Showing 15001 words to 18000 words out of 72176 words
Chapter 6 - KAREN BANA complete by ammey laylerh .txt
 ya sanya Alkhairi yasa ayi damu cikin aminci 
Wata irin ƙima da ɗaraja sarki maleek yake kallon malam Abdullahi rano dashi cike da burgewa  yake faɗin ameen ameen ya Rabbi ya sawati malam 
Nan take yasa aka maida malam Abdullahi gidansa cike da girmama da kuma ƙwarin gwiwa 
Shi kuwa maleek yana fita daga ɓangaren mahaifin nasa, nashi ɓangaren yanufa da wani irin ƙarfi ya tura kofar gidan nashi cikin azabar da bugun zuciyar dake S0n zautashi ya faɗa saman tattausan lafiyayyan gadon dafe da saitin zuciyar sa da yakejin tamkar zatayi bindiga ta fito *Innalillahi* yashiga mai mai tawa yanajin zafin zuciyar nashi yana raguwa  cikin tuƙuƙin baƙin cike yake ayyana yadda zaiyi da duk yarinyar da tayi gangancin shigowa rayuwar shi ' a irin wannan loƙacin 
Zaune yake gaban iyalan nashi harda yaya jamilu daya dawo daga wurin karatu jiya da dare...kallonsu yake ɗaya bayan ɗaya kafin kuma cikin jan numfashi yafara magana kamar haka
Farko ina mai s0n farawa da baku haƙuri bisa wani hukunci dana yanke ba tare da sanin iyalan nawa ba! Bayan zuwana fada 'a ɗazun mai martaba sarki yake mai neman wata al'farma daga gareni, tas0n haɗa iri dani,  
Damm gaban kowanne su yashiga bugawa barin ma JADDAH baiwar Allah 
Kana yaci gaba da faɗin anan yake faɗa min yana nemawa jikinsa *AUREN* ƴar wajena jaddah! Nikuma duba da kamalar mutumin da girman da yake da kana uwaa ubaa tattako da yake da 
Nan take na amince masa ba tare da tunanin wani abu ba  
Wannan loƙaci yayi daidai da loƙacin da jadda ta dafe zuciyarta idanun ta na S0n fidda wani ruwa-ruwa dake cikin su 
Ummey ce dake ankare da ita, tayi saurin janyota jikin ta haba mar'atussa saliha haba uwar Muminai karki gaza mana kamar yadda nasanki da ƙwarin zuciya kiyima mahaifinki biyayya ta nan ne kaɗai zaki saka masa kinji *AUTAR MATA* kai kawai take kaɗawa ummeyn nata sai kuma ta ɗaga kanta tana , kallon ummeyn nata kana take tambayar ummeyn nata wai ta isa *AUREN KUMA* yaa yaa jamilu ne da tunda aka fara gudanar da jawabin baicw komai ba dangane da furucin na baban su yashi dungure kanta 
Yana faɗin raguwa kawai bayan kina age na shakaru ashirin da ɗaya ma  
Hararar wasa ta ɓalla masa tana tashi tabar musu falon....ɗakinta tawuce tana shiga ta fashe da kukan da kanta batasan kona miye shiba tana  sake duban yadda take gani take yi kamar tayi *ƘANƘANTA DA AUREN* 
*Kumuje da zuwa takuce ammeyn laylah ako da yaushe*
*Saimu haɗu a shafi na gaba*
*Wallahi idan banga ruwan comments naku ba tammmm zaku jima baku samu posting ba esheeeeeee nima na huta sosae yadda ya dace*
*By ammeyn laylah 🫶🏻💔**
*🔥❤️ KAREN BANA ❤️🔥*
MA MARYAM NASEER MIRRAH ✨
*Ammey laylah*
FREE BOOK
Page 1️⃣3️⃣
081-04-49-32-15
*Ina miƙa saƙ0n ta'aziyya ta ga ƴar uwaa Hadiza Tukur Maman Mama🙏🏻👏🏻 bisa rashi na maahifinta da tayi ubangiji yasa ya huta yasa Aljannah ce mako marsa🤲🏻🤲🏻*
*Godiya 👏🏻🙏🏻 marar adadi ga baiwar Allah bawan Allah dake turomin DATA kuma amma yane ɓoye kansa*
*Nasan dai ko waye, ko wace zata gani ubangiji ya biya da gidan Aljannatul fiddausi👏🏻👏🏻ngd*
______Ita fa gani take sammm bata isa AUREN ba inaaa ina tamayi ƙanƙanta gaskiya da wannan auren da akes0n ƙaƙaba mata 
Kawai ma zataje tacewa ma da Baffan ta a fasa auren neee kawai
Da haka tasamu bacci yayi awon gaba da ita 
Ɓangaren MALEEK ma hakan ce ta kasance dashi domin shi ɗan maa wani, wahalallan bacci ne yayi gaba dashi, sai gab da magrib sannan ya farka bayi ya shiga ya watso ruwa haɗi da alwula, yanufi masallaci!
