Showing 27001 words to 30000 words out of 55707 words

Chapter 10 - NACINA YA JAWO MIN book1 by Narrnarhh Bukar.docx.txt

31 May 2024

8057

tsoro Maman jummalo? "


Maman Jummalo shiru tayi tana nazari tare da tunanin yanda za'a ɓoye kwalbar ta yadda babu abinda zai sameta,bayan ta gama tunani sannan ta ce


" Mai zai hana tunda yanzu baki da yara duk sunyi aure,ki ɗau kwalbar kisata cikin akwati ƙarami saiki saka a ƙarƙashin gadonki,koya kike ce ƙawas? "


"Haka za'ayi kuwa ƙawas,yanzu dai mu wuce gida ma kammala zancen a can kar a samu matsala don ni tsoro nakeji "


"Haba ƙawas kin cika tsoro wallahi,kidai kula da kwalbar sosai"


Haka suka doshi hanyar garinsu wanda basu suka iso gida sai wajan magrib kasancewar layin da suka bi wurin ganin boka Sankeru wanda a da babu layi saidai kawai ka shiga yanzu saida tabi layin kafin ta samu shiga ciki.


Kamar yadda Maman Jummalo ta bawa Umma Kande shawara akan tasa kwalbar a cikin ƙaramin akwati sannan tasa a ƙasan gadonta haka tayi.Kuma tun daga wannan lokacin kuma a ranar Abban Sa'eeda ya ƙara rikicewa tare da juyawa su Umman Sa'eeda baya haɗi da musguna musu sosai.


Tun a ranar da Umma Kande tazo da kwalbar gidan,abubuwa suka ƙara rincaɓewa,don saida ya kusa dukan Sa'eeda ba tare da tamishi laifi ba,kuma abinda ma baita taba yi ba a baya,yana faɗa tare da zage-zagen da babu dalili haka nan daga shigowarsa gidan kaar yaji a duniya ya tsani ya buɗe ido yaga su Umman Sa'eeda tare da ita Sa'eeda,ji yake kamar ya koresu daga gidan ko zuciyarsa zatayi sanyi.


Ranar Umman Sa'eeda da Sa'eeda sunyi kuka iya kuka a ɗaki babu mai basu haƙuri ko tausaya musu,abinda bai taɓa musu ba a baya duk da a lokacin hankalinsa ba a kansu yake amma bai taɓa musu irin cin mutunci da wulaƙanci kamar na wannan ranar ba.


Umma Kande da Maman Jummalo daɗi kamar ya kashesu saboda abin baita taɓa yima su Umman Sa'eeda ba yau yayi musu wato wulaƙantasu,ita Umma Kande wallahi taso a ce ya kore su Umman Sa'eeda daga gidan,shikenan sun yada ƙwallan mangoro su huta da ƙuda.(Kai kai kai wannan baƙin kishi haka,Allah karka bamu irin wannan zuciyar mai baƙin kishi da hassada🤔🤔🤔)


@@@@@@@@@@


Wai ina amare?




Bangaren Jummalo tun sanda aka kaita gidan mijinta ta soma cin karo da ƙunci haɗe da baƙin ciki tun a daran farkonta.Kamar yadda a al'adar malam bahaushe take,a duk sanda aka kai budurwa ko bazawara ɗakin mijinta,Ango yana zuwa da kaza tare da drinks don raya daren cikin farin ciki da annashuwa tare da amaryarsa.


Amma Jummalo bata samu wannan farin ciki ba saidai ma Angon ya shigo mata ɗaki a bige,ya sha giya yayi tatil sai sumbatu yake tare da jayo duk abinda ya gani ya bugashi a ƙasa yana surutai marasa ma'ana,ita kuma lokacin tana kan gado an lullubeta da mayafi babba,jin surutai da jefe jefen kaya ya sata tayi saurin fitowa daga bedroom ɗin a firgice haɗi da tsoro,fitowarta falo taga abinda ya kusa zautar mata da ƙwaƙwalwa tare da birkita mata lissafi,wai yau da zai kasance ranar farin cikinta,ranar da take so da ganin Allah ya kaita lokacin amma sai yaza mata a matsayin ranar baƙin ciki mara misaltuwa,ace angonta yazo mata ɗaki a bige,wannan wani irin ƙaddara ne,wani irin tashin hankali ne haka.Jin motsi Ibrahim angon nata yayi saurin duban wajan,haba kamar an tsikareshi ya nufota gadan-gadan yana huci kamar wani kurcin maciji tare da ɗaukar abu a hannunsa saikace yaga abokin hamayyarsa.


