Showing 60001 words to 63000 words out of 71023 words

Chapter 21 - ASHE KECE Complete By One Love .txt

One Love   

31 Jan 2025

4664

tafi mutunci fiye da waccen.




Ita kan ta Ikhlas din shi take kallo domin shima yanzu shadda ce a jikin shi sabanin yadin daya saka, Bata san wanne zata ce yafi yi mishi kyau ba domin duka sun mishi kyau.




Kusa da ita ya matsa hannun shi ya kai kan hips din ta ya shafa a hankali,yayin da ya sakarwa lips din ta wani passionate kiss.








A hankali yace"Kinyi kyau",murmushi tayi tace"Na gode sosai, Kai ma kayi kyau", Be amsa ba sai daukar ta da yayi cak ya nufi hanyar fita da ita.










Wannan karan bata wani tsaya bata lokaci ba wajen kokarin kwace kan ta ba,Sai da ya bude motar ya saka ta ya rufe sannan ya juya ya koma.








Wannan ledar da ya shigo da ita ya dauko,Baya ya bude ya saka sannan ya shiga mazaunin driver yaja motar a hankali.










*Comments *
*like and share*






*Maman farouk da elham ce*








💮💮💮💮💮💮💮💮
*ASHE KECE???*💮💮💮💮
(Hypocrite-love-sacrifice)






https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


✍✍✍✍✍✍✍
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION~*
✍✍✍✍✍✍✍




*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*




*written*
-by-
*Deeja one love*








*🏆JAKADIYAR GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION*🏆






*Dedicated*


-to-
*Maryam khamis*




65-66




Suna isa wajen an riga da an fara,Da sauri ta nemi shiga,Janyo ta yayi yace"Excuse me, Ki jira ni malama".










Sauri ta k'ara domin kada ya cimma ta, Da sassarfa ya k'araso gare ta,hannun ta ya rik'e sannan suka jera.










Suna zuwa shiga,Suka ji dj na na cewa"Ga k'anin ango nan haka kuma yayan amarya,Tare da kanwar amarya haka kuma k'anwar ango".












Kallon juna suka yi,Wanda a lokacin kallo ya dawo kan su,Sosai wajen ya dauki shewa,Ango kuwa sai da yaji wani iri a ran shi ganin su tare.










Kan step suka wuce,Maleek ya mik'awa d'an uwan shi hannu yana fad'in"Congrats bro".








Hafsat ta janyo Ikhlas tace"Wato kin tafi soyayya kin manta da yar uwar ki",Harara ta balla mata tace"da wannan mata mazan".








Dariya hafsat tayi tace"Hakane shi yasa naga har canza kaya akayi",Wayan cewa kawai tayi domin kuwa tabbas hakan ne.










Kujera ta nema ta zauna,Maleek kuwa kusa da ango ya zauna,Sai dai fa idanun shi na kan ta.










Feenert tace"Ke dallah Kin tafi soyayya kin manta damu",Shiru tayi bata ce mata komai ba.








Ango saifullahi ma hankalin shi yana kan ta,Domin kuwa tun da ta san bikin shi ne,Har yanzu bata tsaya ta kula shi ba.












Maleek shi ya bada tarihin ango,Ita kuma Bintu ta bada na amarya,Sannan fa dj ya kira Ango da Amarya domin su dan taka.










Sosai suka sha lik'i,sadik ya mik'o mata kud'i yace"K'anwata aje a lik'a mata mana",Hannun Iman ta rik'e suka tafi tare.










Ai fa tana shiga samari kuma suka yo kan ta,Lik'i ya koma kan ta,Cike da jin haushi Maleek ya kutsa tsakiyar su ya rik'o hannun ta yace"Koma wajen zaman ki".












Cike da masifa tace"Ba zan koma ba wai kai kamar wani uba na kana wani bani umarni,Aikin banza kawai.












Ficikar hannun ta yayi yace"Banda lokacin jin wa'innan shirmen naki",Sai da ya dangana ya da kujerar zaman ta sannan yace"Wallahi kika tashi sai ranki ya bac'i".








Ya juya ya koma wajen zaman shi,murmushi Saifullahi yayi ganin yadda ta wani had'e rai.








