Showing 21001 words to 24000 words out of 71023 words

Chapter 8 - ASHE KECE Complete By One Love .txt

One Love   

31 Jan 2025

4584

hold our worlds A production of our pen savour Out worlds for it cause u np pain~*




Wattpad @13 deeja


Or
Deeja1love.blogspot.com


*written
-by-
*Deeja one love*






*dedicated
to
*Maryam khamis*


23-24


Da sallama ta shiga gidan, iman ta fito cikin sauri suka rungume juna,gwaggo data fito daga bayi ta fara murna.






Tana shiga daki ta fara raba idanu,iman tayi murmushi domin tasan me take nema.




Juyawa tayi ta kalli iman tace"ina baby? ",iman tayi murmushi tace"yana wajen baban shi",ikhlas bata ce komai ba ta fara cire kaya.






Sai da tayi wanka sannan ta zauna taci abinci,iman tace"na lura ikhlas bakya son baby yana zuwa gidan abba kabeeru".






Murmushi ikhlas tayi tace"ni na isa na raba shi da gidan abba kabeeru kawai dai naso ace ina dawowa da yaya na na fara hada ido", cuna baki iman tayi tace"nifa wallahi har kishi ina yi da shi",dariya ikhlas kawai tayi.








Har zuwa yamma ba'a dawo dashi ba, ikhlas ta dubi iman tace"iman baby har yanzu shiru", murmushi kawai iman tayi domin tambaya ta wajen shida kenan.






Ganin tayi shiru ne yasa ikhlas mikewa ta shiga daki, jim kadan ta fito hannun ta rike da gyale.






Da mamaki iman da gwaggo suka kalle ta,iman tace"ina zuwa haka? ",hade rai tayi tace"baby zan je na dauko", duka bude baki suka yi.






Gwaggo tace"ke yanzu dan baki da kunya sai kije ki dauko yaron a gidan",kallon gwaggo tayi tace"mai zai hana kuwa? ",gwaggo ta bata rai tace"to koma ba'a garin gaba-gaba muke ba",badan ran ta yaso ba ta maida gyalen.






Ana fara kiran sallah,gwaggo ta dauki buta tayi alwala ta shiga sallah, ikhlas na ganin haka ta dauki gyale ta yi waje, iman dake alwala ta girgiza kai kawai.








Tana zuwa bakin get din gidan suka hadu da hafeez,murmushi yayi yace"barka da dawowa beauty",dariya tayi tana amsar baby dake hannun shi.






Kallon ta yayi yace"beauty ki shiga ki fito sai tafi tare",lumshe idanu tayi tace"wallahi ga wanda nazo dauka nan",da sauri ya kalle ta yace"beauty kin san me kike cewa kuwa? ",murmushin gefen baki tayi tana kauda kai.








Jinjina kai yayi indai ikhlas ce zata yi wanda ya fi wannan,mika mata yayi yace"shiga mota mu tafi",amsar yaron tayi cikin farin ciki, ta bude ta shiga.






Yana yin parking ta bude kofar ta fita, da idanu ya bita har ta shige ciki,ajiyar zuciya yayi sannan yayi reverse ya bar wajen.








Da sallama ta shiga,gwaggo ta dago ta watsa mata idanu tace"wallahi ke kam allah ya shirya ki, yanzu sai da kika je kika dauko yaron nan? ",cuno baki tayi ta wuce daki,iman kuwa dariya kawai take yi.






Bayan tayi mishi wanka ta kwantar dashi,barci ya fara yi,kallon shi take tana murmushi, iman dake zaune ta zubawa sarautar Allah ido.








Wayar ikhlas tayi kara,sai da ta kusa katsewa sannan ta dauka.






A sanyaye tayi sallama, ya amsa mata sannan yace"princess kin sauka amma ko ki kira ni? ".






Tace"ayya yi hakuri, wallahi ina ta dokin ganin baby ne, amma kai ma kasan bazan ki kiran ka ba".








Yace"to ai dama nasan koda yaushe kina da uzurin da zaki kare kan ki dashi,yanzu dai ina baby din? ".






Ta shafa kan baby tace"gashi a jiki na yayi barci",dan jim yayi kafin yace"nifa na fara kishi da babyn nan",dariya ikhlas kawai tayi.






