Showing 66001 words to 69000 words out of 71023 words

Chapter 23 - ASHE KECE Complete By One Love .txt

One Love   

31 Jan 2025

4665

domin duk shigowar da zai yi basa haduwa.










Zama yayi sannan yace"hutawa ake yi? ",k'ara janyo gyalen dake jikin ta tayi tace"eh yaya".










Falon ya kalla sannan yayi k'asa da murya yace"ina Mummy?".








"Tana dakin ta,ai dama bata fitowa kamar yanzu".










"Abinda nake so shine Ikhlas dan Allah ki k'ara hak'uri game da abinda ya faru".












"Babu komai yaya sai dai abinda dama ya dan bani haushi shine yadda ka kasa kira na ka fad'a min".








"Wallahi ina cikin tashin hankali ne shiyasa, princess ba zan iya kiran ki a waya na gaya miki cewa wai mahaifana basu amince da auren mu, yanzu dai kin yafe mini".










"Kwarai kuwa komai ya wuce",langwabar da kai yayi yace"to a taimake ni mana haba princess aje a bawa amarya ta hak'uri ".








"Meya faru da ni zan je na bawa amaryar ka hak'uri wannan wane kalar fad'a ne haka".










"Wallahi princess ba fad'a muka yi ba,kawai dai tak'i sauraro na ne,Ina buk'atar ta bani hakk'ina amma abin ya gagara shine nazo wajen ki domin muje ki sasanta mini ita".










Cikim sauri ta mik'e tace"muje yaya wannan wane kalar shirme ne haka? ".












Cikin sauri shima ya mik'e yana gaba tana bayan shi,Maleek daya shigo yanzu ganin wucewar su yasa ya tsaya yana mamaki.








Gefen varender yaja ya tsaya domin jiran dawowar ta, me kuma yake faruwa tsakanin ta da yayan nashi?,ka manta cewa daman karuwa ce.








Gaban shi ya fad'i tuno hakan, kai haba dai hakan ba zai yiwu ba, amma bari ta dawo dole tayi mini bayanin mai yake faruwa.










Da sallama suka shiga gidan, Hafsat dake zaune tana jiran dawowar mai gidan nata wacce tasha ado cikin riga da wando.








Tana jin muryar Ikhlas tayi saurin mik'ewa ya isa wajen ta,Ikhlas tsayawa tayi tana mamakin halin Hafsat d'in a haka kamar wayayyaya.






Kallon ta ta mayar kan saifullahi wanda yake ji ina ma wajen shi ta nufa ba wajen Ikhlas din ba.










Hafsat da fara'a tace"ai ke baki da mutunci wallahi",Ikhlas tace"ba abinda ya kawo ni kenan ba, wuce muje daki".










Suna shiga dakin Ikhlas ta rik'o kunnen ta cikin wasa tace.............




*manage pls da wannan,na gode sosai masoya*.














*babyn abdul,maman farouk da elham*






















💮💮💮💮💮💮💮💮
*ASHE KECE???*💮💮💮💮
(Hypocrite-love-sacrifice)


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/




*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*








*~We are bearer's of so golden pen🖊~*


*~we write assidiously perceive no pain~.*


*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*


*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*












*written*
-by-
*Deeja one love*














*🏆JAKADIYAR GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION*🏆






*Dedicated*


-to-
*Maryam khamis*




*kuyi hak'uri masoya wallahi ina yin iya kokari na, sosai abubuwa ke cakude mini,amma kuma ina k'ok'ari sosai ni na san kuna hakuri pls ku kara akan wanda kuke*










*aunty mamuh gee a k'ara hak'uri,wallahi makaranta haka suke ki toshe kunnuwan ki kawai,keep moving weather ur enemy likes or not,i know mah aunty bata son damuwa a rayuwar ta, am so sorry mu mun san rubutun ki baiwa ce ba copy ba ki cigaba su ma sun san hakan baiwace daga Allah*














73-74










Suna shiga dakin Ikhlas ta rik'o kunnen ta cikin wasa tace"wannan kunnen da alamu fad'an da Baffa yayi be shiga cikin sa ba".










Zama suka yi sannan ikhlas ta had'e rai tace"malama wai me yasa kika yi hakane,Anya Hafsat kina son aljanna kuwa?, shin kin san duk lokacin da mijin ki ya kira ki kika k'i amsa kiran mala'iku na tsine miki? ".










