Showing 9001 words to 12000 words out of 71023 words
kauda fuska tana goge hawaye.
Wajen umma ya fara zuwa ya gaishe ta sannan ya matsa kusa dasu,ikhlas tana wanke-wanke,hannu ya saka yana taya ta.
Murmushi kawai tayi,sadik yace"babu gaisuwa?",sunkuyar da kai tayi,iman dake hada wuta tace"ina kwana yaya sadik",amsawa kawai yayi hankalin shi na kan ikhlas.
Sai da suka karya sannan kowacce ta kwanta,sai wajen azahar ikhlas ta farka,cikin sauri ta mike ta shiga wanka,tana fitowa iman ta gani,tsaki iman ta ja.
Cikin sauri ikhlas ta janyo ta tace"ke wallahi bazan dauki wannan rainin hankalin ba uban me nayi miki?",cikin tsiwa iman tace"uban ki kika yi mini",kan ta gama rufe baki ikhlas ta dauke ta da mari.
Da sauri gwaggo ta Karaso wajen tana fadin "me zan gani haka?',me yake damun kune?",duka tsayawa sukayi carko-carko kafin iman ta fashe da kuka.
Gwaggo ta dube ta tace"meya faru?",bata amsa ba sai ma juyawa da tayi ta koma daki,gwaggo ta dubi ikhlas tace"meya hadaku?",ikhlas ta tabe baki tace"babu komai",tana fadin haka ta ajiye bokitin ta dau buta ta shiga yin alwala.
A kwance ta sami iman tana kuka,tabe baki tayi tace"aikin banza",cikin sauri iman ta juyo tace"aikin banza ya wuce wanda kike yi banza kawai",ikhlas ta zaro idanu tace"ni kike cewa banza lallai ma!",shinfida abin sallah tayi ta tada sallar ta yayin da iman ta koma ta kwanta tana cigaba da kukan ta.
Koda ta idar addu'o'i ta tsaya tayiwa mahaifin ta sosai sannan ta mike,da mamaki tace"wahala bata ishe ki bane",kamar jira iman take ta mike tsaye,dauke ikhlas da mari tayi tace"ki fita harka ta kinji na gaya miki".
Cikin mamaki ikhlas tace"ni kika Mara?",an mareki ko zaki rama ne?",kan ta rufe baki taji saukar mari dama da hagu",gwaggo data shigo yanzu tace"ni naga abin da yafi karfina ni binta,meye haka?".
Umma data shigo yanzu tace"lafiya kuwa gwaggo?"gwaggo tace"zoki ga abinda ban taba gani ba",umma ta karasa shigo wa,kallon su tayi duka suna tsaye kowa idanu yayi ja.
Umma tace"lafiya kuwa?"gwaggo tace"tambaye su dai halima tun dazu suke mare-mare",umma ta rike haba tace"to abinda yazo muku yau kuma kenan allah ya kyauta",gwaggo ta amsa da ameen.
Yau saura kwana biyu su koma makaranta,har yanzu basu dawo dai-dai ba,amma duk da haka waje daya suke kwana su tashi,suna magana sama-sama.
Ikhlas da yamma ta shirya ta shiga gidan umma,a zaune ta sami umman tayi tagumi,zaunawa tayi kusa da ita ta cire mata tagumin tace"haba umma meye haka?,ajiyar zuciya umma tayi tace"ikhlas rayuwar duniya abin tsoroce wanda baka taba tunanin zai cuce ka ba shi zai cuce ka".
Ikhlas tace"haka rayuwar take umma amana tayi karanci",umma ta numfasa tace"nidai ikhlas abinda nake so na fada miki shine
Kada a baki amana ki sake ki ci kinji,kada ki sake ki kauce kan halayyar da mutane suka sanki,ki kasance Koda yaushe zahirin ki da badinin ki daya ne,kiji tsoron Allah ki rike mutuncin kanki kada ki sake ki watsar da mutuncin ki a duniya.
_Sannan ki rike iman da gwaggo da sadik domin bakida sama dasu duk fadin garin nan,kada ki sake ki barsu a damuwa bayan kinada damar fitar dasu daga wannan damuwar,ki kiyaye bacin ransu kinji ikhlas_.
Daga kai ikhlas tayi sannan tace"insha Allahu zan kiyaye hakan umma",murmushi umma tayi ta kwantar da kanta a kafar ta tana shafa kanta,ita kuwa ikhlas wani dadi ne ke ratsa ta,a haka barci ya dauke ta.
