Showing 6001 words to 9000 words out of 71023 words
kwantar Mata da hankali.
Washe gari tunda ikhlas tayi sallah bata koma barci ba,shara tayi sannan ta hada kwanuka ta wanke,tana gamawa ta dora ruwan wanka,sannan ta wanke bayi,sai da ta juye tayi wanka sannan ta tashi iman.
Mitsitstsike idanu ta fara,harara ikhlas ta galla Mata tace"dalla ni ki tashi nace",mikewa tayi tace"mutum na barci kina wani tashin shi",gidan tabi da kallo,ko'ina tsaf da shi,juyowa tayi ta kalli ikhlas ta kwashe da dariya.
Kaya kala daya suka saka,doguwar riga baka iman tayi rolling Dan kwalin abayar,itakam ikhlas dama kwalliya ba damun ta tayi ba Dan haka daurawa tayi daurin hauwa waraka.
Gwaggo na tashi ikhlas tace"gwaggo ruwan ki na kan wuta,Washe baki tayi tace"iyye! Yan matana an fara girma",kallon tsakar gidan take tana murmushi.
Sallama sadik yayi ya shigo,sai da ya gaishe da gwaggo kafin yace"sannu da aiki gwaggo aiki da safe haka",dariya tayi tace"yau bani nayi ba mutanen ka suka yi",da mamaki yace"kina nufin ikhy da iman?",daga mishi kai Kara gwaggo tayi ta dauki bokiti domin shiga wanka.
Murmushi yayi sannan yayi sallama ya shiga dakin,ikhlas ta dago ta kalle shi sannan ta maida kan ta tana cigaba da jera kayan ta cikin akwati,kusa da ita yazo ya tsuguna yace"ikhy babu gaisuwa",bata dago kai ba balle yasa ran zata mishi magana.
Iman tace"yaya ina kwana?",hankalin shi na kan iman yace"lafiya lau",ganin bazata kula shi bane yasa ya rike doguwar rigar hannun ta,sakin mishi tayi ta mike,kallon iman tayi tace"zo muje wajen umma.
Duka mayafai suka dauka,cikin sauri yace"Ku koma Ku saka hijab nace",iman da sauri ta ajiye ta koma ta dauki hijab,ita kuwa ikhlas kokarin fita take yi,janyo mayafin yayi yace"koma kafin na mare ki",harara ta galla mishi tace"wai dole ne?",daure fuska yayi yace"koma nace,kafin nayi miki dukan tsiya anan wajen",ganin babu wasa a fuskar shi yasa ta juya ta zauna.
Iman tace"kin fasa zuwa ne?",banza tayi da ita,sadik yace"kinji kanwata rabu da ita wuce muje kinji,jan hannun iman yayi suka fice,ikhlas na ganin sun fita ta fashe da kuka.
Ranar Monday ana saura sati daya su sadik su koma makaranta suka shirya domin tafiya makaranta,fuskar ikhlas a hade haka ta shiga mota,Abba da Abba kabiru duka sai da suka yi musu fada sosai.
A riga chikum dake garin kaduna suka tsaya,daga kai nayi na kalli makarantar*NIGERIAN TURKISH INTERNATIONAL COLLEGE (NTIC)*.
sai da suka gama yi musu duk wani clearance sannan suka tafi,kuka ikhlas ta saka,wata data ke age mate din su ita tazo ta rike Mata hannu tana lallashin ta,ganin taki yin shiru yasa ta kaita wajen abler(sister)safeena,sai da ta lallashe ta sannan tayi shiru.
Yau satin su biyu a makarantar amma ikhlas bata saki ba gaba daya ta koma shiru-shiru,ita kuwa iman daya ke tana da saurin sabo har ta wartsake.
Kawar su kwara daya ce khadija muhammad kabir(kmk) itama iman tafi kula ta.
💮💮💮💮💮💮💮💮
*ASHE KECE???*💮💮💮💮
(Hypocrite-love-sacrifice)
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATON~💫💫💫*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~❄we beare's of soon golden we writer's assiduously percieven No pain so magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Out worlds for it cause u np pain~*
*written
-by-
*Deeja one love*
*dedicated to
Maryam khamis*
009-010
Sannu-sannu yanzu su ikhlas an shiga jss 3,rashin ji dai to sai abinda ya karu domin makaranta ce da babu tsawa balle duka.
