Showing 45001 words to 48000 words out of 71023 words

Chapter 16 - ASHE KECE Complete By One Love .txt

One Love   

31 Jan 2025

4668






Daga haka suka jera, suna tafe suna tunani daban daban.






Sai da ya kulle kofa sannan yace"hafeez nasan cewa kaima har yanzu kana bincike akan ikhlas, shin ko ka sami wata makama? ".






"Har yanzu daddy babu wani feed back, har ma na fara gajiya kawai", murmushi abba kabeeru yayi yace"kada ka damu at any time za'a iya ganin ta", shima murmushin kawai ya maida mishi.










Fita yayi daga office din, abba kabeeru ya daga waya yace"hazard ka tabbata kuna bibiyar hafeez duk inda yake zuwa, da zarar ya same ta kuje ku kashe ta ita da yaron nan kawai".






Yana aijye wayar yayi murmushi yace"ikhlas ke wato mai wayo ko? ",zirga-zirga yake a office din yana tunanin abubuwa.








A hankali ya tura kofar office din, kan ta yana kasa tana operating system,cikin sauri ta dago, murmushi ya kuma yi mata yace"ya dai yar kyakkyawa".






Jikin ta yana rawa tace"sann...... u...... sannun ga waje...... ka zauna?", murmushi yayi sannan ya nemi waje ya zauna.










Mummy ta shigo dakin tace"maleek ka shirya gobe zamu shiga cikin garin yola", daga kai kawai yayi, bata kuma cewa komai ba ta fice daga dakin.






Yana zaune saifullahi ya shigo, kallon shi yayi yace"haba lilly meye haka ne wai?,ka wani zauna kamar wanda aka ce za'a kai gidan yari".






"Ba gwamma a kaini gidan yari ba da wannan abubuwa da yake faruwa, jifa wai ni aka daurawa aure da yarinyar da ko sanin inda take ba'a yi ba, waya sani ma ko tana can tana zaman kan ta ne".






"Haba lily me yasa kake haka ne, kasan dai daddy bazai taba cutar da kai ba,kuma umma tana tunowa za'a je a dauko maka matar ka", ya karasa cike da tsokana.










"To idan kuma bana son ta fa? ",ya fad'a yana kallon d'an uwan nashi"haba kai ya za'a yi kace baka son ta".






"I mean idan ba type dina bace fa, kasan dai ina da irin wacce nake so ta zama matata ko? ".








"Hmmm lily kenan, am sure u will like her", i hope so", daga haka suka cigaba da firar su.








"Haba bintu ki natsu ki gaya mini me yake faruwa", hajiya rabi ta fad'a hankalin ta a tashe jin yadda yar ta take rusa kuka.








"Hajiya, wallahi mutuwa zan yi, domin yan uwan ki basa sona kwata kwata, ni yau zan dawo wajen ki kawai".






"Ke ki gaya mini me yake faruwa, daga zuwa yau ki kuma dinga maganar yau zaki dawo".








"Hajiya dan rashin adalci a gaba na daddy yasa aka daura auren maleek da wata fa, daga zuwan mu bema duba yadda nake son shi ba".






Wani zagi hajiya ta lailayo ta zabga sannan tace"wallahi sun yi kadan gobe ina nan zuwa idan allah ya kaimu,sun yi kadan ki share hawayen ki kin ji".






Daga haka ta katse wayar, ita kuwa bintu kan bed ta fada tana cigaba da rero kukan ta domin dai wannan ita gani take kawai rashin kauna ce.








Ranar dai mutane da yawa basu yi barci ba,maleek daya fada cikin tunanin irin auren da ake shirin yi mishi, saifullahi da yake tunanin yadda zai bullowa iyayen shi su yarda da auren shi da princess.






Bintu da kishi da bakin ciki ya hanata runtsawa,hajiya rabi dake ta faman huci tana so taje taji ya akayi haka wato munafintarta yayi kenan?.






Abba kabeeru da yake tunanin ta ina zai ga ikhlas domin ya tura ta inda ya tura yan uwan ta, wato lahira.








Mummy dake tunanin yadda zata kaya, idan suka koma gida hajiya ta sami labarin auren maleek bayan duk sun san bintu na matukar son shi.