Karfe goma da rabi na dare sadik ya shigo gidan da sallama,umma ta amsa,tsugunawa yayi yana murmushi yace"dama dawowata kenan shine gwaggo take ce mini wai ikhlas ta fita tunda yamma bata dawo ba nazo na duba lafiya kuwa?",umma tayi murmushi tace"wallahi lafiya lau ka ganta nan tana ta barci,tashe ta ku tafi".
Sadik ya matsa kusa da ita a hankali ya fara tashin ta cikin kasala ta mike,idanun ta a rufe Dan haka bata ma san waye a kusa da ita ba,mika tayi wanda sanadiyar hakan kirjin ta ya taba shi.
A hankali barcin ya fara sakin ta,sadik kuwa tuni ya bar duniyar nan,da sauri ya fizgo numfashin shi,kamar me hada kalma yace"tashi mu tafi gida".
Jin muryar shi yasa tayi saurin bude idanu,zaro idanu tayi ganin da gaske shine fa,juyawa tayi ta kalli umma ganin basu take kallo ba yasa ta turo baki gaba.
Sadik ya mike yaja hannun ta,dole ta mike,kallon umma tayi tace"na tafi umma sai da safe",murmushi umma tayi tace"Allah ya tashe mu lafiya",har sun kai kofar fita ta Kira sadik.
Duka suka juyo,murmushi tayi tace"ga kanwarka nan ka kula da ita kaji",jinjina kai Kawai sukayi suka fice.
Suna fita gidan ya juyo ya kalle ta yace"ashe dama abinda kike so kenan?,kallon tayi mishi mai alamar me kenan?,fuskar ta ya shafa yace"aure kike so ko?",zaro idanu tayi tace"a'a wallahi ni ba aure nake so ba",yace"to idan bashi kike so ba ya akayi kika iya mika me sa namiji jin zafi",ai da sauri ta shige gida tana fadin"na shiga uku",dariya yayi kawai sannan ya shiga gidan.
Tana shiga ta sami gwaggo na sallah ita kuma iman na kwance tana danna wayar gwaggo,iman tunda ta amsa sallamar da tayi ta juya ta cigaba da abinda takeyi.
Tabe baki ikhlas tayi ta tube kayan ta ta shiga wanka,tana fitowa yana shigowa gidan Colin,sauri ta juya.
Dariya abin ya bashi ma,ganin zata koma bayin yasa yayi saurin riko ta,runtse idanu tayi tana fadin"Dan allah kayi hakuri",dariya yayi yace"meye na cewa nayi hakuri oh!kema kinsan kin sani canza wanka kenan?",kirjin ta ya buga tace"wallahi ba haka bane",hannunta ya rike yace"to gaya mini yaya ne?kawai ki fito kice yaya sadik ka nemo sadaki domin na kosa muyi aure",kasa cewa komai tayi sai kirjin ta dake dukan uku-uku.
Shiru na yan minti na ya biyo,a hankali ta bude idanun ta,lips dinta ya tsurawa idanu kawai yana kallo,da sauri tace"yaya barci nake ji",a hankali ya kai bakin shi cikin Nata.
Kissing dinta yake cikin sanyi,gaba daya ya kwance mata notinan kan ta,sun kai minti goma a haka sannan ya kyaleta,a sanyaye yace"ikhlas ina sonki sosai pls nima ki soni koda rabin wanda nake yi miki ne?,ita kam gaba daya ta zama statue tana kallon shi.
Sai data dai-dai ta nutsuwar ta sannan ta matsa,riko hannun ta yayi,cike da kasala tace"pls yaya ka sake ni kada gwaggo taga na dade ban shiga ba ta biyo sahu",a sanyaye ya sake ta.
Har lokacin tayi mamaki data sami iman idanun ta biyu.
Humra ta shafa sannan ta dauko kayan barci ta saka,sai da tayi addu'a ta tofe jikin ta sannan ta kwanta.
Iman ta taba ta a hankali tace"sisto meya faru dake",sama-sama tace"babu komai",kamar iman zata ce wani abu sai kuma ta fasa.
Shiru ya biyo baya domin gwaggo ta dade da wucewa jidda a barci,ikhlas tace"me yasa kwana biyu kika Dena kula ni ne?iman ta gyara kwanciyar ta tace"kawai bana mood ne?",ikhlas tace"sorry",
For what?",iman ta tambaya,ikhlas tace"akan marin ki da nayi mana",murmushi iman tayi tace"wallahi babu komai ya wuce nima kiyi hakuri da abinda na gaya miki",anan suka cigaba da firar su har barci ya dauke su.
A gigice ikhlas ta farka,iman da tazo tashin ta tayi sallah tace"sisto lafiya?",ikhlas ta share gumi tace"iman umma na ina so naje na ganta",iman ta dafata tace"ikhlas mafarki ne fa ki bari sai anjima",cikin sauri ta mike tayi waje.