Ikhlas na kwance,kmk da iman suka shigo room din kallon ta suka yi,ita kadai ce domin sauran yan dakin duka suna tafi evening prep,iman ta zauna a kusa da ita tace"ikhlas ki taso mu tafi kin San yanzu abla sa'a zata rufe hostel ko",tsaki ta ja sannan ta mike,cikin jin haushi ta kwashi books din ta tayi waje.
A class din ma shirmen ta ta dinga yi karshe dai haka aka tashi bata karanta abin arziki ba.
Suna tafe domin zuwa mosque suyi sallah,iman tace"ikhlas kinga ya kamata ace yanzu mu tsaya muyi karatu domin exam za muyi fa,kuma kin San dai school fees 1.7m ne ya kamata kada mu bari ayi asarar kudin fa",harara ta aika mata tace"to tunda ke kike biya daga yau kada ki kuma biya kinji,tana fadin haka tayi gaba.
Murmushi kawai iman tayi domin halin ikhlas dariya yake bata.
Yau karshen wata Dan haka duka students suna expecting yan uwan su Washe gari domin zuwa visiting,ikhlas ta kalli kmk tace"please bari nazo ki yi mini kalba domin bana so gobe umma ta zo taga kaina a tsife".
Kmk tace"naji zan miki kema ina fatan zaki yi mini ko",tabe baki tayi tace"ni ban iya ba sai dai muje room13 ba za'a rasa ba",suna gamawa suka mike suka shiga room13,students ne baja-Baja anata yi musu kitso cikin tsokana ikhlas tace"ga abler sa'a nan",da sauri kowacce ta dau Dan kwali ta hau daurawa,dariya ta kwashe dashi.
Kowa kan ta yayo cikin dariya tace"Allah ya shirya Ku wallahi ba zaku tashi kitso ba sai ana gobe visiting(kasancewar duk wanda yayi makarantar yasan haka students din ta suke😀),daya daga ciki tace"kema kamar wata gwanar kitson",murguda baki tayi tace"eh naji din",haka suka cigaba da shirmen su.
Washe gari tun da safe duka suka fito compound kowa jiran yan uwan shi yake yi 9 aka bude visiting,ikhlas da iman tun suna jira har suka gaji,lokacin lunch nayi suka nufi dinning sai da suka koshi sannan suka Tafi mosque.
Bayan sun idar da sallah kmk ta shigo tace"ga brothers din Ku can tun dazu suke jiran ku,cikin sauri duka suka fita,a compound suka same su suna zaune suna jiran su.
Kallon-kallo aka fara,tabbas sun yi girma sosai,Abba yace"ku taho mana babu gaisuwa kun tsaya kuna ta kallon mutane,cikin sauri suka gaishe su,sadik yace"dafatan kuna karatu ko",ikhlas ta sunkuyar da kai tace"Muna yi yaya sosai ma",iman ta kalle ta harara ta galla mata.
Hafeez yace"Anya kuwa beauty kina karatun nan naga Wata kalar harara da aka aika mata ne da wannan idanun naki kamar na mage",dariya iman tayi ita kuma ikhlas ta cuno baki hafeez yace"meya faru Iman?",cikin dariya tace"wallahi yaya kamar kasan ikhlas cat eyes suke ce mata".
Duka suka yi dariya,ikhlas ta harare ta tace"wallahi zasu tafi su barmu tare ne",karfe biyar aka rufe visiting,cikin farin ciki suka tafi sallar magrib daga nan kuma suka wuce dinning domin taking dinner,bayan sun gama suka taho.
Iman tace"jifa ai wallahi nayi niyar shiga da abu hostel sai na shiga (kasancewar kome aka kawo maka shopping sai dai kaci a compound domin ba'a shiga koda da complex cikin hostel),kmk tace"bayan waccen cctv camera tana kallon ki",ita dai ikhlas dariya kawai tayi.
Suna shiga daki ta ciro chocolates guda uku manya,cikin mamaki suke kallon ta,dariya kawai tayi ta wulla musu dai-dai,cikin farin ciki suka sha.
Yau su ikhlas suka gama zana jssce sun taho domin shiga hostel,abla sa'a ta Kira su,kallon su tayi tace"kuje ku dauko bags din ku kuje admin block,cikin tsananin tsoro suka dafe kirji suna hada baki wajen fadin" lafiya!",abla sa'a tace"don't worry brother dinku yazo domin ya tafi daku",a sanyaye suka juya suka tafi.
Sadik suka samu a admin block,cikin sauri ya bude boot ya saka musu jakar su,tun da suka dau hanya babu Wanda yace komai sai gaban ikhlas dake faduwa.
