Showing 30001 words to 33000 words out of 71023 words

Chapter 11 - ASHE KECE Complete By One Love .txt

One Love   

31 Jan 2025

4660

shi tayi amma ko motsawa be yi ba.








Hajiya ya kafe da idanu jijiyoyin kan shi sun fito rudu-rudu,jikin shi har rawa yake yi, mummy tace"wuce nace maka",ko motsi be yiba.






Ganin hakan yasa hajiya sulalewa ta fice daga bangaren.






Mummy tayi ajiyar zuciya, sannan taje ta rufo kofar sannan ta zo ta zauna ta dafe kan ta,daga kai tayi ta kalle shi har lokaci be motsa ba,hawaye ya zubo mata yaushe zata bar matsalolin dangin miji ne?.












Zama yayi kusa da ita ya dora kan shi a kan kafar ta.








*ASALIN SU*




Aisha shine sunan mummy, haifaffiyar garin biu ce dake borno, ta taso ta girma a jahar borno.








ta hadu da daddy ne a wani comference da akayi a abuja, lokacin yana da mata daya fatima,shekarar auren su, goma amma be taba haihuwa ba gashi suna matukar son junan su.








A haka ya nunu yana son aisha, be sha wahala sosai ba aka bashi auren ta, inda ya dawo kaduna tare da ita.






Zaman lafiya sosai suka yi da fatima, sai dai fa daddy yana da yaya guda daya wacce take jarababbiya, a dalilin jarabar ta mijin ta ya mutu shine ta dawo wajen daddy da zama, don bazata iya komawa wajen yayan su da zama ba dan yana da zafi sosai.






Tun da tazo ta sawa fatima idanu da habaici,da gori ana haka yayan su yazo ya takura ta ta kuma yin aure.








Shekarar aisha daya a gidan allah ya bata haihuwa,babu kishi ba komai fatima tayi farin ciki da yaron.






Ita ke mishi komai, idan ka ganshi a wajen aisha to nono zai sha,sun shaku da saifullahi sosai.






Sai dai fa duk da haka hajiya rabi takan baro gidan mijin ta tazo ta yiwa fatima gorin haihuwa.






Hakan ba karamin damun ta yake yi ba, amma aisha takan kwantar mata da hankali.




Soyayyar ta da saifullahi karuwa take wanda hakan ke kara mata kima a wajen mijin ta da abokiyar zaman ta.






Yau tun da ta tashi da zazzabi, kasancewar daddy baya nan yasa aisha ta kai ta hospital, gwajin farko a ka tabbatar da shigar cikin wata biyu.






Kowa yayi murna a familyn musamman saifullahi domin yana murnar samun aboki ko kanwa.






Lokacin saifullahi nada shekara biyar fatima ta haifi yaron ta kyakkyawa, murna wajen mutanen gidan ba'a magana.






Hajiya rabi babu kunya take dashe baki a dole dan uwan ta ya fara samun yara.






Ranar suna yaron yaci suna *abdul maleek*sun taso cikin son juna shida dan uwan shi.






Babu abinda suka nema suka rasa daga iyayen su, sai dai fa daga aishar har fatiman babu wanda ya kuma haihuwa.




Gorin hajiya rabi sai ya dawo sabo,wanda hakan ya kara daga hankalin su sosai.








Suna haka suna addu'a allah ciki ya bayyana a jikin aisha,to fa sabon farin ciki ya sake ziyartar gidan.








Cikin na kaiwa watan haihuwa allah ya azirtata da yarinya mace, sun yi murna sosai da sosai.






Sati na zagayowa yarinya taci sunan fatima, suna ce mata zahra.




Yarinyar nada shekara hudu a duniya taje makaranta aka neme ta aka rasa, wanda hakan ya daga hankalin yan gidan.






Maleek ya samo sunan *lily*ne saboda son *lily flower*da yake yi, wannan yasa duka gidan suke kiran shi da haka.






Shi kuma yake kiran dan uwan shi da *lovely*shekarar maleek takwas a duniya saifullahi kuma nada goma sha uku allah yayiwa fatima rasuwa.






