Showing 18001 words to 21000 words out of 55707 words
Chapter 7 - NACINA YA JAWO MIN book1 by Narrnarhh Bukar.docx.txt
wanki ne zai biya mana dukkanin buƙatun mu? "
"Hakane Ummina,Allah ya cigaba dayi mana jagora tare da rufa mana asiri duniya da lahira"
Da"Allahumma Aameen"Umman Sa'eeda ta bita dashi.
@@@@@@@@@@@@@@@
Yau take Monday,Sa'eeda tayi shirinta tsaf,tafito ɗas abinta,doguwar riga six pieces na roba tasa ajikinta,tare da ƴar jakar makarantar ta wanda ƴan wasu litattafai ne sai biro guda biyu a ciki.
Zama tayi bayan tasaka rigar, ta shafa ɗan viseline ɗinta sai ta yamutsa powder kaɗan ba mai yawa ba a fuskarta sai ɗan kwalli a idanunta sai lipglow da tasha fa ɗan ƙaramin bakinta.Maa shaa Allah kawai zan iya furtawa,this is what we call natural beauty a turance,gaskiya Sa'eeda nada kyau sosai duk da ba wata kwalliya tayi ba amma tafi wacca tayi make up kyau da haɗuwa.
Abinci taci sannan tayi nafila raka'a biyu saboda neman sa'a tare da neman tsari daga shirrin abubuwan da suke a cikin makarantar.
Daukan veil ɗinta tayi kalar kayan sai ta yafa sannan ta goyo jakarta a baya,sai ta dubi Ummanta tace"Toh Ummina zan tafi school"
"Ina nema miki tsari na daga abin cutarwa,tare da fatan Allah yasa ki fara a sa'a ki kuma kammala a sa'a tare da samun nasarori masu yawa,Allah ya albarkaci karatunki, ya kuma albarkaci rayuwarki baki ɗaya" haɗe da shafa kanta tana murmushi
"Aameen ya Hayyu ya Gayyum" haka Sa'eeda ta furta tare da ƙara jin so da ƙaunar Ummanta, haƙiƙa tayi dacen samun uwa ta gari mai tsoran Allah haɗe da haƙuri.
Kuɗin mota ta miƙa ma Sa'eeda sannan sukayi sallama,Sa'eeda ta fito daga ɗaki.
A tsakar gida kuwa Maman Jummalo ce tafito yin alwala kasancewar bata tashi sallar asuba ba,hasalima gwara ita akan sauran ƴan gidan don Umma Kande sai wurin 9:00am take sallah su kuma sauran yaran sai sanda suka tashi daga bacci,kai kai kai abun dai babu tsari.
Da wani mayan kallo Maman Jummalo take bin Sa'eeda dashi tana ayyanawa a zuciyarta 'Gaskiya kyawun yarinyar nan ƙara fitowa yake kullum kamar ba cikin ƙangin rayuwa suke ba'
Katse mata tunani Sa'eeda tayi da gaisuwa "Ina kwana Maman Jummalo"
"Lafiya lau,sai ina haka" tayi maganar ne dan ta bigi cikinta
"Makaranta zani" kasancewar Sa'eeda tasan kanta yasa taƙi sanar mata University zata tafi,hasalima ba susan yanayin karatunta ba.
Taɓe baki tayi irin ko ajikinta ɗin nan,saboda yaransu sun wuce da ajinta. (Ni kuma nace sun wuce ajinta a jahilci ba😂😂😂).
Ko irin a dawo lafiya Maman Jummalo bata iya ce mata ba haka tana kallonts wuce zuwa makaranta,dayake tsakanin gidansu da Kasu tafiyar mintuna arba'in ne shiyasa dole ta dinga hawan keke napep zuwa school.
Bayan ta fito gida ta tari mai keke napep a layin nasu kasancewar keke napep suna yawan wucewa saboda hanyar mai kyau ne babu tudu da kwararo sosai.