A haka suka cigaba da firar su irin ta masoya,iman tun tana jira suka gama suyi fira har barci ya dauke ta.








Ko washe gari,ikhlas ce ta yiwa sadik wanka,ta shirya shi dama iman bata damu ba domin idan da sabo sun saba.






Kwanan ta takwas ta shirya domin komawa,islam ta kalli ikhlas tace"yanzu baza ki bar mana baby ba, dashi zaki tafi? ".






Murmushi ikhlas tayi tace"wallahi kawai ina so na tafi dashi ne",hafeez yayi sallama ya shigo, amsawa suka yi duka.








Kallon ikhlas yayi yace"ikhlas yanzu baza ki bar mini aboki na b",ya karasa cikin damuwa.




Ajiyar zuciya tayi tace"wallahi yaya hafeez da zan iya barin baby dana bar shi ko dan kai".




Islam cikin sauri tace"to ai ko dan mahaifiyar shi zaki bar shi ko? ",ikhlas tace"ko ita ba lallai ba, kuyi hakuri ku bari na tafi dashi".






A zafafe islam ta kuma cewa"wai wannan wane iko kike nunawa akan yaron da bake kika haife shi ba? ".








Murmushi kawai iman tayi tace"kada kice haka islam ki bar ta dashi", dafata ikhlas tayi tace"ki dauka da sauki islam, baban shi kan ya mutu ya ni ya barwa amanar dan shi".




islam bata ce komai ba ta figi jakar ta ta fita,murmushi kawai suka yi sannan ikhlas ta dauki baby.






Har gwaggo bata ji dadin tafiya da zata yi da sadik ba,ikhlas tace"gwaggo kuyi hakuri ku bar ni na tafi,ba wai zan raba ku bane,a'a ba zai wuce sati biyu ba zan dawo dashi".










A haka dole suka bar ta ta tafi dashi,ko a mota kallon shi take tana murmushi, kaunar yaron na kara shiga zuciyar ta.














Suna isa kano,gidan hafsa dake hotoro ta wuce, ta tarar da beelert kawai amma hafsat din bata nan,sai da tayi sallah ta huta sannan ta kira saifullahi ta gaya mishi tana gidan kawar ta a hotoro yazo ya dauke ta.









Minti talatin ya karaso, sallama suka yi da beelert sannan suka tafi.








Saifullahi ya kalle ta yac"baby ne ya zama haka? ", murmushi tayi har hakoran ta suka bayyana tace"wallahi kuwa baka ga yadda kamar sa ke kara fitowa da yaya sadik ba", jinjina ka yayi kawai.








Sai da ya sauke ta, sannan ya juya ya tafi, kayan ta ta zauna ta jera.






Ajiye sadik tayi akan bed ta dauro alwala ta sallar isha'i, ta zo ta tada sallah, tana idarwa ta shiga kitchen domin samun abinda zasu ci.










Indomie ta dafa wanda taji vegetables,a hankali take bawa sadik har ya koshi sannan ita ma taci ragowar.






Wanka tayi mishi, tana fitowa saifullahi yayi sallama ya shigo, sai da ta kwantar da sadik sannan ta fita.








Saifullahi yace"wallahi princess kamar ana kara miki kyau", murmushi kawai tayi.








Miko mata waya yayi yace"gashi bari naje na dawo ki kira lily yana ta damu na akan na baki ku gaisa since waccan satin",amsar wayar tayi shi kuma ya fita.








Dubawa ta fara yi, har ta zo kan contact din shi, a nutse tayi dialing.






Cikin muryar shi me dadin sauraro yayi sallama, a cikin tata salon muryar ta amsa.








Murmushi yayi wanda ta jiyo sautin, sannan yace"princess wannan shariya haka ko nema na bakya yi, anya kina kula da yayan nawa? ".






Murmushi kawai ikhlas tayi, sai da ya kara maimaita abinda yace sannan tace"ina kula dashi mana, ai kula dashi din da nake yi ne yasa nake mantawa da kowa ciki har da kai",dariya suka yi gaba daya.








Yace"to yanzu abinda ya kamata shine ki rarrashe ni",dariya ta kuma yi sannan tace"to kai yaron nan, kayi shiru yaron nan, ina uwar dan nan, ta tafi rafi....... "Dakatar da ita yayi cikin dariya yace"gaskiya kin iya waka".