Iman itama ta biyo ta da sauri,gwaggo dake alwala ta fara fadin"lafiya ganin sunyi waje yasa ta janyo hijabi ta bisu,a zaure taci karo da sadik,yace"gwaggo lafiya kuwa ina zuwa naga kina ta sauri haka?",Gwaggo tace"biyo ni dai".
Gidan suka fada a zaune suka sami ikhlas tana kuka,iman na rungume da ita,gwaggo tace"meye ke kuma kike kuka ina umman taki?",shiru babu wanda ya amsa,cikin sauri sadik ya fara kwalawa umman Kira.
Iman ta share hawaye tace"yaya sadik umma ta bace mun duba ko'ina bamu ganta ba",shiru wajen yayi kafin gwaggo ta dau salati.
Wasa-wasa har yamma ba'a ga umma ba,an bincika duk inda ake tunanin za'a ganta amma shiru,Abba kabiru kuwa har cigiya ya bayar gidan talabijin da radio.
Zuwa lokacin idan kaga ikhlas sai ta baka tausayi,tayi kuka har ta bawa uku lada,hartana gwaggo sai da tayi kuka,sai jaje makwabta ke zuwa.
Ikhlas ta kwance iman na zaune a gefen ta tana jera kayan su na komawa makaranta washe gari,sadik yayi sallama ya shigo.
Kusa da ita ya zauna,hannu yasa ya dago ta,kasancewar babu karfi jikin ta yasa ta fada jikin shi,kan kafar shi ya kwantar da ita,hannunta ya rike yana murzawa a hankali.
Cikin sanyin murya yace"ikhy kiyi hakuri ki tashi kici abinci kinji",shiru tayi taki cewa komai,iman data mike zata fita yace mata"ki zubo mini abinci ki kawo mini",amsawa tayi kawai ta fita.
Jimawa kadan ta shigo ta ajiye abincin a plate,sai da ya taimaka mata ta dauraye bakin ta sannan ya zaunar da ita,cokali ya dauka ya debi abincin ya kai bakin ta,rau-rau tayi da idanu,daure fuska yayi yace"maza amsa",idanu suka kafe da juna,kallon shi take har tana lumshe idanu.
Bude baki tayi ya saka mata empty spoon,da sauri ta kalli plate din,ganin babu abincin yasa ta zaro idanu,dariya ya fara mata,ita ma kanta abin ya bata dariya,dubgure mata kai yayi yace"dama yunwa kike ji kika wani lafe",murnushi kawai tayi bata ce komai ba.
💮💮💮💮💮💮💮💮
*ASHE KECE???*💮💮💮💮
(Hypocrite-love-sacrifice)
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATON~💫💫💫*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~❄we beare's of soon golden we writer's assiduously percieven No pain so magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Out worlds for it cause u np pain~*
Wattpad @13 deeja
Or
Deeja1love.blogspot.com
*written
-by-
*Deeja one love*
*dedicated
to
*Maryam khamis*
013-014
Da kanshi ya lallabata sannan ta shirya kayan ta,ita dai iman yar kallo ce.
Washe gari sai da suka biya gidan Abba kabiru,ya kara yi mata nasiha sannan suka tafi,wannan karan yaya sadik kawai ya kaisu.
Yau suke shirin barin makaranta domin dai alhamdulillahi sun Riga da sun gama,cikin tsananin farin ciki suke,idan kaga iklas da iman sun kara zama yan mata,yanzu kam babu rawar kai Dan tun batar umma ta dena.
Hada kaya take cikin sanyin ta Wanda idan baka San halin ta ba sai kace tsabar iyayi ne,kmk ta shigo dakin tana fadin" babies ku fito yayan ku ya zo".
A bakin get suka same shi,ikhlas ta rungume kmk tace"insha Allahu zamu kawo miki ziyara",itama iman rungume ta tayi,tana tsaye har suka shige mota.
Gaba ikhlas ta zauna,ita kuma iman as usual ta shiga baya.
Iman ta dube shi tayi murmushi,kallon ta yayi yace"lafiya?",murmushi ta kuma yi sannan tace "babu komai",titi ya kalla sannan yace"ke dai fadi gaskiya ko kinga na miki kyau ne?",tabe baki tayi tace"komai kyawun ka ai na fika",be kuma cewa komai ba.
A haka har barci ya dauke ta,suna isa iman ta bude kofa ta fita,kallon ta yayi yace"jeki gida zan sa a shigo miki da kayan idan gwaggo ta tambaye ki ina ikhlas kice muna tare",daga kai tayi sannan ta juya ta shiga a sanyaye.