@@@@@@@@@@@@@@@
Lokacin da mai keke napep ya sauke Sa'eeda,ɗalibai maza da mata suna shiga cikin makaranta, mutane ne ba bambamta addini,al'adu da yaruka,itama sawunsu tabi zuwa cikin makarantar, dayake sanda suka zo screening har department ɗinsu sunje ita da Maryam yasa bata wani ɓata lokacin neman faculty ɗinsu ba,direct ta wuce department ɗinsu,sannan ta nemi ajin ƴan 100L ta shiga.
Tana shiga ta samu front sit ta zauna kasancewar ita ma'abociyar zaman gaba ne tun tana primary,bata daɗe da zuwa ba sai ga Maryam ta shigo,tasha tsadaddun kaya kamar zata biki ga make up da tasha,ta ɗauro jakar ƴan gayu ,ga takalmi high heel da tasaka,tana wani cat walking ita ala dole ƴar jami'a.
Nufo inda Sa'eeda take da zama tayi tana murmushi suka gaisa sannan tace ita bazata iya zaman gaba ba daman itama tun primary a middle seat take zama,ai kuwa taci sa'a mace ɗaya ce a seat ɗin,tako je ta zauna.
A haka ɗalibai sukaita shigowa har Head of Department ɗinsu ya shigo yayi welcoming ɗinsu tare da yi musu nasiha da jan hankali akan karatunsu,sannan daga baya lecturers suka fara shigowa haɗe da introducing kansu ga ɗaliban da course ɗin da zasu dinga offering ɗinsu dashi.
@@@@@@@@@@@@@
A nan ne kowa ya bada number wayarshi saboda za'a buɗe class group,haka kowa ya bada number shi,kasancewar Sa'eeda sabon layi ne akan wayarta bata haddace ba ya sakata ciro wayarta dan ta duba number nata,ji tayi a bayanta ance
"Ikon Allah ashe daman har yanxu akwai vivo,ai duk na zaci ƴan primary suke amfani da vivo dan yin games ba ƴan University ba" cewar wata matashiyar budurwa
Ta kusa da itace ta amsa da cewa"Wallahi kuwa kamar ma second hand ne a hannunta"
"Second hand ne kuwa,tabb wallah ko ƙanina wanda yake secondary infinix daddy ya siya mai"
Suko ƴan aji kowa kallonta yakeyi ,wasu na zunɗenta,wasu kuma na gulmarta,duk tana jinsu amma babu wanda ta kula,hasalima haddace numbanta tayi sannan ta maida wayarta jaka ta bada number ko a jikinta.
Kasancewar yau ne aka fara karatu,ajin nasu bai ciki ba kuma ma lecturers ba kowa ya shigo ba sai next week karatu zai fara zafi,shiyasa suka tafi gida da wuri.
Bayan tun fito ne Maryam ta dubi Sa'eeda ta ce"Yanxu ki rasa wayan da zaki siya sai vivo kuma ma vivo ƙarama,haba wannan ba class ɗinki bane wallahi,duk da bani aka yarfa a ji ba amma duk naji kunya"
Dariya Sa'eeda tayi sannan ta ce"Akwai wanda a cikinsu ya bani kuɗin shiga wannan makarantar ne,ina ruwansu da wayana,inason wayana kuma ina jinta kamar iphone ,don ko a jikina don sun yarfani,hakan bai dameni ba,karatu ya kawoni ba nuna waya ba"
Taɓe baki Maryam tayi sannan ta ce" Mu kuwa duka ya kawo mu"
"Toh Allah ya bada sa'ar haka"
Dayake hanyarsu ɗaya ne haka suka nemi mai keke napep suka nufo gida wurin ƙarfe biyu.
Haka Sa'eeda ta cigaba da zuwa school har satin ya ƙare,a sannan ne class time table ɗinsu ya fito,zama tayi tama kanta special time table na gida don tanaso tafito da flying colours kuma hakan bazai samu ba sai ta maida hankalinta ɗari bisa ɗari a karatunta sosai. Wannan kenan
@@@@@@@@@@@@@@@
Bangaren su Umma Kande kuwa sai dai sambarka,kamar yanda boka Sankeru ya musu alƙawarin yaransu za suyi aure to hakan ta kasance.
