Showing 18001 words to 21000 words out of 71023 words

Chapter 7 - ASHE KECE Complete By One Love .txt

One Love   

31 Jan 2025

4676

pampers,sai da ta kwantar dashi sannan tace"iman wallahi ina da gaskiya ta kawai kina zargi na ne kuma ba haka bane", mikewa iman tayi ta fita.








Sau hutun su ikhlas ya kare dan haka ta tattara ta koma kano,gidan da ta nemi saifullahi ya siya mata ta tarar da ya siya,kallon shi tayi bayan ta gama zagaye gidan tace"zuma na gida yayi na gode sosai",hannu ya dora akan leben shi yace"kada ki damu komai zan iya yi miki",murmushi kawai tayi.






Kasancewar shi din babba ne yasa suka sami abinda suke so, dan haka yanzu sun koma business admin.






Yau sun dawo daga lectures,feenert ta kalli ikhlas tace"har yau baki kuma yi mini magana akan wa'inan mutanen ba? ",ikhlas tayi murmushi tace"to meya faru ne? ",ajiye jakar ta tayi sannan tace"ya kamata ki shirya muje gidan tukunna", bedroom ta wuce ta bar ta a falo.




.






Sai da ta shirya sannan ta fito suka tafi, a hanya ta dubi feenert tace"wallahi baki ji ba ina ji zan cewa iman ta turo mini da baby, hankali na be kwanta da zaman shi a can ba", murmushi kawai tayi.












Hotoro suka sauka,sai da suka nuna card sannan suka shiga,wani tangamemen gida suka buga, sai da wani police ya leko ya gansu sannan ya barsu suka shiga.








Ita dai ikhlas bin ta kawai take yi,sai da suka wuce get uku sannan suka shiga ainihin gidan.






Wata yar yarinya suka tarar a falo,da murna ta tare su,sannan ta wuce, wajen minti biyar sannan wannan suka fito,da sauri feenert ta mike ta tare su, rungume juna suka yi sannan suka suka zauna.








Wannan yarinyar ta kawo musu abin motsa baki, sai da suka gaisa, sannan feenert tace"hafsat wannan itace wacce muka je gidan su kin gane ta ko? ", jinjina kai tayi tace"na kuwa gane ta sosai ma,ikhlas cat eyes ko", dariya suka yi gaba daya.








Feenert ta kalli ikhlas tace"sis wannan itace beelert wannan kuma itace hafsat baban ta shine minister of education zata gabatar miki da kanta dai",murmushi ikhlas tayi kafin tace"nifa sis bangane bayanin ki ba",beelert tace"yanzu zaki fahimta",.








Gyara zama tayi kafin tace"ni da kika ganni sunana nabeelerh abdulmalik fantami, mahaifina shine chief of justices na nigeria gaba daya.






Ni kadai ya haifa mahaifiya ta tun a wajen haihuwa ta ta rasu, nayi rayuwa tajin dadi har na girma,dan a kasar waje nayi gaba daya karatu na,hafsat ma acan muka hadu da ita,duk gata da kika sani na samu a wajen mahaifi na, ban dawo kasar nan ba sai da na zama babban lawyer me zaman kan ta".










Bayan na fara aiki baba na ya fara nema mini mijin da zan aura,ganin cewa yanzu maza basu fiye son mace da tayi zurfin karatu ba,hakan sai ya so ya damu mahaifi na domin dai duk yanda yake tunani abin yafi haka".










nima tun abin baya damu na har yazo ya fara damu na, muna wannan halin sai dan aminin baba na ya dawo daga england, yana dawowa ya nuna ni yake so".










"Wannan abu ya faran ta ran mahaifi na sosai, sati biyu aka daura aure na da kamal,farkon auren mu lafiya lau muke zaune cikin so da kauna har tsayin wata takwas, a lokacin Allah ya yiwa mahaifi na rasuwa.








Kamal da mahaifin sa da mahaifiyar sa su suka kara mini karfin gwiwa da nasihohi da lallashi, watarana muna zaune, mahifin kamal ya aiko da takardu akan nayi signing".








Banji dar ko wani abu ba nayi signing duka,tun daga lokacin komai ya canza,abinda zan ci sai ya gagare ni,ga karamin ciki a tattare dani,gashi kwata-kwata basu damu dani ba.