Ikhlas da take tunanin wace hanya ya kamata tabi domi kwato dukiyar maraya wanda a yanzu ya rage jini daya na sadik da kuma tunanin halin da mahaifiyar ta take ciki.






Umma dake k'ok'arin tunano ina yarinyar ta take, domin ta san dai tana da yarin ya mai suna ikhlas amma ta manta wane gari ta zauna da ita.








*kuyi hakuri da wannan domin yau kaina ciwo yake yi,dan ma kada kuce ban yi muku bane, na gode da irin soyayyar da kuke nuna mini*






*one love(maman farouk) duka nice insha Allah*😘














💮💮💮💮💮💮💮💮
*ASHE KECE???*💮💮💮💮
(Hypocrite-love-sacrifice)






https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


✍✍✍✍✍✍✍
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION~*
✍✍✍✍✍✍✍




*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*




*written
-by-
*Deeja one love*






*🏆JAKADIYAR G. P. W. A*🏆


Special thanks goes to:


Harira yar fillo
Hassana tafarki +your group ILHAM.
Sanaz kema ke da group din ki.
Dijency
My group *deeja one hausa novels*.




*Ina godiya sosai da sosai, wa'inda suka yi mini magana ta pc har gajiya nayi da amsawa akan lafiya,to ni dai lafiya ta lau kawai comments din ku yayi k'asa ni kuma naga bari na huta kawai, to amma yadda kuka dinga bina pc da tambaya nasan cewa har yanzu kuna bibiyar littafin *na gode da k'aunar ku a gare ni*.






*dedicated*
to
*Maryam*





49-50






Tun daga harabar gidan take surfa bala'i,gaban mummy ya fad'i domin tasan zuwan nasu ne.








Baffa dake zaune a d'akin shi yayi murmushi yace"jabeer,muhammad, sa'eed kada wanda ya tanka mata kun ji".






Cike da ladabi suka had'a baki wajen fad'in"insha Allah, babu wanda zai tanka mata".






Daga haka ta k'araso cikin d'akin,ganin dukan su a zaune dan bata ma lura da daddyn adamawa ba tace"haba baffa abinda kayi ka kyauta kenan".






Shiru suka yi,shigowar su umma da mummy da daneji yasa ta juya tana fuskantar su tace"nasan da sa hannun ki munafika kawai, me yasa baki had'a auren da d'an da kika haifa ba sai d'an rik'o".






Juyawa tayi ta kalli daddy tace"wallahi muhammad kayi kad'an ka juyawa umarni na baya,shin a can kaduna ya muka yi da kai ne?,amma kana zuwa nan zaka canza".








Sun kuyar da kai yayi, cikin d'aga murya tace"ba magana nake maka ba muhammad yanzu mata tafi yar uwa ko dan kaga ina zaune a gidan ka ne? ".








"Kiyi hak'uri wallahi hajiya bani na d'aura auren ba kuma kin san...... ",ya isa haka waye ya d'aura auren, nace waye ishasshe da man daya d'aura auren yarinyar da ba'a san inda take ba? ".








Cikin fushi daddyn adamawa yace"ni ne nan na d'aura auren, ko da abinda zaki aikata ne?, kuma naji kina wata magana da ban san da maganar ba".






Baffa yace"jabeer ba muyi haka da kai ba",kallon baffa yayi yace"kayi hakuri ban so na sab'awa umarnin ka ba sai dai dole na tsawatar mata".






Hajiya rabi tayi dariya tace"yaya ina wuni, ai ban san kana wajen bane".dan duk rashin mutuncin ta tana tsoron yayan nata.






"Ba wannan na tambaye ki ba, aure dai ni na d'aura sannan ki tabbata kin had'a kayan ki kin koma gidan mijin ki, kafin rai na ya b'aci,",daga haka ya fice, daddy da daddyn abuja suka bishi.










Suna fita taja tsaki tace"wallahi kayi a banza dan babu inda zan je",baffa ya girgiza kai yana mata fatan shiriya.








Daneji kam kota kan ta bata biba, ta ja hannun umma suka bar wajen, baffa shi yace mata"zauna mu gaisa mana".