Mutuwar data razana gidan gabaki daya kenan,rashin kwanciyar hankalin da yaran suka kasa samu yasa daddy tura su kasar india, inda suka cigaba da karatun su acan.


hajiya rabi kuma tana da yara mata guda uku, babbar su itace,shamsiyya sai sadiya da bintu.






Tunda bintu ta kyalla ido taga maleek zuciyar ta ta kamu da son shi, yayin da ita kuma sadiya ke mutuwar son saifullahi.






Ita dai shamsiyya ce babu ruwan ta da maza, harkar ta take yi kawai wanda yanzu haka business take.


Ita kam sadiya kamar ba hajiya rabi ta haife ta tana da saukin hali da hakuri, inda bintu ta debo masifar hajiya rabi.






Mutum daya take saurarawa maleek shima dan tana son shi ne, sai saifullahi shi kam dama baya shiga harkar ta.




*WANNAN KENAN*.




Yau ikhlas sauri take a tashi aiki ta wuce gida domin irin gajiyar data yi.








Tun da suka nufo ta ta gane shi sai dai bata wani tada hankalin ta ba,shikam maleek be ma lura da ita ba.






Yana faman yiwa abokin shi idris, ajiye kayan yayi domin ta irga, cikin natsuwa ta fara irgawa har ta gama.






Juyowa yayi domin mika mata atm suka hada ido, dogon tsaki yaja sannan ya kalle ta kallon kyama da tsana yace"ke kam akwai mayya uban me kike a kaduna kuma? ",








Matsowa ya kuma yi yace"wane tsohon najadun kike tunanin zai kwashe ki?, wato kin gama dana kano da gombe kin dawo kaduna,to ki sani matukar baki tattara kayan ki kin bar kaduna ba zaki sha mamakin abinda zan yi miki, banza karuwa kawai".






Murmushi tayi tace"sir your balance is 89k",shako ta yayi yace"kada ki kuma yi mini magana idan ba haka ba zan wulakan ta rayuwar ki, banza karuwa".






Manager da sauran mutanen wajen ne suka karaso, cikin sanyin murya manager din yace"sir kayi mata hakuri dan allah baza ta kuma ba",kallon gargadi ya aikawa manager din kan ya sake ta ya juya ya fice.








Ikhlas na ganin ya fita ta koma ta zauna, manager ya fara mata fada,"haba ikhlas muna jin dadin aiki da ke yanzu kuma kina so ki saka wasa a ciki", fada sosai ya kama yi mata wanda ran ta ya bace sosai.








Kuka ta fashe dashi me tsanani,kifa kan ta tayi a table din gaban ta wannan waye yake kokarin dagula mata lissafi"banza karuwa",kalmar da ta rinka yawo a kan ta kenan.




Wani tsanar shi taji a zuciyar ta wato tabar kaduna kamar wani garin uban shi,to bata gano izan unan shi meda kadunar.








Kwankwasa table din idris yayi, dagowa tayi ganin abokin shi ne yasa taja tsaki ta galla mishi harara, kallon ta yake yana murmushi cikin zafin rai tace"lafiya malam? ".




Atm card ya miko mata, fuzgewa tayi sannan ta saka a atm machine din ta cire iya kudin su, sannan ta ajiye mishi ta mike tabar wajen.






Da idanu ya bita yana murmushi, wata abokiyar aikin ta ta kira ita kuma ta bude wata kofa ta shige.






Dariya yayi sannan ya dauki kayan da atm card din ya fice, besa ran maleek zai jira shi ba, haka kuwa be jira shin ba, mai keke napep ya tare sannan ya fada mishi inda za shi.








Yana tafe yana tuno yadda take masifar ta da komai yana burge shi yayi, a hankali ya furta"maleek rigimamme kenan, wato tsabar masifa data rufe mishi idanu be lura da kyan yarinyar ba".






Can kuma yace"to kodai love fight ne? ", mai keke yace"malam magana kake ne", idris yace"a'a cigaba da aikin ka kawai".






Bangren maleek kuwa a zuciye ya bude motar ya fito bayan ya isa gida.






Bintu dake faman mishi magana, cikin fusata ya juyo ya tsinke ta da mari, hajiya tace"kai maleek ka fita ido na tarinyar tawa kake duka, to kuwa baka da mata sai ita".