Kamal na gane ina da ciki ya tada ballin sai na zubar, hakan dashi da mahaifiyar shi suka dinga kunta ta mini, karshe da daddare na gudu,gudun da nasha domin fitowa bakin titi yasa mara ta kullewa.






Da kyar na karaso bakin titi, kan jiri ya kwashe ni na fadi,hafsat kawata ita ta ganni ta dauke ni ta kawo ni garin kano domin na zauna anan sai dai fa cikin ya zube.






Daga baya na hadu da feenert a facebook shine ta bani labarin kan ta da kuma naki, shine naji mai zai hana inzo mu hadu may be mu taru mu taimaki juna".






Zufa ta goge sannan ta kalli feenert ta galla mata harara tace"wato daga haduwa da mutum a social net shine harda sakin baki kina bata labarin ki ko? ",shiru feenert tayi.








Kallon ta tayi tace"gaya mini me kika bata labari wanda da gani ni bansan shi ba",murmushi feenert tayi tace"da farko dai kiyi hakuri wani tunani nayi na cewa ya kamata mu hadu mu taimaki juna shiyasa, kuma ta bani labarin ta sai naga why not nima na bata nawa", tsare ta da idanu ikhlas tayi.








Dan bata rai tayi tace"ni dan allah ki dena kallo na haka wallahi har tsakiyar kaina nake jin kallon",ikhlas tayi murmushi tace"bafa abinda na tambaye ki kenan ba, da alamu kin boye mini wani abu",hafsat tayi murmushi tace"ikhlas mu fara yin sallah tukunna mu ci abinci then sai ta baki labarin",kallon ta tayi kafin tace"ok",






Duka mikewa suka yi suka hau sama,wani daki ta bude wanda yayi kyau sosai da sosai,bathroom ta nuna musu tace"mu fara alwalar",shiga suka yi daya bayan daya.






Bayan sunyi sallar sannan habeeberh(me aikin hafsat) ta kawo musu abinci, zama suka yi suka ci sosai,.








Jeruwa suka yi a bakin gado,ikhlas ta kalli feenert tace"oya ke nake jira malama",.






Hawaye ta share sannan tace"ni dai................









To! Ku biyo one lurhv๐Ÿ˜˜domin jin labarin nafeesert.












๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ
*ASHE KECE???*๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ
(Hypocrite-love-sacrifice)






*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATON~๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ*


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~โ„we beare's of soon golden we writer's assiduously percieven No pain so magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Out worlds for it cause u np pain~*




Wattpad @13 deeja


Or
Deeja1love.blogspot.com


*written
-by-
*Deeja one love*






*dedicated
to
*Maryam khamis*
Aunty Feenert (matar soja) dis page is urs,na baki shi kema kiyi yadda kike so dashi.
21-22


Wayar ikhlas tayi kara,kallon mai kiran tayi kamar baza ta daga ba sai da ta katse aka sake kira sannan ta kalli su hafsa tace"excuse me pls,"sannan ta mike ta fita.






Bayan some minutes ta dawo,zama tayi sannan ta kalli nafeesert tace"bismilla muna jin ki",murmushi tayi mai matukar ciwo sannan tace"..................










kamar yadda kuka sani, suna na nafeesert jibril jasawa, haifaffiyar garin jos,mu hudu iyayen mu suka haifa, mun taso cikin rufin asiri da kwanciyar hankali tare kaunar junan mu.




Nice ta biyu, sai kanne na guda biyu,fahad shike bina sai autar mu naja'atu,babban mu kuwa sunan shi kamal.










Bayan na gama secondary baba na ya bani waya,a lokacin na samu damar dora karatu na,mass com suka bani, na fara karatu na cikin sa'a.








Akwai wani mus'ab dan yayan baban mu ne,tun ina secondary muke tare, muna son junan mu sosai,ana haka na fara chat.








Sosai hakan ke debe mini kewa, kuma chat baya hanani karatu, har zuwa lokacin da muka hadu da kabir,a wani group a facebook.








Bayan mun yi barkwanci haka sai ya turo mini friend request, ni kuma nayi comfirm,tun muna gaisawa har ya zama na mun shaku sosai, idan baya online bana jin dadi haka shima.