Kofar gidan cike yake da mutane,cikin sauri ta bude mota ta fito,gidan ta shige da gudu,umma ta kalla dake zaune tana hawaye gaban ta mutum ne shinfide an rufe shi da farin kyalle.
Jiki na rawa ta tsuguna ta bude,Abba ne kamar ka kira shi ya amsa,iman ta dafata tana fadin"ikhlas Abba ne fa yake kwance kice ya tashi,kowa na wajen tausaya mata yake yi.
Ikhlas kuwa kamar mutum-mutumi ta zama a wajen ita bata rufe shi ba ita bata bude duka ba,sadik da hafeez suka karaso wajen domin daukan shi.
Tashin hankali fa domin babu yadda ba'a yi ta saki ba abu ya gagara,da kyar sadik ya kwace likafanin daga hamnun ta.
Jan numfashi tayi sannan ta fadi a sume,abba kabiru ya shigo yace"hafeez ku dauko shi mu tafi ita kuma a zuba mata ruwa".
Iman cikin sauri ta debo ruwa ta zuba mata,amma shiru ita kam umma ta kasa mikewa ma daga wajen,iman ta fashe da kuka tana fadin"sis ki tashi Dan allah,sai a lokacin umma ta yunkura ta mike,daukar ta akayi aka kaita gidan gwaggo har loakcin bata farka ba.
Suna dawowa daga kai shi sadik yace da umma"ina ikhlas din take",murya a dashe tace"tana gidan gwaggo",bece komai ba ya juya ya tafi can.
Har lokacin bata farka ba,iman kuwa na gefe tana aikin kuka,ruwa ya debo a randa yasa towel yana goge mata fuska,bude idanu take a hankali har ta bude su tas,a hankali komai ya fara dawo mata,kuka ta fashe dashi tana fadin"Abba me yasa ka tafi ka barni",da sauri sadik ya rufe mata baki.
Cikin lallashi ya fara fadin "haba ikhlas kamar ba musulma ba baki yarda da kaddara bane,ko kin manta kowa sai ya mutu ne,ki daina fadan haka addu'a ya kamata ki rinka mishi ba wai kuka ba,dan ta hakan ne zai gane cewa ya bar 'ya ta gari da take mishi addu'a",haka dai ya cigaba da mata nasiha har tayi shiru.
Yau akayi bakwai gida ya koma babu kowa domin babu wasu yan uwa daman duk abokan arziki ne,umma fa mutuwa ta dawo mata sabuwa domin ita daya yanzu take kwana.
Ikhlas kuwa ta koma miskila ta kin karawa domin idan bata so ba sai ta wuni a daki bata cewa komai,sai idan ta ishi gwaggo ne take tura su gidan Abba kabiru domin su Dan yi wasa,aikuwa babu laifi domin takan sami saukin damuwar.
Gobe zasu koma hutu dan haka iman keta shirya kayan ta,kallon ikhlas tayi tace"wai ke ba zaki shirya bane?",ko kallon ta bata yi ba,iman ta fita ta gaya wa gwaggo,haka gwaggo tazo ta gama fadan ta amma ko kallo bata isheta.
Kallon iman tayi tace"kije ki gayawa umman ku,koda tazo itama bata tashin ba,iman ta dauki wayar gwaggo ta Kira sadik tace"yaya sadik ikhlas fa taki shiryawa mu koma makaranta",sadik yace"bata wayar".
Cikin sauri ta mika mata ways,sadik yace"meye haka ikhlas zaki zauna babu ilimi ne ko kuwa baki so ki cikawa Abba burin shi na kiyi karatu?",hawaye ta share tace"yaya bana son boarding school fa",jim yayi kafin yace"ok to kiyi hakuri ki karasa kinga Abba kabiru ya riga da ya biya muku kudin dis year ko kina so ayi asara ne?",girgiza kai tayi.
Murmushi yayi yace"kin san me?,Abba har yazo mutuwa fada mini yake da ya bani amanar ki,na baki ilimi sannan na aurar dake,baki so na cikawa Abba alkawarin Dana daukar mishi ne?",shiru tayi murmushi ya kumayi yace"ki dage ki gama koda secondry ne sai nayi miki auren ko Dan naga kin fara girma",da sauri ta kashe wayar tana dariya.
Da mamaki iman take kallon ta,Dan rabon da tayi dariya kalar wannan har ta manta.
Bangaren sadik ma hakane yana jin ta kashe wayar yayi dariya yana fadin"rigimammiya kawai",hafeez dake zaune yana jin wayar tasu yace" kace tun yanzu na fara ce maka yaya kenan?"da sauri ya kalle shi yace"kamar ya fa?",hafeez yayi dariya yace"ina nufin ina so ka bani auren ta mana nan gaba".
