Showing 9001 words to 12000 words out of 55707 words

Chapter 4 - NACINA YA JAWO MIN book1 by Narrnarhh Bukar.docx.txt

31 May 2024

8063

ALLAH kasa mufi ƙarfin zuciyoyinmu, wannan kafirci haka duk don son abin duniya🤔).
Bukkar naga tafara girgiza kamar samanta zai buɗe, ga bishiyoyin kukan nan sai jijjiga suke,ga wani irin wari mai saka mutum kamar yayi amai ya fara tasowa (my esteem fans dole na saka nose mask ɗina saboda warin da yake tasowa don idan bansaba sumewa zanyi shikenan ba ɗauko muku rahoto 😷😷😷), wani jibgegyan mutum ya bullo cikin bukkar kamar walƙiya, mummuna dashi, ga ƙaton timbi kamar randa, gashi a tsirara ya bayyana garesu, Umma Kande da Maman Jummalo sai duƙar da kai suke, duk da ba zuwansu na farko bane.
Bayyanarshi keda wuya ya fara tintsirar dariya, timbinsa na wata girgiza kamar ana bubbugata ƙwarya ,can bayan yaɗau wasu ƴan mintuna yana sheƙa dariyarsa can kuma ya tsaya a sannan ne ya fara magana cikin sautin da yake sa bukkar girgiza haɗe da bishiyoyin yana faɗin"Basai kun ɓata makunanku wurin sanarmin ba nasan meke tafe daku, kuma wannan kamar yankar wuƙa ne, amma kunason ƴaƴan naku susamu kowani irin masu kuɗine"
Cikin ladabi suka amsa da"Eh mai sha re kukanmu"(Ni kuma nace zai saku ku cikin wahala da bala'i ba😂😂😂).
Dariya ya kuma sakeyi wannan karon harda miƙewa yana taka rawa da juyi duk ilahirin jikinsa yana raws saikace wani alade in yana gudu,su Umma Kande kansu dai har yanxu a duƙe yake, can kuma ya dakata da rawar, sannan ya nufa wata ƴar ƙwarya ya ɗauko kullin magani ya cilla musu da cewa "Ku basu acikin abinci suci dukkansu alokaci guda"
Godiya sukai ta faman yimishi tare da kirari, daga baya Umma Kande taciro kuɗi zata miƙa mishi sai ya dakatar da ita da cewa"Yau jikinku shi ne fansarku don haka kowacce saina kwanta da ita"
Basu kaɗai ba har ni mai ɗaukar rahoto saida na zaro ido, sake cewa yayi " In kuma kukayi jayayya to tun anan zaku fusanci hukunci don dole sai kun haukace"
Da sauri suka amsa da"Mun aminci "
Dariya ya kece dashi ya faɗin" Shegu mayun kuɗi", can ya sake miƙewa yana taka rawa kamar alade(Fans anya wannan bokan bai fara hauka ba, wannan irin rawa haka😂😂😂).


@@@@@@@@@@@@@@


Da Maman Jummalo aka fara masha'ar, saida ya shafe tsawan awa 2 cur kana tafito dayake Umma Kande tafito waje saboda umarnin boka Sankeru, sai Umma Kande ta shiga yayi bidirinsa da ita har tsawan awa biyu da rabi sannan itama ta fito.
zai goge zufa sukeyi, haka suka lallaba har zuwa bakin dajin duk jikinsu sai wari yake kamar mushe, can Umma Kande tace"Wai ba naga kamar kin ɗauko turare ba sanda zamuzo har kika sake fesawa a mota"
Maman Jummalo tashe"Wannan haka yake bara na ɗauko mufesa don kar a ƙi ɗaukar mu''
Da ƙyar suka samu mai machine suka hau su biyu, basu suka dawo gida ba sai wurin yamma lilis.
A daren kamar yanda boka Sankeru ya Umurcesu, suka sa musu maganin cikin abinci suci a tare, kamar yanda yace.