Har ta kai ga mun yi exchanging number,ya kan kira ni mu gaisa har ma muyi fira, kalmar so tun bata shiga tsakanin mu ba har ta kai ga ya furta mini,a lokacin fa muka sake wata shakuwa sosai duk da bamu taba haduwa ba.












Kawai watarana muna waya ya nuna ya kamata mu hadu, a lokacin na nuna mishi cewa bazai yiwu ba tun da baba na yana sa idanu akan mu sosai.








Cikin shagwaba yace"dama nasan baki damu dani ba kamar yadda na damu dake",yana gama fadin haka ya kashe wayar,kwana daya biyu uku shiru be kira ba.






Hankali na ya tashi sosai, duk wanda na sani suna da connected dashi sai da na kira amma shiru.






Watarana ina zaune kawai sai ga kiran shi, jikina har rawa yake na daga,cikin damuwa nace"haba honey wannan shariya haka? ", murmushi yayi kafin yace"to ai kece darling gaba daya na lura baki damu dani ba kin fi damuwa da wancan me ma sunan shi", cikin sauri na karasa da"mus'ab",kwafa yayi yace"kinji har da wani saurin karasawa, nan dai muka yi fira dashi sosai da sosai.








Ranar cikin farin ciki na yini,daga nan muka dawo lafiya lau,har na bashi number din mus'ab,sai dai bai taba kiran shi ba, zuwa wani lokaci ya kara bijiro da maganar haduwa.






Ina tsoron fushin da zai yi dani yasa nace"to akwai aunty na dake gombe zan ce zan je wajen ta idan yaso sai mu hadu(tun da dama dan gombe ne), cikin murna muka rabu.








Kafin na shirya tafiya gombe sai da yasan yadda yayi na bashi number din mus'ab,ana haka na tari mama na da maganar cikin sa'a kuwa ta barni haka ma baba na.






Sallama nayi dasu na tafi, tun akan hanya na kira shi nace masa mun taho, ina kuwa zuwa ya tare ni a motor park,taxi ya sama mana, sai dai me a hotel muka tsaya.






Kallon shi nayi da mamaki nace"meye haka kabeer? ", murmushi yayi yace"just relax bafa wani abu bane kawai abu zan nuna miki mu wuce", gudun laifi shi yasa nayi shiru.








Muna shiga reception ya amshi key din daki muka shiga,gabana ke faduwa amma duk da haka ban fasa bin shi ba.






Muna bude kofar muka shiga,flowers aka jera daga kasa har saman bed,nan kuma anyi designing heart,daga jikin bango kuwa wani bulb ne ke walwali,yana rubuta*WELLCOME TO GOMBE*MY HEART*,abin ya bani sha'awa sosai da sosai, na shagala da kallo kawai naji an rungume ni ta baya.






Cikin sauri na juyo, kabeer na gani yana mini murmushi,hade rai nayi nace"meye haka ne?kaga ka tashi mu tafi haka",murmushi ya kuma yi kafin yace"yanzu zamu tafi sweet, but kan nan kawo hannun ki",zobe ya ciro mai kyau da nufin na mika hannu yasa mini.






Dana mika hannun maimakon yasa mini sai ji nayi ya fara shafa hannu na kan nayi wani yunkuri ya janyo ni ya fara kissing dina(wallahi da gaske hakan ya faru dan wata kawata ta bani labarin hakan ya faru da ita, sai dai dan wani abu kadan dana kara,ya Allah! Samari mai kuka maida kanku yanzu ne? ,yan mata mai yasa baku tunani mai zurfi n?Allah ya datar damu, ameen).




Tana zuwa wajen kukan ta ya karu,shiru dakin yayi, dan hafsat har ta fara taya ta kukan,murmushi kadan ikhlas tayi kafin tace"sai me ya faru? ",feenert tace"me kuwa zai faru a tunanin ki a wannan lokacin? ".






Ikhlas bata kuma cewa komai ba wannan yasa, dakin yayi shiru,ikhlas ta kuma katse shirun ta hanyar cewa"meya dawo daku kano".






Feenert tayi ajiyar zuciya tace"bayan wannan abin ya afku, yayi ta lallaba ni har ya samu na koma jos,muka cigaba da waya da komai dashi.