AMMEYN shi yayi farin ciki dajin wannan babbar magana ta mahaifin shi maleek ɗin domin kuwa,
 ita kanta saitafi jin, nutsuwarsa da mata ba kamar bashi da matar ba 
Ita kuwa Mommah loƙacin da taji wannan al'amari gani take tafi kowa farin ciki da wannan maganar auren na maleek ɗin ta domin babban burinta kenan  
tsabar farin ciki harda hawayena daɗi tayi 
Gaba ɗaya cikin gidan nasu babu wanda bai ji maganar auren yaayaan nasu ba masu farin ciki nayi haka ma masu baƙin ciki nayi domin kuwa  kar 'a tona zuciyarsu a gani! domin suna jin tamkar su cire zuciyarsu daga cikin gangar jikin su haka sukeji
ADAMAWA
************** 
Zaune yake gaban Little momman nashi  ya fuskance ta da kyau,gaba ɗaya yabata dukkan wata nutsuwa tasa
A hankali take masa jawabin abinda yafarun kafin zuwan nasa har kwanciyar asbitin da tayi  da yanda aka tattauna akan maganar baki ɗaya s0 dan haka ya kwantar da hankalinsa loƙaci kawai suke jirah 
In Sha Allah 
Ya fashimta ya Kuma gamsu da dukkan wani bayani da ƙaramar momin nashi tayi mai kuma shima zai ci gaba da roƙon Allah ya sassauta musu  ya warware musu komi cikin aminchinsa 
Daga nan ya fita ' a ɗakin nata, hakan yayi daidai da fitowar mahaifiyar sa  hajiya laura, itama daga nata ɓangaren 
wata bahaguwar hararar da ta watsa mishi ne yasa shi saurin sauƙe kansa ƙass
Itafa tagaji da wannan  likimo ɗin da takeyi akan matar da dukk duniya tanajin babu wanda tafi tsana sama da ita, matar da indai har zata ganta saitaji ƙirjinta  ya buga da wani irin tsalle 
to me yasa hakan?
