Showing 33001 words to 36000 words out of 55707 words

Chapter 12 - NACINA YA JAWO MIN book1 by Narrnarhh Bukar.docx.txt

31 May 2024

8062

to wallahi zansa a koreki daga makarantar nan sai inga uban da zai tsaya miki munafuka,da alama baki san koni wacece ba ,ina ƙara faɗa miki ki kula,idan na sake ji kin aibanta Sa'eeda,hmmmm Wa Rabbul Ka'abah you will regret staying in this school"




Nuna Maryam Iman tayi da yatsa ɗaya tare da cilla mara harara har saida Maryam ta tsorata kasancewar Iman akwai manyan idanu sannan ta wuce abinta ba tare da tabi ta kansu ba.Kowa a wurin shuru yayi har da Maryam saboda sun san mahaifin Iman ƙani ne ga VC wato Vice Chancellor ɗin makarantar ,sannan Uncle ɗinta HOD ne a department of computer science banci yayyinta da suke lecturing a makarantar don haka babu yadda zasuyi da ita dole su shiga taitayinsu.Haka kuwa akayi tun daga ranar idan suna gulmar Sa'eeda da zarar sunga Iman tazo wucewa zasu kamar bakinsu.




Ƙawancan Sa'eeda da Iman ƙara ƙarfi yake,babu laifi Iman akwai ƙoƙari da maida hankali a karatu shiyasa Sa'eeda take ƙaunarta sosai,wanda a yanzu komai tare sukeyi,ko masallaci tare suke zuwa.






Ƴan aji sun rage yima Sa'eeda wulaƙanci haɗi da gulmarta saboda Iman, koda ma zasu mata shegan taka sai in sunga Iman bata nan sannan suke mata iya shege. Wannan kenan






@@@@@@@@@@@@






A ɓangaren soyayyar Sauban da Sa'eeda yanzu dai sai a hankali saboda Sauban ya fara canjawa Sa'eeda daga yadda ta sansa a da zuwa wani Sauban na daban,ba kodayaushe yake kiranta ba sannan koda ya kirata basa tsayawa hira sosai kamar da,bayan haka ya daɗe da dena zuwa gidansu hira,koda Sa'eeda ta mishi magana akan rashin zuwansa sai ya ce abubuwa sun mishi yawa sosai.Kalaman soyayyar da yake mata a da yanzu ya rage in fact ya daina .Haƙiƙa Sa'eeda kwanakin nan bata cikin hankalinta saboda sauyawar da Sauban ya mata kuma idan ta tambayeshi ko ta mishi laifi ne sai ya ce a'a kawai dai yanzu aiki yana riƙesa sosai.






Haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya da daɗi da babu daɗi,ta fannin Sa'eeda kuwa kwata-kwata hankalinta baya jikinta kullum cikin tunanin Sauban take gashi exams ɗinsu na second semester ya kusa,karatun ma da ƙyar take yinsa ba kamar da ba.Ummanta ne ta kula kwana biyu Sa'eeda da sauya kullum shiru sannan karatun da take yawanyi ta rage .




Wata rana a ɗaki suna zaune kasancewar asabar ne dukkansu suna gida,Sa'eeda na zaune akan tabarma ga littafi a gabanta tayi shiru kamar wata mara lafiya da ita.Umman Sa'eeda ta dubeta da kyau sannan ta ce






"Sa'eeda, wai meke damunki ne kwana biyu duk kin susu ce kamar wata mara lafiya,saidai ki zauna kina tunani,gashi kin daina karatu kamar da kuma kinsan exams ɗinku ya kusa,karki ɓoyemin komai,meke damunki Sa'eeda? "




Shiru Sa'eeda tayi tana tunanin kota faɗama Ummanta ne sauyawan Sauban gareta ko kuwa,wata zuciyar ta ce mata kawai ta faɗa mata tunda bata ɓoye mata komai da ya shafi rayuwarta,katse mata tunani Umman Sa'eeda tayi da cewa




"Dake fa nake Sa'eeda"




"Ummm,umm Ummina daman Sauban ne"




"Sauban kuma! Yayi me? "




"Sauban ne.......................


