Haka aka zo aka mana baiko nida mus'ab,sai dai fa komai nawa a sanyi nake yin shi, ana saura sati daya biki ciki ya bayyana,ranar naga tashin hankali,mama kuka kawai take yi, baba kuwa anan ya fadi hawan jinin sa ya tashi,kuma yace kada na sake naje inda yake.








Tun ina ganin abin wasa ne har na tabbatar da gaske ne, fitowa ta gagare ni dan duk inda na bi mutane na tsegumi na,hakan yasa na dena fita.








Abin mamaki har yan uwan baba na suka fara nuna kyama a gare ni wanda hakan yasa baba na yayi shawarar mu tashi mu bar garin, to amma wane gari zamu koma?,shine fa abokin shi ya nemo mishi gida muka dawo.






Abin mamaki tun da na gayawa kabeer ina da ciki shikenan ya dena kira na, aure na da mus'ab dama ba'a maganar shi dan ya tashi.




A nan kano na haifi yarinyar wacce taci suna *suhaila*yanzu haka shekarar ta uku kenan,tana wajen mama, itace wacce kika gani ranar da kika zo gidan mu kwanaki.






Har yanzu kabeer be kuma kira na ba nima kuma ban kuma neman shi ba, a lokacin da muka hadu naso na baki labari sai dai ganin kamar baki wani damu dani ba yasa na kyale ki, amma kiyi hakuri.








Zuba mata idanu kawai ikhlas tayi,bata rai feenert tayi tace"na gaya miki bana son wannan idanun naki a kaina wallahi har tsakiyar kaina nake jin shi.






Murmushi kawai tayi sannan ta mike, taku biyu tayi kafin ta juyo tace"dole idan muna bukatar wannan aikin ya zama na muna da lawyer da kuma police, sannan dole ya kasance mu hakura har mu kammala karatu gudun samun matsala a makaranta",duka sun yarda da shawarar ta.






Hafsat tace"baki da masala da wannan my brother is a lawyer,sannan my nephew is an ASP(assistant superintendent of police)na gombe state, i think he may help us", jinjina kai ikhlas tayi kafin tace"in dai kudi ne kuma nasan bama da matsalar wannan",daga haka taron ya watse.






Sai da suka yi dinner sannan suka tafi gida,feenert ta ajiye ikhlas a gida,sannan ta wuce.






Wanka tayi ta canza kaya zuwa na shan iska kafin ta daga wayar dake ringing tun dazu.






Ajiyar zuciya yayi kafin yace"princess kina wahalar da zuciya ta",murmushin gefen baki tayi kafin tace"zuma na wallahi abubuwa ne suka sha mini kai",numfasawa yayi kafin yace"gani nan zuwa", kashe wayar yayi, wayar tabi da kallo tana murmushi.








A yadda take haka yazo ya same ta,da farin ciki ta tare shi,da idanu yake bin ta,gira daya ta daga mishi akan lafiya?ajiyar zuciya yayi yace"princess ban san wane kalar so nake miki ba wallahi,pls kada ki guje ni", yadda ya koma kalar tausayi yasa jikin ta yayi sanyi.






Haka dai suka cigaba da firar su har wajen ten sannan ya tafi,har mota ta rako shi,hannun ta ya rike yace"princess ki kula mini da kan ki kinji", daga kai tayi tana waving mishi hannu har ya bar gidan, ajiyar zuciya tayi sannan ta koma cikin gidan.






Tun daga lokacin wata irin shakuwa ta shiga tsakanin kawaye hudun, sai dai har lokacin ikhlas bata bari su rakata bauchi.






Ta bangaren saifullahi kuwa soyayyar ikhlas karuwa take a wajen shi.






Yau ikhlas take shirya kayan ta domin wucewa bauchi, kamar koda yaushe, saifullahi ya dauko ta domin kai ta motor park.






Murmushi tayi tace"ni kam ina so naga wannan lilyn baka da magana sai tashi"dariya yayi daga gani yana ji da wannan kanin nashi.