Hade rai sadik yayi yace"gaskiya bazan iya baka abin da nake so ba tun tana karama nake son ta fa sai kawai na dauka na baka?",murmushi hafeez yayi yace"kayi hakuri dai ka bani kawai",sadik yace"bafa zai yiwu ba haka kawai",hafeez zai yi magana sadik ya dakatar dashi yace"nace bazan baka ba dole ne",tabe baki hafeez yayi yace"babu dole amma ka bani iman ko",daga kafada yayi yace"kaje ka nemi soyayyar ta dai".
A sake ta hau shirya kayan ta komai sai da ta saka kowa yayi mamaki daya ga ta saki ran ta,Washe gari suka dauki hanyar *gamji garin yan boko*.
Duka students din sai da suka mata gaisuwa,haka karatu ya cigaba da tafiyar musu,yanzu kam basu saka ran mai zuwa yi musu visiting domin dai su yaya sadik suna makaranta.
A yau suka gama qualified exam,cikin tsananin murna take domin zata koma gida taga umman ta.
Jaka ce goye a bayan ta kamar pink ita kuma iman purple,sanye suke da uniform ash riga da white long sleeve din hannu sai skirt iya gwiwa check ruwan light pink da white da ash,farin hijab Dan karami irin me tsayawa a kafada,janye suke da trolley din su.
Sun Kara zama yan mata kyawawa da su suna tafe suna fira har suka fito bakin get,islam kanwar hafeez tazo daukar su.
A gajiye suka isa bauchi kasancawar doguwar tafiya suka dauko,cikin sauri ta shige gida,umma dake tsaye tana shanya ta rungume tana murna,iman dake bakin kofa tayi murmushi ta shigo,sai da suka gaida umma sannan suka wuce gidan gwaggo.
Suna shiga ikhlas ta rungume gwaggo tana fadin"I missed you my gwaggo",buge ta tayi tana fadin"sake ni Ja'ira",sakin ta tayi tana cuno baki.
Washe gari da wuri suka tashi suka yi aikin da zasu yi,suna karyawa suka shirya suka ce da gwaggo sun tafi gidan Abba kabiru.
A kasa suka tafi kasancewar babu wani nisa sosai,suna tafe duk inda suka gifta sai an kalle su,doguwar riga ce a jikin su ta atamfa me six pieces,ta zauna a jikin su das gyale duka suka yafa suna tafe suna fira.
Suna shiga gidan suka hada ido da sadik,cikin mamaki da haushi yake kallon su,da sauri ya karaso kusa dasu yace"Dan baku da hankali sai ku fito a haka kuna tafe kuna karairaya sai kace yan talla".
Cuno baki ikhlas tayi tace"haba yaya sadik a haka shine muke karairaya",daure fuska yayi yace"ina wasa dake ne ko?",cuno baki tayi,Daka musu tsawa yayi yace"kun wuce kun bani waje ko sai na fasa bakin ku",da sauri suka shige cikin gidan.
Islam na zaune tana chatting suka shigo da gudu,cikin sauri ta mike ta haye saman bed tana ihu,tsayawa kallon ta suka yi kafin ikhlas ta ja tsaki tace"banza ko mu da aka dakawa tsawar ta fimu rudewa",dariya suka yi duka.
Sai da yamma sannan su yaya sadik suka dawo,tun a waje ya fara jiyo hayaniyar su,cikin sauri ya karaso,yana yin sallama sukayi shiru,harara ya galla musu sannan yace"ku tashi mu tafi gida",jiki na bari suka mike.
Hafeez na parking lot din suka fito,tun data taho ya zuba mata idanu be San sun karaso ba sai da yaji iman na cewa"ina wuni yaya hafeez",ajiyar zuciya yayi yace"lafiya lau,ikhlas ya karatu",murmushi tayi tace"lafiya lau",har ya bude baki zai kuma magana sai ya fasa.
Iman ta bude gaba,tsayawa kawai ikhlas tayi,sadik yace"baza ki shigo mu tafi ba",ikhlas ta tabe fuska tace"yaya ni gaba nake so",kallon iman yayi yace"koma baya iman",hade rai tayi sannan ta fita ta koma baya,ita kuma ta shiga gaba ta zauna,sadik yayi murmushi sannan ya ja motar suka tafi.