Cikin fushi yace"idan ke zaki daura auren ba sai ki auren ita na gani ba, me zan yi da wannan abu kamar muciya da zani".





Yana fadin haka ya wuce ya bar ta tsaye tana faman surfa masifa, bangaren shi kawai ya wuce.






Kan gado ya fada yana huci, lallai yarinyar nan zata dagula mishi lissafi dole ya takura ta tabar kaduna ko kuma shi ya bar ta, haka ma za'a yi domin ko matsalar hajiya ta ishe shi.


















💮💮💮💮💮💮💮💮
*ASHE KECE???*💮💮💮💮
(Hypocrite-love-sacrifice)






https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


✍✍✍✍✍✍✍
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION~*
✍✍✍✍✍✍✍




*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*




Wattpad @13 deeja


Or
Deeja1love.blogspot.com


*written
-by-
*Deeja one love*






*dedicated
to
*Maryam khamis*




*sis harira aliyu (jinnul aashique) wannan page din na sadaukar dashi gare ki, kiyi yadda kike so dashi*.


Na gode da yadda kike bibiyar littafi na.












33-34






Ita kuwa ikhlas tana shiga, rest room ta fashe da kuka_banza karuwa_wannan kalma ita tafi mata ciwo a rai.








Wajen manager taje ta dauki excuse,domin tafiya gida, shi kam manager ganin abinda ya faru yasa ya barta.








Makarantar su baby ta wuce ta je ta dauke shi sannan ta wuce gida,gaba daya bata da walwala.






Tana zuwa, wanka tayi ta kwanta ta shiga tunani, baby ya turo kofar ya shigo, ganin ta a kwance ya zauna kusa da ita.








Cikin kulawa yace"baby baki da lafiya ne? ", daga mishi kai kawai tayi,bed side drawer ya bude ya dauko sudrex ya miko mata.








Fita yayi babu dadewa ya dawo da ruwa a glass cup, murmushi tayi sannan ta amsa ta sha,gyara mata blanket yayi sannan ya ja mata kofa.








Yana fita tayi murmushi domin yaron allah ya bashi hankali,wayar ta ta fara ringing,a hankali ta janyo wayar.








Cikin nutsuwa take amsar wayar, zaro idanu tayi tace"zuma na da gaske ranar juma'a zaka dawo kaduna? ".






Yace"princess bazan iya jurar rashin ki bane shiyasa, kawai na ajiye aiki gwara na dawo kaduna na cigaba".








"To yanzu idan ni kuma na koma kano din fa? ", ta fada cikin tsokana.






Cikin sauri yace"kin isa ma, tab aikuwa da nima kano din zan dawo", dariya suka yi gaba daya.






Haka suka cigaba da firar su har ta manta da abinda maleek yayi mata.








Sai yamma sannan ta tashi, wanka kawai tayi ta shirya sannan ta fito parlour, baby dake zaune ya juyo yace"baby wannan wankan fa? ".








Dariya tayi tace"nayi kyau ne", yatsu biyu ya hade mata alamar yayi,cikin farin ciki yace"ko zamu shiga gari ne? ",ya fada yana kashe ido daya.






Gaban ta ya fadi, domin sak yadda baban shi yake yi kenan,ajiyar zuciya tayi tace"shirya muje kaji".








Da sauri ya tashi yaje ya shirya, cikin annashuwa suka fice daga gidan,wajajen shakatawa suka dinga zuwa.








Kowa ya gansu sai yayi tunanin dan data haifa ne, dan mutane da yawa suna son zuwa wajen ta amma ganin baby sai yasa su fasa domin suna tunanin ko tana da miji.






Amma da yawa sukan ce wannan wane kalar wawan miji ne da zai bar mace kamar wannan tana yawo a gari.






Suna parking a fahad stor, baby yace"ah baby ki shiga bari na dawo", kallon shi tayi kamar zata ce wani abu sai ta fasa.






Da sauri ya koma ita kuma ta shiga ciki,sauri yake domin ya dauko tab din shi dan yana so suyi pics da mum din shi.








Yana rufewa shi kuma ya bude kofa, faduwa yayi, jin zafin da yayi yasa yayi kara,cikin sauri na motar ya fito.