Zuba mata idanu yayi yana kallon ta yana murmushi,a haka har tsayin minti talatin.
Ikhlas ta bude idanu a hankali tana lumshe idanu,ganin su a kofar gida yasa tayi saurin zaro idanu,kallon shi tayi taga Danna waya yake yi.
Cikin murya me nuna daga barci ta tashi tace"mun iso ne yaya?",be kalle ta ba yace"tun dazu muke nan kin wani shanya ni",tabe fuska tayi tace"kai yaya maimakon ka tashe ni",ajiye wayar yayi yana kallon fuskar ta,ita kuwa Kara cuno baki take.
Murmushi yayi yace"ki dena idan ba haka ba,nayi maganin ki",kauda kai tayi tace"bude mini na fita",murmushi yayi yace"to princess",fita yayi ya zagayo ta bangaren ta ya bude mata.
Iman dake labe bakin kofa tayi saurin shigewa ciki tana share hawaye,da sallama ta shigo gidan,gwaggo ta amsa kusa da ita taje ta zauna.
Gwaggo ta dube ta tace"kin dawo kenan?",daga kai kawai tayi,sadik kuwa juyawa yayi ya fita,da kan shi ya shigo musu da jakar tasu.
Yau kam cikin farin ciki take domin zata kwana a gida,duk da tasan baza ta ga umma ba but amma ance no place like home.
Yau tunda suka tashi suka shirya domin tafiya gidan abba kabiru,riga da zani na titin abuja ja da ratsin blue suka saka.
Gyale da takalmi duka green haka ma yan kunnayen su.
As usual ikhlas na gaba suna fira,ita kuma iman na baya tana tana kale-kalle.
Yana yin parking ta fita daga motar,itama Islam tana jin tsayawar mota ta fito da gudu,cikin farin ciki suka rungume juna.
Hararar su yayi yace"dalla kin cika mana kunne,sukam bama su San yana magana ba.
Hannun islam da iman taja sukayi cikin gida da gudu,murmushi kawai yayi ya girgiza kai,ba zasu taba girma ba kenan.
Kamar yadda ya zata kuwa Abba kabiru yana gida,sai da suka gaisa da mama sannan ya gaida abban.
Mama ta mike ta nufi kitchen,sunkuyar da kai yayi yace"dama Abba akan maganar ikhlas ne",gyara zama Abba kabiru yayi yace"inaji mai ya faru?",shafa kanshi yayi yace"dama wai cewa nayi tunda sun gama secondary me zai hana kawai a mana aure tunda dama ita nake jira".
Shiru Abba kabiru yayi kafin yace"to ni dai bazan ce komai ba sai dai zan zo muyi magana da gwaggon naku abin da tace shikenan".
Cikin farin ciki sadik yace"ba gode sosai Abba allah ya kara budi",da murmushi a fuskar shi ya amsa da "ameen,yauwa magana akan wa'innan documents din da zakayi signing akai",sadik yace"Abba zan yi amma mu bari zuwa nan da lokacin da * M Y GIMI TRADING COMPANY* zasu sayi share din daga wajen mu,kaga a lokacin brr.bashir ya dawo daga course din daya tafi".
Jinjina kai yayi yace"hakane ka fini gaskiya,allah ya kaimu da rai da lafiya",sadik ya amsa da "ameen, Abba bari naje wajen Dan uwa na",da kai Abba kabiru ya amsa,murmushi sadik yayi ya juya ya tafi.
A kwance ya sami hafeez,tashi yayi cikin farin ciki yace"ya meya faru?"Dan karamin ajiyar zuciya sadik yayi yace"wallahi maganar auren mu nida ikhlas nayi wa Abba shine yace zai je yayi wa gwaggo magana",dariya hafeez yayi yace"allah ya taimaka",da amen sadik ya amsa.
Ikhlas kam suna shiga dakin Islam suka baje babu abinda suke sai fira,duk sun cika da farin cikin ganin juna.
Islam tace"yanzu ke ikhlas aure zaki yi,tab maimakon ki cigaba da karatun ki",murmushi ikhlas tayi kan tace"kada ki damu Islam idan da rabon nayi karatu ko bayan auren ne zan yi",Islam ta tabe baki kawai,ita kam iman bata ce komai ba.
Sai da suka yi sallar magrib sannan suka tafi, a kofar gida yayi parking,iman kam fita kawai tayi.
Sadik yayi murmushi yace"amarya ta ya dai",fari tayi tace"kai kuma ango ko?",dariya suka yi gaba daya.