***Gareku ƴan uwana mata, haƙiƙa wani lokacin idonmu yakan rufe saboda abun duniya kamar yanda su Umma Kande da Maman Jummalo nasu ya rufe ruf, saboda son abin duniya mai ƙarewa suka lalata rayuwarsu da na ƴaƴansu baki ɗaya, haƙiƙa sun tafka babban kuskure domin ko sallarsu bazata amsu ba har na tsawan kwana arba'in kuma sun kafirta kamar yanda yazo acikin hadisin manzon ALLAH (S. A. W) yana cewa "Duk wanda yaje wurin boka ko mai duba haƙiƙa ya kafirta kuma sallarsa baza ta amsu ba har na tsawan kwana arba'in",.ALLAH kasa mufi ƙarfin zuciyoyinmu gaba ɗaya.***


@@@@@@@@@@@@@
Tun daga ranar su Umma Kande sukaga sauyi wurin ƴaƴansu don yanzu kowacce cikinsu nada saurayi mai kuɗin gaske gashi suna sakar musu da kuɗi sosai. Tabbas kamar yanda Umma Kande tace sunyi hannun riga da talauci lallai kuwa sunyi don suna fantamawa da kuɗi sosai.
Bangaren su Sa'eeda sun fara shirin 1st term exams na SS2 har time table ya fito, ita da uwarta basa shiga sabgar ƴan gidan haka Abban Sa'eeda yanxu ko ɗakin Umman Sa'eeda ya daina shiga kwata kwata. Sa'eeda karatu ta ke baji babu gani, yanda ta ke karatu zakayi tunanin a University ta ke, haka sukayi exams ɗinsu cikin hukuncin Ubangiji.
A lokacin saura kwana biyu sallah, haka suka fara shirye shiryen tafiya ƙauyen Damari, ana gobe sallah kuwa suka kama hanya.


@@@@@@@@@@@@@


ƘAUYEN DAMARI


Dayake da safe sukayi tafiyar, sai wurin 11:00am na safe suka iso tashar garin, haka suka ɗau mai machine da ƴan kayansu kala bibbiyyu saboda ba daɗewa zasuyi ba. Wani gida mai ginin ƙasa naga mai machine ɗin ya faka, suka sauka Umma Sa'eeda ta biya mai machine ɗin kana suka shiga cikin gidan da sallamarsu.
Wata tsohuwa nagani mai kumanin shekara 69 zana zaune kan tabarma tare da ita kuma ɗan ƙaramin radio ne tanajin labarai, ganinsu yasa wannan tsohuwa miƙewa zunbur kamar an tsikareka tana faɗin "Miya kawoki gidan nan, ba nace miki karki kuskura na sake ganin baƙar ƙafarki agidan nan ba"
Russunawa Umman Sa'eeda tayi cike da girmamawa ba tare tabi takan zantuttukan tsohuwar ba ta gaishe ta, ƙin amsawa tayi tare da cewa"Riƙe gaisuwarki, in kinje birni tamiki amfani marar asali kawai"
Hawaye suka fara kwaranya a idanun Umman Sa'eeda, a zuciyarta tana faɗin 'ALLAH ka kawomin mafita nida ƴata, kabamu ikon cin wannan jabawar'.
Jin sallamar wani dattijo mai kimanin shekara 76 amma inka ganshi zakace baikai haka saboda jikin mutan da dana yanzu ba ɗaya bane,shigowarsa ya katse mata tunani da faɗin"Lale marhabin da mutan birni, Hussaina ce nake gani ba'a mafarki ba"
Umman Sa'eeda ne juyo tare da russunawa wurin gaisheshi da cewa"Baba mun sameku lafiya"
Cike da murna Baba ya amsa da "lafiya lau Hussaina, ya kuke, ya bayan rabuwa"
Umman Sa'eeda tace"Alhamdulillah Baba duk sunce a gaisheku"
suna cikin gaisawa wannan tsohuwar da katse musu hirar da faɗin "Tsintacciyar mage bata taɓa zamowa mage"
Daka mata tsawa tsohon nan yayi tare da cewa "Ladi ya isheka haka, wannan gidana ne, kuma ni nakeda iko akansa bake ba, kar na sakejin maganarki anan, ko kuma ranki in yayi dubu wallahi sai ya ɓaci", (Fans dama tsoho kamarsa yana fad'a haka, tabbb, ni nayi nan karya had'a dani wallahi🙃🙃🙃).
Shiru kuwa wacca aka kira da Ladi tayi , can kuma ta wuce ɗaki, juyowa yayi gun Umman Sa'eeda tare da cewa"Kiyi haƙuri nasanki da haƙuri kamar mahaifiyarki, ga ɗaki can kukai kayanku ciki,zansa Mairi da girko muku abinci yanxu"
da "Toh" Umman Sa'eeda ta bishi dashi, Sa'eeda mutuwar tsaye tayi tunda suka shigo gidan da farajin masifar Ladi ta tafi nisan zango a ranta tana cewa'Wai yaushe zamuyi masoya a duniya, kowa bai son mu,toh meyasa ta ce Ummina batada asali, daman ba ita bace kakata toh wacece kakata................








Daga alk'alamin
🖍️📚Narnarhh Bukar 📚🖍️


Comments and share 🙏🙏🙏Fisabilillah.






