Showing 51001 words to 54000 words out of 71023 words
-by-
*Deeja one love*
*🏆JAKADIYAR GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION*🏆
*Dedicated*
-to-
*Maryam khamis*
55-56
Kan shi tsaye ya tura kofar ya shiga,abba kabeeru da yake hada takardu ya kalle shi yace"ka iso kenan? ".
"Eh na dawo, abba ina zuwa haka naga sai sauri kake yi ne? ".
"Eh akwai wanda zamu hadu dashi ne yanzu, amma bazan dade ba zan dawo", jinjina kai hafeez yayi sannan ya nemi kujera ya zauna yana fadin "to Allah ya kiyaye hanya".
Yana amsawa da ameen yana fita,hafeez na ganin ya fice yayi sauri ya mike,takardar da islam ta bashi ya dauko, zanen office din mahaifin shi ne, sai inda aka yi arrow.
Dai dai wajen ya duba, ganin karamin frame yasa ya matsa kusa ya danna, kamar da wasa kofa ta fito, ganin akwai code yasa ya tuna *19051886* yana danna wa kofar ta bude.
Falo hadadde yaci karo dashi,da sauri ya kalli cikin wajen, can bayan kujera ya hango ta da alamu ma abba kabeeru ya mata duka domin yadda jikin ta yayi shatin bulala.
Ga hannuwan ta da kafafun ta a daure, da sauri ya karasa kusa da ita ya kwance ta,sannan yace"am sorry dear wallahi ban san kina nan ba da tuni na fitar da ke".
Cike da wahala tace"babu komai ai",hannun ta ya rike sannan yace"muje,jikin curtain ta ga ya ja wani zare,glass din wajen ya bude.
Wata hanya ce yar karama ya ja ta suka bi, tafiya mai dan tsayi suka yi kafin suka iso wata karamar lifter, bude mata yayi ta shiga sannan shima ya shiga.
Suna sauka ya bude kofar wajen sai gasu a waje ta bayan company din, jinjina kai beelert tayi tana mamakin irin wannan wato dai alamun rashin gaskiya kenan.
Kallon ta yayi yace"abba ya kusa dawowa kuma nasan ta wannan hanyar zasu biyo dan haka ina so kiyi sauri ki fice,idan kika mike hanyar nan zaki fita bakin titi daga nan sai ki wuce wajen ikhlas".
Kallon shi tayi tace"na gode sosai,",murmushi yayi sannan ya juya ya koma ta hanyar.
Ganin ya bace mata yasa ta juya tabi hanyar, gudu take sosai, tana daf da fita bakin titi wata mota tasha gaban ta.
Jikin ta har rawa yake yi,glass din motar tinted ne dan haka bata ganin na ciki,bude baya aka yi aka sa hannu aka jata ciki sannan motar ta bar wajen da gudun tsiya.
Bangaren maleek kuwa duk wani abu daya kamata ace yayi ya aikata, bangaren gayyata da duk wani events da za'ayi idan an kawo amarya, sannan ya juya ya koma adamawa.
Bangaren amarya hafsat ma yau suka wuce adamawar domin dai aure ya kusa ya kankama,duk wani abu daya kama ta ayi to sai da tayi shi kan ta tafi adamawar.
Tun da taje take faman kiran su ikhlas, amma kodayaushe ce mata suke suna nan zuwa,yau ma tana zaune a falo ta kira ta.
"Dan allah ku taho haka mana, haba cat eyes so kike nayi ta zaman jiran ku ne",.
"Wallahi hafsat bawai naki zuwa bane,beelert muke ta jira har yanzu bata dawo ba, kuma hafeez ya riga da ya fito da ita".
"To ni dai dan allah da kun gama ku taho",insha Allah zaki ganmu as early as possible".
Umma tayi murmushi tace"amarya sai faman kira kike a waya, da alamu suna da mahimmanci ne? ".
"Wallahi hakane umma suna da mahimmanci sosai da sosai, amma nasan zasu zo ne, tun da har sun amsa".
Mikewa tayi tace"umma bari naje bangaren daneji na dawo", daga haka ta fice.
Maleek da saifullahi dake zaune saman mota suka hango ta,tun daga nesa saifullahi ya zuba mata idanu.
"Lallai hafsat ta girma sosai, ji yadda ta zama",maleek ya dube ta yace"lovely gwara kai kasan wacece matar ka nifa an barni sai bulayi nake yi".
Dai dai lokacin ta karaso kusa dasu, tace"sannun ku da hutawa", murmushi saifullahi yayi yace"yauwa sannu da fitowa,ke baki zumanci ko? ".
"Wallahi ba haka bane, kasan ayyuka sun yi yawa, kuma nima dai na dade banga kazo gidan mu ba".
"Oh tunda bama zuwa kema ba zaki zo ba kenan? ",maleek ya bata amsa.
"Haba lily ya zaka ce haka, ai ba ina nufin hakan bane",ta fada tana dariya.
"To yanzu dai ina auntyn tamu zata je",kallon hanyar tayi tace"bangaren daneji".