"Bbbanna kiraki tun ɗazo ba,amma sai yanzu kkkika ga ddammann zuwa ehe!!! Sssaboda ni ni ɗanki ne ko!!! Kkkaruwa,shegiya mayyar mmmaza kawai"


Jummalo da take tsakanin falo da bedroom tayi saurin juyawa tare da rugawa toilet a guje haɗe da saka key,ganin akwai abu a hannunsa kuma kanta yawo tare da surutai wanda bama fahimtar me yake cewa take ba.Kamar kuwa ta sani kanta yayo,tsayawa wurin ƙofar toilet ɗin yayi tare da bubbugawa haɗi da faɗin


"Ki buɗe na ce!!!,madara da kaza zan baki,ki buɗe! Ki buɗe mmana Jummalota,tawan taaawan...."


Bai ƙarasa da zancan ba ya fara kwararo amai babu ƙakƙautawa,mai uban wari da ɗoyi sai kace mushe.Jummalo dake a toilet ta fashe da matsanancin kuka a ranta tana faɗin 'Yanzu a daren farkona a ɗakin mijina nake fuskantar wannan baƙin cikin,meyasa na biyewa mamata ne da Umma Kande akan saina aure mai kuɗi kaicona ni Jummalo,gashi tun kan aje ko'ina,a daren farkona na fara fuskantar bacin rai da damuwa,kaicona da biyewa mamana akan dole saina aura mai kuɗi,gashi yanxu na aura mai kuɗin amma babu kwanciyar hankali tana zancen zuci a lokaci guda tana kuka.(Hausawa suka ce kwaɗayi mabuɗin wahala😁😁😁,gashi tun a daren farkonki kin fara fuskantar baƙin ciki,Allah ka tsare mana imaninmu 🤔🤔🤔)


Shiru taji ɗakin yayi,a tunaninta ko yafita ne,a hankali da buɗe toilet ɗin,ta fito da sanɗa,taka ƙafar da zatayi a ƙasa sai taji ƙafarta ta tako wani abu mai yauƙi yauƙi,da sauri ta ɗaga ƙafarta haɗi da duba wajen,ai ba arziƙi ta toshe hancinta da mayafinta jin wani wari ya taso kamar mushe tare da duban mijin nata a gefe yana ta sharɓar baccinsa hankalinsa kwance,ko'ina na wurin ƙofar toilet ɗin duk ya ɓaci da amai,da sauri da yaye mayafin nata tare da cillashi kan gado sannan ta koma toilet ɗin,ruwa ta zubo a bucket saita saka dettol haɗe da omo sannan ta ɗauko mopper ta fito.


Tana kuka tana mopping ɗin aman,saida ta goge wurin tsaf sannan ta saka air freshner a ɗakin lungu da sako sannan ta cire kayanta ta saka na bacci tayi kwanciyarta haɗe ta tunani iri iri wanda ya sata kasa bacci da wuri,sai wajan 2:12am bacci ɓarawo yayi awan gaba da ita.


Da safe kuma ita ta rigashi farkawa,still yana nan a wurin yana bacci abinsa,ɗauro alwala tayi don yin sallar Subhi duk da gari yayi haske tar haka tayi sallarta kasancewar ko a gida sai wurin 9:00am suke yin sallar subhi wani lokacin ma bayi suke ba harda iyayen nasu.


Sai wurin 10:39am ya farka haɗe da miƙa babu salati babu adduar tashi daga bacci ya wuce toilet direct, wanka yayi sannan ya fito yasa kaya,a lokacin da yake saka kaya ne Jummalo ta shigo cikin bedroom ɗin tare da sallama,amsawa yayi babu yabo babu fallasa.Wuri ta samu a gefan gado ta zauna,saida ya kammala shirinsa tsaf sannan ta dubeshi hade da yi mishi maganar abinda ya faru jiya da daddare,har complain din rashin kawo mata kazar amarci da yayi duk saida ta fadama masa.


