a cikin ƙirjin ko wannensu tare da wata iriyar ZAZZAFAR S0YAYYA💔❤‍🔥 da ban al'ajabi da kuma burgewa, mai tafe da tausayawa juna sadaukarwa CAPTAIN IHSAN itama da nata kudirin duk Acikin SOYAYYAR MALEEK da JADDAH**🔥❤️ KAREN BANA❤️🔥*


{👉MAGANIN ZOMON BANA👈}






NA MARYAM NASEER MIRRAH ✨
*Ammey laylah*




FREE BOOK
Page 1️⃣8️⃣&1️⃣9️⃣






081-04-49-32-15








_____ Tana mai nufar palon ammey kai tsaye, tana zaune baiwar Allah ta ɗaura kan ummita asaman cinyarta tana shaluma tsakiyar kanta zuwa keyarta, ahakan barci yayi awon gaba da ita,....sai kawai ji tayi an wani irin turo ƙofar palon nata da ƙarfin gaske ,ummita dake barcice tayi saurin tashi zaune tana mirtsike idanunta..


Ko sallama batayi ba, tafara zubawa ammey ruwan bala'in dake famar sukar zuciyarta, ci kanki ammeyn batake mata ba...saida tayi mai isarta kana ta fuce daga palon nata bayan ta barwã ammeyn manyan kashedu game da surukuwar tata!¡!




Ita kuwa JADDAH tana zuwa palon nata ta zube kan ɗaya daga kujerun palon tana sakin ajiyar zuciya, idanunta da sukayi raurau suka ciko da hawaye ta lumshe, ji tayi gaba ɗaya zuciyarta ta karye, da wannan al'amari na sabuwar rayuwar data tsinci kanta a ciki, harse zuwa yaushe zata fara farin ciki nekammm
Ita? Gaba ɗaya rayuwa neman juyin waina takeyi ƙoƙarin yi da ita!


Tunda ta shigo wannan gidan gaba ɗaya al'amura suke naiman juye mata, a wurin ammey ne kaɗai take samun duk wani farin cikin rayuwa tun farkon shigowar ta gidan sai kuwa abbie,


A yanxun bata buƙatar komai domin brain ɗin ta gab take da juyewa, wanda hakane kuma yayi sanadiyar hautsinewar tunanin ta....






Bataji duk uban sallamar da MALEEK ɗin ke faman yiba, kansa ya sawo cikin tsakiyar palon, ganinta kwance tayi irin kwanciyar Nan ta rub da cikine yasa shi tunanin koba ƙalau ba dammm yaji zuciyarsa ta wani irin buga da ƙarfin gaske,
A sukwane ya ƙaraso gare ta haɗi da birkitota ta faɗa saman jikinsa, cikin kiɗima haɗi da zallar MURADI da kuma FATAN abinda zuciya ke tsananin ƙauna amma taurin kai haɗi da kuma ƙaryata zuciya yaƙi aminta da hakan;

Yake faman jijjaga ta haɗi da ɗago saman fuskarta, ganin hawaye kwance saman fuskar nata yasa shi faɗin "MENENE meya sameki haka ?"


Cikin Muryar kukan datake yi ne ta furta


"please ka barni"


Cikin wata zallar kiɗimar daya sama kansa a cikin ta ya ƙara birkitota jikinsa, yana ɗaura kanta saman cinyarsa ya ƙara furta "please keda waye?"
"Minene yake damu ki?"


A wannan karon kamm bazata iya jurewa yanda Amon muryarsa ke fita ba, gashi kuma duk ta ƙosa ya tafi ya barta.... Hakan ne yasa ta furta masa "UMMIENAH" cikin kasalalliyar murya! Tana ƙarasa faɗawa saman jikinsa¡!¡




Sauƙar lallausar fatar jikinta akan nasa jikinne yayi sanadiyar miƙewar tsikar jikinsa take yaji ƙofofin sadarwa tunanin sa sun tsaya, yayinda taushi da kuma laushin jikinta suka birkita masa tunani da lissafin sa loƙaci ɗaya suka kuma sauƙar masa da nannauyar kasala, idanunsa da suka ɗan soma marairaicewa ya zubawa ƙyaƙyƙywar fuskarta wacce tayi smooth take kuma shining ɗin kyau , ahankali ya kuma sauƙe ganin sa bisa tsayayyun albarkatun haɗaɗdun ƙirjinta, saurin kawar da kansa da tunanin sa yake ƙoƙarin yi amma hakan naiman fin karfinsa yake yi..