Mu haɗu a pages na gaba my Esyeem Fans,ina yinku over🤗🤗🤗🙃🙃🙃🌹🌹🌹🏵️🏵️🏵️🌼🌼🌼










****Hausawa suka ce idan wani ya ƙika wani a lokacin zai soka,Sa'eeda dai ta samu aminiya mai sha re kukanta🙃🙃🙃










****Shin me Sauban yake nufi da Sa'eeda ne??? Mai yake ƙullawa a ransa game da Sa'eeda??? Miye dalilin sauyawarsa a gareta???






Ku cigaba da zubo ruwan comments 🤗🤗🙃🙃🌹🌹🏵️🏵️🌼🌼 Ni kuma aradun Allah bazan gaji ba wurin suburbuɗo muku new updates wanda zasu ilmantar,nishaɗantar tare da faɗakar daku In shaa Allah🤗🤗🙃🙃🌹🌹🏵️🏵️🌼🌼💗💗














Daga alƙalamin
🖍️📚Narrnarhh Bukar 📚🖍️


Comments and share 🙏🙏🙏Fisabilillah.
[5/23, 8:09 AM] Narnarhh Bukar: 🏵️ NACINA YAJAWOMIN🏵️









Narrnarhh Bukar✍️










🌹Perfect Essential Writer's
Association🌹
✨ P. E. W. A✨










Wattpad:@AISHAABUBAKAR812
Arewabook:@Narrnarhh002








Masu telegram zaku iya following ɗina ta wannan link ɗin🤗,🙃🏵️👇👇👇
https://t.me/+439Pdx2UbLZlOTNk








Wannan pages ɗin sadaukarwa ne gareku my Esteem Fans,ina sonku,ina ƙaunarku,ina jin daɗin comments ɗinku Allah yabar ƙauna🤗🤗🙃🙃🌹🌹🏵️🏵️🌼🌼














2⃣9⃣----3⃣0⃣










Shiru Sa'eeda tayi tana tunanin kota faɗama Ummanta ne sauyawan da Sauban yayi gareta ko kuwa,wata zuciyar ta ce ta faɗa mata tunda bata ɓoye mata komai da ya shafi rayuwarta,katse mata tunani Umman Sa'eeda tayi da cewa




"Dake fa nake Sa'eeda"


"Ummm umm Ummina daman Sauban ne"


"Sauban kuma! Yayi me? "


"Sauban yanzu baya sona Ummina,bansan me nayi masa ba,yanzu ko kirana ya dena yi "


Fuskarta da matsanancin damuwa take sanarwa Ummanta rashin kulawar Sauban a gareta kwana biyun nan ba kamar da ba,Ummanta dake saurararta ta ce


"Yanzu akan Sauban ne duk hankalinki ya tashi kika kasa karatu Sa'eeda, saboda kwana biyu ya sauya miki shi kenan kuma saiki canja daga yadda nasanki Sa'eeda, akan soyayya kike tada hankalinki"


Shiru Sa'eeda tayi tana sauraran Ummanta, jin faɗan da take mata,baza ta gane soyayya ba,batasan yadda take mutuwar so da ƙaunar Sauban bane wanda take ji bazata iya rayuwa babu shi ba,kaunarshi ta riga da gama zama jinin jikinta,zata iya komai saboda ƙaunar da take mishi.


Sa'eeda tasha faɗa sosai wurin Ummanta wanda daga ƙarshe sai ta bita da nasiha ta cewa


"Sa'eeda idan zaki so mutum,ki soshi ba dayawa ba sannan idan zaki ƙi mutum ki ƙishi ba dayawa ba saboda yanayin rayuwa,mutum yakan canja a kowani lokaci,na daɗe da sanin kina ma Sauban so wanda ya zarce ƙa'ida Sa'eeda shi yasa daga sauyawarsa gareki har hankalinki ya tashi,ki dawo cikin hayyacinki Sa'eeda,ina alƙawarin da kikamin akan maida hankalinki kacokar a karatunki Sa'eeda, ina yake ko soyayya ta rufe miki idanu yanzu ko "


Tabbas ko ba'a faɗa ba nasihar Umman Sa'eeda ta ratsa Sa'eeda sosai ganin yadda jikinta yayi sanyi.


