Showing 12001 words to 15000 words out of 55707 words

Chapter 5 - NACINA YA JAWO MIN book1 by Narrnarhh Bukar.docx.txt

31 May 2024

8050

ƙwaƙwalwata, duk da a lokacin banfi shekara 12 a duniya ba, mahaifiyar Baba ta rasu, Ina gab da shiga shekara da 13 mamata tabar duniya, nayi kuka iya kuka wanda babu mai lallashina daga Baba sai Mairi wacca ɗiyarta ta kawo mana abinci ɗazu, duk da sa'a ta ce amma tanada hankali, ita kadai da Baba nake samun natsuwa wurinku.
Bayan rasuwar mamata rayuwa ta ƙara min zafi don lokacin na fara fuskantar asalin gallazawa wurin Gwaggo Ladi, ga aikin gida duk da ƙarancin shekaruna haka nake komai agidan sai afakai ce Mairi ta ke tayani aiki, kasancewar Baba ba zama yake a gida ba shiyasa baisan meke faruwa dani ba,sai dare yake dawowa, a daran ne nake samu naci abinci sosai.
Haka rayuwa da cigaba da tafiya ina a wannan yanayin har na zama budurwa, kyakkyawa dani, don samarin garin nan sunyi harsashe babu wacca ta kaini kyau, hakan ba ƙaramin batama Gwaggo Ladi rai yake ba saboda lokacin itama ƴan matanta sun girma, don akwai mata biyu wa'inda suka girmeni sannan Mairi wacca muke sa'a da juna, haka samari sukaita zuwa wurin Baba neman aurena alokacin inada shekara 16,gasu masu kuɗi harda yaron mai gari,saboda wannan farin jini da ALLAH ya bani na ƙara samun ƙuntata gun Gwaggo Ladi.
Alokaci guda aka saka mana rana da sauran ƴan matan Gwaggo Ladi har da Mairi,duk samarinsu a ƙauye suke har da na Mairi, Ni kuma mahaifinki a lokacin ba laifi yanada kuɗi kuma a birni yake da gida, haka aka daura mana aure wanda ko tsinke ban samu daga Gwaggo Ladi ba saidai Baba,shi yayi ruwa yayi tsaki, bayan ɗaurin aure aka wuce dani birni gidan mahaifinki duk da bamu samu tarbar arziƙi wurin Umma kande ba, haka suka tafi suka barni, inata kukan rabuwa dasu, a da maihaifinki na matuƙar sona wanda baya iya ɓoyewa a gun kowa, sai daga baya lokacin na haifeki kinyi yawo, na fara ganin sauyi wurinsa har yakai ya fara nuna min kyara da tsangwa, wanda ni kuma na rasa abinda nayi masa, a haka dai har aka kawo yanxu, wanda a kullum nake Addu'ar ALLAH ya karkato da hankalinsa guna dake.
Toh kinji tarihin kakarki mai suna Maimuna, kuma har yanxu ban cira rai da saduwa da ahalina ba kamar yanda mamata ta ke faɗamin duk sanda aka min gorin marar asali***


@@@@@@@@@@@@@@@


Cikin labari


Sa'eeda dai tun sanda Ummanta ta fara bata labari da natsu har zuwa ƙarshe sannan ta saki nauyayyan ajiyar zuciya har seda Ummanta taji kana ta fara magana " Ummina yanzu baki san asalinki ba koda gari ne"
Umman Sa'eeda murmushi tayi sannan tace " Tabbas bansan asalina ba, kuma mamana bata taɓa sanar min daga wani gari muke ba, saidai a kullum tana maimaita inada asali, ni ƴar gatace kuma ƴar dangi ce haka ta ke fadamin, kuma inaji a jikina zan sadu da asalina"
Sa'eeda ce tace " Ummina shi Uncle Hassan har yanxu bakisan inda yake ba",(Uhmmm su Sa'eeda masu Uncle tun Kan aganshi har an bashi wannan respect d'in😂😂😂).
Dariya Umman Sa'eeda tayi kana tace " Niko ina zan sanshi tunda tun muna Yara ya ɓata, kinga bazan sanshi ba, saidai mamata na yawan cemin muna kama dashi sosai sede nafishi hasken fata"
Shiru ɗakin yayi kuwa na nashi tunanin,Umman Sa'eeda ce ta katse shirun da cewa" Dare yayi zoki kwanta, yanzu dai sai a sakarmin mara na huta tunda kinji tarihin kakarki ko"
Dariya Sa'eeda tayi tare da cewa " Eh Ummina yanxu na gamsu sosai da bayananki, kuma zan cigaba da yi mana addu'ar ALLAH ya sadamu da ahalinmu"
murmushi Umman Sa'eeda tayi sannan tace"yawwa sayyin idaniya na, ALLAH ya amsa mana"
da "Allahumma Ameen" Sa'eeda ta bita dashi kana kowa ya kwanta.