Cikin kasalalliyar muryar daya kusa zauta tunanin JADDAH ya raɗa mata "kuma shine duk wannan abin dan kinason birkitani da kuma tunani JADDERH"


Sakinta yayi ganin zuciyarsa na ƙoƙarin ingiza shi akan wani abu na daban wanda bai shirya wa hakan ba kuma, da sauri ya hawe saman sa cikin wani irin yanayin dashi kansa ya rasa na mainene,




Yana zuwa ya zube kan makeken gadonshi yanaji tamkar zuciyarsa zata tarwatse kan wani dalili nata na daban wanda shi kammm sammm baiyarda da abin da zuciyar nasa ke ƙoƙarin tursasashi akai baaaa, ahaka wani wahalallan barci yayi awon gaba da shi ko takalman ƙafarsa bai samu damar cirewa baaaa






Ita kuwa JADDAH saida tayi kukanta mai isarta, wanda kuma tarasa takamaimai da kuma dalilin na menene shi kafin itama barcin yayi awon gaba da ita anan kan sopa ɗin palon






Hajiya lubna Mommah ce keta faman kaiwa da komowa a makeken palon nata duk abin duniya yadameta, ganin ɗan ƙaramin abu na neman gafarar ta taje aƙalla gun malamai ƴan tsubbu wanda suke cin dunduniyar musulunci suke amsa sunan malamai a baiyane, amma duk inda taje maganar ɗaya ce ba sanja zani shine ta rabu da wannan Auren domin kuwa akwai rabo mai tsananin gaske, tsakanin MALEEK da JADDAH , idan kuwa harta dage akan sai an raba wannan Auren to kuwa itace zata *MUTU*; idan ta tuna wannan maganar tanajin tamkar ta janyo zuciyarta ta jefar akasss
Cikin zafin zuciya ta kaima iska naushi haɗi da furzar da wani irin turirin baƙin ciki mai ɗacin gaske




"Nice ajalin ahlinki Aysha" domin daidai da rana ɗaya bantaɓa jin koda kwatankwacin ƙaunarki keda yaranki ba shima MALEEK saboda wani dalili nawa nake tsananin ƙaunarsa! Amma a yanzun nayi watsi da wannan banzan dalilin nawa bayanku kawai nakeson gani kota halin ƙaa ƙaa nee kuwa Aysha galadima, ta faɗa cikin ƙara ji tamkar wata ƴar daba ko wacce ta shawuuuu






Ammey kuwa bayan fitar Hajiya talatu nera daga palon nata kai tsaye palon JADDAH ta nufo domin ja mata kunne, akan duk wani harka na gidan ta fita a sabbar kowa sai kawai wanda yace zai yi da ita to itama tayi dashi sai kuma tana zuwa bakin palon ta tura ƙofar kenan taga JADDAHN ajikin MALEEK, shine dalilin da yasa ta komawa baya ba shiri




Yau zaɓe saura kwanaki biyar kenan cibbb wanda iya tashin hankali su Alhaji Atiku sun shiga, na rashin baiyanuwar Kashim baba har wannan loƙacin,
A kuma wannan karon sun shirya tsabbbb ko babu domin ganin sun fuskanci maleek gaba da gaba sunyi fito na fito dashi, domin sunga ma yarda maleek ne kaɗai zai iya musu wannan ɗanyen aikin;.... Saidai kuma wani tarin al'ajabi daya ziyarar ci ko wannen su bayan gama taron nasu washe gari da safe baiyanuwar Kashim baban ta tarwatsa kwanwarsu dama tunanin su


Domin kuwa a washe garin da suka gabatar da wannan zaman Kashim baban ya baiyana, anan suka haɗa wani sabon meeting na gaggawa sukayi zama mai sunan zama, dan kuwa sun tattauna sosae akan al'amura da dama da kuma buruka mabanbanta;.....




Cikin tsananin azabar ciwon dake sukar zuciyarsa yake buɗe idanunsa wanda suka sauya launinsu daga farare zuwa jajaye ƙiran sallar la'asarin da ake ta faman yi, shine ya tashe shi a nannauyan barcin da yayi awon gaba dashi
daƙyar ya iya kai kansa cikin toilet ɗin sa yana zuwa baiyi wata wata ba ya sakarma kansa shower, yafi ƙarfin sama da 15 minutes ruwan na sauƙa saman lafiyayyar fatar jikin sa, amma ko gezau baiyi ba kuma baida niyar barin toilet ɗin,
Sallar dayaji an tada ne yasa shi saurin kashe shower ɗin tare da ɗaura towel ya fito yana tsane gashin kansa da wani mini towel ɗin dake hannun sa cikin hanzari irin nasu na kartin sojoji yayi maza maza ya shirya kansa cikin doguwar riga ta maza kamfanin kimono a gurguje ya fice a ɗakin nasa,