Tunda ta fara magana yake kallonta sheƙeƙe,a ransa yana faɗin 'Wai mai wannan yarinyar take dashi a jiki ne da ya sakani nace dole saina aureta,ko fasali bata dashi,mtwsss' saida ta kammala ƙofarinta sannan ya fara magana cike da izgilanci.


"Ke! Ni sa'arki ne da zaki dinga min magana irin haka,to indai shan giya ne kike ma wannan ƙorafin to yanzu na fara ke banda ma shan giya har ƴan mata inna gadama zan kawosu gidan nan muyi yadda mukeso babu abinda zaki iya saboda gidana ne inada iko dashi,don haka karki sake min magana akan shan giya na,is my choice so you can't change me,ok"


Shiru tayi a zuciya tana faɗin 'Ni Jummalo na ɗebo ruwan dafa kaina da kaina.


Haka dai rayuwar Jummalo ta cigaba da tafiya a gidan mijinta duk da bata taɓa faɗawa mamanta ba don kar hankalinta ya tashi,gashi ko nan da can ya hanata fita,kullum cikin ɗibo ƴan matansa yake kala kala,kuma buba abinda ta isa tayi.Duk da bai hana ci da sha amma fa wani lokacin har duka yake mata idan ƴan iskan nasa suka motsa.Wanan kenan.


@@@@@@@@@@@@


Ɓangaren Zaliha kuwa sai dai in ce gwara Jummalo so dubu akan nata zaman auran.A sanda aka kaita gidan mijinta bayan kowa ya wuce,angon ya shigo ɗakin nata babu sallama lokacin ita ma kamar Jummalo an lulluɓeta da mayafi,zama yayi kusa da ita baice mata komai ba,can sai taji abu na mata waiwayi a jiki,da sauri ta yaye mayafin nata takai duba gun inda abun yake.


Wani irin ihu ta saki tare da ƙanƙame mijin nata tana tura fuskarta cikin ƙirjinsa duk ilahirin jiki yana rawa,shi kuma mijin nata kunnanta ya lalubo ya fara magana.


"Ɗayan mijin naki kike gudu ummmm Zaliha,shima yazo angonci ne haɗe da kazarsa"


A razane ta ɗago kanta tare da fashewa da matsanancin kuka, tana kukan ta fara magana


"Na shiga uku ni Zaliha!!! Wayyo ni!!! Wayyo ni!!! Don Allah ka fitarmin dashi,wallahi ina matuƙar tsoransa,na roƙeka da Allah"


"Mijin naki kike tsoro kuma"


"Don Allah ka cireminshi daga kan gadon nan"


Ƙara ƙanƙameshi take tare da runtse idanunta da ƙarfi


"Wallahi babu inda zaije Zaliha,kamar yanda kowani ango yake angoncewa a daren farkonsa tare da amaryarsa to haka shima zai angon ce dake"


"Niii!!! Kana nufin da...................












Mu haɗu a pages na gaba My Esteem Fans,domin tafiyar ta fara ɗaukar🔥🔥🔥🤗🤗🤗🙃🙃🙃🏵️🏵️🏵️🌹🌹🌹💝💝💝💖💖💖










****Hmmmmm🤔🤔🤔,ita kuwa Zaliha da wani abu ne zata angon ce haka gashi tana tsoransa??? Dama maza biyu ne ta aure ba ɗaya ba??? kai kai kai gaskiya da alama ita ma ta ɗebo ruwan dafa kanta da kanta😁😁🙃🙃🏵️.






