Showing 3001 words to 6000 words out of 72176 words

Chapter 2 - KAREN BANA complete by ammey laylerh .txt

flate na abinda yake so gaban sa, ƙarasowa yayi yana faɗin.


"Barka da dare abbey naaa"


"Barka my Happiness s00n"
Cewar Abbie yana amsa yaron nashi.


"Yauwa abbey naaa"


"arka da dare Yaya"
ummie ta auta ta shiga gaida yayan nata.


Kujera yaja yazauna bayan ya amsa gaisuwar autan ammey.


"Ammey copy"
ya faɗa hakan yana wani yatsine fuska , sammmm yau bayajin daɗin jikin shi, kuma yasan baya rasa nasaba da ruwan da ake shekawa har yanxun.
wanda yake sauka da ƙarfin sa babu kuma alamun tsayawarshi yanzun.


"To babban mutum bari na baka"
ammey ta miƙe tanufi kitchen domin haɗawa shalelenta baƙin copy nashi.


"Y a fama da aiyuka s00n?"


abbi ya faɗa yana fuskantar yaron nashi.

"alhamdulillah abbie Naaaaaa"


ƙara duban yaron nashi yayi yana faɗin.
"kiddnapping ɗin da akayi na kashim baba sammm ba imani a zukatan waɗannan bayin Allah, saida sukaga zaɓe ya taho! kana sai kawai suyi kiddnapping nashi, na rasa mene mutane suke naima har haka, dan Allah s00n a tsananta binciken nan"


Cikin ladabi irin nashi da girmama maganar mahaifin nashi yace.
"In Sha Allah abbie zanyi iya tsanani, har kamo gaskiyar wannan cukurku ɗaɗɗan al'amari ya baiyana kansa in Sha Allah"


"ALLAH yashige gaba a dage Sosai freind"
Cewar Abbie


"Ameern ya rabb, insha Allah zan tsananta"
Cewar maleek yana aiyana abubuwa masu dama acikin ranshi.


Ammey ce tafi to daga kitchen, hannun ta ɗauke da plate with cup. soyayyan ƙwai da tumatir ta soya mashi sama-sama da kuma haɗaɗɗan copy nashi, wanda yasha kayan ƙamshi, sai kunun daya zame masa tamkar rai da mutuwa, ita ammey bata wani yarda da wani copy nashi ba cennnn.
Hakan yasa ta haɗo masa da abu mafi soyuwa acikin zuciyarsa wato Kunun markaɗaɗɗiyar gyada, tasan dole zai sha idan har yayi ida huɗu dashi.


" Ummmm iyeeeee kaga ɗan gatan ammeyn shi ba"
Abbie yafaɗi hakan yana shafa kan my s00n ɗin nashi.
Wani c00l smile ne ya kwace mishi wanda baiyi niyar barin sa ya fito ba.
Iya tsanani kammm suna ƙaunar junansu waɗannan family.
************


Alhaji toufiq shararran ɗan kasuwa ne wanda yayi ƙaurin suna, a harkar business (kasuwanci) na sarrafa motoci campanyn sarrafa auduga, dadai sauran abubuwa masu yawan gaske.


yana da mata uku


Hajiya Lubna
Hajiya aysha galadima
Hajiya talatu nera


Hajiya Lubna itace uwar gidan alhaji taufiq, tana da yara biyu dukkan su matane Sumayya, yusrah.


Hajiya aysha galadima tana da yara biyu maleekb, sai auta ummitah.


Hajiya talatu nera tana da yara uku mata biyu, namiji ɗaya yusuf,hauwa'u husna.


Gidane da suke tsananin ƙaunar junansu,
A wannan gida Akwai mugunta da kirki Akwai hakuri! Rashin haƙuri zalumci Cin amana mai tattare da ɗaukan fansa.
baka taɓa ware wannan kace shine mugun,haka kuma baka taɓa ware wancen kace shine na kirkin, haka wannan gida yake tun mufiri
Wannan kenan.


A wurin hajiya lubna maleek yatashi dan da kammm baizaci ba itace ta haifeshi ba sai daga baya yasani.


Hankali kwance yake sipping copy nashi Sannu a, har yayi rabin cup ɗin ajjewa yayi kana ya janwo flate na soyayyan haɗɗaɗiyar wainan ƙwainshi,
lomar farko dayakai ne yasa shi wani irin lumshe luhu luhu eyes nashi tare da rolling na eye balls nashi, daɗin wainan na ratsa duk wata sassa da gangar jikin shi zuwa saman harshen sa.
*AMMEYN SHI* gwanace wajen iya sarrafa girki, ko yaya tayi girki saikaji kamar kada abincin yaƙare...
bayan kammala cin wai nan cup ɗin kunun gyadar shin ya janwo, bai ajje kofin ba saida ya tabbatar daya shanye kunun nan tass.