Idanun ta ta kai kan amarya hafsa ta mata alamu da hannu akan soyayya ko?,Jan tsaki tayi tana juyar da kanta.










Haka har aka tashin kuwa bata mik'e ba,yana zuwa inda take yace"Tashi mu tafi",Banza tayi dashi kamar bata ji shi ba.












D'aukar ta yayi cak ya fita da ita,Ikhlas kam sai faman surfa masifa take,Su Iman sai kallon ikon Allah suke suna dariya.








Rufe k'ofar yayi sannan yazo yayi musu sallama kafin ya koma ya shiga motar shi ya ja ya bar wajen.












Gudu sosai yake yi kuma babu wanda yayi magana a cikin su,har suka isa gidan.








Kallon gidan tayi,Kafin ta juyo tace"Wai kai me ka mayar dani ne?,Gida zaka kai ni malam,Ka juya ka kai ni wajen mahaifiya ta".










Be yi magana ba dan kan ta ta gaji tayi shiru,Fuska a had'e yace"fito mu tafi",Banza tayi dashi.








Kara d'aukar ta yayi,Kan kujera ya ajiye ta sannan ya kalle ta yace"Kin ga ki bini a hankali idan ba haka ba wallahi zaki kwana a gidan nan".










Juyar da fuska tayi tace"ba sai naga wanda zai sani na kwana ba,Tun da an gaya maka ni 'yar iska ce".








Dariya abin ya bashi,Sai da ya dara kuwa sannan yace"Haka kika ce ko?,To zaki gani kuwa,ki shiga kitchen ki dafa mini abinci".








murgud'a baki tayi tace"sai naga wanda zai sani nayi girkin",Kusa da ita ya matso yace"abinda kika ce kenan?".










Bata ce komai ba,Zama kusa da ita yayi yasa hannu ya janyo ta jikin shi,Hannu yasa ya zagaye hips din ta yace"Ni zan ce ki mini girki ki kiyi ko".








A hankali ya zame fuskar shi ya sauke ta akan saman kirjin ta,Hannun shi yasa ya dan tura ta kad'an ta fad'a kan kujerar.








Bin ta yayi ya had'e bakin su,sosai yake tsotsar harshen ta,yayin da hannun shi yake saman kirjin ta.








Jikin ta gaba d'aya ya mutu,sak'on ta fara amsa yasa ta rike shi sosai ita ma ta fara taimaka mishi.








Maleek kuwa gaba d'ayaya fice hankalin shi,nishin su kawai ke tashi daga d'akin,Hannu yasa ya zage rigar ta.










Wanda yayi dai-dai da k'arar wayar shi,da sauri ya matsa daga jikin ta ya kife a wajen yana dafe da marar shi.










A sanyaye ya d'aga wayar ganin mummy ce,Yana dagawa tace"ka dawo da Iklas gida yanzu nan,ina jiran ta kaji me nace ai".










Sosai yayi k'ok'arin dai-dai ta nutsuwar shi kan ya amsa da"to,gamu nan",Gaban mummy sai da ya fad'i jin yanayin muryar shi.








Fatan ta kawai Allah yasa be yiwa Ikhlas d'in komai ba.










Abinda ya faru kuwa shine,Bayan yan dinner sun koma gida,Umma tana ta faman zuba idanu taga Ikhlas ta dawo bata gani ba.










Gashi tana jin kunyar tambayar su ita take,Ganin ta kasa jurewa yasa ta kira iman,Sai da ta jata can bayan gida sannan take tambayar ta ina Ikhlas din takeⁿ










Nan Take gaya mata suna tare da maleek,Tun dazu yaci ace ma sun dawo,Umma tace"Kada ki damu,Zasu dawo ne",Suna fad'in haka suka tafi.










Ashe Mummy da aunty meenat suna zaune a wajen,Jin haka yasa ta kira shi tace ya dawo da ita.








Can kuwa tun da ya kife ya kasa ko motsawa,Ikhlas tace"Ka tashi ka kai ni gida na gaji".








Mik'ewa yayi yana tafe yana tangad'i ya shiga motar,Sai da ya dai-dai ta kan shi sannan ya tada motar.