"Wallahi ki zauna wasa ranar daya gaji zai je ya nemi wata a waje, shikenan kina zaune a gida kin hanshare baki shi kuma zai je ya k'aro miki kishiya".










"To ga mai tsoron Allah kenan,idan kuma ba haka bane yaje ya fara neman matan banza a waje, kinga kina nan zaune ya kwaso cuta ya goga miki, idan ba haka ba ma ya fada ga halaka".










"Yanzu maza tattalin su ake ana tarairayar su,amma ke babu haka gaba daya kin wani zauna jagwab ai wannan kece *matar bahaushen*".








"Haba sis kamar ba zaman kano kika yi ba, ai wannan kama ta yayi ace wacce tayi zaman wani garin take hakan ba wai ke da kika zauna a garin da zaurawa da yan mata suke da yawa ba, haka kuma suke farautar namiji kamar zasu goya shi a baya".












"Dan allah ki dawo cikin hankalin ki, ban son haka mana, haba my aunty kin fa tuna dake zan yi koyi haka ma sauran kannen mu".










Hafsat cikin sanyin jiki tace"hakane yar uwa sai dai wallahi na kasa ne, saboda a kullum gani nake kamar naci amanar ki ne".










"Kalli ki manta da wannan domin kuwa saifullahin da Suka yi soyayya da Ikhlas ya mutu, wannan saifullahin mijin Yar uwar Ikhlas ne".








Murmushi Hafsat tayi tace"na gode sosai, Hakika ina godiya ga Allah daya bani yar uwa mai hankali da take nunar dani abubuwa da yawa, a gaskiya ba karamar asara nayi ba a shekarun baya da bamu hadu ba".










"Nima haka yar uwa dan haka yau dai a tausayawa yaya na a bar shi ya shiga fadama ya sha ruwan cikin ta, suna dariya suka fito.








Saifullahi yayi ajiyar zuciya domin ya san an dai-dai ta kena,har kofa ta rako ta,Ikhlas ta matsa kusa da ita tace"sai nazo gashi da safe".










Duka ta kai mata Ikhlas ta goce tana dariya,har bakin bamgaren su ya fitar da ita, anan suka yi sallama ya juya ita kuma ta tafi.










Tazo shan kwana taji an janyo ta,cikin sauri ya toshe bakin ta ganin tana so tayi mishi ihu,cikin sanyi yace"nine nan fa".










Jin muryar shi yasa ta saki ajiyar zuciya, hannun ta ya rik'e kam yace"beauty mu je mana", babu musu ta bishi.








Daki ya bude ya shiga itama ta biyo shi,hannun shi na rik'e da nata ya wuce da ita bedroom.






Gefen gado ya zaunar da ita,kasa ya koma ya tsugunna,tafin hannun shi ya dora saman cinyar ta ya zuba mata idanu, zuciyar shi ta dinga bugawa da karfi.










Ita ma idanun ta zuba mishi,kallon juna suke sosai kuma suke karantar juna,a hankali ya janye nashi idanun.








Kan shi ya dora saman cinyar ta,a sanyaye yace"na gode da kika taimake ni dazu",runtse idanu tayi tunowa da abinda ya faru.














Cikin sauri tace"ya jikin? ",yayi sauki",wayar ta ne ya yi k'ara ganin sunan Mummy yasa gaban ta fad'uwa.










A sanyaye ta d'aga,Mummy cewa tayi kawai"Kizo to",Daga haka ta kashe wayar.








Kasancewar yaji abinda Mummy tace yasa ya d'aga ta, da sauri ta mike ta fice, Shima tashi yayi ya bita.








Tana shiga falon Mummy ta fara hararar ta,k'asa tayi da kai tace"Mummy yaya saifullahi ya zo ya kira ni naje wajen aunty haf........ ".








Sallamar da yayi ne ta katse mata maganar da take yi,Mummy ta galla mata harara tace"wuce ki bani waje banza shashasha.






Da sauri Ikhlas tayi sama tana kunkunai,Mummy tq bita da kallo tana girgiza kai wai 'ya'yan zamani kenan.












Ikhlas kuwa tana shiga d'aki ta cire hijab kayan ta cire sannan ta wuce toilet, Wanka ta sake yi sannan tayi alwala tayi sallar isha'i.