Kwana ɗaya da wanke fuskokinsu samari musu kuɗi suka musu ca wurin neman auran yaransu.A satin ne kowaccansu ta fidda miji wanda iyaye suka shigo ciki,haka Maman Jummalo ta tafi ƙauyansu dan sanar da auran Jummalo, itama Jummalo da saurayinta suka je ƙauyansu gaishe da dangin mahaifinta , saurayin ya gabatar da kansa kuma yace nan bada jimawa ba zai turo da iyayensa ayi maganar aure.
Bangaren Abban Sa'eeda hakan ta kasance saida yaje garinsu duk da ya jima rabonsa da garin nasu dayake iyayensa duk sun rasu saidai yayyi da ƙanne,duk da Umma Kande taso ta hanashi zuwa amma Maman Jummalo ta hane ta saboda gulmarta za'ayi a ce babu dangin mahaifin yara sai dai na uwa kuma hakan ba daidai bane ,da wannan yasa Umma Kande haƙura don batason danginsa su raɓeshi gashi ba sonta suke ba sunfi son Umman Sa'eeda.
Duk wannan zancen auran da akeyi banda Nusaiba, hakan baima Umma Kande daɗi ba amma babu yadda ta iya,ƙarya Nusaiba ta shiryawa Mamanta wai ƙawarta zatayi aure a sokoto kuma sun shaƙu da juna sosai tanason taje bikin,babu musu Umma Kande ta amince da tafiyar.(Anyi daƙiƙiyar Uwa a nan,gaskiya su Nusaiba basuyi dacen Uwa tagari ba🤔🤔🤔)
Haka ko Nusaiba ta shirya ƴan kayanta a ƙaramin akwati a cewarta ta tafi sokoto biki,ashe Dubai zasu ita da Alhaji Sagir,fitarta gida ta kirashi yazo ya dauketa daman ya daɗe da mata visa nafita ƙasar waje,a ranar suka cillar sararin samaniya zuwa Dubai.(Nusaiba ikon Allah,ba sabamba an hau jirgi,banda ƙauyanci dai acan😂😂😂)
Bayan dawowan Abban Sa'eeda ya sanar da Umma Kande akan amincewar danginsa,sai kuma ya ƙara da cewa"Lokaci kaɗan za'a sa ranar bikin nasy,ayi a huta gaba ɗaya"
Hakan yama Umma Kande daɗi sosai,kamar yanda yace lokaci kaɗan za'a saka bikin,haka kuwa akayi dan wata ɗaya aka saka bikin nasu su ukun,haka su Umma Kande suka fara shirye shiryan biki.
@@@@@@@@@@@@@@
Bangaren su Sa'eeda kuwa lectures ya soma zafi,gashi kullum sai sunje school harda ranar asabar wani lokacin.
Duk karatun da aka musu a aji idan ta dawo gida sai ta tabbatar da ta iya sosai kuma ya zauna a brain ɗinta sannan hakalinta yake kwanciya,ta lura ƴan ajin basa sonta saboda yanda idan akayi tambaya a aji take bada amsa har wani lokacin lecturers na mata kyautan marks hakan baya musu daɗi sai suyita hararta wasu har tsokanarta suke da hajiyar Vivo,tana jinsu amma bata tanka musu hasalima ita ta saba da irin wannan halin na ƴan aji tun tana secondary ake mata hassada kuma hakan ba damunta yake ba karatu tasa agabanta,duk da ba cika son bada amsa take ba sai idan malamin zai zagi ƴan aji shi ne take tashi ta bada amsa.