"Lovely taso mu kai ta dan mu baza mu yarda ki tafi ke daya ba", saifullahi ya mike.
Suna tafe suna fira, hakan ba karamin dadi yayiwa iyayen ba, kasancewar sukan wuce su, daidai balcony hajiya rabi ce ke tsaye gefen ta sadiya da bintu.
Da idanu suka bisu kafin hajiya rabi taja tsaki tace"wannan karuwan ci har ina daga zuwa an kama mannewa juna, waya sani ko tuni dama ana lekawa".
Babu wanda ya tanka mata, suka wuce hafsat tace"ni kuwa lily naji ance an baka mata".
Dariya suka yi gaba daya kafin yace"haka nima naji ana cewa",firar su suka cigaba hankali kwance.
Zaune ikhlas take gefen ta asp abdallah ne tare da feenerh,hafeez da kuma islam suma suna zaune a wajen, sallama brr bashir yayi musu sannan ya zauna.
Bayan sun gaisa yace"jiya kamar yadda na gaya muku,alhaji kabeeru yazo kuma nayi signing akan takardun hannun shi".
"Kada ka damu, ba original bane wa'innan, yanzu dai gaya mini abinda kake so ka gaya mini".
"Da farko dai,lokacin da alhaji sadik adam zai rasu ko ince za'a kashe shi,a daren yazo ya same ni,yake gaya mini yana ganin ana bibiyar shi may be kashe shi ake son yi dan haka ga amanar yara na nan ya bani, in inganta rayuwar su".
Ina kuka na amshi wannan amanar, a lokacin da na fahimci alhaji kabeeru ke son kashe alhaji sadik abin ya bani mamaki.
Ranar da yaje wajen alhaji sadik domin ya kashe shi a ranar ina wajen, domin nakan bi takun alhaji kabeeru".
Miko wata recorder karama yayi yace"duk abinda ya faru na wannan kisan yana cikin nan".
Bayan ya kashe shi,ya haye kan kujerar shi tun lokacin yaso kashe sadik da iman amma na bashi shawara kan ya bar su har su girma domin sai da signing dina dana su sannan dukiyar zata dawo wajen shi.
Ni kuma na bashi shawarar ya cigaba da basu ilimi domin hakan zai sa baza'a zargi komai ba.
Bayan sadik ya girma na koma na bashi labarin duk abinda ya faru,sannan na kirkiri tafiya course.
Lokacin da ya shirya kashe sadik duk na sani, hakan yasa na tura yaro na domin ya cece shi wanda yaron nawa shi ya dauke shi ya gudu dashi sannan ya kona motar a matsayin kamawa da wuta motar tayi.
Mikewa tsaye ikhlas tayi tana nuna shi tana fadin "karya kake wannan maganar taka ba gaskiya bace taya zaka ce mini yaya sadik yana raye na yarda".
Asp abdallah ya dafa ta yace"calm down mana ikhlas ki kwantar da hankalin ki, ki bari mu gama jin labarin abinda ya faru".
"Bayan ya kai shi can garin da nace ya kai shi sai ya dawo ya cigaba da sa mini idanu akan alhaji kabeeru".
"Wanda lokacin da ya shirya zai kashe su gwaggo duka sai da yayi shawara dani, a lokacin da ya sawa gidan wuta yaro na yana ciki hakan yasa duk ya dauki abinda ya faru sannan kuma ya fitar dasu daga gidan".
Ikhlas ta bude baki zata yi magana,asp abdallah ya hana ta,barr bashir ya cigaba da cewa"bayan ya fitar dasu ne shine nace mishi yaje ya hada su da sadik ya dinga kula dasu har na dawo".
"Yanzu haka maganar da nake yi suna nan tare a waje na kuma beelert da aka dauke ta jiya ni na tura, domin a lokacin hanyar da ta biyo daf da alhaji kabeeru ya gan ta ne".
Islam ta mike tace"wannan maganar karya ce kace wai iman da gwaggo suna da rai".
Murmushi yayi yace"ku biyo ni muje ku gan su",daga haka suka mike, asp abdallah ne yace"ya ka mata a biya a dauki baby", ita dai ikhlas ta zama speechless".
Sai da suka biya suka dauke shi sannan suka wuce,tafiya suka yi mai tsayi sosai kamar zasu bar garin bauchi, sannan suka dauke hanya can wajen azare,cikin wani dan karamin gari.
Yar siririyar hanya suka bi kafin su isa wani gida, flat ne me kyau amma ba complete gini bane.
Sai da brr ya fita ya bude get sannan suka shiga, daga waje kam gidan bashi da kyau amma daga ciki hadadden gida ne sosai.
Jiki a sanyaye suka sauko,cikin falon yayi musu jagora,da sallama a bakin su suka shiga,tana tsaye ta juya baya tana goge dinnig table ta amsa musu.
Ikhlas ta matsa kusa da ita a hankali tace"tabbas wannan bayan iman ne,na yarda iman dita tana raye".
Da sauri ta juyo suna fuskantar juna, hawaye yana zuba daga idanun su, kuri suka yiwa juna.