Kana suka yi sallama wa junansu kowa yakama makwancin sa.


Saman sa yanufa kai tsaye, cikin toilet ya shige tare da ɗaurayo bakinsa.
gefen gadonsa yazauna yana janyo jakar laptop nashi, Akan cinyarsa ya ɗaura laptop ɗin kana yadebo wasu files ya shiga wasu ƴan danne-dannensa, copying komi yayi cikin laptop nashi kana ya rufe Adda'ar bacci yayi cike da tarin nutsuwarsa, kana ya kwanta tare da tasbihi wa cen qasan ranshi. Ahaka har barci yazo yayi gaba dashi.




Washe gari tara da rabi
A wurin aikinsa tayimai, kasan cewarsa shine da al'haƙin wannan cese


Computers rooms nasu yanufa yana wannan tafiyar ta cikakken namiji, kana ganin tafiyar kasan tafiyace ta zaratan mazan gaske. yana shiga ɗakin da ihsan fandallah yafara cin karo, wacce ta matse cikin kaƙin sojoji tana zaune daga gefen el-basheer, kusan ma cinyarsu manne da juna waisu ala dole aiki sukeyi Ahakan.
Da wani irin kallo mai cike da begen wanda ake s00 ake muradi da tsananin ƙauna IHSAN tabi maleek da wannan mayen kallon nata.


Yanayin fuskar el-basheer yaƙub ne ya. Sanja daga farin ciki zuwa akasin hakan.
Ganin irin mayen kallon da IHSAN ɗin take bin maleek dashi.


Cikin girmamawa gaba ɗaya suka miƙe suna ƙamewa, hannun su saman goshi nansu
Kai kawai ya ɗaga musu yayi abinda zaiyi yafita abinsa yama bar ɗakin baki ɗaya.




Cikin motor shi yanufa da Alamu wani wuri mai muhimmanci yanufa,
tafiya yake cikin kwanciyar hankali da tarin nutsuwarsa. Ahankali yake mirza starryn motorn, yana bin sautin karatun dake tashi acikin motar.


Ban tashi aune ba naganshi gaban gidan.


*KASHIMU BABA FAMILY HOUSE'S*


abinda yabani mamaki kenan nima




Muje zuwa


Yanxun wasan ya fara






Domin jin yadda wannan wasan zai fara kuci gaba da bina aahhhhha


*By ammeyn laylah 🫶🏻*🔥❤️ KAREN BANA ❤️🔥


*NA MARYAM NASEER MIRRAH ✨*
*Ammey laylah 🫶🏻*


FREE BOOK
Page 4️⃣


✯D͟A͟Z͟Z͟L͟I͟N͟G͟ S͟✯T͟✯R͟'✯W͟R͟I͟T͟E͟R͟S͟




Whatpad
Ammey laylah


081-04-49-32-15


*Alhamdulillah forever and always*


BISMILLAHIR'RAHMANIR'RAHIM


************


Kashim baba family house's, naganshi gaban gidan horn ya danna mai gadin gidan ne ya leƙo. ganin ko waye domin ance kada wanda aka ƙara bari ya fita, a gidan sannan kada wanda aka kuma bari yafita ganin kamar motar ɗazuce ta sojojin nan yasashi, ƙara leƙowa da kyau , Again dai motar ce ya kuma gani hakan yasakashi wangale ƙaton bakin get ɗin nasu.
Cikin gidan ya nausa da ƙatuwar motar shi saida yayi kamar minti biyu sannan ya diro daga cikin motar, Sanye cikin kakin sojojin daya gama amsan jikin shi, daga saman kayan nashi kuma ya ɗaura wata jaket ruwan madara. Kasan cewar antashi da sanyi, saka makon ruwan da aka kwana sheƙawa jiya.


Baba mai gadine yaƙaroso,gaban maleek yana gaida shi, ce masa yayi ayi mai magana da neman iso daga cikin gidan,
Da to amsa shi yana shigewa Asalin cikin gidan! babu daɗewa yadawo yana cewa.