Kawai tana ga zata fito mata'a asalinta na zahiri bawai wanda ta ara ta azawa kanta baaaaaa tagaji shekaru ɗaɗɗai har shekaru ashirin da tara amma kullum cikin sakin fuska da hada hada suke mata 
Dan haka tagaji da haɗa mata tuggu ta ƙasa kawai zata fara fitoma mata a baiyane neee ta faɗi hakan tana sauƙe ajiyar zuciya kafin ta gallama ƙofar ɗakin nata harara, ta wuce  zuwa cikin harabar wajen masarautar tanajin zuciyar ta tamkar zata fasa ƙirjinta ta fito
Cikin yanayi na razana, ƙiɗima, tashin hankali, take  tafiyar  a dokar dajin Allah subhanahu wata'ala cikin tafiya ta rashin tsoro take tunkarar dajin haiƙan 
Abaya ce baka wulik a jikinta ƙafarta, hannayenta, duk ta rufe su da safa 
Saman fuskar ta kuwa liƙab ne gaba ɗaya babu inda kake gani a cikin jikinta 
Gaban wata ƙatuwar bishiyar kuka  taja ta tsaya  tana wasu surkulle masu kama da, dalassumai 
Cikin wani irin ihuuu da ƙara ji wani ƙaton boka ya baiyana gabanta  yana kururuwa iya ƙarfinsa da wata irin murya tasa mara daɗin ji, ya fara magana 
Kamar haka 
"Tabbas wannan karon zaiyi AUREN"
 kuma harda rabo a tsakanin su
Sannan idan har kikayi ƙoƙarin dakatar da hakan to kuwa tabbas zaki mutu LUBNA
kuma tabbas  sannan inada da tabbacin babu wani gurin boka ko malamin da zai iya miki wannan aiki akansu tunda nakasa 
Nasan kina tafe neeee akan zancen Auren MALEEK 
Cikin wani yanayi marar daɗi jin mai kama da  tsafi yanayin lubnan yasau ya tana zubar da  hawayen jini 
 Tace Kasani ba yau ba, ba jiya, ba shekaran jiya ba  nake musu aiki akansu shida tsinanniyar uwar tasa
Amma wannan karon tashi ɗaya kace  aikina bazaici 
Boka  TUNKAS  kasan wannan aikin daidai yake da cikar maradina boka dan haka zandakar da hakan !!
Kota halin yayane kamar yadda nasaba 
*FITAR  'AZABA TAMKAR FITAR CIWO HAKA YAKE*
*DAN HAKA DOLE WAJEN GUSHE WARSA*
*DOLE SAI DA WATA AZABAR BOKA!!!*
Kafin ya ankare tuni harda  ɓacewa ganinsa ɓatttt
Wata iriyar dariya ya kuma kecewa da ita yana mata kallon tsirara domin kuwa ai shine ginshiƙin 
Ita kuma tsiro 
Shima ɓattt ya bace a wurin yana barin wani baƙin hayaƙi a gurin 
 ******** Kwanci tashi hasarar mai rai zancen auren nan sai ƙara bazuwa yake yi....loƙacin da Hajiya talatu nera taji wannan zancen kuwa  saitaji kamar an soka mata kibiya ne a ƙirjinta 
Ta cennnn ƙasa kuwa wasu irin shirye shirye ne sarki maleek ibn suffyan yake wanda babu wanda, ya isa yace ga asalin abinda yake ma shirin!.....yanaji kamar ya mats0 da wannan auren domin cikar maradinsa
Tamkar abin wasa haka gidan su malam Abdullahi rano, suma suka fara shirin bikin aurar da ƴar tasu..... Jaddah kuwa hankalin ta idan yayi dubu toya rida, daya tashi domin ganin tabbas da gaske shirin bikin tane  ake  
Ummeyn ta tashiga gyaran ƴar tata tako ta inaaaaaa
____ Su alhaji atiku  kuwa sun riga sun seta wata ƙayataccir diner da tashin hankali a zuciyar maleek taufiq 
Wanda yayi daidai da ranan ɗaurin auren saaaa
Cikin yanayi na cikon wani cikar muradi tashi addu'a babu dare babu rana 
*Kuyi haƙuri yau TYPING kaɗan ne ba yawa*
Nerth PAGE in Sha Allah 
*By Ammey laylah 🫶🏻💔**🔥❤️ KAREN BANA ❤️🔥*
NA MARYAM NASEER MIRRAH ✨
*Ammey laylah*
FREE BOOK
Page 1️⃣4️⃣
081-04-49-32-15
*RAYUWA TAƘAITACCIYA CE, KARKA CIKATA DA DAMUWA.*
*HAƘURI DA JURIYA SUNE SILAR  CIKAR   KOWANE BURI*
______- Cikin yanayi na cikon wani cikar muradi nata, ta shiga ambaton sunayen Allah babu dare babu rana.
Haka ma na hannun damar nata wato Sufyan Abdulphata ba'a barshi a baya ba wajen taya Little momman nashi adda'o'i,wajen sauƙaƙa musu wannan lamari 
****Cikin jimami da fargaba da take ciki take tafiya cikin sanyin jiki haka kawai takejin kar ba kalau ba kamar wani abu gagaru na shirin faruwa da rayuwanta, saidai tana ƙoƙari wajen danne hakan, dalilin kada mahaifan nata susan halin da take ciki,
A hankali take taka ƙasa kamar wacce take tausayinta ko kuma irin anyi mata dolen nan?