Lokaci zuwa lokaci yakan waiga ya kalle ta,itakam kallon hanya kawai take,abinda yasa take son zaman gaba kenan,yana yin parking ta bude motar ta fito.
Sadik ya kira sunan ta"ikhlas",tsayawa tayi yayin da iman ta shige cikin gida kawai.
A hankali yace"ikhlas dama akan maganar auren ki ne idan har kina da wanda kike so ki gaya mini idan yaso sai na gaya wa abba kabeeru da kin gama secondry sai na aurar dake",cikin sauri ta rufe fuskar ta tana dariya,shima dariyar yayi yace"jeki nidai kawai ki tabbatar da baki boye mini komai ba".
Bata ce komai ba ta juya ta tafi,sai da yaga shigar ta gidan sannan yayi ajiyar zuciya ya juya ya tafi.
A dakin gwaggo ta sami iman a kwance,kusa da ita ta zauna tace"iman ya dai da kwanciya kuma",shiru tayi taki cewa komai,tabe baki ikhlas tayi ta mike ta cire kayan ta ta shiga wanka.
Tana shiga iman ta bude ido taja tsaki tana fadin"aikin banza kawai",ikhlas dake bayi tayi murmushi ta cigaba da wankan ta.
Koda ta fito iman dai na kwance bata tashi ba,ikhlas ta dauko wata riga light brown da wando milk,rigar iya gwaiwa sai wandon dogo,bata yi kwalliya a fuska ba,powder kawai ta shafa sai lip gloss data saka,turaren happiness time da ice and hot ta feshe jikin ta dashi.
Iman dake kallon ta taja tsaki kasa-kasa tace"mutum kamar aljani sai iyayi",sarai ikhlas ta ji ta amma tayi kamar bata ji ba,gyalen kayan ta yafa ta fita.
Gidan umma ta shiga,a zaune ta sami umman tana karatun al'qur'ani,murmushi tayi domin tasan tayi sa'ar mahaifiya mai ibada da tawakkali,zama tayi sannan ta gaishe ta,amsawa tayi cikin farin ciki,nasiha tayi mata sosai da sosai,kafin ta fara Jan ta da fira.
Sai wajen Tara sannan ta baro gidan,a kofar gida ta tarar da yaya sadik,a kofar gida,murmushi yayi mata yace"daga ina da daddaren nan ko tadi kika je?",rufe baki tayi tace"haha yaya shi saurayin ba zai zo kofar gidan mu ba sai dai ni naje?",d'aga kafad'a yayi yace"na sani abu a duhu",baki ta cuno tace"kai yaya ka dena tsonata mana".
Sadik yayi murmushi yace"komai kika yi yana miki kyau ikhlas,mijin ki beda case",yi tayi kamar bata ji me yace ba,hannun ta ya rike yace"kina jina",daga kai tayi murmushi yayi yace"ki maida hankalin ki akan karatu ikhlas domin cikawa Abba burin shi sannan kada ki dinga wasa",daga kai Kawai tayi.
Fira ya dinga Jan ta dashi har wajen sha daya,ita ta fara lura da lokacin,zaro idanu tayi tace"yaya lokaci fa",shima zaro idanun yayi yace"lah!kinga kin tare ni kin hanani barci da wuri ko?",Dariya abin ya bata ma.
Mikewa tayi ta wajen ta da sauri,duka sunyi barci hakan yasa tana shiga ta cire kayan ta ta fada wanka,shaf-shaf tayi ta fito,rigar barci iya gwaiwa ta saka sannan ta shafe jikin ta da humra me kamshi sosai.
Iman ta ja tsaki,ikhlas kam yi tayi kamar bata San tayi ba,addu'a tayi ta shafe jikin ta sannan ta kwanta.
💮💮💮💮💮💮💮💮
*ASHE KECE???*💮💮💮💮
(Hypocrite-love-sacrifice)
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATON~💫💫💫*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~❄we beare's of soon golden we writer's assiduously percieven No pain so magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Out worlds for it cause u np pain~*
*written
-by-
*Deeja one love*
*dedicated to
Maryam khamis*
011-012
koda safe da suka tashi babu wanda ya kula wani,ikhlas ita ta share gida tayi wanke-wanke,ita kuma iman ta wanke bayi da gyaran daki.
Sai da suka yi wanka sannan gwaggo tace"kuje wajen umma ku Dora abin kari",amsawa kawai sukayi sannan suka tafi
Ko acan ma babu wanda yayi wa Dan uwan shi magana,ana haka sadik yayi sallama ya shigo,kallon juna suka yi Sannan suka sakarwa juna murmushi,iman ta