🏵️ NACINA YAJAWOMIN🏵️



Narrnarhh Bukar✍️


🌹Perfect Essential Writer's
Association🌹
✨ P. E. W. A✨




Wattpad:@AISHAABUBAKAR812
Arewabook:Narrnarhh002


9️⃣----🔟


Sa'eeda mutuwar tsaye tayi tun daga shigowa gidan da kuma farajin masifar Gwaggo Ladi ta tafi nisan zango a ranta tana cewa 'Wai yaushe zamuyi masoya a duniya, kowa bai son mu,Toh meyasa ta ce Ummina batada asali, daman ba ita bace kakata, toh wacece kakata, kenan Gwaggo Ladi ba ita bace ta haifi Ummina ba'.
Haka taita karatun zuci daga ƙarshe ta dauki kayansu zuwa inda Baba ya umurcesu, ɗaki ne ɗan ƙarami da ƴar katifa itama ƙarama wacca batafi ta kwanciyar mutane biyu ba, sai labulen ƙofa da na window, ɗakin ba laifi a gyare yake kamar ansan da zuwansu.
Ciki ta iske Ummanta a zaune akan katifar tayi tagumi, da sauri Sa'eeda ta ajiye kayan hannunta ta nufi gun Ummanta don arayuwarta bata ƙaunar ganin damuwa a fuskar Umman nata, haka da sassarfa ta isa gunta tare da cewa " Ummina don ALLAH kidena tagumi, Banaso please kidaina "
Sai kuma ta fashe da kuka,har da shashsheka, don ita ta rasa wannan baƙin jinin da suke dashi, kowa baya sonsu, ko a makaranta haka ta ke fuskantar tsana da tsangwama daga ƴan ajinsu, wurin Maryam kaɗai ne ta ke samun sassauci.
Ummanta ne riƙo haɓarta tare da girgiza maka kai alamun tayi shiru duk da itama kanta hawayan ne suke kwaranya a bisa kuncinta tare da cewa " Duk wani ƙunci da tsanani maganinsa yana ga UBANGIJI ne, haƙuri da juriya suna kai mutum mataki babba arayuwa, kasancewarmu a wannan yanayi baya nuni akan dawwamarmu cikinsa, don haka mu cigaba da haƙuri tare da juriya wataran sai labarin kinji sanyin idanuwa na"
Sa'eeda da tunda Ummanta ta fara magana ta ke shashshekar kuka ɗan ɗaga mata kai tayi tare da tambayarta alokaci guda " Ummina meyasa Gwaggo Ladi ta kiraki da mara asali?
Tirƙashi lokaci guda yanayin Umman Sa'eeda ya sauya ita a tunaninta Sa'eeda bataji surutan Gwaggo Ladi ba, saida ta ɗan sauke nauyayyan ajiyar zuciya kafin ta fara magana "Banso kika ji zantuttukan Gwaggo Ladi ba, hasalima shiyasa tun kina ƙarama rabona da zuwa garin nan saboda banason hankalinki ya tashi,nabar hakan ya zamo sirri agareni ba tare dana sanar miki ba, amma tunda allura ta tono garma, kibari anjuma da daddare bayan munyi sallar Isha'i sai na baki tarihina kamar yanda nima mamata ta sanar min, kinji"
Sa'eeda da ke kallon Ummanta ta amsa da "Toh, ashe nima inada kaka"
Murmushi Umman Sa'eeda tayi ganin wauta da shirme irin na Sa'eeda tare da cewa "Daman ance miki babu wanda baida kakane, kema taki ALLAH Yayi mata rasuwa ne"
Ɗan lunshe sexy eyes ɗinta Sa'eeda tayi sannan ta ce " Allah ya kai haske a ƙabarinki kakata da na al'ummar musulmai baki ɗaya"
da "Ameeeeeen", Umman Sa'eeda ta bita dashi, kana suka cigaba har hirarsu.


@@@@@@@@@@@@@@


Kamar yanda Baba ya faɗa za'a girko musu abinci hakan ta kasance, don ɗan saƙon da aka aika gidan Mairi yana sanar ma ta fara murna saboda duk acikin ƴaƴan Gwaggo Ladi tafi kowa sonta tare da mahaifiyarta kafin ta rasu.
Habawa ai da ɗan aiken ya sanar mata, daman tana kiyon zabbi , kaji da awakai, sai tasa a yanka mata zabbi guda biyu, bayan an yanka mata su, tayi zaman gyaransu ita da ƴarta mai kimanin shekara 14 dayake bata haihu da wuri ba,sannan ta ɗora sanwan girki, tayi musu tuwon dawa da miyar kuka wacca tasha manshanu haɗe da naman zabbi duk da ba duka tayi miyar dasu ba, ta soya sauran tasa alanga haɗe da na tuwon da miyar, nan fa ta aiki ƴarta ta dashi a babban kwando.