Cikin sanyi murya tayi sallama  a cikin gidan nasu wanda yafara tara ƴan uwansu na rano, da suka fara zuwa domin gudanar da biki 
Ko wannensu ɗauke da tarin farin ciki maɗaukaki suke amsa sallamar nata,har wasu daga cikin su na tsokanarta amayar baƙya laifi koda kuwa kin kashe ɗan masu gida,gaidasu tashiga cikin ladabi hadi da tarin nutsuwarta 
___Gidan su MALEEK TAUFIQ kuwa cike da tarin farin ciki marar ɓoyuwa ammeyn nashi take saukar bakin nata, wanda take ganin kamar ' a mafarki wai yau waɗannan jama'ar sun tarune domin bikin gudan jinin MALEEK 
Ɓangaren hajiya Lubna kuwa idan hankalin ta yayi dubu toya gama tashin kanta,domin ganin abin take kamar madubin mafarkinta MALEEK maleek daiiii maleek ɗin ta shine yau harya samu zarrar fitar da matar aure, to shin ina asirin da tayi mai?
 na tsanar mata gaba ɗayansu kai ita da s0ma tayi tarabashi shida munafukar uwarsa saidai hakan ya gagara
Badan tas0 ba ta ƙyalesu a haka suke mu'amulatar junansu a duniya idan da matar dafi tsana to kuwa yabi bayan aysha galadima ta auna kasheta ita da yaran nata saidai hakan ya gagara, kuma yasan hakan baya rasa nasaba da wancan shegen uban nata wato sarki maleek ibn suffyan domin tsaye yake akan duk wani abinda, ya danganci ahalinsa.da tarin adda'o'in kariya daga sharrin masharranta 
Cikin tsananin azabar dake tsikarin tsakiyar ƙirjinta tafi to daga bayin ɗakin nata bayan ya dauraye idanunta  
Sumayya, yusrah ihsan,jamila Sune ta tarar a tsakar parlon  nata   sai autarta nabeelah wacce take jingine da jikin Aunty Sumayya tana buga game  'a wayanta  fuskarta ta ƙara saki tana duban yaran nata cikin tsananin ƙaunar ƴaƴan nata.....gaisheta suka shiga yi cikin girmamawa amsasu tayi har tana tambar yaransu domin dukkanin su ko wacce yana ɗakin mijinta iya autar ta ce nabeelah a gabanta...
 
Ita kuwa hajiya talatu nera barin ma ƙasar tayi gaba ɗaya tace baza'yi wannan abin baƙin ciki da itabaaaa.....
Dan haka maaa tabar ƙasar baki ɗayanta ta lula ƙasar masu jajayen kunne ita da yaranta sai kasar swinzlan  
Yau takamaa   21 ga watan 5 Na june  wanda yayi daidai da ranar daurin auren MALEEK TAUFIQ da amaryarsa MARYAM ABDULLAHI RANO 
A babban filin harabar masarautar wanda matakan tsaro na manyan sojoji sukawa Masarautar ƙawanya da tarin  tsaro  mai tsanani  
Sha biyu daidai aka ɗaura auren *MALEEK TAUFIQ*
              DA
        Amaryarsa
*MARYAM ABDULLAHI RANO*
Akan sadaki dubu ɗari biyar  lakadan ba ajaran ba wanda mangan shugabanni ƴan siyasa tattawa masu tattako suka shaida....