Haka suka cigaba da firar su har saifullahi ya dawo, da murna yace"anya bazan fara kishi da kai ba".






Yayi dariya yace"lovely kenan",cikin murna yace"to yadda take sakin jiki kuyi fira ni bata mini haka",dariya kawai yayi.










Washe gari, da wuri ta shirya sannan ta shirya sadik,direct hotoro ta wuce, ta ajiye sadik sannan ta kira feenert tazo ta dauke ta suka wuce makaranta.








Sai six suka fito, hakan yasa hankalin ta gaba daya yayi wajen sadik, a hanya feenert tace"ni na lura kin fi son sadik a kan mu ne",murmushi kawai tayi.








Sai da ta biya ta dauke shi, sannan ta wuce gida, tana sane da tun da ta taho babu wanda ya kira ta, murmushi ta kan yi idan ta tuna haka.






Yau tana zaune, gefen ta sadik ne yana wasa, wayar ta ta janyo ta nemo number din hafeez, bugu daya ya daga.








Sai da suka gaisa sannan tace"yaya kai ma fushin kake yi dani? ".


Murmushi yayi yace"ni na isa nayi fushi da sarauniyar mata",dariya tayi sannan tace"wallahi duka sun ki kira na".






Sai da ya numfasa sannan yace"ke ce baki kyautawa, idan kika so abu bakya duba sauran ya zasu yi".




Ajiyar zuciya tayi kafin tace"wallahi ba haka bane, ni ina da dalilin daukar shi", gyara zama yayi yace"ina ji gaya mini dalilin".






Tace"ina so ya saba da zama a kusa dani ne, domin wata rana nan zai dawo gaba daya, sannan kuma naga dai ai an yaye shi ko, dan na dauka ban yi laifi ba".






Murmushi yayi yace"beauty wannan bashi bane dalilin",gefen lip din ta na kasa ta ciza tace"yaya hafeez u are very smart i know".






Murmushi yayi yace"duk wani abu da kike ina sane dashi ikhlas",dariya kawai tayi kafin suyi sallama.






Shiru tayi tana tunani, tabbas hafeez tasan yana da basira sosai,jinjina kai tayi tace"like father like son, sai dai u have different habit i know, but ya kamata na zama one step ahead of you, abba kabiru".










Baby na da shekara hudu suka gama makaranta, alhamdulillahi ikhlas da first class upper ta fito, ita kuma feenert second class upper, sun sami kyaututtuka sosai da sosai.










Sai dai fa abba kabiru bai sami damar zuwa ba,yaya hafeez da gwaggo da feenert suka zo, anan kuma hafsat bata gari ita tana abuja, beelert ce kawai ta halarta.






Sun yi hotuna sosai, kowa ka gani yana cikin farin ciki.








Saifullahi shi kan shi yayi farin ciki, domin yasan gama makarantar ikhlas alama ne na sun kusa yin aure.








Suna zaune a varender na gidan ta,wayar saifullahi tayi kara, cikin farin ciki ya dauka, ikhlas ta tabe baki ta kauda kan ta.








Kallon ta saifullahi yayi yana dariya ya mika mata wayar, harara ta galla mishi, kafin ta juyar da kan shi, kasa ya kalla.








A sanyaye ya maida wayar kunnen shi yace"lily am sorry, she is not in mood now,so she can't answer ur call",bata ji me yace ba.








Be dago ya kalle ta ba ya miko mata wayar,yi tayi kamar bata san yana miko mata ba.








Kasa-kasa taji yana cewa"am sorry princess, wallahi visa ce bata samu da wuri ba",kamar bada ita yake ba.








Saifullahi ganin taki kula shi ne, yasa ya kashe wayar tare da mikewa yana fadin"sai da safe, am busy yau bazan sami shigowa ba",tabe baki tayi domin tasan dalilin rashin amsar wayar shiyasa yace ba zai zo ba.








Ko Rakon yau be samu ba, shima kuma be nemi rakon ba.








Sadik ta ajiye a gefen ta, sannan ta dauko wayar ta, ta bude data ta fara chat dasu hafsat.






Sallama yayi, tun da ta dago ta kalle shi bata ce komai ba, shima daga sallamar be kuma cewa komai ba.