@@@@@@@@@@@@@@


Yau ta ke babbar sallah,da sassafe su Sa'eeda suka tashi tare da gyaran gida sukayi wanka sannan suka shirya zuwa masallaci kasancewar Umman Sa'eeda tasan masallacin.
Bayan sallah suka dawo gida wanda a lokacin ne aka yankawa Baba ƙaton ragonsa, a nan Umman Sa'eeda da Sa'eeda sukayi ma Baba Barkha da sallah, sannan suke nufi cikin gidan, direct Umman Sa'eeda ta musu jagora zuwa ɗakin Gwaggo Ladi, a nan ta tarar da ƴaƴanta tare da jikokinta suna hira haɗe da raha abinsu, suna ganinta suka tamke fuska banda Mairi wacca tun shigowarta gidan ta ke alla alla su dawo taga ƴar uwata ta.
Russunawa sukayi ita da Sa'eeda suka mata Barkha da sallah, a daƙile da amsa sannan suka gaida ƴan ɗakin, suma dai a daƙilan suka amsa musu sannan suka wuce ma saukinsu.
Mairi ce ta bisu da fara'arta ko takan ƴan ɗakin bata bi ba ta wuce wurinsu. Koda zuwansu ɗaki sukaga an ajiye musu abinci wanda babu shakka Mairi ce ta kawo musu, zamansu keda wuya sukaji sallamar Mairi, da fara'a Umman Sa'eeda ta amsa mata sannan suke rungume juna haɗe da murnar ganin juna bayan rabuwa.
Haka dai sukayi hirarsu cike da annashuwa, sallah kadai ta ke tayar dasu kasancewar agidan Mairi zata kwana haka al'adar garin take.
Haka dai su Sa'eeda sukayi shagulgulan sallah sannan suka dawo gida tare da ɗumbin alkhairai daga wurin Baba da Mairi.
Bayan dawowarsu da wasu kwanaki su Sa'eeda suka koma makaranta. Wannan kenan


@@@@@@@@@@@@@@


ABUJA


Kasancewar duk babban sallah wannan family suke taruwa wurin shagalin bikin sallah yasa wannan Karon ma haka ta kasance.
Maa shaa Allah kawai zan iya furtawa ganin wannan family duk sunzo tun daga wa'inda suke Nigeria har ƴan UK ba sunzo banda Fadila saboda ƙaranci hutu da suka samu yasa Dad ɗinta yace baza tazo ba tunda ai tazo tayi 1 week a Nigeria, haka tayi ta kumbure kumbure daga ƙarshe haka ta haƙura da zuwan saboda school.
Garden ne nagani an ƙawatashi da wasu balloons kala kala anyi decorating garden yayi kyau sosai gashi an shimfiɗa wata babbar tabarma ammafa mai shegen taushi kamar carpet ƴan aikin sunata kai kawo wurin ganin an cika wurin da abubuwan ci da na sha tun daga soyayyun kaji, abinci kala kala tun daga na Nigeria har na ƙasar larabawa haka aka jerasu ga gasashshan naman rago an banƙareshi a tsakiya, haɗe da wuk'an yanka mai kyau.
Gaskiya wurin nan ya ƙayatu matuƙa ainun, bayan gama gyaran wurin da ma'aikata sukayi sannan wannan familin suka zagaye wurin suna murna da ganin juna, haka suka ci suka sha suna dariya da shewa.
A nan ne na hango Hajiya zaune a tsakiyar jikokinta tayi shiru, yaran suna mata wasa amman sama sama ta ke amsa musu,babbar ɗiyarta ne ta kula da yanayin mahaifiyartasu kasancewar tana kusa da ita.