Kwantawa tayi tana murmushi,Sallama aka yi aka turo kofar,lumshe idanu tayi, Mummy tayi murmushi.










Tace"yau an k'oshi da soyayya ne ba za'a sauko a yi dinner ba",Runtse idanu tayi ji take kamar k'asa ta tsage ta shige.










Mummy kam tayi dariya ta fice tana fad'in"ki sauko muna jiran ki",Ajiyar zuciya ta sauke tana dariya.












Sai da ta kimtsa kan ta sannan ta sauka kasa,su uku ta tarar, Daddy da Mummy sai oga kwata-kwata wato Maleek.










kasa cin komai tayi saboda jin yadda idanu ke yawo a kanta,juya cokali take kawai tana wasa dashi.












D'agowa tayi ta d'an saci kallon shi, caraf sai a cikin nashi idon, kashe mata ido d'aya yayi yana murmushi.










Jin yanayin jikin ta daya sauya yasa tayi saurin mik'ewa,Daddy yace"ba dai har kin k'oshi ba".












D'aga kai kawai tayi jikin ta har rawa yake,Mummy tace"Ina fa kallon ki ko loma uku baki kai bakin ki ba".










A d'an daburce tace"eh wallahi na k'oshi ne,shiyasa saboda d'azu nasha fruit salad.










mummy ta bude baki zata yi magana Daddy ya dakatar da ita,kallon Ikhlas yayi yace"Je ki 'yata", juyawa tayi har tana tuntub'e tayi sama.












Maleek ya ya mutsa fuska ya dauki plate na abincin shi yayi hanyar sama,Mummy tace"Ina zuwa kuma".








Ba kunya yace"zan je sama ne, wajen Ikhlas sai muci wannan abincin tare".






Bude baki tayi zata yi magana sai kuma ta fasa saboda hannun ta da Daddy ya rik'e.








Ikhlas tana shiga tayi ajiyar zuciya, gaskiya dole ta san yadda zata yi domin kuwa gaba haukacewa zata yi, wai yama akayi ne ina k'iyayyar da suke wa juna ne?.








Ni dai nace oho! Ikhlas kya tambaye ni,ni ban ma sani ba😂.












Juya kallon ta tayi zuwa mirror,dole duk namijin da ya ganta in dai yana da lafiya ya ji yana kaunar kasancewa da ita domin kuwa duk wani abu da d'a namiji zai so to tana dashi.














Bata ji shigowar shi ba sai jin an rungumo ta ta baya,ta cikin mirror suka zubawa juna idanu.










Murmushi yayi mata,sannan ya sak'alo kan shi ta tsakanin wuyan ta, hannun shi yasa ta saman kirjin ta yace"me kike tunani, ko kuwa kayana kike kallo? ".








Juyar da fuska tayi tana ya mutsa fuska,A hankali tace"pls ka fita,idan ba haka ba Mummy zata iya shigowa".










"To ai da sanin ta na shigo", Kallon shi tayi domin gasgata abinda yace, Jan ta yayi yace"kin ga muje kici abinci".












Zaunar da ita yayi ya mik'a mata plate din,girgiza kai tayi,saukewa yayi sannan ya d'ebo ya miko mata.








Kallon da yayi mata ne yasa ta kasa yi mishi musu,bud'e baki tayi ya zuba mata, a hankali take taunawa.






Lips din ta ya tsurawa idanu, wani iri yake ji a jikin shi,da kyar yake janyo numfashin shi.














Haka har ta gama,harshen shi ya fito dashi yasa ya lashe lips din nata.








Bata ce mishi komai ba domin ta rasa me yasa bata iya hana shi abinda yake yi mata.










Wanko bakin ta tayi sannan ta zo ta kwanta, shima bayan ta ya bi ya kwanta, janyo ta yayi ya rungume.








Idanun shi a lumshe,Hannu yasa cikin rigar ta yana wasa da kirjin ta.




Kasa ko motsi tayi sai dai runtse ido da tayi domin har yanzu tana jin zafin ya mutsa ta da yayi d'azu.












Shi kuwa Maleek tuni hankalin shi ya fara barin jikin shi,sosai yake son kasancewa da ita.