Zama tayi tana tabe baki tace"baffa yanzu dan allah kana kallo akayi abinda be kamata ba, taya za'ayi ace bintu na son maleek sosai amma a ka rasa wanda zai had'a auren ta dashi, sai gashi a sama an d'aura auren shi da........ ".








"Ina wuni, mun wuni lafiya",baffa ya katse ta,sosa kai tayi tace"lafiya lau baffa ya kake? ",murmushi yayi yace"lafiya lau, yanzu tashi ki je ki gaishe da mahaifiyar ki".






Badan ran ta yaso ba ta mike ta shiga ciki,yayin da baffa ya bita da kallo yana girgiza kai,"rabi rigima",daga haka ya mike domin tafiya masallaci.


Umma na zaune ta idar da sallah, hajiya rabi ta shigo,umma tace"ina wuni hajiya".




"Da ban wuni ba zaki ganni ne?, munafika tsabar had'a yan uwa,kin wani d'auki 'yar ki kin bashi kamar wata kayan gabas ce".








Girgiza kai umma tayi hawaye na zubo mata, tabbas be kamata ta bari a d'aura wannan auren ba.






Daneji da ta shigo yanzu ta kalle ta tace"wallahi kin ji haushin rayuwar ki, an gaya miki wannan abin da kike yi shine birgewa, to bari kiji kinyi kad'an ki warware auren da ubangiji ne ya had'a",daga haka ta fice.






**** **** ****






Ikhlas ta dubi nabeelert tace"kada ki damu,ki bari ku sami kusanci, ni nasan yaya hafeez bashi da matsala da abinda abba kabeeru yake aikatawa, kinga ta nan zamu sami wasu information".








Feenert tace"hakane cat eyes to amma baki tunanin kamar hakan zai ja mana matsala, idan kika yi la'akari da mahaifin shi ne? ".








Girgiza kai tayi tana murmushi, sannan ta d'auko wani file ta mik'a ma beelert tace"gashi idan kin isa da two weeks ina so ki san yadda zaki yi ki bawa abba kabeeru takardun nan yayi signing".








Beelert tace"idan na bashi yayi, na aiko miki dashi ne ko kuwa na bar shi a hannu na? ".






Dariya tayi ta mika mata wani agogo tace"ki tabbata kin d'aura wannan a hannun ki, sannan ga wannan ki mak'ala a gashin kan ki".








Hafsat tace"amma ida hakan ya faru,kin ga kenan saura one week mu tafi abuja kenan? ",feenert tace"hakane ana saura sati biyu bikin ki kenan? ".








Ikhlas tace"hakan yasa muna da ishashshen lokaci sosai, amma kada ki damu ai zamu halarta".






Beelert ta bud'e mota tace"ni dai na wuce, idan allah ya kaimu gobe,zan kira ku naji me yake tafiya".






Duka suka yi mata fatan alkhairi, sannan suka juya suka koma cikin gida.






Maleek kuwa kwance yake yana tunani,be san me yasa wani b'angare na zuciyar shi yake son ganin ta ba.






Idan ya lissafa dai-dai yau kwanan shi talatin rabon da ya gan ta,to amma ai da kunya yace da lovely zai je ganin karuwa.






Tsaki ya ja,ga wannan da aka d'aura mishi aure da ita ko yaya take oho!tsakin ya kuma ja.






Saifullahi yace"lily tashi muyi magana",zaune ya mik'e amma kuma idanun nashi a rufe.






Saifullahi yace"lily, kowa da yanayin rayuwar da take zuwar mishi, yanzu haka zaka zauna kullum tunani, hakan fa zai sa bp dinka ya hau".








Dafa kan shi yayi yace"lovely nifa ba wannan nake tunani ba,abinda nake tunani daban".






"To shikenan yanzu dai me kake tunani, tunda kace ba wancan kake tunani ba? ".






"Yaushe zaka je wajen princ......... ", kasa k'arasawa yayi, shi kam saifullahi yayi murmushi yace"karuwa ko dai?,gobe ko jibi zani mana ko zakaje ne? ".








D'aga kai yayi yace"eh to, watakila naje amma me zai hana muje gobe ne,ko kuwa? ".