Suna tafe babu wanda yace da kowa komai,Shi kam damuwar shi,Shine yadda zai yi barci yau.






Ita kuwa tunanin ta ya ake take biyewa Maleek alhalin tasan ba mijin ta bane sannan kuma ba soyayya a tsakanin su?,Ita ta san ko lokacin da suke soyayya da yayan shi hakan baya faruwa.












Yana parking ta bude motar ta fito, Har ta fara tafiya taji an riko hips din ta an maida ta baya.








Juyo da ita yayi ya manna ta da jikin motar kallon cikin idanun ta yake yi, cikin sarkewar murya yace"babu sai da safe? ",bata ce komai ba domin irin matsar da yayi mata.










hannun shi ya dora saman kirjin ta sannan ya hade bakin su, sai da yayi kissing din ta sosai sannan ya sake ta.








Kan shi ya dora saman kafad'ar ta ya riko hab'ar ta yace"pls yau ki bari mu kwana tare mana".








Kallon baka da hankalin tayi mishi,Cikin idanun ta yake kalla wanda yaga zallar masifa amma babu bakin yi.








Murmushi yayi sannan ya juyar da ita,Hannun shi na hips din ta suka fara tafiya a haka, sai da ya dangana ta da kofar bangaren da suke sannan ya sake ta.








Hannun shi ya saka ya shafa lips din ta sannan yace"sai da safe", Daga haka ya mik'a mata ledar hannun shi sannan ya juya ya tafi.










A wajen ta tsaya har sai da ta sami k'arfi kadan sannan ta shiga ciki.








*like*
*comments and share*.










*one love*








💮💮💮💮💮💮💮💮
*ASHE KECE???*💮💮💮💮
(Hypocrite-love-sacrifice)






https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


✍✍✍✍✍✍✍
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION~*
✍✍✍✍✍✍✍




*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*




*written*
-by-
*Deeja one love*








*🏆JAKADIYAR GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION*🏆






*Dedicated*


-to-
*Maryam khamis*










67-68








Duka sun kwanta amma idanun su biyu, Tana shiga suka bita da kallo,Harara ta balla musu sannan ta cire kaya ta shiga bedroom.










Dariya suka kwashe dashi, Beelert tace"ana so ana kaiwa kasuwa",Feenert tace"haba dan ma baki ga show d'in tafiya ba".










Fitowar ta yasa suka yi shiru, K'in kula su tayi,Tana gama shiryawa ta, ta dauki ledar ta bude.








Matsowa suka yi duka,Harara ta kuma balla musu tace"wallahi ku fita ido na, Banzaye munafikai".












Hafsat tayi dariya tace"uhumm,Kanwa ta kenan, Yanzu dai a bude mu ci ko? ", Dariya suka yi gaba daya.










Tura musu tayi,suna ci suna fira,Ikhlas tace"Me yasa Hafsat baki gaya mini tun ainihi cewa Maleek dan uwan ku bane?".












"Wallahi kiyi hakuri, gani nayi bashi da wani amfani na gaya miki,Shiyasa ma na hana abdallah shima ya fada miki".










Ajiyar zuciya tayi tace"ina so naji ya akayi umma ta bar garin bauchi",Iman tace"Ni ina gani kawai ki bar maganar domin tone-tone bashi da amfani".










Feenert tace"Hakane kuma,Gaskiya kawai ki bar maganar",Ikhlas ta kalli Hafsat tace"Ina baby".










"Haba Ikhlas kema ai da abin dariya kike, Sai da kika gama soyayyar ki sannan kika tuna dashi, To yana wajen abdallah", Beelert ta bata amsa.














Gyara kwanciya kawai tayi,Tunanin abinda ya faru dazu take tayi, Sosai wasu abubuwan suke bata mamaki.












Bangaren maleek ma hakane domin kuwa barci dai ya gagare shi, dan daya rufe idanun shi ita kawai yake gani,surar ta da fuskar ta, wani irin murdawa marar shi tayi wanda yasa ya fara juye-juye.










Cikin barci saifullahi yaji kamar nishin shi,a gigice ya tashi yana tambayar lafiya kuwa? ",sai zufa yake hadawa.