@@@@@@@@@@@@


Bayan an kammala ci da sha suka koma cikin gida,direct Hajiya ta nufi ɗakinta don batason hayaniya yau hasalima tun sanda shaiɗanin bokan nan ya mata maganar basu mutu ba hankalinta ya gaza kwanciya, bacci ma saidai ya saceta saboda tunani da zullumin daya addabi ruhunta, haka akayi sallama a ƙofar ɗakinta bata amsa ba saidai ta bada umarnin a shigo.
Babbar ɗiyarta ce Amina tashigo ta zauna kusa da ita tare da cewa "Hajiyata meya sameki ne ko bakida lafiya ne"
murmushi tayi a ranta tana cewa 'dama rashin lafiya ne ai mai sauƙine akan tashin hankalin da nake ciki'
sai kuma afili tace " kwana biyu nan ina fama da ɗan zazzaɓi da kuma rashin bacci"
habawa ai tuni Amina ta rikice da sauri ta ɗauki wayarta jikinta na rawa ta ke danna ma number family doctor sun don arayuwarta batason damuwa ko kuma rashin lafiya atattare da Hajiyarta, kiransa tayi tare da cewa yazo yanzu yanzun nan banda ɓata lokaci.
Abinka da Naira duk da lokacin sallah ne amma haka Doctor ya taho gidan saboda yana girmama ƴan gidan sosai. (Ni kuma nace yana girmama Hajiya Naira ba😂🙃😇).


@@@@@@@@@@@@@@


Haka Doctor yazo ya dubata amma ya ce shi gaskiya baiga abinda yake damunta ba, hasalima tana cikin ƙoshin lafiya,duka familin suna ɗakin don Amina ta sanar da rashin lafiyar Hajiya ga kowa, suma da tashin hankali suka isa ɗakin nata.
Bayan Doctor ya gama bayaninsa ya tafi,ɗakin ya koma shiru can Amina ya katse shirun da cewa " Kodai ashirya miki Visa ne yau, gobe mu wuce India a dubaki acan"
Hajiya ce tayi murmushi tare da cewa "karku damu zan samu sauki don hakan na faruwa dani tun kuna yara, karkusa damuwa aranku"
Haka dai sukayi jimaminsu sannan kowa yayi shirin komawa inda ya fito. A haka aka bar Hajiya cikin tunanin da yanxu ya zamo mata jiki.


@@@@@@@@@@@@@@


KEBBI


Familin Alhaji Kabir Dikko family babbane kuma sanan ne acikin birnin Kebbi, wanda ko mai machine ka sanar ma gidan Alhaji Kabir Dikko zai Kaika, yasan gidan kasancewar babban gidane wanda ya shafe layi guda cur da zuri'ar Alhaji Kabir Dikko da na ƴan uwansa, gidan yakama tun daga ƴaƴan Alhaji Kabir Dikko da ƙannansa, wanda duk sun rasu saura ƴaƴa da jikoki suka rage kuma har yanxu suna zumuncinsu ba tare da nuna banbanci ba.
Cikakkun ƴan boko ne kuma ƴan kasuwa sanannu a harkar kasuwancin cikin Nigeria da wajanta.Mom da kuka sani Maman Sadam(Auta) ta kasance jika ga Mariya ita ce babbar ƴa ga Alhaji Kabir Dikko.
Duk babban sallah suke haɗuwa a family house ɗinsu ayi shagalin sallah tare da family meeting wanda ya ƙunshi magance matsaloli da kuma tallafama juna wurin ganin family ya samu daidaituwa.
Alhaji Abubakar ɗa ne na biyu ga Alhaji Kabir Dikko kuma wanda ya rage a duk gidan tun daga kan ƙannan Alhaji Kabari Dikko har sauran ƴan uwansa wanda keda kimanin shekara 80 a duniya yanada yara hud'u a duniya. Kowa a familin yana matuƙar girmama Baba Garba wanda haka suke kiransa dashi tun daga kan yara har jikoki da ƴaƴan jikoki haka suke kiransa dashi.
Wannan Karon ma haka suka gudanar da shagulgulan sallah tare da family meeting ɗin da suka saba na kowani babban sallah, daga haka taro ya watse kowa ya nufi idan ya fito.


@@@@@@@@@@@@@@


UK


Bangaren Sadam autan Mum karatu ya soma zafi gashi Dad ɗinsa ya hanashi zuwa Nigeria sai ya kammala degree ɗinsa complete sannan ya dawo bautar ƙasa na shekara ɗaya, kana ya ƙara tafiya China don yin Masters ɗinsa don ƙara sanin harkar.....................










Daga Alk'alamin
🖍️📚Narnarhh Bukar 📚🖍️










Comments and share 🙏🙏🙏Fisabilillah.
[4/25, 1:38 PM] +234 814 129 2044:


🏵️ NACINA YAJAWOMIN🏵️



Narrnarhh Bukar✍️


🌹Perfect Essential Writer's
Association🌹
✨ P. E. W. A✨




Wattpad:@AISHAABUBAKAR812
Arewabook:@Narrnarhh002






1⃣1⃣----1⃣2⃣


UK


Ɓangaren Sadam autan Mom karatu ya soma zafi gashi Dad ya hanashi zuwa Nigeria sai ya kammala degree ɗinsa complete sannan ya dawo bautar ƙasa na shekara ɗaya.