@@@@@@@@@@@@@


Da sallama ɗiyar Mairi ta shiga gidan, sai tayi sa'a Gwaggo Ladi na ɗaki kasancewar lokacin azahar ne, sai ta wuce ɗakin baƙi dayake mamanta ta faɗa mata inda baƙin suke.
Sallama tayi a lokacin Sa'eeda na sallah ita kuma Umman Sa'eeda ta kammala sallah tana zaune,jin anyi sallama yasata amsawa tare da cewa"A shigo"
yarinyar ce ta shigo tare da russunawa ta gaisheta, Umman Sa'eeda cike da fara'a ta ke amsa mata ganin kamannin ƴar uwarta ta kuma masoyiyarta wacca bata da kamarta, cike da ladabi yarinyar ta ce"Mamata ta ce gashi in kawo muku kuma tana muku sannu da zuwa, gobe bayan sallar Idi tana nan zuwa "
faɗaɗa murmushinta tayi da faɗin" ALLAH ya kaimu, kice mata ina godiya sosai, sannan tsarabarta na nan saita zo"
yarinyar tace "Toh", har lokacin Sa'eeda na sallah bata idar ba.
Yarinyar na tafiya Sa'eeda ta kammala sallah,ta cire hijab ɗinta suka fara cin abinci, duk da yau ake hawan Arfa, Sa'eeda na period ita kuma Umman Sa'eeda na fama da chronic ulcer kuma yanxu an ɗorata akan magani shi ya hanata ɗaukar azumin Arfa. Haka suka kammala cin abincinsu tare da hamdala sannan kowa ya sami wuri don warware gajiyar tafiya.


@@@@@@@@@@@@@@@


Baba dai har lokacin bai dawo ba, dayake Umman Sa'eeda tasan ɗabi'arsa na sai bayan Isha yake dawowa, yau ma sa'a tayi ganinsa a gidan.
Bayan sallar Isha ya dawo gida, ita dai Gwaggo Ladi alwala ce ta ke fito da ita sai kuma girkin abin shan ruwa da tayi su kaɗai ne yasaka ta fitowa don ita ta tsani Umman Sa'eeda matuƙa ainun gashi tana aure a birni ita kuma yaranta a ƙauye dukkaninsu suke aure, a duk sanda ta tuna sai ranta ya baci(Fans da alama dai batasan baƙar wahalar da Umman Sa'eeda da ƴarta suke sha a gun Umma kande da Maman Jummalo ba shiyasa ta ke wannan bacin ran🤔).
Gwaggo Ladi ce ta fito da tabarma don shimfiɗama Baba kasancewar yafi son cin abinci a waje, bayan ta shimfiɗa tabarmar sai ta kawo mai abinci sannan ta wuce ɗaki don batason haduwa da Umman Sa'eeda kuma tasan yana gama cin abinci sai kirata(Gwaggo Ladi duniya🙃, wannan tsana sai kace kishiyarta ai ko kishiyarta sai haka😂😂😂).
Kamar ta sani bayan ya kammala cin abin yako kira Umman Sa'eeda, tako fito ta samu wuri gefan tabarmar ta zauna.
Ƙara gaisawa sukayi sannan suka fara hirar yaushe gamo, tun tana ƙarama ta saba da Baba,saboda yana jawota a jiki sosai kamar ƴaƴansa,sun shaƙu da juna sosai. Sun daɗe sun hira abinsu har kusan awa sannan sukayi saida safe, shi ya wuce ɗakin Gwaggo Ladi ita kuma ta wuce masaukinsu.