Saidai wani abin mamaki sama ƙasa anrasa ango anrasa dalilin sa murmushi kawai sarki maleek ibn suffyan yayi domin shi yasan abinda yasa ya gudarma ɗaurin auren nasa a loƙacin da jama'a suka rigada sukawa Masarautar ƙawanya a loƙacin ne shi kuma MALEEK TAUFIQ yasa daman shiga cikin asalin fadar sarki maleek ibn suffyan kakan nashi, wanda yarufe fuskarsa da glas da p-carp , wannan dalili yasa babu wanda yagane asalin wanene  sai idan yaje gurin masu tsaron ƙofa ne yake dage p-carp ɗin sa 
A zaune ya tadda Sarki maleek ibn suffyan wanda ya kishingiɗe a saman ƙayatacciyar  kujerar SARAUTAR SA!..... Shima kujerar yaja yazauna yana fuskantar kakan nasa
  haɗi da haɗe ƙyaƙyƙhawar fuskarsa.
sammm babu wani annuri dayai saura ' a saman fuskar nashi cikin magana mai kamada bada umarni yafarawa kakan nashi magana 
"Yaka mata kayi gaggawar baza wannan dandazon tarin jama'ar daka tara"
"Tunda na fashimci kai kawai takurawa mutum ka iya kuma shine aikin"
"Dan haka tun wuri kasan yadda zakayi da tarin jama'ar ka"
"Ko kasan yadda zakayi da ita yarinyar domin bani zaka ɗaurama baaaaa"
Yana gama faɗar maganar dake ransa  ya fice a fusace fuuuuuuuuu saikace wata kububuwa 
Yana fitowa ya faɗa matar shi yajata da mugun gudu na masifa 
Wani murmushin sarki maleek ibn suffyan yayi yana shafa saman fuskarsa, da sammm bata da maraba data ɗiyarsa little daughtern shi aysha  
 
Alhaji TAUFIQ ne ya ƙara s0 gurin mai martaba sarki maleek yana bashi hannu musaba sukayi yana ƙara masa godiya bisa hidima da ɗauwanir jikin nasa  maraji...
Shi kuwa maleek gudu yake kamar zai tashi sama
Kamar a mafarki kamar almara yaga wata ƙatuwar mota tazo tasha gaban sa!, Kuma cikin S0n halaka abinda yake cikin motar dama motar kanta; wannan ƙatuwar mota ta iyo kanshi gadan gadan
Cikin wani irin sauri da jajircewa ta ƙwararrun sojoji ya wani sha kwana ta kan motar nashi!! yana  zaro bindigar sa, dake maƙale jikin wando jikin sa  
Dai-dai tayar motar ya ɗa na harbi ji kake tushh, tayar motar ya fashe  
Su kuwa mutanen cikin motar ganin an harbi tayar sune yasasu fito da nasu muggan  makaman nan suka, fara musayar wuta,  a tsakanin su 
*******
Ganin hakan bazai kaisu bane yasasu fitowa suka tunkaro motar maleek ɗin duk kuwa da uban harbin da yake zubawa 
Tifffff sukaji harbin ya kuma tsaya kamar sauƙar ruwa da ɗaukewarsa haka abin yafaru' maleek kuwa ganin babu bullet  nashi ya zubar dukka 
Yasa shi dirowa daga cikin motar nashi, shima ya shiga tunkararsu.....nan aka fara kabta uban faɗa tsakanin ƴan ta adda da maleek  cikin baiwar da Allah ya bashi nan da nan yagama da mutanan, nan  ya kamesu yashigar dasu cikin motar sa yajaaaa yayi gaba dasu!!!!!
Gaba ɗayansu sun gama galabaita dan haka babu mai ko iya cira hannu a cikin su 
Cikin gidan da ya ajje Kashim baba kai tsaye ya nufa saidai wani ɓangare na daban ya nufa bana kashim baban ba
Loƙacin daya shiga yayi yayi daidai loƙacin  da aka ƙira wayan shi ringing ɗin ammeyn shi dayaji ne yasa shi tsayawa cakkk
Cikin azama ya ciro wayan nashi daga gefen aljihun sa kana yakatse ƙiran ammeyn nashi ya tafi wani ƙiran nata kai tsay,.....cikin tashin hankali da kiɗima haɗi da gunjin kuka mahaifiyar tashi tashiga faɗin....