" yallaɓoi anbaka izinin shiga daga hajiya babba"


da sassarfa ya nufi cikin babban falon gidan nasu


Hajiya umma diomon ce zaune ita da yaranta uku. nawar jaabit sai fareedah wacce ta ɗaura kanta saman cinyar haiyanta! daga gefe kuma Amaryar alhajin ce zaune ita da yarinyar ta sai kuma ƙaton cikin dayake jikin ta wanda haihuwa yau ko gobe tana iya zuwar mata akoda yaushe.


Da sallama ya ƙara so cikin falon gidan yana cire sau cikin takalmin ƙafar shi


Gaba ɗaya mutanen falon ne suka ɗago suna kallon mai sallamar haɗi da amsawa.


Kurrrrr fareedah ta ƙure lieutenant general maleek taufiq da idanun ta, wanda gilas ɗin dake ɗauke saman fuskar ta wanda shine garkuwar ganinta,
A jikinsa yaji ana kallon sa.


Hakan yasa shi saurin juwoya dan ganin wacce mai zarrar ce tasama, damar ƙurewa ganin nasa har haka, da wata mai gilashi ya haɗa ido wacce tayi saurin sadda kanta ƙasa, tana wasa da yatsun ƙafarta saurin ɗauke kansa yayi.
Akan ta yana juyowa kan matan gidan.


Ɗan gyaran murya yayi yana tambayarsu shin dama alhajin yanada wasu abokan gaba ko kuma suna zargin dasa hannun wani.
A wannan kiddnapping ɗin ne, ɗan jim uwar gidan tayi sai kuma ta girgiza kanta tana faɗin.
"wallahi bana zargin kowa kan wannan lamarin"
Kan amaryar ya dawo da ganinsa, ita ma ya ɗan tattabbayeta,
tabashi amsa daidai da wacce uwar gidan ta bashi.
Sallama ya musu bayan ya ɗan samu amsoshi ƙaɗan da kuma yawan abokanan mai gidan nasu.
nan kuwa sun bashi haɗin kai dan kuwa tsab suke shiga jero mashi sunayen abokan nashi kamar haka.
Ibrahim nera,isa hasarara, alhaji atiku isa tanbuwal
Ya kuwa gamsu da jawaban nasu dan haka...


Yasa a ranshi In sha Allahu zaiyi iya bakin ƙoƙarin ganin ya gano wannan cukurku ɗaɗɗan al'amarin.
daga nan wurin aikin sa ya koma yaci gaba da bibiyar shige da ficen waɗannan bayin Allah, wata ɓoyayyar ajiyar zuciya ya saki loƙacin dayaci karo da wani abinda ya hargitsa tunaninsa dama lissafin sa.


Yana nan zaune ƙira yashigo wayarsa chief Of ARMY, shine kwance saman screen ɗin wayan nashi, Cikin girmamawa ya amsa ƙiran yana karawa a kunnenshi.

"ka shigo kano yau zuwa gobe ina S0n ganinka"
Shine kawai abinda aka faɗa daga cen ɓangaren, tare da katse wayar.


"To ranka shi daɗe in sha Allah ina nan tafe"


Kitt yakatse ƙiran yana miƙewa tsaye, tare da tattara komi nashi ya nufi gida Agaggauce.*🔥❤️ KAREN BANA❤️🔥*


NA MARYAM NASEER MIRRAH ✨
*Ammey laylah🫶🏻*




FREE BOOK
Page 5️⃣


081-04-49-32-15


*DUK ZUCIYAR DATA SAMU HASKE TA DALILINKA ALLAH ZAI SAKA MAKA DA MAFIFICIN ALKHAIRI😌🤏🏻🤌🏻*
*MUSANI WAYARWA DA ƊAN UWANKA MUSULMI KAI AKAN YABI HANYA MADAIDAICIYA JAHADI NE ALLAH YASA MU GANE🙏🏻🫂*
*MARYAM NASEER GARKUWAR MUSULUNCI💪🏻*
____________________________


A gaggauce yashiga haɗa duk wani abinda yasan zai iya naima, na kayan amfanin sa ya zuba cikin bag nashi. Irin tasu ta sojojin nan,
Cikin parlourn su yafito
tsaye, ya tarar da ammeyn sa tare da. Ummie ta.
Ido ammeyn nashi ta zuba mishi, tanajin kamar ba lafiya ba, ita fa sammmm shiyasa bata son wannan aikin nashi na SOLDIER!!..
duk wani aiki da zai taso tofa shalelen yaron nata shine shan kundin.
Badan ma Abbie yana qara qarfafa mata gwiwa ba, da batasan yadda zatayi ba.


me yasa?