Mummy ce ta turo kofar ganin su kwance yasa ta fara salati cikin fad'a tace"Wai Maleek me ka maida ni ne, oya get out now".








Jiki a sanyaye ya mik'e,yace"Mumm........... ",hanyar waje ta nuna mishi tana fadin"out nace",waje ya fice cike da takaici.










Mummy ta juya ta kalli Ikhlas wacce ko idanu bata bud'e ba tsabar kunya da take ji,Mummy ta girgiza kai kawai ta fice.




____________________________________________________________________________________________________________________________________








Ajiyar zuciya yayi yace"finally i give up, INA SON TA sudeis!, sai dai matsalar ban san yadda zan yi da mumny ba".










"To ai tun farko laifin ka ne, Domin Mummy sai da ta so kayi amfani da lokaci da damar ka".








"Yanzu dai Sudeis meye shawara,domin kaina ya kwance wallahi a yadda nake ji idan har ban samu abinda nake so ba zan iya mutuwa".










Sudeis yayi murmushi yace"Yanzu abinda ya kamata shine kaje ka nemi yardar Ikhlas d'in domin kuwa idan kuka shirya kan ku to Mummy dole ta kyale ku".










"Amma baka ganin kamar Ikhlas bata sona ba? ",girgiza kai yayi yace"bana ganin haka kayi k'ok'ari ka shawo kan ta kawai".










"Shikenan zan gwada daga yau insha Allah domin ganin wane feed back zan samu".








Sudeis ya mik'e ya fice daga office d'in shima kuma Maleek duniyar tunani ya fad'a tabbas ya yarda yana son ta.






Gaban shi ya fad'i, idan kuma bata amince ba fa?,mik'ewa yayi yana zagaya office d'in tabbas idan tak'i amincewa mutuwa zan yi".










Tattara kayan shi yayi ya bar office d'in cikin sauri,Sosai yake sauri domin yaje ya tarar da ita.












Cike da d'oki ya isa gida,da sallama ya shiga mummy dake zaune ta amsa mishi, cikin fara'a ya k'arasa gare ta.










Kan shi ya d'ora saman cinyar ta yace"Mummy! Na gaji",Shafa kan shi tayi tace"sannu ya gajiya,? ".








Cuno baki yayi yace"wallahi mummy ni ji nake kamar na gudu",Dariya tayi tace"Tashi ka bani waje ragon namiji kawai".












Mik'ewa yayi yace"Mum a kawo mini abinci",murmushi tayi wanda ba zai iya fassara me take nufi ba tace"yanzu kuwa".










Cikin sauri ya k'arasa d'akin yana fatan ganin ta,Domin dalilin da yasa yace a kawo mishi abincin kenan.












Wanka ya yi ya zauna yana taping wayar shi,Sallama aka yi aka turo k'ofa da sauri ya kalli wajen yana murmushi.










Gaban shi ne ya buga tare da d'aukewar murmushin fuskar shi, sosai ya had'e rai.








*maman elham da farouk*







💮💮💮💮💮💮💮💮
*ASHE KECE???*💮💮💮💮
(Hypocrite-love-sacrifice)


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/




*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*








*~We are bearer's of so golden pen🖊~*


*~we write assidiously perceive no pain~.*


*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*


*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*












*written*
-by-
*Deeja one love*














*🏆JAKADIYAR GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION*🏆






*Dedicated*


-to-
*Maryam khamis*










75-76






K'arasowa tayi jikin ta yana rawa,daka mata tsawa yayi yace"waye yace ki shigo mini d'aki, fita".








Da sauri ta fice kamar wacce ake hankad'awa,huci yayi yana danne zuciyar shi kafin ya mik'e ya fita.








A kan dinning ya sami mummy tana cin abinci, kusa da ita ya zauna yana tab'e fuska, murmushi mummy tayi domin sanin dama za'a yi hakan.










Kan shi ya dora saman kafad'ar ta yace"Mummy yanzu dan allah da mata na da komai amma a rasa wacce za'a aiko ta kawo mini abinci sai house mai..... ".








Be k'arasa ba sakamakon abincin da ta tura mishi a baki,Sannan tace"To ai ita matar taka ta tafi kano".








Ji yayi abincin ya sark'e shi hakan yasa ya k'ware,Tari ya fara yi ba k'auk'autawa, Mummy sai faman sannu take yi mishi.