Sudeis wanda dama yazo daurin aure ya rike shi gam, Jikin shi har rawa yake yi,duk ya hada zufa.










Bakin shi ya bushe, kokarin jan numfashi yake da samawa mak'ogoron shi miyau wanda zai hadiya.












Duk tambayar da suke mishi ya kasa basu amsa,sai dai nuna musu jakar kayan shi da yake yi.










Sudeis ya lura da inda yake nunawa, Yayi saurin sakin shi ya nufi wajen jakar, Sai da ya bincika sosai sannan ya dauko wani tablet.








Da sauri yazo ya balla ya sa mishi a baki,Saifullahi ya miko ruwa ya sha,Sannu a hankali ya dinga ajiyar zuciya har ya samu relief.










a hankali barci yayi awon gaba dashi,Sai da yayi barcin sannan suma suka sami damar kwanciya.










Da asuba bayan ya tashi sai da yayi wanka,Saifullahi da sudeis suna zaune ya fito,sudeis ya bishi da idanu.








Hararar shi yayi yace"wai meye ne ka wani sa mini ido? ", Dariya yayi yace"Banza dan iska, mutum yana son aure amma girman kai ya hana shi yayi bayani".








Banza yayi dashi,Saifullahi kuwa bece komai ba sai dai yana mamakin yadda dan uwan nashi yake yanzu.










Zaune suke duka a falon Baffa,'Yan matan suma suka yi sallama suka shigo,Waje suka samu suka zauna.








Maleek da tunda ta shigo yake bin ta da idanu, sosai tayi kyau cikin shigar doguwar riga ta atamfa.








Mafarkin jiya ya tuna, murmushi yayi ya shafa kan shi, Wanda yana dagowa suka hada ido da mummy.










Baffa yayi gyaran murya yace"To Hafsat kin san dai yanzu kin shiga sahun manya,Ga dan uwan ki nan mijin ki kuma, ki bishi kiyi mishi biyayya domin samin aljannar ki".










"Manzon Allah (S. A. W) yace"da ace za'a iya yiwa wani sujadda bayan Allah, To da an umarci mata ta yiwa mijin ta sujjada".










"Haka kuma ki sani cewa,kiwo aka baki kuma ranar kiyama za'a tambaye ki game da wannan kiwon,kada kiyi abinda zai bata ran shi ki zamo mai yi mishi biyayya, wannan shine nasiha ta a gare ki".










"Sannan sai magana a kan ki", ya fada yana nuna Ikhlas"muna so muji shin kina da aure ne, ko kuwa kin yi aure kafin zuwan ki nan".












Kan ta a kasa ta girgiza alamar a'a,murmushi yayi yace"to masha Allah komai yazo da sauki, tun da har hakan ya kasance, Ki sani kafin bayyanar ki, yan uwan mahaifin ki sun zo, kuma an daura auren ki da dan uwan ki *ABDUL MALEEK*gashi nan zaune", ya fada yana nuna shi.












Da sauri ta dago idanun su ya hadu,Wanda dama Maleek so yake ya ga ya reaction din ta zai kasance?.












Baffa da be lura da yanayin su ba ya cigaba da cewa"yanzu abinda muka yanke shine, ba zaki tare ba har sai kun fahimci junan ku".










"Sannan kai ango,Ga amanar kanwar ka nan, idan har ka zalince ta ka sani Allah yana kallon ka, kuma zai bi mata hakkin ta, Ka kara hakuri kai ne babba ka fita hankali, Duk abinda zata maka kayi hakuri da ita".










"Idan da me magana zai iya yi? ",kasa da kai saifullahi yayi yace"Insha Allah Baffa ba zaku sami kowacce matsala daga gare ni ba, Sai dai ina neman alfarma daga gare ku akan a taya ni bawa Ikhlas hakuri na rashin adalcin da banyi mata ba".








Baffa ya kalle shi da mamaki yace"Dama ka san ta ne kafin yanzu? ".








"Eh itace wacce na kawo maganar ta wajen su daddy amma suka hana ni auren ta saboda zaman kan ta da tayi".






Shiru duka akayi,Baffa ya katse shirun da cewa"To ke Ikhlas kin ji, Sai kiyi hakuri".