Kana ya ƙara tafiya China don yin Masters ɗinsa don ƙara sanin harkar kasuwanci,sosai hakan bai masa daɗi ba,yaso tafiya hutunsa na farko wurin sister ɗinsa Aunty Sadiya wacca a da take Pakistan kafin yanzu su dawo India da zama saboda yanayin aikin mijinta,haka dai ya haƙura da zuwa ko'ina ya ƙara maida hankalinsa kacokan a karatunsa.


Sadam miskili ne na ajin ƙarshe don yanzo miskilancin nasama ƙaruwa yayi saboda ganinsa a wata ƙasar,ƴan mata tun daga kan turawa da na baƙaƙen fata suna son ya kulasu saboda classy guy ne haɗadɗe ga girman jiki wanda idan ka gansa zakayi tunanin ɗan shekara 30 saboda ya aje ƙasumba sosai.


Yanada aboki guda ɗaya ɗan Nigeria amma shi ɗan kaduna ne mai suna Sadiq,kusan halinsu ɗaya shiyasa abotar tasu tazo ɗaya,duk da course ɗinsu ba ɗaya bane,shi Sadiq yana karantar ɓangaren Computer Engineering ne,hakan baisa abotar tasu ta lalace ba, kowan nansu yana ziyartar ɗan uwansa duk da faculty nasu ba ɗaya bane amma haka suke abotar tasu,har takai yanzu iyanyansu sun san da abotar tasu.


Haka Sadam ya cigaba da karatunsa a UK don cika burin mahaifinsa akansa kasancewarsa ɗa ɗaya wurin mahaifinsa ,gashi mahaifinsa ya soma tsufa duk yayyinsa mata ne saboda haka dole ya jajirce sosai akan karatunsa dan nan gaba harkar kasuwancin mahaifinsu da kamfanoninsa duk zasu dawo hannunsa ,shiyasa yake jajircewa sosai.Wannan kenan


@@@@@@@@@@@@@


KADUNA


Bayan sallah hutun su Sa'eeda ya ƙare,sai suka koma makaranta don cigaba da karatu.Sosai Sa'eeda take mai da hankalinta akan karatunta a bangare ɗaya kuma tana koyawa Maryam inda bata gane ba kasancewarta very slow learner ce duk da tana da lesson teacher a gida amma haƙarta bata cimma ruwa ba,gashi koda yaushe Mum ɗinta cikin zigata take akan Sa'eeda hakan yasa take ƙara shige ma Sa'eedan jiki sosai,ita ko Sa'eeda da zuciya ɗaya take tare da Maryam.


Haka suka kammala SS2 cikin nasara da aminci wanda a lokacin Sa'eeda ta samu matsala da ƴan ajinsu saboda shugabancin ɗalibai da aka bata wato Head girl,haƙiƙa ta fuskanci tsana da barazana akan sai ta sauka daga Head girl ɗin don a ganin ƴan aji ƴar talaka bata cancanta da wannan muƙami ba sai dai ƴaƴan masu kuɗi irinsu,da ƙyar abubuwa suka lafa daga baya ƴan aji suka yarda duk da wasu basa sonta da Head girl ɗin.


@@@@@@@@@@@@@


Sun shiga SS3 wanda kowanni ɗalibi na shirya shiryen zana jabawan waec,neco da jamb ,hakan ta faru ga Sa'eeda don Ummanta ta shiga adashe har kala biyu duk don karatun ɗiyarta bancin savings ɗin kuɗi da take yi a account tun daga #100,000 wanda Sa'eeda ta samu lokacin saukarta har da adashen da take kwasa tana saving ɗinsu duk don karatun ƴarta ta,koda yaushe tana samun wankin kayan mutane duk da ma Sa'eeda na tayata sosai da yake Sa'eeda ba raguwa bace akwai son aiki,wani lokacin ma cema maman take ta bari ita zatayi duk don su rufama kansu asiri tunda Abbanta an mallakeshi,sai yadda akayi dashi a gidan.


Wasa wasa su Sa'eeda sun fara shirin zana exams ɗinsu na ƙarshe,sun fara rubuta Jamb wanda within 1week sakamakon su ya fito.


Alhamdulillah yawancin ɗaliban makarantar sun samu nasarar wuce cut of mark na jamb har da su Maryam don ta dage akan sai ta wuce Sa'eeda a score. (Haba Hajiya Maryam na gaba yayi gaba,sai dai a nema wani sarkin dan ko Sa'eeda tayi zarrah😂😂😂).