Bangaren Umman Sa'eeda kuwa ta fara zuwa aikinta na sharan titi ta wurin makarantar su Sa'eeda kasancewar nan ne portion ɗin da aka ɗibar mata, kullum a tare suke fita gidan ita da Sa'eeda,dayake da wuri Umman Sa'eeda take kammala sharanta ta dawo gida sannan kuma da ɗora da wankin mutane.(Allah sarki Umman Sa'eeda wataran sai labari😞😞😞)
Umman Sa'eeda tasan da maganar auransu Zulaiha amma tunda ba'a sata ciki ba,nata kallo ne,don wani lokacin habaici da gori suke mata wai ƴarta batada farin jinin samari,idan taji suna wannan zancen sai tayi dariya tace kwata kwata nawa Sa'eedar take da za'a ace batada farin jinin samari.
@@@@@@@@@@@@@@@
Wasa wasa lokacin biki ya ƙarato,baifi saura kwana biyar ba.A wannan lokacin ne akaita kawo lefan ƴan matan guda uku,babu laifi Naira tayi kuka,saboda dukkaninsu akwati 12 aka kawo musu kamar haɗin baki(Ni kuma nace maganar asiri ce fa ske malam,ai har fin haka ma zasuyi,saidai su jira sakamako 😀🤔), ga kayan ciki nagani na faɗa ne bancin gwala gwalen da aka narka aciki.
Maƙota da ƴan layi kowa zuwa ganin kwakwaf yake don aji daɗin gulmar dakyau,su Umma Kande da Maman Jummalo sai ɗaga kai suke suna yada magana tare da habaici akan gorin da ake ma yaransu akan sun ƙi aure sai tara samari yau gashi Allah yayi ƴan baƙin ciki saidai su mutu.
Ƴan uwa na nesa da na kusa sun fara zuwa tun daga dangin Umma Kande na Maiduguri,da na dangin Abbansu Sa'eeda tare da dagin Maman Jummalo duk sun fara zuwa,kasancewar gidan an sake gyarashi haɗe da ƙarin ɗakuna dayake gidan akwai fili sosai.haka baƙin suka samu wurin kwana.
A wannan satin ne Musa ya iso garin bayan tsawan lokaci rabonshi da gida,yana sallama cikin gida kowa ya bishi da kallon kurilla kowa bakinsa a sake don mamaki da al'ajab da ya cikasu........................
****Tofa ya akayi daga sallamar Musa Kowa ya bishi da kallo har da sakin baki,mai hakan yake nufi🤔🤔🤔
***ya kuke tunanin rayuwar Sa'eeda a jami'a,shin halayanta masu kyau zasu ɗaure ko ko zata sauya hali.....???
***My Esteem fans ga dai su Umma Kande da Maman Jummalo ana shirin aurar da yara,shin kuna tunanin sunyi dacen mazaje ko ko akasin haka kamar yadda Boka Sankeru yace zasu samu kowani irin mazaje.........???
Duk ku biyoni zuwa next page don jin amsoshinku✍️✍️✍️
Ina Matuƙar alfahari daku my Esteem Fans💖💖💖
Daga alƙalamin
🖍️📚Narrnarhh Bukar 📚🖍️
Comments and share 🙏🙏🙏Fisabilillah.
[4/25, 1:38 PM] +234 814 129 2044:
🏵️ NACINA YAJAWOMIN🏵️
Narrnarhh Bukar✍️
🌹Perfect Essential Writer's
Association🌹
✨ P. E. W. A✨
Wattpad:@AISHAABUBAKAR812
Arewabook:@Narrnarhh002
1⃣7⃣---1⃣8⃣
A wannan satin ne Musa ya iso garin bayan tsawan lokaci rabonshi da gida,yana sallama cikin gida kowa ya bishi da kallon kurilla kowa bakinsa a sake don mamaki da al'ajab da ya cikasu.
"Mai zan gani ni Hafsy,Musa haka ka koma !!!" cewar Maman Jummalo wacca fitowarta kenan daga ɗaki.
Wa'inda ma basu san da dawowarsa ba kowa ya bisa da kallon ƙurilla,gaskiya dole Maman Jummalo ta ce mai zata gani ita Hafsy,haƙiƙa duk wanda yasan Musa dole yayi mamakin ganinsa haka.