Mai yasa sai shi?

kodai duk sauran
ba maza bane matane bata sani ba ko kuma bata da labari..


zuciyarta tana yawan karyewa akan wannan aiki nashi, so dama takanji tamkar tace ya dena aikin kwata ²
Ga rayuwarsa da mutanen da bata san ko su waye baa!!, suke son ɗauka kota halin qaqa, gaba ɗaya anbi ansako mata yaro gaba.

"Zan tafi ammey kisamin albarka kamar kullum"

Shine yakatse ta daga dogon tunanin data faɗa,
Kyakkyawar ajiyar zuciya ta sauke tana mai ɗora hannun ta saman tsakiyar kan shi, tashiga jero mashi adda'o'in kariya daga sharrin masu sharri, masu son ganin bayan sa...
Shima ajiyar zuciyar ya sauke yana ƙara duban ammeyn nashi, da yanayi na babu komi fa ammey Allah na tare dani a duk inda nake,kuma shine zai ci gaba da kareni da kariyar sa.
Kai kawai ta iya ɗaga mai tayi saurin shigewa ɗakinta, domin wani kuka taji yana ƙoƙarin zuwar mata, aloƙacin da ita yakamata ace tana bashi ƙwarin gwiwa bawai shine zai bata ƙwarin gwiwar ba.
Kan ummitah ya shafa yana sakar mata tattausan murmushin da ba kowane ke da ikon samu daga wajen sa ba. sai mai matuƙar sa'ar gaske idan ka ɗauke family nashi..
Itama murmushin ta mayar masa tana faɗin


"big Yaya solders ka kula mana da kanka"


ƙara shafa kan nata yayi yana ɗaga kansa alamun in Sha Allah zai kula ɗin.


Daga nan yanufi harabar ƙatuwar tsakar gidan nasu, wanda matakan tsaron da aka zuba domin tsaron lafiyar sane reras sai faman kaiwa da komowa suke, daga ɗaya ɓangaren kuwa.
wasu manyan motocine fake daga wurin da aka tanada dan ajiye su..


Parking space ɗin
yanufa wanda masu tsaron nan, suna ganin ya tunkaro wurin suka ƙara dai-dai ta nutsuwarsu, haɗi da ɗaga hannun su zuwa saman goshi nansu ' suna Sara ma ogan nasu: kafin kuma a guje sunufi motocin su suma.


Gaban wata ƙatuwar mota ƙirar Hilux 2023.
Ya nufa sabuwar samfurice da sabon CAMPANYN abbeyn shi suka fitar, Acikin wannan shekarar ta 2023 sakk, Irin Hilux daka sani sai wasu ƴan ban-bance-bancen zamani da aka samu..


Car key nashi yasa yabuɗe motar... Nashi mai numfashi adda'ar shiga sabon abun hawa yayi, domin yaune zai fara hawan motar in Sha Allah. da sunayen Allah fall bakin sa yashiga, tun kamin ya tada motar bala mai gadi ya wangale musu ƙofar ƙaton get ɗin gidan.


A 36 suka ja motocin nasu suna cillawa kan babban titin garin abuja....gudu suke tamkar zasu tashi sama
Ikon Allah ne kawai yakawosu garin na Kano lafiya.


NIGERIAN ARMY &AIRFORCE AND NAVY RECRUITMENT 2023/2024
*****************


Motocin nasu sukayi fakin, dirowa suka fara yi ɗaya bayan ɗaya harsuka gama fitowa,
kana sukawa motar ogan nasu ƙawanya kafin kuma su saki ruwan harsasai jikake tas! tush!! taratsatsa!!!.
suka fara sakin harbin Alamune na nuna cewar wani babban mutu ko shugaba ya yaziyarci guri, wannan shine alamar sojawan ƙasata Nigeria💪🏻.


Motar suka buɗe masa yafito jikin shi yana tsuma domin kuwa sungama taɓo maza. guns nashi dake ɗaure daga bayan wandon jikin sa ya zaro, yana harba ta sama fareti suka farayi suna kaiwa suna komawa sunfi ƙarfin muntuna talatin.
sunayi kafin kuma su tsaya cakkk! Ganin ogan nasu yanufi *CHIEF OF ARMY STAFF* (COAS).
Yana tafe cikin tafiyar nan ta mazajen fama mazajen gaske wanda ruwa,iska,tsanani, bayasa su gudu 'a filin yaƙi.


A jiyar zuciya chief of army ya sauƙe bayan yagama ganin komai ta glasses ɗin, ɗakin wanda aka seta da ctvv Camera na ɗakin, kan kujerar sa yakoma yana kuma sauƙe wata ijiyar zuciyar again.