"Kana ina kazo sun kashe mana alhaji! sun kashe mana shi MALEEK "
cike da tsananin razana maleek yasaki wayar hannunsa yana kaiwa ƙasa  mai kuma ya tuna cikin abinda bai wuce mintina uku ba yafice a gidan baki ɗaya....
Yana cikin sharara uban gudu ne yakuma jin rurin wayar shin cikin zafin zuciya ya ɗaga ƙiran,......
wata iriyar dariya  yaji an kece da ita kana kuma aka shiga faɗin nasan ya zuwa yanzun kana cike da tashin hankali na  mutuwar mahaifinka
 tunda kai ka tserewa mutuwar taka ayau,!!!!
Cikin ƙara ji haɗi da kasheɗi yashiga 
"Faɗin zakuyi dana sanin sanin MALEEK TAUFIQ a cikin rayuwarku"
"Domin kuwa saina zamewa rayuwarku annoba mara  kar̃ewa harya zuwa numfashin ku na ƙarshe"
"Sannan idan har tsageranci naku yakai tsageranci"
"Kufus kanceni gaba da gaba nidaku mu gwabzaa"
Kitttttt yakashe wayar shi baki ɗaya 
Darect cikin asbitin da ammeyn shi ta faɗa mishi ya nufa, yana zuwa ummita dake jikin ammey ce ta,  taho da gudu  ta ɗane jikinsa tana fashewa da kuka,...yaa yaa kagansu k0 suna S0n kashe maka abbeyn mu k0 yaa yaa; kan yarinyar yashiga shafawa  yana ɗora kanta saman ƙirjinsa , a haka ya ƙara sa  gaban momma da Ammeyn shi  
Yana zuwa Mommah ta kuma fashe da kuka tana  faɗin basu kashe shi baa MALEEK 
Da sauran ransa Allah yayi yana da sauran kwana ' a duniya kashiga kaga mahaifinka maleek!!
Mommah ta faɗa tana jan sheshsheka  
Cikin azama da ƙwarin gwiwa najin mahaifin nasa mai mutu baa nee  yasa shi nufar emagency r00m ɗin da abbeyn nashi yake a ciki 
Ita kuwa Ammey k0 bakin maganar ma bata gani ba sai jan numfashi kawai da take sauƙewa akai akai
Turussss yaja ya tsaya loqacin dayaga mahaifinsa gaba ɗaya ko ina na jikinsa jone da na'urori 
Muje zuwa yanxun kuwa wasan zai fara 
*Domin muggun yanxu ne zasu, samu kutsawa cikin rayuwar MALEEK TAUFIQ*
Takuce dai ammeyn laylah
Muhaɗe a page na gaba 
Yawan comments yawan typing naku 
Ina alfahari daku haƙiƙa basu bani goyon baya da masu bani ƙwarin gwiwa a koda yaushe
*MIRRAH ✨ bata da bakin gode muku masoya littafin 🔥❤️ KAREN BANA ❤️🔥👏🏻🙏🏻🙏🏻*
Saidai nace ilahu yabar ƙauna ta har abada nagode*🔥❤️ KAREN BANA ❤️🔥*
NA MARYAM NASEER MIRRAH ✨
*Ammey laylah 🫶🏻💔*
FREE BOOK
Page 1️⃣5️⃣
081-04-49-32-15
*Do good for others it will come back to you on unexpected time🙏🏻🙏🏻*
_______Saurin dafe jikin glasses ɗin yayi da kuma wani irin sauri ya fice a asbitin baki ɗaya 
Kan kace meye gaba ɗaya asibiti ya cika da ƴan uwaa da abokan arziƙi  shima mai martaba sarkin Kano maleek ibn suffyan ya biyo jirgi zuwa abuja, dandanan labarin harya karaɗe Social media  ta ko ta ina labarin mummunan accident ɗin da alhaji TAUFIQ majeed ake 
Kai tsaye maleek gidansa na sirri da babu mahalukin da babu wanda yasan da zaman sa yanufa cikin zafin zuciya da tururi