Kallon ta yayi yace"kada ki damu princess ya kusa dawowa, yana dawowa zan hadaku",jinjina kai tayi alamaar gamsuwa.








wayar shi ce tayi kara, kallon ta yayi cikin sauri ya dauka yana fadin"lily ina driving idan na koma zan kira ka",shiru yayi da alama magana yake yi, sai dai yadda yake murmushi zai tabbatar maka da yana matukar son wanda yake magana dashi.








Langwabe kai yayi alamar ban hakuri kan yace"am so sorry,i promise you that muna yin hutu zan zo na duba ka",shiru ya kuma yi kan yace"lily ina hanya ne zan kai auntyn ka motor park",still na can bangaren magana yake yi,saifullahi yace"lily rigima to yi hakuri gata", mikawa ikhlas wayar yayi.








A nutse ta ansa,
"Assalamu alaykum",
"Wa'alaykumus salam, aunty na ya karatu? ",murmushi tayi kafin tace"lafiya lau ya naku",sai da ya dan yi jim kan yace"alhamdulillah, muna ta fama..... Kullum ana bani labarin princess yau dai gashi muna waya koma ki damu dani"ya karasa maganar da shagwaba.






Tsigar jikin ta ne ya tashi cikin sauri tace"ba haka bane time ne beyi ba mu gaisa, yanzu da time yayi ba gashi muna gaisawa ba", murmushi yayi wanda sai da taji sautin shi har cikin kan ta sannan yace"hakane,lovely yace wai baki so ya kai ki gida? Meyasa?".






Wayyo ikhlas ita da ta saba tsare mutum yau gashi itama an tsare ta cikin sauri tace"saboda tafiyar da nisa mana",murmushi yayi yana kwaikwayar muryar ta wanda hakan ya bata dariya, ta kuwa dara.






Saifullahi kuwa farin ciki kamar me,mutanen da ya fi so suna fira cikin nishadi.






Itakam ikhlas turo baki gaba tayi sannan tace"meye na mini dariya", dariya ya kuma yi kafin yace"da alamu aunty na raguwa ce, kani kike yiwa shagwaba", wayyo kamar kasa ta tsage ta shige haka taji,ta gefen ido ta kalli saifullahi, idanun shi nakan titi amma da alamu hankalin shi yana kan su,thank god ma baya jiyo firar su.






Muryar shi taji yana fadin"are you there?hello",uhum kawai tace,dariya ya kuma yi kafin yace"tun da sai na roka ya sunan auntyn tawa? Ko na cigaba da cewa princess din nima", ya fada cike da tsokana.






A hankali tace"ai dan uwan ka ya kamata ya gaya maka bani ba",kara shagwabe fuska yayi yace"haba princess dan gaya mini mana",oh gaba daya wannan so yake ya birkita ta cikin kagara tace"kai ma ai baka gaya mini sunan ka ba",murmushi yayi yace"kawai kice lily",lily ta sake maimaita sunan.








Ajiyar zuciya yayi yace"wayo kike so kiyi mini abi?da mamaki tace"me?dariya ya kuma yi yace"shekarar ki nawa ne?"cuno baki tayi tace"47",a hankali yace"to ai kin kusa haifar lovely ma kenan",daga kai tayi kan tace"eh mana.




"Sugar mummy gaskiya bama so"ya fada yana dariya,cikin shagwaba tace"bana so Allah ka dena", da sauri ya katse kiran yana fadin"bye.






Murmushi tayi tana bin wayar da kallo,dago idanu tayi karaf ana saifullahi, murmushi kawai taga yana yi,cikin wayan cewa tace"ka kalli gaban ka", murmushi yayi ya nuna mata da ido,zaro idanun ta tayi tana fadin"har mun iso? ", dariya yayi kawai ya bude ya fito.




As usual sai da ya biya mata kudin mota sannan ya tafi,a hanya babu abinda take tunawa sai firar ta da lilyn saifullahi, murmushi kawai tayi kan ta ciro wayar ta.






Feenert ta kira tace"mun tashi yanzu fa", allah ya kiyaye hanya tayi mata,haka ta kira beelert da hafsa suma dai haka allah kiyaye hanya suka yi mata.










๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ
*ASHE KECE???*๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ
(Hypocrite-love-sacrifice)






*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATON~๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ*


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~โ„we beare's of soon golden we writer's assiduously percieven No pain so magical Our creative golden pen Be

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login