Ganin yaro kyakkyawa yasa yayi saurin dago shi,shafa kan shi yayi yace"sannu fa aboki me kake a nan? Ina maman ka da baban ka? ", duka ya jefo mishi tambayar.








Baby ya bi tab din shi da kallo, da sauri shima ya juya yana kallon inda tab din take,"oh gosh! Ya haka?, da sauri ya dauko.






Ganin taci screen yace"aboki sai dai mu shiga ciki a canza ta domin wannan ta sami matsala".




Matse kafada yayi yace"akwai abubuwan da nake so a wannan, beside ma ban san ka ba sai na bika".






Murmushi yayi yace"sunana daddy, muje ciki", yana fadin haka ya rike hannun shi suka shiga.






Ikhlas kuwa ganin ya dade be shigo ba yasa hankalin ta tashi, cikin sauri ta fito domin neman shi.






Ganin baya wajen motar yasa gaban ta ya fadi, a rude take tamabayar mutanen wajen ko sun gan shi.




Dama neman damar suyi mata magana suke nema hakan yasa suka fara mata kwatance, kowa da hanyar da zai nuna mata ya bi.




Cikin tashin hankali ta shiga mota tana bin hanyar da suka gaya mata,wayar da bata gani ba yasa ta gane tana wajen shi hakan yasa ta fara kira, amma iz not reachable.










Cikin tashin hankali ta dawo bakin super market din,clashing suka yi wanda kayan hannun shi sai da suka zube.








Da sauri ta tsuguna domin kwashewa, shoma haka,bayan ta gama ta dago don bashi hakuri,suna hada ido ta daure fuska.








Cikin fusata ya daga hannu ya tsinke ta da mari,hannu ya daga ya nuna ta yace"ni kam na tsane ki wallahi, wai ke wace kalar mayya ce, ki dena bibiya ta haka, banza karuwa kawai, mtsewww", yaja tsaki.








Juyowa tayi ta kalli compound din, kusan kowa harkar gaban shi yake yi,ganin hakan yasa tayi ajiyar zuciya.






Shi kam maleek, hannun baby wanda shi wasa yake da teddyn hannun shi be lura da abinda ya faru ba.






Juyawa tayi ta kalle shi,ganin baby a tare dashi, zaro idanu tayi tana mamakin me ya hadasu.








Cikin fusata ta nufi wajen, finciko shi tayi sannan ta kwace kayan hannun shi ta wurga mishi.








Nuna shi tayi tace"gwara ni a karuwan ci na tsaya bana satar yaran mutane,sannan ka sani kamar yadda ka tsanane ni haka na tsakane ka, banza mata-maza kawai".






Tana gama fadin haka ta ja hannun baby ta bude mota ta saka shi ta tada ta bar wajen, cikin sauri.






Bangaren maleek kuwa tsayawa yayi kawai kamar statue, tabbas yarinyar nan ta fara crossing limit din ta.








Cije lips yayi tunowa da yayi wai "mata-maza",kamar yayi ihu haka ya ji,kallon kayan da ta watsa mishi yayi ya juya a fusace ya bar wajen.






Baby kuwa a mota sai kuka yake yi, ganin ba zai yi shiru bane yasa ta tsayar da motar tace"kayi mini shiru ko na wanka mari, wawa wanda baya kishin mum din sa".






Shuru yayi yana ajiyar zuciya, ita kuma a fusace ta tada motar ta bar wajen.








Tana zuwa gida tayi parking, ko kula shi bata yi ba ta fice daga motar,bedroom din ta ta wuce kawai ta haye kan bed din ta.








Cikin sanyin jiki ya shigo dakin,tunda ta dago ta kalle shi ta maida kan ta,ajiye key din motar yayi ya hayo kan bed din.










Juya fuskar ta tayi,a hankali ya rungume ta yace"mummy kiyi hakuri kinji, bazan kuma zuwa wajen wani wanda ban sani ba".








Banza tayi dashi, hakan yasa ya fara kuka, jin kukan ahi yasa tayi saurin mikewa, ta kalle shi tace"baby kayi shiru kaji komai ya wuce".