****
Da sallama yashigo cikin babban Ofishin na chief of army.
cikin tsananin kulawa da jin yaron cannn ƙasan zuciyarsa yake amsa sallamar tashi, haɗi da nuna mashi wurin zama saida ya sara mishi kafin ya zauna, yana fuskantar ogan nashi wanda daga shi sai shi 'a matakin matsayi.
Hannu yamiko mar kamar kullum musabaha sukayi kamar yadda suka saba.


Fuskantar sa yayi da kyau kana yana numfasawa, tare da faɗin.


"lieutenant maleek taufiq kana ganin wannan karon bazaka bar wannan aikin, A hannu naba kuwa domin ta ko ina rayuwarka kewaye take da magautanka!! kana ganin wannan karon bazaka fito musu A mutum ba, domin ganar dasu kuskuren da suke son jefa kansu?"


Hannayensa ya miqar tare da lankwasa su, cikin girmama ogan sa kuma tamkar mahaifi yake, a wurin shi yace.

"Kabar komi 'a hannuna sir. Kamar dai kullum ɗin, kada ka manta niɗin horon kane dan me kakejin kamar zan gaza wannan karon,Fito musu A mutum kuma bawai shine mafita ba domin hakan bazata taɓa sanja rawa ba, Idan zaka kama tsuntsu mai wayo, tofa ta wuya zaka kama shi sir."


Ya faɗi maganar yana kallon wani gefe daban,ba kamarda da yake kallon chief of army ba.


Kurrrr chief of army yabi *MALEEK* da kallo, tamkar bai taɓa ganin saba sai yau ɗin yake more wa ganin sa.
Lalle sai yanzun yaƙara yarda ɗari bisa ɗari wannan shine renon shi. Ba kamar sauran ba, kai yashiga gyaɗawa yana tafa hanna yensa yana faɗin.


"weldone yarona haka akeson mazan gaske tamkar dai kai ɗin nan"


Sajen fuskar shi yashiga shafawa haɗi ta faɗin

" wannan ɗin *horonka ne* sir."






Chief of army kuwa wani alfahari yaji yana kama shi, na kasan cewar maleek A matsayin babban yaronsa wanda shine mafi kwazo a cikin sauran.


"Ka tabbata ka ɓoye mana *kashim baba* guri mai tsaro kuwa??"

murmushin da bai shirya zuwan shi bane ya subce wa maleek ,
yana jijjiga kai yace


" kadama kasa wannan damuwar A ran ka sir! Yana nan A wuri mafi killacewa da tarin tsarona, bana kowaba"

Cike da zallar alfahari da maleek ɗin chief of army ya shiga faɗin.




"Da kyau yarona tashi kaje abunka, lallai naji dadin wannan maganar Allah ya dafama yaci gaba da shiga cikin lamuranka"
da amin ya amsa yana ƙara jin ƙaunar dattijon har ƙasa ranshi.


Fita yayi bayan ya tabbata babu wani sauran annuri dake saman ƙyaƙyƙyawar fuskarsa...


***
Darmanawa tudun fulani suka nufa, yana son anguwar saboda shiru-shirunta shiyasa yazaɓa zam, Acen a bakin get ɗin suka tsaida motocinsu , soldier ɗayane yafito da gudu ya buɗe musu ƙofar get ɗin. saida yabari motocin sun gama shiga kana yabi bayansu yana ƙara rufe Kofar get ɗin.


Basu shiga cikin gidan ba kasan cewar ana ta ƙiraye kirayen sallar la'asar, alwala
Suka shiga yi kana suka nufi masallacin anguwar.


Basune suka dawo ba sai bayan sallar isha'i domin sun ɗan leƙa gari.


Wanka yayi kana yaɗanyi wasu ayyuka nashi,
a laptop nashi sai wajen sha biyun dare ya kwanta bayan yayi sallar nafila haɗi da karatun Alqur'ani mai girma...asba ta gari lieutenant maleek taufiq.


Washe garin ranar.
Wajajen yamma suka ƙara fita, bayan sun dawo sunyi wanka wajen cin abinci suka nufa. restaurant kowa yabuƙaci abinda yake so, aka kakkawo musu, ogan kuwa babu komi A gabansa banda robar faro guda ɗaya, kanshi duƙe akan waya nashi yana ɗan ne danne.

Kamar ance cira kanka yakuwa cira ido huɗu sukayi..... Ai kuwa da wani irin mugun sauri yafito yana ƙara jan p-carp ɗin dake kansa, yana bin bayan mutumin da yabiyo abaya, Cikin motarsa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login