"Babu komai, ni dama ban rike shi da komai ba,Dama nasan babu me yarda dan shi ya aure ni a wannan halin".








Daddyn adamawa yace"To me zai hana a fara bikin su Ikhlas din idan yaso sai a wuce dasu duka kawai".










Baffa yace"A'a hakan ba zai yiwu ba, su fara fahimtar juna tukunna,Ko abdul maleek kana son ta a yanzu".










Kallon ta yayi ta gefen ido, ganin ta kafe shi da idanu ya san me take so yac, Maida kallon shi yayi kan mummy, d'aga mishi kai tayi alamar ya amsa.








Shafa kan shi yayi yace"a'a baffa", Baffa ya maida kallon shi gare ta yace"ke fa? "Ba tare da wani tantama ba tace"a'a".








Baffa yace"ka gani ko jabeeru, dan haka ka bari kawai idan sun fahimci juna",Daddy yace"To ina neman alfarmar a bari mu tafi da ita can kadunar".








Baffa yace"wannan babu matsala,Zaka iya tafiya da ita, Dan haka kuje ku shirya jirgin ku na karfe biyu ne".








A haka taro ya tashi, Maleek kuwa zuciyar shi kamar zata fashe, idan ya tuna yadda tace bata son shi, tunawa da tare zasu tafi yasa yayi murmushi yace"zamu hadu ne a kaduna yarinya".








.








🌼🌼🌼🌼🌼🌼
🌼🌼🌼🌼🌼🌼
🌼🌼🌼🌼🌼🌼
* One love ce! *🌼
🌼
🌸










💮💮💮💮💮💮💮💮
*ASHE KECE???*💮💮💮💮
(Hypocrite-love-sacrifice)






https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


✍✍✍✍✍✍✍
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION~*
✍✍✍✍✍✍✍




*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*




*written*
-by-
*Deeja one love*








*🏆JAKADIYAR GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION*🏆






*Dedicated*


-to-
*Maryam khamis*






*deeja one love hausa novels thanks for your support ga naku nan na sadukar muku dashi*.








*Anty fatee kuma ina godiya sosai, comments din ku na kara mini shauki kuma ina jin dadi sosai*.


69-70








suna shiga cikin daki,Hafsat ta kalli Ikhlas tace"Dama wai Saifullahi shine zuman ki? ",Murmushi Ikhlas tayi.








Suna shirya kaya Ikhlas tace"Ki ga wai shekara wajen nawa rabo na da mahaifiya ta amma wai ba za'a bari na zauna wajen ta ba".










Iman tace"Hakan fa cikin gata ne, Kada ki manta shekara nawa kina da burin zuwa dangin ki, Yau Allah ya cika miki ba sai kiyi murna ba, Ni ba gani ba ban san wacece mahaifiya ta ba ban san waye mahaifi na ba ballantana dangin su,Kuma ina rayuwa cikin farin ciki, Kin san saboda me? ".










Ikhlas ta girgiza kai, Iman tayi murmushi tace"saboda ina godewa Allah a duk yadda na sami kai na".








Sosai maganar ta ta yiwa umma dadi wacce tazo shigowa dakin,Haka suma su feenert.










Umma tayi sallama ta shigo,Kasa suka yi da kai bayan sun amsa mata,Hannun Ikhlas ta rik'e ta zaunar da ita.














"Haba Ikhlas babu abinda yafi dangi dad'i, Ban fahimci hakan ba sai yanzu, A lokacin da 'yan uwan mahaifin ki suka sako ni a gaba, Haka dan uwa na ya yarda d'an shi ya aure ki ba tare da sanin ina kike ba,Wallahi Ikhlas bakida gatan da ya wuce nan".










Muryar Ikhlas na rawa ta amsa da"Hakane Umma tabbas 'yan uwa suna da matukar girma, To amma Umma bana son Maleek tun ba yanzu ba,Shima haka baya sona".










"Kada ki damu da wannan idan har kika je kika zauna a kusa dashi zaki so shi haka shima zai so ki, kinji", Daga kai kawai tayi ba dan ta yarda ba.










Karfe biyu dai-dai jirgin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login