Tana kwance inda ya barta har yayi kamar zai wuce sai kawai ya fesa mata saurin ruwan alwulan dake bakinsa saman ƙyakykyawar fuskar ta firgigit kuwa ta farka, tana mutsurtsuke idanuwanta ganin shine yasa ta saurin sadda kanta ƙasa, alamu ya mata da tatashi tayi sallah kai kawai ta ɗaga masa tana miƙewa tsaye ta nufi cikin ɗakinta, shi kuma yayi waje




____________________


Bayan 2 week's anyi zaɓe angama cikin aminci da kwanciyar hankali inda duk masu mugun nufi suka ajje gefe sabo da samun nasarar su, inda kuma suɗin neee suka ƙara lashe zaɓen , a sannu kuma zasu fara fitowa MALEEK ta inda baiyi zato ba , sunbarwa kansu sani iyakar kansu




Yayin da zaman JADDAH da MALEEK yafara sauya wa daga yanayi na kai da kai zaman nasu yafara sauya wa anata samun ci gaba da saka makon shigar sabgar juna dasu ka fara.......






A gefe guda kuma maleek shi kaɗai yasan irin abun da ya shirya wa su Kashim baba sai shi sai zuciyarsa




Kamar kullum yauma zaune suka bayan sallar isha'i suna kallo a arewa 24, wani series suke kalla na indian hausa gyangyaɗi ta fara daga zaunen da take, kibbbb ta faɗa kan maleek dake zaune ya miƙe ƙafafunsa, hakan nema yasa ta faɗa saman cinyarsa ba tare da tasan tayi hakan baaaa....... Shi kuwa sai wajajen sha biyu da rabi ya saɓeta a kafaɗarsa yayi ɗakinsa da itaaaaaa










Sai anjima








*By ammeyn LAYLERH*






*🔥❤️ KAREN BANA❤️🔥* karen bana *KAREN BANA*








Kada ayi babu keeeeeeeeee






Shering and comments fisabilillah👌🏻👏🏻🙏*🔥❤️KAREN BANA❤️🔥*


NA MARYAM NASEER MIRRAH
*Ammey laylerh*




FREE BOOK
page 2️⃣0️⃣






081-04-49-32-15


*Dedicated to ya sapwan*


*Special tnx to my people masoya masu ƙaunata Ako da yaushe🤝💅*






_____________-Akan ƙayataccen gadon shi ya shimfiɗeta tare da gyara mata konciyarta, kai tsaye toilet ya wuce tare da watso ruwa ajikinsa, koda ya fito saman sopa yayi kwanciyar sa bayan ya tofesu da addu'ar bacci..
Ahaka har bacci yayi awon gaba dashi ƙiran sallan farko ya farka, toilet ya wuce yasakarma kansa shower tare da ɗauro alwala, darduma ya shimfiɗa tare da ɗaukar Alqur'ani nafila yayi raka'a biyu, Kur'ani ya ɗauka yasoma karatunsa cikin ƙira'arsa mai kyau mai daɗin sauraro, jin ana ƙoƙarin shiga sallar ne yasa shi tashi tare da ƙarasawa gaban gadon,


Ɗan bubbuga gefen gadon yayi tare da ƙiran sunanta in slow voice, ɗan juyawa tayi tare da wani irin juyi kamar zata faɗo cikin azama irin ta matan gaske yayi saurin tarota, tare da zaunar da ita


"*JADDERH*" yaƙira sunanta cikin wata irin sillent voice ɗinsa kitashi kiyi sallah




Ahankali tashi ga ware idanunta harta sauƙe ganinta tsabb, a cikin ƙayataccen ɗakin maleek ɗin saurin ƙara ware idanunta tayi,ɗan ganin ɗakin da take da sauri kuma kamar wacce aka tsikara ta miƙe cikin al'ajabin mene kuma ya haɗata da ɗakin maleek, ahankali kuma komai daya faru ya fara dawowa cikin braind ɗin ta tasan dai kallo kawai sukeyi, saita farajin barci daga nan kuma bata sake sanin maiya faru ba,


Ahanzarce ta miƙe miƙe tsaye tare da nufar bakin ƙofa handle ɗin ɗakin ta tura tana ziri ƙyawawan ƙafafunta xuwa cikin tanƙamemen falon nashi, kai tsaye ɗakinta tanufa toilet kawai ta shige alwula ta ɗauka tare da tura dogon shimar ɗin ta na sallah...


Bayan idar da sallar nata Qur'aninta ta ɗauka kamar yadda ya zame mata sabo tashi ga rera karatunsa cikin muryanta daɗi


Ganin garin yayi haske sosae hakan yaɗata aje Alqur'anin ta nufi kitchen domin sama musu abinda zasu yi kari


Agurguje ta haɗa musu abu mafi sauƙi ganin kamar tana naiman makara


kan dining table tajere masa nashi ita kuma ta nufi ɗakinta da plat na abincin nata , tura handle

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login