***Shin a tunaninku Umma Kande tayi kyakkyawan ajiya ga kwalbar da boka Sankeru yabata kuwa???




Ku biyoni don jin amsoshinku a pages masu zuwa🔥🔥🔥




Ina matuƙar alfahari daku My Esteem Fans,taku har kullum Narrnarhh Bukar✍️✍️✍️ 🤗🤗🤗




Ku cigaba da zubo ruwan comments🤗🤗🤗🤗🤗🌹🌹🌹🌹🏵️🏵️ni kuma bazan gaji ba wurin sambaɗo muku new updates wanda zai nishaɗantar daku tare da fadakar daku haɗi da wa'azantar daku🤗🤗🤗🤗🙃🙃🙃🏵️🏵️🏵️🌹🌹🌹🔥🔥🔥








I love y'll My Esteem special fans,ina alfarahi daku sosai,Allah yabar ƙauna 🤗🤗🙃🙃🙃🏵️🏵️🌹🌹🌹










Daga alƙalamin
🖍️📚Narrnarhh Bukar 📚🖍️


Comments and share 🙏🙏🙏Fisabilillah.
[4/25, 1:38 PM] +234 814 129 2044: 🏵️ NACINA YAJAWOMIN🏵️







Narrnarhh Bukar✍️






🌹Perfect Essential Writer's
Association🌹
✨ P. E. W. A✨






Wattpad:@AISHAABUBAKAR812
Arewabook:@Narrnarhh002










Masu telegram zaku iya following ɗina ta wannan link ɗin🤗,🙃🏵️👇👇👇
https://t.me/+439Pdx2UbLZlOTNk










2⃣5⃣----2⃣6⃣










"Wallahi babu inda zaije,kamar yanda kowani ango yake angoncewa a daren farkonsa to haka shima zaiyi dake"


"Kana nufin da wannan ƙasurgumin macijin zan angon ce dashi yau ba dakai ba? "


"Sosai ma kuwa,ai daman shi naje nema ma auran bani ba,ko kin zaci ni ne angon?"


"Innalillahi Wa'inna ilaihi Raji'un,na shiga uku na lalace ni Zaliha,Don Allah kace wasa kakeyi ba da gaske ba,kace mafarki nake ba'a zahiri ba,na roƙeka da Allah Ubangijin halittu kace wasa kakeyi,Shikenan ni Zaliha na kawo kaina ga halaka,wayyo Allah ni Zaliha!!! Wayyo Allah na!!! Na shiga uku na lalace!!! "




Kuka takeyi harda majina,ji take kamar a mafarki hakan take faruwa da ita,ina zata kai wannan ƙasurgumin macijin mai girman gaske,ita fa tunda take bata taɓa ganin maciji kamarsa ba.




"Wasa! Wasa!! Wasa!!! hhhhhhh!!!! Lallai ma yarinya,kinga na miki kama da mai tatsuniya ne,ko ko mai wasan kwaikwayo ne ehhh!!! "




"Na shiga uku ni Zaliha na lalace,wayyo mamana Don Allah ka rufamin asiri kace wasa ne"


"Ke!!! Baki shiga uku ba yanzu zaki shiga uku yarinya kuma dole sai ya lashi gabanki kullum,sannan kisani babu ke babu fita a gidan nan,kin riga da kin shigo,don irin ku nake nema ruwa ijallo,sai gashi na haɗu dake,sannan an tabbatarmin kece sauran cikon ɗaukaka tare da arziƙin da ya rage nayi,na aure mata ɗaiɗai har 29,saura ɗaya su cika 30 kamar yadda dodona ya bayyanamin saura ɗaya,shiyasa farkon ganinki da nayi dodona ya tabbatarmin da kece cikon na 30 ɗin,sannan kisa a ranki mutuwarki tazo kuma a ƙasƙan ce domin bazaki taɓa kuɓuta daga hannuna ba,son kuɗi da dogon burinki zai zamo ajalinki Zaliha!!! Hhhhhhhhhhhhhhhhh!!!"