Bayan ya lafa ya dubi Mummy ya bata fuska yace"Haba Mummy yanzu dan Allah da izinin waye ta tafi? ".










"Da izini na, ko ban kai bane?,Gobe za'a shiga court akan maganar Abba kabeeru hakan yasa ta tafi domin lawyer yana buk'atar ganin ta".










Bece komai ba amma shi ba haka ya so ba, shi da yaso a yau ya fara gwada mata irin son da yake yi mata amma Mummy ta bata show.










Tashi yayi jiki a sanyaye ya bar falon, waje ya fita ya zauna a balcony,tagumi ya zuba yana tunanin halin da yake ciki.










Wayar shi ya ciro ya kira yaya sadik,bayan sun gaisa yake tambayar shi yaushe ne daurin auren su feenert.








Yaya sadik ya bashi amsa da nan da kwana shida, lissafawa yayi yaga nan da ranar juma'a kenan.










Anya kuwa zai iya zama har ranar juma'a kan su had'u, gashi dole ya jira su tafi tare dasu daddy dan gobe zasu wuce adamawa dukan su.












Sosai hakan ya b'ata mishi rai,number d'in ta ya kafawa idanu, yana kallo tabbas yana son ko muryar ta ne yaji.








To amma ya san yanzu ba zai samu abinda yake so ba, domin kuwa dai yanzu ya san tana busy.








Washe gari da wuri suka shirya domin wucewa adamawa,Maleek ke driving,Saifullahi yana kusa dashi.










Daddy yana baya, sai Mummy sannan Hafsat,Saifullahi ya kalle shi, Fuskar shi tayi fayau sai dai yayi kyau cikin shadda light blue.












Murmushi yayi yace"Lily wai ya akayi ne?, naga ka rame sannan kuma ka zama wani so pale ne? ".












"Lovely ai yanzu ka dena damuwa dani,Yanzu ta matar ka kake yi, Idan ba haka yaushe zan kai iya yanzu baka ji me yake damu na ba".










"Haba lily me yasa zaka yanke hukunci haka?, oh!, wato dalilin da yasa kak'i zuwa gida na kenan".








Dariya yayi yace"taya zan zo gidan ka bayan nima ina can ina so in gina nawa gidan", dariya suka yi gaba d'aya.










"Wai me kuke wa dariya ne?,kuna gaba Allah yasa ba gulma kuke ba?,",mummy ta fad'a tana dariya.










"Kai Mum wallahi ba gulma muke ba, muna fira ne tskanin mu, kuma ai zaku iya yin taku",Saifullahi ya bata amsa yana dariya.












Ita kan ta Mummy taji dad'i ganin yadda Maleek ke farin ciki yau harda dariya.












Koda suka isa adamawa wanka yayi kawai ya kwanta.












_______________________________________________________________kano____________________








Ikhlas tana zuwa suka gana da lawyer ta bashi duk wata sheda da ya dace sannan ya bata tabbacin zai yi iya nashi kok'arin.














Washe gari da sassafe suka wuce garin bauchi,domin fara shari'a.








Shi kuwa abba kabeeru ana kai mishi takardar sammaci gaba d'aya ya rud'e, sai dai duk da haka bai k'asa a gwiwa ba ya nemi lawyer ya biya mak'udan kud'i domin ya san yadda zai yi ya siye judge din.








Amma abu bai yiwu ba, koda suka je court d'in basu wani sha wahala ba domin kuwa sun bayar da shedu sosai.












Takardun aka amsa duka akan aje ya tabbatar da wanne ne original wannene fake, Tun daga wajen Abba kabeeru ya sare.










Bayan sun fito court d'in Abba kabeeru ya dube ta yace"Ikhlas kina k'ok'ari sosai wajen kwatar wannan dukiyar dake da wannan yaron na na hannun ki".










"Ai baka gama ganin komai ba,kaje akwai abubuwa masu girgizarwa nan da d'an lokaci zaka gani",feenert ta bashi amsa tana murmushi.












Kallon yaya hafeez yayi yace"ku wuce muje gida, kasan an kusa auren ka", yana kama hannun shi.








Tafiya suka yi yayin da Ikhlas da feenert suka fashe da dariya,daga haka suka wuce gida a ranar suka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login