Ganin shirun yayi yawa, yasa yace"wai ke princess fushin be isa haka bane?, kallon shi kawai tayi ta juyar da kai.








Kusa da ita ya matso yace"am sorry kinji", murmushi tayi tace"ok, ya wuce", firar su suka cigaba dashi.




💮💮💮💮💮💮💮💮
*ASHE KECE???*💮💮💮💮
(Hypocrite-love-sacrifice)






*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATON~💫💫💫*


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~❄we beare's of soon golden we writer's assiduously percieven No pain so magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Out worlds for it cause u np pain~*




Wattpad @13 deeja


Or
Deeja1love.blogspot.com


*written
-by-
*Deeja one love*






*dedicated
to
*Maryam khamis*


25-26


*muddansir and brothers*anan ta sami aikin da taimakon saifullahi.








Yanzu sadik(karami)bakin shi ya bude haka tafiya babu inda baya zuwa, ya fara wayo sosai.










Yana zaune yana buga game a tablet, saifullahi kuma yayi tafiya zuwa india domin duba lily din shi da yayi rashin lafiya.










bayan sun gama waya da saifullahi, har ya bawa lilyn sun gais,lokaci zuwa lokaci takan ziyarci bauchi, ta gaishe dasu gwaggo.








Yau tun safe ta shirya ta dauki baby domin kai shi makaranta daga nan ta wuce wajen aiki.






A hanya ranta ya bace, domin yawan cinkoso,waya ta dauka ta kira feenert tazo ta dauke ta.








Suna ajiye baby a makaranta suka wuce,sai da feenert ta dire ta a bakin complex din sannan ta wuce.








Lokacin tashi nayi, hankalin ta ya koma kan baby, domin tasan yana can yana jiran ta,cikin sauri ta tari adaidaita ta wuce makarantar.






Gidan Hafsat ta kai shi sannan ta koma wajen aiki, haka da ta taso daga wajen aiki ta biya ta dauke shi.






Gaskiya ta gaji bari saifullahi ya dawo ya nema mata mota.




Bayan baby yayi barci, sannan ita ma ta shiga wanka ta fito, wayar dake ajiye a gefe ce tayi kara.






Jim tayi tana mamaki, me iman ke nema da bata kwanta har yanzu ba?clock ta kalla gaban ta ya fadi,after one fa!.






A sanyaye ta dauka, abinda kunnuwan ta ke jiyo mata yasa ta girgiza.




_Ga yarona nan ki kula dashi ikhlas kamar yadda zaki kula da kanki,kada ki bari yayi maraicin uwa, ki maye masa gurbin uwa da uba da yan uwa_.


_Kiyi mini alkawarin baza ki bari yayi Kuka ba ikhlas,kiyi mini alkawari ikhlas......._






Abin da yake yawo a kwakwalwar ta kenan,jikin ta har rawa yake tabar kuka,a hankali ta zame ta zauna a kasa.








Hoton rungume a kirjin ta kamar wacce za'a kwace mata.






Dafata da taji anyi yasa ta waiga da jajayen idanun ta,shima tsaye yake yana zubar da hawaye.








Cikin tsananin tashin tausayi yace"baby ki dena kuka, kiyi hakuri nasan abinda na gaya miki ne yasa kike kuka....... Kiyi hakuri bazan kuma ba",janyo shi tayi ta rungume,suka cigaba da kukan su.










Cikin kuka tace"baby bani da kowa sai kai, da farko mahaifi na Allah yayi mishi rasuwa,na biyu mahaifiya ta ta bace har yau ban san ko tana raye ko ta mutu ba, na uku mahaifin ka da yayi hatsari ya mutu wanda ko gawar sa Bamu gani ba, na hudu gwaggo da mahifiyar ka da gobara ta tashi suka kone gaba daya.










Ya zan yi ya kasance cewa nafi son wani sama da kai, ka sani kai amana ce agare ni har na mutum biyu, yaya na wanda ya soni sosai da kuma aminiya ta yar uwata wacce ban da kamar ta.








Idan na bar ka ka shiga wani hali naci amanar yar uwa ta,haka naci amanar yaya na", kuka ta kuma saki Mai karfi haka shima babyn.








Sai da suka gaji dan kan su sannan suka hakura.