@@@@@@@@@@@@


Shigarsa ɗaki ya samu wuri kusa da Gwaggo Ladi ya zauna don yanada buƙatar magana da ita saboda ya gaji da wannan ƙiyayyar da ta ke nunawa marainiyar ALLAH, ya isheshi haka, tun tana yarinya ta ke fuskantar ƙalubale har auranta.
Gwaggo Ladi da tun shigowarshi ɗakin tana kwance tana jinsa amma tayi burus sai tayi kamar tayi bacci, don yau ya bata haushi sosai akan marar asali yake daka mata tsawa wanda rabon da suyi hayaniya ko fada ta manta ranar.
Zama yayi tare da cewa " Ladi ina son magana dake yanxu"
tana jinsa amma taƙi amsawa, saida ya sake magana kana ta tashi daga kwancen ta zauna.
Shiru ɗakin yayi , sai can Baba ya katse shurun da faɗin"Yanxu Ladi abinda kikayi ya dace kenan, yarinya tazo ko zama bata yi ba, kike mata masifa tare da faɗa mata marar asali, wai shin kinada hankali kuwa,kina da tabbacin marar asalin ce da kike kiranta dashi tun kan tasan hankalinta har girmanta, wata hujja kike da ita Ladi "
Gwaggo Ladi dai ko Uhmmm bata ce ba, tana nan zaune, saida ya ɗan lunfasa sannan ya ɗora da cewa" Don ALLAH ki canja halinki, tsufa kike ƙarayi amma kullum kina abu kamar wata yarinya haba, a kullum inaji a jikina Husaina na da asali saidai ƙaddarar da ta afka ma mamanta na ciwo "
Yanxu ne Ladi ta buɗe baki tace" Ni tunda ka kawo su gidan nan na tsane su,bara kaji har na koma ma mahaliccina da tsanarsu zan koma musamman Husaina, don haka ba ruwana da har karta, tunda gidan kane, ta shekara a ciki wannan kai ta shafa bani ba,sannan idan wa'azin kake sonyi ka tafi masallaci kayi, baza kazo kana min wata nasiha ba, ehehhh!
haka Baba ya kyaleta ya kwanta tare da roƙon mata shiriya don da alama tayi nisa. (Ni kuma nace hassada ne da baƙin ciki ya mata katutu a zuciya 😂🙃😇).


@@@@@@@@@@@@@


A bangaren su Umman Sa'eeda kuwa, bayan ta shiga ɗaki ita duk a tunaninta Sa'eeda tayi bacci, ashe tana nan tana karatu,(Jikar Mongo Park ba ko kuma Al huda huda🙃🙃🙃) .
shiga ɗakin tayi tare da cewa"Ashe bakiyi bacci ba, duk azatona zanzo na nasamu kinyi bacci"
murmushi Sa'eeda tayi sannan tace "Ummina Ina zanyi bacci banji tarihin kakata ba, ai bacci bai ganni ba"
dariya Umman Sa'eeda tayi sannan tace " Toh karkaɗa kunnuwanki yanxu zakiji tarihin kakarki"
Gyara zama Sa'eeda tayi tana fuskantar Ummanta, sannan Ummanta tafara bata tarihin kakarta.
Labari
***Na taso a gidan nan tare da mahaifiyata cikin ƙasƙanci, a lokacin mamata tana da tsohon ciki ni kuma ban wuce skekara 6 ba,Baba na kula ta mamata tare da ni sosai kasancewar cikinta na a watan haihuwa,a lokacin mahaifiyar baba na araye,duk sanda Gwaggo Ladi kema mamata masifa mahaifiyar Baba wacca muke kira da Tasalla ta ke shigar mamata faɗan tayiwa Gwaggo Ladi tatas, don Tasalla na son mu kamar yanda Baba ke son mu.
Sanda mamata zata haihu alokacin babu asibiti, Tasalla ta amsa haihuwar, mamata ta haifo ƴan biyu duk maza kyawawa amma ɗaya yazo babu rai sai kuma ɗan uwansa yabi bayansa, bayan haihuwa da kwana huɗu, tun sanda mamata ta haihu ta kamu da ciwo kuma ankasa gane kan ciwon, wanda ko fita da ƙyar ta ke yi.
Kuma duk sanda aka tambayeta ina ne ahalinta suke to ranar babu wanda zai rintsa, ta dinga firgita haɗe da iface iface a gidan, dalilin haka yasa tunda su Baba suka tambayeta sau biyu hakan ta faru basu ƙara tuntuɓarta da batun inane ahalinta suke ba.
A duk sanda Gwaggo Ladi tai min gori ko ta kirani da marar asali sai mamata tace min "Husaina ke ƴar gata ce, kuma kinada asali, kin fito daga tsatso mai kyau, kuma ƴar dangi ce, bancin ƙaddar da ta afka mana tare da ɓatan ɗan uwanki Hassan wanda kullum zuciyata dashi ta ke kwana kuma dashi ta ke tashi, inaji a jikina yana araye bai mutu ba,nasan ko ba daɗe ko bajima zaki sadu da ahalinki, inaso kikasance mai haƙuri da juriya a duk inda kika tsinci kanki,ki kasance mai ibada a koda yaushe, don inajin lokacina ya kusa Husaina "
Haka mamata ta ke faɗamin a duk sanda Gwaggo Ladi ko ƴaƴanta suka kirani da marar asali,na ɗau nasihar mamata na adanata acikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login