"In shaa Allah zan cika miki alƙawarin da na ɗauka akan maida hankalina akan karatuna sosai sannan kuma zan rage tunanin Sauban a zuciyata duk da bani na ɗaurawa kaina ba"


"Hakan yanada kyau,Allah ya miki albarka ya kuma shige miki gaba a al'amuranki gaba ɗaya"


"Ameen Ameen Ummina"


Haka suka cigaba da hirarsu,Umman Sa'eeda na ƙara nusar da Sa'eeda akan abubuwa da dama.


Sa'eeda ta rage tunanin Sauban sannan ta maida hankalinta a karatunta sosai kasancewar exams ɗinsa na second semester 200 level baifi 1week ba,haka tayita karatu babu ji babu gani har sukayi exams ɗinsu cikin nasara da aminci sannan aka sabu hutu.


Duk da alƙawarin da Sa'eeda tama Ummanta akan rage tunanin Sauban amma ina zuciya bata da ƙashi,haka zaka ganta a class tayi shiru a lokacin kafin suyi exams,wani lokacin ma koda akwai littafi a gabanta haka take kasancewa,ƙawarta Iman tasha tambayarta meke damunta kwana biyu kodai bata da lafiya ne amma amsar ita ce a'a,daga ƙarshe Iman ta fara fushi da ita wai tana aminiyarta amma ta kasa sanar mata da damuwarta alhalin fuskarta ta nuna ƙarara damuwa fal a cikinta,ganin ran Iman ya ɓaci ne yasa Sa'eeda sanar ma Iman a kan halin da take ciki game da Sauban don yanzu kota kirashi baya picking wani lokacin ma number busy yake danna mata.(Maza maza hmmm abarsu kawai da halinsu🤔🤔🤔).




A gaskiya ran Iman ya ɓaci sosai jin wannan wulaƙancin da Sauban yake ma Sa'eedarta duk da bata taɓa ganinsa ba amma lokaci guda tsanarsa ta shiga ranta.Haƙiƙa Iman aminiyar kirki ce mai hankali da hangen nesa,sosai tayi ta ba Sa'eeda haƙuri tare da shawara akan kawai da rabu dashi don yaga tana mutuwar so da ƙaunarsa ne yasa yake mata wulaƙanci amma idan zata iya kawai ta fita daga harkarshi ko don karatunta kar ya samu matsala,haka Iman tayi ta ba Sa'eeda haƙuri tare da nusar da ita abubuwa da yawa a rayuwa kasancewar Iman tasan kan rayuwa sosai.Wannan kenan




@@@@@@@@@@@@@




BACK TO SCHOOL






Maa shaa Allah yanzu su Sa'eeda suna a shekarar ta kusa da ƙarshe wato 300 Level,farin ciki fal a ran ƴan aji saboda sun kusa zama graduate nan da shekara ɗaya,kamar yadda aka saba,satin farko ba'a wani lectures sosai sai sati na biyu,a sannan ne lectures ya fara zafi sosai kasancewar suna a advance class ne sannan level ɗin da yafi kowani level wahala musamman a University.




Sa'eeda ta rage son Sauban a ranta tare da fawwala ma Ubangijin talikai lammuranta sannan ta maida hankali sosai a karatunta kasancewar yanzu lectures ya ɗau zafi sosai,tare da Iman suke karatu abinsu.




A haka result ɗinsu na second semester na 200 level ya fito,Alhamdulillah Sa'eeda kamar yadda ta saba ita ce overall ɗinsu duk da current Gp ɗinta ya sauka saboda tunani da tasa a ranta amma duk da haka ta kasance jagaba a ajin nasu,Itama Iman result ɗinta yayi kyau sosai,amma squad ɗinsu Maryam sai a hankali wasunsu ma harda carryovers,Maryam dai Allah ya tsallakar da ita bata da carryover.
Haka suka cigaba da karatu a first semester na 300 level wanda yanzu suna gab da fara exams kuma daga shi zasu tafi IT na tsawan wata shida sai kuma sannan su shiga final year wato 400 level.Wannan kenan






@@@@@@@@@@@@


Bayan sati ɗaya da fitowar results




Sa'eeda ce ke zaune a seat ɗinta ita kaɗai kasancewar yau Iman batazo school ba suna da biki a faliminsu,hakan yasata duba wasu handout ɗinta kafin lecturer ya shigo aji,tana a zaunan kawai taga an ɗaura mata wani envelope me ɗauke da flowers akan handout ɗin da take karatu a saman desk,ɗago kanta tayi tana duban wacca ta ɗaura mata envelope ɗin ba tare da yi mata magana ba.