Kan shi ya dora akan kafar ta yace"mummy kece kika ki kula ni",shafa kan shi tayi tace"ya wuce yanzu muje muyi girki".








Da sauri suka mike suka nufi kitchen din hannun su sarke da juna, indomie suka dafa sannan suka dawo parlour suka ci kamar babu abinda ya faru.










Bangaren maleek kuwa a fusace ya isa gida, bangaren mummy ya shiga tun daga parlour yake kwala mata kira.










Cikin sauri ta fito, rungume ta yayi yana fadin"Mummy a yau an yi disgracing dina", da sauri tace"subhanallah! Waye wannan? ".






"Wata yarinya ce", da mamaki tace"maleek mace fa kace?, haba dai yanzu ai bana tunanin akwai macen da zata wulakanta ka, kodai kai kayi mata laifi?".








Shafa kai yayi yace"mummy yaron ta na taba shine fa ta wulakanta ni",kallon shi tayi tace"tashi ka bani waje maleek, matar aure kuma? ",.






Cuno baki yayi yace"mummy bafa tada aure",murmushi tayi tace"oh! Dama kasan ta kenan",da sauri yace"a'a mummy, ni yau na taba ganin ta",dariya kawai mummy tayi.
















Ikhlas ke zaune bayan sallar isha'i baby kwance kan kafar ta yana barci, wayar ta ta fara ringing.






Dubawa tay, ganin nabeelert yasa ta daga, cikin farin ciki tace"baby ya dai? ".








"Dole zaki fadi haka mana, tunda kin koma yar kaduna, kin manta damu ko?,ko dan kiran nan bakiyi".








"Haba dai beelert ba haka bane, wallahi kin san yanayin aikin mu,babu hutu sosai da sosai yadda ya kamata, to yanzu ya su hafsat da feenert".








"Feenert nacan gidan su, hafsat kuwa gata nan, nima gobe nake son shiga gombe, domin naga ya harkokin can yake tafiya".








"Hakan yayi amma ki bari, sai next week domin bana so a sami matsala, kin san idan bamu gama da wancan dan iskan ba akwai matsala".








"Kamar ya fa?,kin san da bukatar naje can din ko, saboda meetings din da za'ayi".






"Kada ki damu zan kira asp abdallah sai ya je can din, kin san dai company din ki babba ne, yan jarida zasu iya bukatar fira da CEO na company din, kin ga kuma kabeer a garin yake".






"Hakane kuma,shikenan zan hakura din idan yaso mext week din sai na je".








"Ai kada ki damu beelert, amma zuwan ki gombe ki hakura ba yanzu ba, na fiso ki bari idan kabeer yazo kaduna sai ki je can".






"Hmm, hakane kuma, yaushe zamu zo kadunan? ".








"Nan da two week, insha allah,idan kun zo sai kuji plans din, sannan zan kira asp abdallah na gaya mishi".








"Shikenan, ki shafa mini kan baby",daga haka suka rabu.






Tana ajiye wayar wani kiran ya shigo, cikin farin ciki ta daga.








"Assalamu alaikum, zuma na",ajiyar zuciya yayi kafin yace"wa'alaikumus salam, princess har na kosa gobe tayi na dawo wallahi".








Dariya tayi tace"kada ka damu zuma na,insha allah da yau da gobe duka daya ne",haka suka cigaba da firar su cikin nishadi kafin suyi sallama.










Maleek ya kalli yayan shi yace"lallai na yarda princess ta murza kambun ta, babu yadda mummy bata yi ba akan ka dawo kaduna kaki amma yau a dalilin princess ka dawo".










Yace"kasan me yasa bana son dawo wa garin nan da zama, na farko matsalar mummy da zata dame ni akan na fito da mata, na biyu kuma wannan rigimammiyar hajiyar".








Jin ya ambaci hajiya yasa ya ja tsaki,hannhn shi saifullahi ya rike yace"ka tashi ka shirya muje wajen princess yau".








Maleek ya gyara kwanciyar shi yace"lovely na gaji sosai, sannan ina tsoron na fita yanzu a kaduna wallahi, saboda ina fita nake haduwa da wannan karuwar".








Dariya saifullahi yayi yace"haba dai kamar wata aljana, kun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login