Dariya saifullahi yayi yace"me yasa ka k'osa kaje ne? Ko dai kayi budurwa a kano ne, ko kuwa princess din kayi missing? ".








Gaban shi ya fad'i, idan fa yayi wasa lovely zai gane me yake tunani, ya mutsa fuska yayi yace"allah ya kiyaye nayi missing karuwa, my son nayi missing ba ita ba".






Zuba mishi idanu saifullahi yayi yana murmushi,maleek kuwa k'in kallon shi yayi domin yasan zai iya gane abinda ba haka ba.








Washe gari da wuri suka wuce kano,yayin da mummy tayi musu fatan alkhairi,maleek kuwa zuba gudu kawai yake yi domin ji yake kamar yayi tsuntsuwa ya isa wajen ta haka yake ji.








Awa biyu ta kai su kano daga kaduna,be tsaya a ko'ina ba sai k'ofar gidan ta.




Abin haushi gidan a rufe yake,cikin jin haushi maleek yayi parking yace"lovely kira ta a waya mana".






Saifullahi yace"mu wuce hotoro, na san tana can",maleek ta dube shi yace"au yanzu kuma d'an hotoro aka samu ne? ".








Saifullahi be kula shi,har bakin get sannan suka yi parking,number d'in ta ya kira.








"Hello Princess, wannan irin shariya haka? ","lah! Ba haka bane wallahi kasan nayi busy but amma ina baka hak'uri".






"Yanzu dai gani a k'ofar gida ki fito",zumana bana gida fa".








"Na sani ba kina hotoro bane",a'a zuma na ina sokoto fayanzu haka fa".








Ajiyar zuciya yayi yace"baby fa, dan lily ya zo ganin shi".






Murmushi tayi,tace"bari na kira a turo muku shi",daga haka ta kashe.






Me aikin hafsat ta kira tace ta tura baby akwai bak'i a waje suna jiran shi.








Beelert ta dube ta tace"su waye ne? Ko zuman naki ya dawo ne? ".








Ikhlas ta taba jikin hafsat wanda dama gyara ya kai su, tace"kai amarya wannan jiki haka, gaskiya adam ya more, eh shine yazo".








Dariya hafsat tayi tace"feenert kina ji ko, baki ce komai ba".




Feneert tace"ai nima nan zan zo a gwangwaje wa abdallah ni",dariya suka yi gaba d'aya.






Feenert tace"ruqayya ai nima zaki gyara ni ko? ".






Ruqayya tayi dariya tace"kada ki damu, kizo idan bikin ya matso".










*ku cigaba da hakuri, ku cigaba da bina, ku cigaba da comments, haka masu sharing su cigaba da sharing,masu lab'ewa idan an karanta, pls ku gyara ko kadan ne kuna comments hakan zai kara mini karfin gwiwa nayi muku typing*












*ummu farouk*. (One love)


















💮💮💮💮💮💮💮💮
*ASHE KECE???*💮💮💮💮
(Hypocrite-love-sacrifice)






https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


✍✍✍✍✍✍✍
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION~*
✍✍✍✍✍✍✍




*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*




*written
-by-
*Deeja one love*






*🏆JAKADIYAR GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION*🏆




51-52






Da gudu ya k'araso wajen maleek ya rungume shi,cikin farin ciki yayi peck d'in shi a goshi yace"i missed you daddy a lot".






Maleek ya k'ara rungume shi yace"me too son, ina mummy d'in ka? ".






"Baby,ai ta tafi zamfara, an kusa biki mum hafsat shine suka je gyaran jiki".






Saifullahi yayi murmushi yana jinjina wayon yaron yace"wato baby ni baka yi missing d'ina ba kenan".






Dariya yayi yana rufe ido yace"uncle nayi mana, sai dai nafi missing daddy na saboda shi yake kai ni shopping".






Dariya suka yi gaba d'aya,maleek ya sauke shi yace"yanzu abinda ya kamat shine zo muje wani waje".








Da murna baby yace"dat's mah dad, shi yasa nake son ka sosai da sosai", daga haka suka shiga mota suka tafi.








Kwanan su biyu a kano amma su ikhlas basu dawo ba, haka suka shirya suka koma kaduna ba tare da sun had'u ba.