Mutumin da a da baƙi ne sosai yanzu ya koma fari sai kace bature,bancin haka ga wani askin ƴan iska da yayi,an saisaye ƙeyar kan ambar tsakiyar kai da mirɗe-mirɗen gashi sai kace kan zakara,ga kayan da ya saka wanda zakayi tunanin cikakken inyamuri ne ba Bahaushe ba kuma ɗan musulmi,wannan duk bashi ne matsalar ba kuma bashi ne abin mamakin ba yanayin maganarsa duk ta canja takoma kamar na ɗan daudu.
Cike da barikanci Musa ya fara magana kamar mace"Hi Maman Jummalo ƴar uwa, ya jin nice,kwana da yawa,ashe zamu aurar da yara"
Sai wani lanƙwasa da karairaya yake kamar wata mace,macan ma karuwa.Haba gida ba sai ya kaure da salati da sallalami ba,ma gulman layi an samu sabon rahoto.Matan gida na cikin wannan yanayi sai ga Umma Kande ta shigo gidan,dama bata nan ya dawo ba,taje siyayyar wasu kayan biki a kasuwa,saukanta kenan daga keke napep aka ce mata Musa ya zama ɗan daudu sai zance yakeyi a gidan da matan aure,bata ɓata lokaci ba ta shiga gidan cike da tashin hankali.
"Musa!,Musa!!,Musa!!!,kai ne haka!!!"
Waro idanu tayi waje tare da dafa ƙirjinta hannu bibbiyu sai kuma ta fashe da kuka har da shassheƙa don tayi mamakin a ce wai yau ɗan da ta haifa da cikinta ya zama ɗan daudu,to ya hakan ta faru ne,mai ya maida shi haka,tana kukan ne ya zo kusa da ita tare da cewa
" Oh My God,haba mommy na,why cry naaaa,keda zaki ji daɗin ganin ƴan matanki amma sai kuka,no no no,stop mommy na"
"Ƴan matana fa kace Musa,da hankalinka kuwa,kai macace da kake kiran kanka da ƴan mata,mai ya shiga ƙwaƙwalwarka Musa,wayyo ni Saratu jikar sarkin ruwa,naga ta kaina!!! "
"To miye a ciki don na zama mace,ai normal ne wallahi chass Mommy na,kinga nazo miki da tsaraba harda kayan mata ma wallahi sai kiba su Zaliha su gyara jikinsu kinsa ina harka da kayan mata kuma ina saidasu,naga ƙannena zasuyi aure shiyasa nace bara na kawo musu suma"
Ai ba shiri da tsagaita kukanta,jin ɗanta na wa'inan kalamai,yau mai ke faruwa da ita ne.
"Musa anya ƙwaƙwalwarka a daidai take aiki kuwa,kodai maƙiyana suka ma asiri ne,na shiga uku ni Saratu,wayyo ni wayyo ni shikenan sun mai damin ɗa ɗan daudu!!!
Kowa a gidan na mujiya ya zuba musu,jin wannan sabon salo sharri wai asiri a aka ma Musa,habawa tuni Umma Kande ta katse ma kowa tunani da kururuwanta wanda ya karaɗe gidan gaba ɗaya,har wasu ƴan waje sun fara shigowa cikin gidan don kashe kwarkwan idanunsu saboda har an fara kai rahoton Musa ya zama ɗan daudu.
" Wallahi bazata saɓuba,wannan aikin asiri ne! Wallahi bazan yarda ba,asiri akama yarona don anga arziƙi ya fara samun mu,to wallahi ƴan baƙin ciki sai dai su mutu,wallahi bazan yarda ba,sai na ɗau mataki wallahi kawai a maida min ɗa mace, wayyo ni Saratu,wayyo ni sarere jikan sarkin ruwa,yau naga ta kaina,yiiiiiiiiii,yiiiiii,wayyo niiiiiiii!!!"
Da sauri Maman Jummalo tayi cikin ɗaki da ita saboda ta fara sakin layi,kar ƴan layi suji sirrinsu,da ƙyar ta shigar da ita ɗaki,ta ce kowa ya wuce gidansa.