"Lafiya babu magana sai ajiye envelope ba tare da magana ba"


Ƙawar Maryam ce da suke zama tare tunda daga 100 level har zuwa yanzu da suke a 300 level suna zama tare,aminiyarta ce yanzu ta ƙut da ƙut.


"Lafiya lau Sa'eeda kasancewar bakisan da auran Maryam bane yasa mukaga ya dace kema ayi inviting ɗinki don bikin baifi saura sati biyu ba,kinga kenan kafin muyi exams ne,shi yasa na baki katin gayyata "


Shiru Sa'eeda tayi tana mamakin Maryam a ce suna ƙawaye amma ta kasa sanar mata da bikinta sai a wajen wasu wa'inda a nan ta haɗu dasu,sune zasu gayya ce ta ,haba hakan ba daidai bane hasalima ita ya dace a ce take rabawa ƴan aji invitation card ba wasu ba, Rahma ce ta katse mata tunani da cewa


"Baki duba card ɗin ba"


"No karki damu zan duba ai"


Maryam ce ta shigo class ɗin tana wani taku da takalminta mai tsini,ji kake ɗas! ɗas! ɗas! kowa na ajin ya juyo kasancewar Maryam latti tayo lecturer sun san yana hanya.


"Amaryar 2 weeks"


cewar wata daga cikin ƴan ajin,Maryam ko sai murmushi take zubawa tana wani ɗadɗaga kai.


"Mrs Sauban in 2 weeks coming "


Cewar Rahma da a lokacin take wurin seat ɗin Sa'eeda. kamar mashi Sa'eeda taji an caka mata a ƙahon zuciyarta zaro ido tayi tana cewa


"Mai naji kinje Rahma,Mrs Sauban? Wani Sauban kenan"


"Keda ga invitation card a gabanki ai ba sai kinya tambaya ba,sai ki duba ki gani wani Sauban ne malama Sa'eeda"


Maryam da tazo wucewa ta side ɗinsu ta tsaya jin abinda Sa'eeda take cewa,a zuciyarta ta ce 'Yau akwai ƙaramin hauka a ajin nan kuwa'. Sai kuma ta fasa zuwa wurin seat ɗinsu taja gefe da tsaya tana kallon yadda Sa'eeda ta wani daburce tana kici-kicin buɗe invitation card.Miƙewa Sa'eeda tayi da sauri tana zaro ido tare da cewa


"What! Me zan gani yau anya ba mafarki nake ba ni Sa'eeda"


Duk ta ru ɗe,jikinta sai rawa yake kana ganinta kasan a rikice take,ƴan aji kowa yakai dubansa gun Sa'eeda.


"Ba mafarki kike ba Sa'eeda tabbas abinda kika gani haka yake"


Cewar Rahma da take kusa da ita tana cilla mata harara,ita daman tun a 100 level ta tsani Sa'eeda kasancewar duk tafi ƴan ajinsu kyau da ilimi ga uwa uba natsuwa,shi yasa tayi duk yadda tayi ta raba Sa'eeda da Maryam hasalima ita ce ta cigaba da bawa Maryam shawarar ta auri Sauban tunda tana sonshi sosai duk dan ta ƙuntata ma Sa'eeda saboda ta gano tana mutuwar sonsa ganin yadda Maryam take yawan basu labari idan Sa'eeda ta bata labarin Sauban,duk da itama Maryam akwai shirin da suke akan Sauban ɗin ita da Mom ɗinta, bayan haka Rahma ce tabawa Maryam shawarar ta dena tafiya gida tare da Sa'eeda kar ta shafa mata baƙin jini gun samari aƙi sonta tunda ita kadai samari suke ma magana banda Maryam,haka kuwa akayi don ta aminta da Rahma sosai kuma tana jinta a ranta.