Kamar a marfarki Zaliha take jin wannan zancen,maganar zuci ta fara 'yau ita ce da wannan ƙaddarar aurar ɗan mafiya kai bama ɗan mafiya ba mai aiki da dodo ,mamana da maman Jummalo sun ja min wahala,kaicona ni Zaliha,kaicona da biyewa ruɗin duniya mai ƙarewa,garin kwaɗayina da son abin duniya na jefa kaina ga halaka,na rasu ni Zaliha,na mutu na lalace,daman ance kwaɗayi mabuɗin wahala yau gashi ya tabbata a kaina,wayyo wayoo' tana cikin wannan zancen zucin ya katseta da cewa




"Kashe dinki Zaliha! Idan naji daidai da rana ɗaya kin sanar ma wani ko iyayanki ne akan wannan mijin naki to ki tabbata a ranar mutuwa ki tazo kenan,kuma dole ya lashi gabanki ko kinƙi ko kinso,tunda auran kuɗi kikayi,kuma gashi kin masu kuɗin ,iyayenki ma sun samu musamman mamarki mai kama da dumɓaru,shegiya mayyar kuɗi,kunci kuɗina kuma dole in samu abinda nakeso wurinki Zaliha! Hhhhhhhh!!!"




"Na haƙura da auran,ka sakeni don Allah,wallahi na haƙura da auran kuma zamu maido maka da kuɗinka Allah,ka yarda dani zamu maido maka komai kuma koda tsinke ne wallahi"


Hannu bibbiyu take haɗawa tana roƙonsa haɗe da magiyar ya saketa ta haƙura da auran,ga hawaye sun kasa tsayawa a idonta,idanunta har sun fara kumbura kasancewar tanada manyan idanu,gashi fuskarta tayi ja sosai saboda kukan da tayi,bleaching ne iya bleaching dole fuska tayi kamar jan ƙosai.(Da sauranki Zaliha badai kuɗi kikeso ba ai gashi nan ki ɗiba iya ɗibarki amma zakici ubanki lakada awaje wallahi😂😂😂).




Dariya ya tintsire dashi harda bubbuga ƙafa,shi kuma kumurcin macijin ya nannaɗe kamar kwando sai kuma ya miƙar da kansa yana fitar da harshensa waje tare da huci,baƙi ne macijin sosai gashi yana da tsawo da kauri kai in taƙaice muku zan iya cewa Anaconda ne saboda girmansa da tsayinsa,kansa babba ne sosai.Sai da yayi dariya mai isarsa kana ya tsagaita tare da dubanta,ita ko jikinta sai rawa yake ga gumi sai ƙara tsuttsubo mata yake a duk ilahirin jikinta.




"Kin makaro yarinya wallahi,kefa da kanki kikace zaki aure ni,kina sona har na biya kuɗin sadakinki dubu ɗari lakadan ba ajalan ba,nayi lefe,sannan a daran farkonki dan na kawo miki angonki tare da kazar amarcinki gasassa sai kice kin fasa auran ai wannan zancen ƙanzon kurege ne ƴan mata,kidai sake tunani Zaliha"




Macijin ya wani fasa kai tare da kai fuskarsa wurin fuskar Zaliha yana kallonta ita kuwa mai zatayi inba sumews ba,a haka mijin nata ya tuɓe ta sannan wannan macijin yayi yanda ya keso da ita.






*TUNATARWA*




****Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un,yake ƴar uwata mai dajara tare da ƙima shin bakya tunani akwai mata dayawa masu shiga irin wannan bala'i kamar yanda Zaliha ta shiga duk saboda son abin duniya,idan a inda kike babu amma kisani a wasu wuraran akwai su da dama.Akwai maza masu kuɗi wanda ba na halal bane,sun sameshi ne ta hanyar haram,kodai ta hanyar sata,ko kidnapping,ko safaran miyagun ƙwayoyi,ko ta hanyar tsafi da shan jini da dai sauransu,sannan irin wa'innan mazajen suna sakarwa mata kuɗi sosai ta yadda zasu ja hankalinsu dana iyayensu wadda a ƙarshe wahala ce zasu shiga.