Ƴan uwan Umma Kande ne da dangin Maman Jummalo d'a ɗakinta tare da ita kanta Maman Jummalo suna bama Umma Kande baki akan tayi haƙuri,ta kwantar da hankalinta bayan biki sai a bi lamarin na Musa a hankali.
Haka dai suka lallaɓata har da rage kukan sai dai shassheƙa wanda lokaci bayan lokaci take ajiyar zuciya.
Shiko Musa ko a jikinsa hasalima fita daga gidan yayi,daman baida niyyar kwana gidan,hotel na garin yaje ya kama na kwana huɗu har a gama biki ya koma Calabar abinsa.
Ƙarin Haske
*****Abinda bata sani ba game da Musa shi ne,tun farkon tafiyarsa Calabar halayansa suka fara canjawa,duk da lokacin akai-akai suna waya da Umma Kande, zuwanshi gida wanda daga shi bai ƙara zuwa ba sai wannan zuwa duk halayansa sun canja,kasancewarsa mai sanyin murya,gashi ba mai hayaniya ba yasa a lokacin da yaje Calabar abubuwa suka mishi wuya,tunda baida zafin nama da karsashi a komai nasa kamar wata mace haka yake ji da kansa.Farko ya fara dako sai daga baya yaga babu ci ya daina,sai wani abokinsa da suke kwana a ɗaki ɗaya yaji tausayinsa yayi mishi hanyar aiki gidan abinci wanda yawancin ƴan aikin hausawa ne amma fa cikakkun ƴan bariki mai gidan abincin ma bahaushiya ce,haka ya fara aiki gidan abinci wanda daga ƙarshe ƴan daudun gidan abinci suka fara bashi sha'awa ganin suna samun kuɗi sosai,manya-manyan matan garin suna zuwa ɗaukarsu fita cikin manyan motoci,shima kawai ya tsunɗuma cikin wannan harkar,abinda yafi ƙarfafa mishi son shiga harkar shi ne Mamansa Umma Kande,a duk sanda sukayi waya da ita sai ta mishi ƙorafin rashin turo kuɗi akai-akai da ba yayi,wai ya cika son jiki kamar mace,shi yasa bai samun komai a acan, ga abokanansa wasu har da gidaje da mata amma shi ko sisi bai turowa balle tunanin yin aure,shi kuma a gaskiya maganganunta suna ƙona mai rai sosai,shi yasa ya bama kanshi shawaran zai naima kuɗi kota y'halin ƙaƙa ne in har Mamansa zata daina ce mishi rago ne.Wannan ne asalin dalilin da yasa Musa shiga cikin harkar ƴan daudu a Calabar har shi ma yanzu yayi suna a can ana kiransa da Pretty Mussy,don ba laifi tana kai mai yanda ya kamata.Daman wannan zuwan da yayi bayan biki yake son ya siya gida sannan ya siya shagugguna a kasuwa wanda kuɗi zai dinga shigo masa akai-akai har Mamansa tayi alfahari da shi kamar yadda take alfahari da Nusaiba wai tafishi samun kuɗi kuma tana tallafa musu a gidan****.
@@@@@@@@@@@@@@
Bangarensu Sa'eeda ita da Ummanta Allah yasa basama gidan a lokacin da Musa ya dawo,balle suga abin mamaki da al'ajab,kuma koda suka dawo ɗaki suka shige abinsu,daman ba shiga harkar bikin suke ba tunda ba'a sakasu ciki ba,Sa'eeda da take budurwa ma babu wacca a cikin ƴan uwan nata ya gayyace ta balle taje ƴan matanci a bikin.
Dangin Abbansu Sa'eeda tun fil-azal ba son Umma Kande suke ba shi yasa koda wannan lamari ya afku suna ɗaki basu fito ba sai dai Allah ya kyauta suka iya cewa, dayake mata uku ne sai namiji ɗaya sukazo bikin.Ƙannan Abbansu Sa'eeda mata