"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un!!!,Allahumma La Sahla Illama Ja'altahu Sahla Wa'anta zaja'alul Hujni iza shi'ita Sahla!!!"




Abinda Sa'eeda take ta furtawa hawaye na gangarowa bisa kuncinta ba tare da gogesu ba,zuciyarta wani zafi yake mata wanda tunda uwarta ta haifeta bata taɓa jin irinsa ba,ga gumi na tsuttsubo mata a koshinta sai kace mai zazzabi.Duban Maryam tayi idonta cike da hawaye ta fara magana cikin murya mai rauni


"Maryam yanzu abinda zakimin kenan,cin amanata zakiyi ki auri saurayi na bayan kinsan ina sonsa,sannan kinfi kowa sanin alaƙata dashi mai ƙarfi ce kuma akwai maganar aure a tsakanin mu,mai nayi miki Maryam dana cancanci irin wannan muguwar sakayya,mai nayi miki Maryam, Why Maryam! why!! why!!!..."




Haba sai ta fashe da matsanancin kuka mai tsuma rai ba tare da ta gama maganar.Maryam da Rahma kallon junansu sukayi tare da taɓe baki irin ko a jikinsu kukan da take yi.ƴan aji kowa ya bar abinda yakeyi sun natsu tare da sauraron abinda ke faruwa,wasu ma har da miƙewa duk don suji gulmar dakyau.(ƴan aji akwai gulma😂😂😂)




"Maryam mai yasa kika yaudare ni keda Sauban, me yasa kinsan kina sonsa tun farko baki sanar min ba,ni mai iya bar miki shi ne,amma sai yanzu da na shaƙu dashi,ina sonsa shi ne kuka munafurceni Maryam"


Kukan nata sai ƙara ƙarfi yake saboda tanada raunin zuciya abu kaɗan ke sakata kuka,tana kukan sai kuma ta cigaba ta maganarta duk da ba sosai ake gane maganar ba saboda kukan da takeyi.


"Maryam mai nayi miki haka,mai na shige miki a rayuwa, babu abinda nake ɓoye miki na game da rayuwata duk saboda yarda da amintar da nayi dake ashe aaaashe........"




Nan ma kukan ta sake fashewa dashi tuno sirrika da dama da ta sanarwa Maryam wanda ya shafi rayuwarta ita da Ummanta ,haƙiƙa tayi kuskure babba a rayuwarta kuma yanzu ta tuno da maganar Iman da ta ce ' Ba'a yarda da mutum ɗari bisa ɗari,saboda yakan iya canjawa a kowani lokaci'.


Sai a yanzu Maryam ta samu damar yin magana cike da izza da taƙama take maganar.


"Naji duk abinda kika ce Sa'eeda, amma na taɓa cewa ki faɗamin sirrinki ne ko ko na taɓa tambayarki akan dole sai kin faɗamin sirrinki,ni ba yaudararki nayi ba saboda shi ya ce yana sona bani nakai kaina ba da zakizo kina min wani gani-gani ba ehehh! "


Tana maganar tana wani juye idanunta haɗe da murguɗa baki.






Waiwaye








Abinda Sa'eeda bata sani ba shi ne,tun ranar da suka haɗu da Sauban, Maryam ta mutu akansa hasalima ita a tunaninta da farko ita yakeso sai kuma daga baya taga Sa'eeda ce yakeso,wannan abu ya ɓatama Maryam rai matuƙa ainun.tunda taji ya ce yanason ta bashi aron Sa'eeda ta tsinke da lamarinsa kenan duk surutun da take mishi yana kulata duk ba ita yake so ba?.