Karfe tara na dare,ikhlas na hango ta tsantsanra kwalliya kamar me shirin zuwa gasar kyau,wani material ne a jikin ta orange da akayi mishi kwalliya da milk colour.










Gyalen ta da takalmin ta duka milk colour,hannun ta agogon azurfa ne, haka necklace din ta da earings,glass ta sakaye idanun ta mai kama da na mage.








Tafiya take cikin natsuwa da yang, amma fa a hankali domin bata so baby ya ga fitar ta.








Tana fita tayi ajiyar zuciya, kallon parking space tayi, ganin babu motar da zata fita yasa tayi karamin murmushi domin tasan habu mai gadi ya fitar mata da shi.








Tana mai da karamar kofa tana rufewa tayi karamar ajiyar zuciya, key ta amsa a hannun mai gadin sannan ta shiga ta tada motar.




Baby dake tsaye jikin window ya saki labulen yana mai takaici da halin mom din tashi.








Ita kuwa ikhlas sauri kawai take yi,hotoro gidan hafsat ta shiga,wanda yayi daidai da isowar feenert, murmushi suka yiwa juna sannan suka shiga.








A zaune suka tarar da hafsat tana tapping computer, ita kuma beleert tana chatting a waya.






Feernert ta daka mata duka, tace"kina kwance kina chatting ko,wallahi idanun ki zasu sami matsala",










"Meye naki a ciki? Idan na zo aron naki idanun kada ki bani",hafsat da ikhlas suka yi murmushi.








Ikhlas tace"yanzu dai fada mana meya faru ake neman mu? ".






"Alhaji yahya hassan kaura ya shigo gari, yanzu haka ma yana cikin garin kano, feenert ta fada.






Ikhlas ta dora da cewa"yana zaune a diamond hotel,room 47,yazo taron da yan siyasa suka yi dazu karfe hudu zuwa shida, yanzu haka yana so a bashi takara ne,yaje haske store domin neman mai taya shi kwana".








Numfasawa tayi kafin tace"sannan yaje dorayi karama,wajen wani abokin shi alhaji ibrahim gwala-gwalai,daga nan ya wuce government house in da suka yi taron su,yana fitowa ya wuce zango acan yayi sallar magrib da isha, daga nan ya wuce masaukin shi".








Kallon su tayi ta daga gira daya,feenert tayi ajiyar zuciya tace"yaushe kika yi wannan binciken?".








"Lokacin da kike can kina shirme", ikhlas ta bata amsa", duka suka yi dariya.






Hafsat tace"to yanzu ya za'a yi? ",ikhlas ta mike tace"kada ki damu, dazu mun hadu a haske wanda hakan yasa yake bincike a kaina, ko ince yayi bincike a kaina, yanzu zuwa gobe zai zo inda nake domin kuwa an bashi irin labarin da yake son ji".








Beelert tace"wane kala kenan?,ikhlas ta bata amsa da"zaman kaina nake, a yawon karuwan ci har da nake da".










Hafsat tace"kenan ke zaki shiga kuyi soyayya?, to kamal din fa? ",ikhlas ta ce"eh zan je muyi soyayya tare dashi, ke kuma feenert zaki tafi gombe domin kiyi mana traping wancan dan iskan".






Kai kawai feenert ta daga,beelert tace"ni kuma zan cigaba da zuwa miki wajen aiki",hafsat tace"zan dinga saka idanu in case ko za'a sami matsala".






Murmushi ikhlas tayi,cikin farin ciki,wayar dake hannun ta tayi kara,ganin me kiran yasa ta mike tace"babies ni nayi gida, sai da safen ku".








Mikewa feenert tayi ta biyo ta, a tare suka fice daga gidan.






Tana komawa gidan, ta shiga da sauri domin ta gashi tana son hutawa.






Kallon-kallo suka tsaya yi, agogon ya kalla daya da wajen minti talatin.






Cikin dakiya tace"me kake yi anan har yanzu baka yi barci ba? ",jiki a sanyaye yace"nayi barci yanzu haka ma ruwa na fito sha".






Bata ce komai ba ta wuce, bin ta da kallo yayi kafin ya juya ya shiga daki, ruwan da be sha ba kenan.








Washe gari da safe, da wuri ta tashi, sai da tayi shirya sannan ta fito.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login