Sai da ya tsagaita sannan yace"wato ikhlas ina miki son da ban taba yiwa wata 'ya mace a duniya ba,na fara son ki tun kina kwaila (kamar namesy khadeeja duhu😜)".
Murmushi tayi tace"nima yaya sadik ina sonka tun kana kwaila",zaro idanu yayi yace"ke waye yace miki namiji yana zama kwaila?",cuno baki tayi tace"eh mana idan namiji bashi da gemu ai sunan shi kwaila".
Dariya abin ya bashi sai da ya dara sannan yace"to masu askewa kuma fa?",lumshe idanu tayi tace"ai duk da haka sun girma ai",zuba mata idanu yayi yana kallon ta zuwa can yace"to ita kuma mace idan tana meye ake dena ce mata kwaila?".
Wayyo!ai da sauri ta bude motar ta fice tana dariya,shima dariyar yayi kafin yace"my beauty I like your childish too",motar yayi reverse sannan ya bar wajen.
Bayan sun gama abinda suke ,suka kwanta iman tace"ni wallahi wannan rashin wayar ya isheni gobe idan allah ya kaimu zan sami yaya inyi mishi magana",ikhlas tayi murmushi tace"da kuwa kin kyauta wallahi sis".
Da safe bayan sun gama abinda suke yi,ikhlas tace"dama yaya zai bari ai da mun je saloon wallahi kaina babu dadi",iman tace"ki bari gobe sai mu tambaye shi tukuanna sannan mu tafi kin San hali dai".
Ikhlas tace"ke kuma matsoraciya dai kawai",haka suka gama abin da suke yi sannan suka wkwanta.
Sai bayan la'asar ya dawo,a zaune ya same su a tsakar gida, ikhlas na jajjage,ita kuma iman tana hada wuta, gwaggo kuma ta fita makwabta.
Sannu da zuwa suka yi mishi,kallon ikhlas yayi yace"beauty zo kinji",Dan murmushi tayi kafin tace"yaya girkin fa?",hade rai yayi yace"yau ku bar girkin mana".daga kafada tayi alamar ok.
Hannun ta yaja yayi waje da ita,murfin motar ya bude ya saka a ciki,bece da ita komai ba yaja ya fara tafiya,ganin haka itama taja bakin ta tayi shiru.
Wani k'ayataccen wajen shakatawa ya kaita,bayan sun zauna ya kalle ta yace"beauty gaya mini gaskiya me yasa kike sona?",sunkuyar da kai tayi bata ce komai ba.
Can tayi murmushi tace"nima yaya bansaniba nidai naji kawai ina sonka ne",murmushi yayi yace"ni kuma ina sonki ne saboda kina da yawan kula da addini sannan kina da duk abinda nake son matata ta kasance tana dashi",haka dai suka cigaba da firar su ta masoya kafin yamma tayi.
A shahara restaurant yayi musu take away,suna komawa tayi alwala tayi sallah sannan suka zauna zaman cin abinci.
💮💮💮💮💮💮💮💮
*ASHE KECE???*💮💮💮💮
(Hypocrite-love-sacrifice)
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATON~💫💫💫*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~❄we beare's of soon golden we writer's assiduously percieven No pain so magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Out worlds for it cause u np pain~*
Wattpad @13 deeja
Or
Deeja1love.blogspot.com
*written
-by-
*Deeja one love*
*dedicated
to
*Maryam khamis*
15-16
Washe gari da wuri suka tashi sai sa suka gama ayyukan su sannan suka shirya domin zuwa saloon.
Gidan su Islam suka biya sannan suka wuce,abin ka da me gashi na ikhlas yafi ba kowa yin kyau, sai da aka gyara musu farce sannan suka taho.
Suna dawowa gida suka yi sallah,sun daura girkin dare kenan Abba kabiru yayi sallama,gaishe dashi suka yi sannan suka cigaba da aikin su.
Yaya sadik yayi sallama ya shigo,dakin gwaggo ya shiga,ya jima kadan sannan gwaggo ta kwala musu kira.
Cikin sauri suka shiga,waje suka samu suka zauna,Dan da alamu maganar tana da mahimmmanci.
Abba kabiru ya fara magana"alhamdulillahi yanzu kun gama secondary school, kuma ku kunsan cewa amana ce agareni ku,Dan haka duk wani nauyi naku ina kokari wajen ganin ba sauke shi,Dan haka jiya sadik yazo mini da maganar yana so ya auri ikhlas domin sun shirya kan su".
Numfasawa yayi sannan ya ci gaba"to a lokacin nace mishi ya bari nazo mu zanta da gwaggo,sai dai zuwa yanzu take nuna mini da cewa auren