Bayan Sauban ya wuce ita da Sa'eeda kowa yabi hanyar gidansu,da kuka ta shiga parlonsu inda ta samu mom ɗinta da wata yayar mom ɗinta suna hirarsu kice da annanshuwa,kawai sukaji an banko ƙofar ɗaki babu sallama, Maryam suka gani fuskarta jiƙe da hawaye alamun kuka tayi,duk a tare suka ce




"Lafiya Maryam! "




Bata basu amsa ba ta faɗa jikin Mom ɗinta haɗe da sake fashewa a wani matsanancin kuka,duk ta ruɗasu ,yayar Mom ta matso kusa dasu tana tambayar Maryam lafiya mai ya sameta ,shiru babu amsa sai kuka,saida ta gaji don kanta ta fara basu labari cikin shasshekar kuka da jan majina


"Mom inason sonsa,shi kuma Sa'eeda yake so Mom,ya zanyi da rayuwata wallahi ina sonsa,zan iya mutuwa idan ban auresa ba Mom help me plsss...."




Bata ƙarasa maganar ba ta ƙara fashewa da kuka,kallon junansu sukayi ita da yayarta cike da mamaki.


"Daman saboda namiji ne kike wannan kukan kamar wani babban abu ya sameki duk kin tada mana da hankali eh Maryam"


Cewar yayar Mom ɗinta,ita dai Mom kallon ɗiyarta take da mamaki ta kasa magana,yayarta ta ce ta ƙara da cewa


"Wanene shi? "


"Sauban Muhammad Ja'afar Ƙaraye,ya ce shi manager ne a wani kamfanin sarrafa shinkafa"


"Sauban Muhammad ƙaraye,ƙaraye dai da na sani"


Kallonta dukkansu sukayi alamun ƙarin bayani,murmushi tayi tare da cewa


"Indai Sauban ne to sha kuruminki kamar anyi angama kin zama matarsa"


Maryam ce ta kalleta tare da zaro ido alamu mamaki sannan ta ce


"Da gaske Aunty? "


"Sosai ma kuwa,ai mahaifiyar Sauban aminyita ce sosai muna zumunci da ita sosai,kuma tanada kirki,shi Sauban shi ne ɗa na Uku a yaranta"


"Maa shaa Allah,faɗuwa tazo daidai da zama"


Cewar Mom wanda sai yanzu ta fara magana,sai murna Maryam take can kuma ta ce


"Aunty shifa baya sona Sa'eeda yake so,to ya kike ganin zai aureni bayan yasan ni ƙawar Sa'eeda ce"


Tana magana cike da damuwa,ɗan murmusawa Auntyn ta tayi tare da cewa


"Wannan ai mai sauƙi ne Maryam,kissa da makirci zamu haɗa tare da aibanta yarinyar kun Mahaifiyarsa,kinga ai dole tasa ya haƙura da ita,sai kuma na bijiro dake a matsayin ko zai aureki tare da yabonki da kururuta kyaunki"


"Nice Aunty,wannan shawara ce mai kyau,dan tabbas Sa'eeda nada abun ai bantawa saboda a lokacin da muna secondary ta taɓa sanarmin Mamanta batasan danginta ba hasalima a wani ƙauye ne aka tsinci kakarta da mamanta suna garari a tiri wani ya taimaka ya daukosu zuwa gidansa "


"Kenan basuda asali"




"Eh Aunty"


"Kinga kuwa wannan ma hujja ce babba wanda zamu riƙe,shima kansa nasan bazaiso auran mara asali ba balle mamansa da take son surukai masu nasaba,kinga kuwa auransu bazaiyu ba kenan"




"Wannan haka yake,don wallahi na tsani yarinyar nan,gata ƴar talakawa sai shegen kyau da ilimi" ,Cewar Mom.




A ranar suka ƙulla komai akan yadda zasu rushe auran Sa'eeda da Sauban don ya dawo kan Maryam.




Haka kuwa akayi don a lokacin da Auntyn Maryam ta sanarwa maifiysr Sauban rashin asalin Sa'eeda ta ce dole Sauban sai ya fasa auran Sa'eeda, da ya tambayi dalili sai ta sanar masa,haka shima ya ce ya fasa,nan kuma maganar Maryam mahaifiyarsa ta bijiro masa akan ya aureta tafi Sa'eeda komai,a da yaso jajjaya ganin ƙawar Sa'eeda ce amma da mahaiyarsa da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login