Sa'eeda tafi kowa marking a school ɗin har ma tawuce 270 a Jamb ɗinta, da wannan score ɗin ba ƙaramin ƙarama kanta baƙin painti yayi ba a idon ƴan ajinsu,hakan bai dameta ba don basa gabanta.


Bayan sun kammala jamb sai suka zana waec da neco sai bayan wasu watanni waec da neco ɗinsu suka fito shima sakamakonsu yayi kyau sosai ,haka Sa'eeda da Maryam sukayi applying post utme a Kasu kasancewar shi suka sa a Jamb ɗinsu sai lokacin screening yayi suka tafi wanda cikin hukuncin Ubangiji duk suka tsallake har aka basu admission a Business Administration 100L.wannan kenan


@@@@@@@@@@@@@@@


Bangaren su Umma Kande liyafa ta cigaba don yanzu haka an canja tsarin gidan nasu,anyi painting gidan baki ɗaya sannan aka siminta gidan ya fito kamar sabo,duk wannan aikin ba na kowa bane sai na Nusaiba wacca yanzu ta zama karuwar kanta ,bata cika zama a garin ba yanzu,bata waccan state ɗin bata waccan.


Duk wannan abun da take yi bai damu Umma Kande ba,duk da ansha kawo mata gulmar layi akan maza take bi kuma tana luwaɗi amma sai ta ce ana ma ƴarta sharri da baƙin ciki don anga tanada farin jinin samari.Ƴan layi sunyi gulmar har sun saka ido don har mazan layi sukan tun kari Abbansu Sa'eeda da magana akan abinda yaransa sukeyi amma sai yace baisan yanda zaiyi da uwarsu ba koya mata magana ba amsa shi zatayi ba,gashi baida ikon yima yaran faɗa zata hayayyaƙo mai da masifa akan ya tsana yaranta,ko kuma tace yana bin zugar mazan layi,babu yanda ya iya sai dai ya zuba ido.


@@@@@@@@@@@@@


Umma Kande ce da Maman Jummalo zaune a ɗakin Umma Kande sun baje pepper soup din kaza suna ci haɗe da gwangwanin maltinarsu mai sanyi suna ci suna ƴar hirarsu cike da annashuwa.


Maman Jummalo ce ta sauya hirar tasu zuwa magana mai muhimmanci game da yaransu don ita gaskiya tafi son suyi aure akan wannan tara samarin da sukeyi gashi idan suka fita waje aita zunɗansu akan sun bar yaransu babu aure sai tara samari a layi.
Gyara zama tayi sannan tace "Ni kuwa ƙawas nazo da wata shawara akan yaran nan "


Umma Kande dake gwaguyar ƙashin cinyar kaza ta ajiye sannan ta baida hankalinta sosai ga Maman Jummalo sai ta ce "Ina jikin ƙawas hala wani alkwairi ne ya ƙara samuwa"


Maman Jummalo tace "Kinga yaran nan duk Allah ya basu samari masu kuɗi sosai gashi shekarunsu ƙara yawa yake ba raguwa ba,shi ne wani tunani ya zomin akan mai zai hana muce musu su fidda samarin da suke so ayi musu aure don gaskiya hankanlin mu zaifi kwanciya kuma zamu hutu da gulmar ƴan layi,ko ya kikace ƙawas?


Ɗan shiru Umma Kande tayi tana nazari don maganar ƙawarta na kan hanya gwara suyi aure suma su hutu da zunɗen ƴan layi da ba dama su fita sai an nunasu da yaransu,ɗan lunfasawa tayi sannan tace " Maganarki dutse ƙawas, to yanzu ya kike ganin zamu ce da su,don kinga na farin jinin samari masu kuɗi kawai muka amso musu banda na aure,kinga koda mun musu maganar aure samarin ba fitowa za suyi ba"


"Hakane ƙawas, to yanzu menene mafita" cewa Maman Jummalo


"Mafitar ɗaya ce,sai dai mu sake komawa gun boka Sankeru akan maganar auran nasu,ko ya kikace"


"Tafiyarmu wurin boka Sankeru wajibi ne gaskiya,gwara suyi auran mu huta"


Umma Kande dake matsar da tiran pepper soup ɗin ta ɗora da cewa "Yaushe kike ganin zamu je wurin boka Sankeru ɗin"


"Mu shirya ranar alhamis tunda baya son ana zuwa ranar jumma'a da litinin sai dai lahadi da alhamis" cewar Maman Jummalo


"Na tuna kuwa,Allah ya kaimu"


Da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login