Kaicon wasu mata masu kwaɗayi da son abin duniya,wallahi musulinci yayi a rayuwa, ki duba ƴar uwata mai dajara hadisin manzon Allah (S.A.W) daya ce''Ana auran mace don abubuwa guda hudu ne,don addininta,arziƙinta,nasabarta,kyawunta amma duk a cikin abubuwan babu abinda ya bada shawara abi illa addini,ya cigaba da cewa "ina baku shawara da ku aure mace mai addini''. Kisani ƴar uwata mai daraja hadisin nan ba ga mata kawai ya tsaya ba a'a harda maza suma hadisin ya shafesu,don auran namiji mai addini amma mara dukiya yafi kwanciyar hankali akan auran namiji mai dukiya amma babu kwanciyar hankali.Allah ya tsare mana imaninmu,ya bamu wadatar zuci ya kuma bamu ikon yin daidai a rayuwarmu****








Cikin Labari






Zaliha ba ita ta farka ba sai wurin 10:02am,a hankali ta buɗe kumburarrun idanunta,da ƙyar ta tashi ta zauna sai ta duba jikinta taga babu kaya,tuno da abinda ya faru jiya da daddare yasa ta fara russan kuka babu ji babu gani,tana da nasanin auran kuɗi,gashi ya mata kashe din karta kuskura da faɗawa wani koda iyayenta ne, tayi da nasanin biyewa mamanta da maman Jummalo akan auran mai kuɗi gashi yanzu tana cikin masifa tare da tashin hankali wanda tasan yanzu zamanta a gidan ya fara.




A sanyaye ta tashi duk jikinta na mata ciwo musamman gabanta,ji take kamar tayi tsarki da barkono saboda zafin da yake mata.Wanka ta shiga tare da gasa jikinka,tana yi tana kuka wannan wace irin musiba ce ta sameta, wace irin ƙaddara ce haka,Allah sarki Sa'eeda haƙiƙa tayi dacen uwa ta gari ba mai son abin duniya irin na mamanta ,gashi yanzu ta biyewa mamata ta aura ɗan mafiya mai aiki da dodo,haka dai tana wanka tana tunanin zuci har ta kammala wankan ta fito,tana cikin shiri ne sai ga mijinta ya shigo babu sallama,sai ya samu wuri ya zauna tare da cewa.




"Amarya bakya laifi ko kin kace ɗan masu gida,to ya baƙunta ya kuma daran farkon naki ya kasance da jarumin angonki duk da ma sume masa kikayi,hhhhhhhhh!!! "




Bata ce dashi ko kanzil ba ta cigaba da abinda takeyi a zuciyarta tana tsine masa tare da adduar Allah ya fitar fa ita daga gidan ko ta naimi yafiyar Ummansu Sa'eeda tare da Sa'eeda domin tasan hakƙinsu ne ya fara bibiyarsu,surutansa ya gama ba tare da tace dashi komai ba ya fita abinsa.




Haka dai rayuwar Zaliha da cigaba da gudana a gidan mazajan nata guda biyu,wanda kullum sai wannan kumurcin macijin ya lashi gabanta tun tana sumewa har ta daina wanda yanzu idonta biyu yake lasar gaban nata babu yadda ta iya sai kuka,gashi yanzu gaban nata wani irin ruwa yake fitarwa mai ɗoyin gaske duk da gashin gabanta da take tare da fesa turare amma haka ruwan yake fita daga gabanta.




A duk sanda su ka yi waya da mamanta,idan ta ce mata akwai matsala saita ce da ita a'a,tuno da kashe din da ya mata akan karta kuskura ta sanarwa mutane,haka dai Zaliha ta cigaba da rayuwa a wannan gida cikin ƙunci da baƙin ciki duk da akwai kayan mo re rayuwa a gidan amma na banza a wurinta,ji take gwara ta aura talakan talaka wanda baida ko sisi akan wannan ƙaddararran auran da takeyi(Allah sarkin daɗi inji ɓarawon takanɗa,haba Zaliha yanzu kuma talakan kikeso,tab ai kin makaro😂😂😂😂😉🙃).




Gashi a gidan babu halin guduwa saboda matakan tsaron da suke a gidan masu tsauri ne,akwai sanda ta taɓa yunƙurin guduwa amma haƙarta ta kasa cimma ruwa saboda mai gadin gidan uban gidan nashi ya mishi kashe din kar ya bari ko nan da can ta fito,kuma haka a kayi,tun daga ranar bata sake yunƙurin guduwa ba saita haƙura tare da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login