Beelert da yaya hafeez ne zaune a wani garden, fira suke sosai.






"Nifa da gaske nake, ban k'i gobe a d'aura mana aure ba".








"Hmm, meye na wani zumud'i kai dai kawai ka bari zuwa nan da d'an lokaci".






"Ni dai ba zan gaji da cewa ko gobe a shirye nake domin a d'aura mana aure".






"To kada ka damu, akwai lokaci yanzu dai mu bari time yayi".






"Wallahi sai naga kamar bakya so na yanzu?".






"Ni na isa nace bana son ka, hafeez kai ma sheda ne na irin son da nake maka, kuma zan cigaba da son ka har abada".








Haka suka cigaba da firar su cikin kwanciyar hankali.










Daddy ya dube su yace"to masha Allah kamar yadda muka tsara sai shi kuma Allah ya tsara na shi tsarin, kuma tsarin Allah shine dai-dai".








Sai da ya numfasa sannan ya cigaba da cewa"kai abdulmaleek yanzu abinda nake so da kai shine,duk ranar daka sami matar da kake so ka gabatar da ita anan".








"Kai kuma saifullahi, idan har da yarinyar da kake so ka gabatar da ita kai ma,yau ba gobe ba".








Sunkuyar da kai yayi yana jin kirjin shi na bugawa,cikin tsananin tsoro yace"eh daddy ina da ita".






Cikin farin ciki daddyn abuja yace"wacece ita haka? ",cike da k'arfin gwiwa yace"daddy a kano take".








Washe baki suka yi suna fad'in "masha Allah",daddyn adamawa yace"yanzu abinda za'a yi shine kai sa'eed da ni zamu je can kano d'in sai ka bamu cikakken address na iyayen ta".










Share zufar da ta tsattsafo mishi yayi yace"wato daddyn adamawa iyayen ta sun rasu, shekara biyar da ta wuce yanzu haka ita kad'ai take zaune ita da yaron ta".










Shiru suka yi kafin daddyn adamawa yaja tsaki yace"kaji shirmen banza ina 'yan uwan nata, kuma ina uban yaron? ".






Tab ai ji yayi kamar ya mike ya zuba da gudu,tattaro ragowar jarumtar shi yayi yace"mahaifin yaron dai ya rasu,ita kuma bata da yan uwa".








Kallon lallai ka raina daddyn adamawa yayi mishi yace"saifullahi kana da hankali kuwa?,sa'eed ka kai shi a fara bincikar kwakwalwar shi".


Saifullahi idanun suka yi ja domin dama ya san da wuya su yarda ya aure ta,maleek kuwa tunda ya fahimci akan Princess yake magana ya dinga jin zuciyar shi na zafi, amma fa yadda yaga yayan nashi ya shiga ya sa ya fara tausaya mishi.








Saifullahi yace"daddy lafiya lau, wallahi ba tada wata matsala kawai dai dan tana zaune ita kadai ne, kuma iyayen ta rasuwa suka yi".




Daddyn adamawa yace"wallahi baka isa ba,kayi kadan me zaman kan ta,ina yan uwan iyayen nata, sannan kuma bazawara".










Shafa fuskar shi yayi yace"daddy bata taba aure ba",duka suka mike, daddy ya tsinka mishi mari.




Cikin mamaki da kaduwa suke kallon mahaifin nasu, ba saifullahi ba har tana maleek jikin shi yayi sanyi.






Abu ne wanda be taba faruwa ba tun da suke,tsananin soyayyar da yake wa yaran shi yasa baya iya marin su.








Daddyn adamawa yace"karuwa wacce tayi zaman kan ta har na tsayin shekara biyar har da rabon d'a sannan kace zaka aure ta hakan bazai taba faruwa ba".






Kallon daddyn abuja yayi yace"yaron da yake neman hafsat a maida musu da kayan su,ba za'a canza date ba,nan da sati uku za'a maida bikin kan d'an uwan ta saifullahi wannan itace matsaya".






Baffa yayi murmushi yana mai jin dadin yadda yaran nashi kan nasu yake had'e.






Cikin ladabi daddyn abuja yace"shikenan yaya hakan kawai za'a yi",daddy kuwa be ce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login