Cikin kuka ikhlas tace......................
💮💮💮💮💮💮💮💮
*ASHE KECE???*💮💮💮💮
(Hypocrite-love-sacrifice)
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
✍✍✍✍✍✍✍
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION~*
✍✍✍✍✍✍✍
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
*written*
-by-
*Deeja one love*
*🏆JAKADIYAR GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION*🏆
*Dedicated*
-to-
*Maryam khamis*
Afuwan readers nayi mistake wajen saka sunan mahaifin sadik alhaji mustapha ibrahim azare zan saka dafatan zaku gafarce ni, na gode😘.
57-58
Ikhlas cikin kuka tace"iman daman kina raye amma kika barni nake wahala, a rayuwa, iman ina alkawarin da kika yi mini?".
Ikhlas ta fada tana girgiza iman din tana kuka mai ban tausayi,kofa aka bude waye zai fito, gwaggo ce tsayawa tayi cak, tana kallon ikhlas.
Ikhlas taja numfashi tace"kun kyautawa rayuwa ta, juyawa tayi dubi asp abdallah tace"abdallah mu tafi kawai, a yau na tabbatar uwa ce kawai zata iya kula da yar da ta haifa".
Iman ta karaso da sauri cikin kuka ta rungume ta tana fadin"yar uwa ki yafe mini, nayi miki ba dai dai ba, na zauna cikin farin ciki yayin da ke kina can kina wahala".
Gwaggo itama da hawaye yake zuba daga idanun ta tace"ikhlas kiyi hak'uri, rayuwa takan canza ba yarda ka so ba, duk laifin kabeeru ne".
Hannun ta iman ta rike ta zaunar,sannan ita ma ta zauna tace"brr bashir shine mutumin da ya hana mu fitowa domin gudun kada abba kabeeru ya gane muna da rai".
Ikhlas tayi murmushi hawaye ya kuma zubo mata tace"hakane kuma,gaskiya na godewa Allah da na hadu daku cikin koshin lafiya, ina ma wa'inda ke mini gorin yan uwa zasu ganni da sun ji kunya".
Sabuwar gaisuwa aka sake, sannan ikhlas ta yiwa brr bashir godiya,murmushi yayi yace"kada ki damu ikhlas wannan alkawarin da na yiwa alhaji mustapha ibrahim azare".
Ikhlas tayi dariya tace"wai ina yaya na ne ban ganshi ba? ", iman tayi dariya tace"ya shiga kasuwa anjima nan zai dawo.
Beelert ta shigo dakin hannun ta rike da baby mai kyau,da mamaki ta tsaya tana kallon su ikhlas.
Hararar ta feenert tayi tace"dallah malama ki karaso muna can muna neman ki, ke kina nan kina hutawar ki".
"Wannan baby fa, kyakkyawa haka? ",ikhlas ta fada yayin da take amsar yarinyar.
"Yarinyar dana haifa kenan, sunan ta ikhlas, yayan ta yana makaranta".
Sai lokacin ikhlas ta kalli baby tace"baby ga fa mummyn ka?",kallon iman yayi ya kauda kai yace"baby ke kadai na sani a mahaifiya ta".
Duka suka yi murmushi, ikhlas ta matsa ta rike hannun shi tace"baby wannan fa itace mum iman", ya mutsa fuska yayi yace"na sani fa baby".
Tashi yayi ya matsa kusa da ita yace"ba ke bace kike yawan saka mummy na kuka ba, da kema", ya fada yana nuna gwaggo.
Gwaggo tayi dariya tace"ikon Allah kai kuma haka kake dama? ".
Iman ta rike hannun shi tana jin soyayyar yaron har cikin ran ta tace"baby dama wasa mummyn ka take maka, itace maman ka".
Fincike hannun shi yayi, ya koma kusa da feenert ya cigaba da danna tab din shi wanda dama abinda yake yi kenan.
Fira sosai suke yi,wanda baka jin komai sai dariya, ikhlas kam ji take yi yau iskar da take shaka ma daban take, domin kuwa gata ga wa'inda ta cire rai da sake ganin su a rayuwar ta.
Tana kwance jikin gwaggo ta kira hafsat,ita kuwa hafsat a lokacin tana tare da angon ta saifullahi gefen shi kuma lily ne.
Wayar ta dauko ta amsa, cikin sauri tayi sallama itama ikhlas ta amsa mata.
"Wai dan Allah yaushe zaku taho ne? ",hafsat ta fada cike da damuwa.
"Sai jibi idan Allah ya kaimu, yanzu ma na kira nayi miki albaishir ne, ashe gwaggo da iman da yaya sadik basu mutu ba".
Cikin murna hafsat tace"dan Allah da gaske kike kuwa?",ikhlas tace"wallahi da gaske nake, may be ma mu taho tare dasu".
"Kai amma dana ji dadi wallahi, kai sis na taya ki murna saura umma kuma".
"Itama insha Allah tana kan hanya, ina jin hakan a jiki na zan gan ta nan bada dadewa ba".
Fira suka yi sosai da sosai sannan suka rabu.
Bangaren abba kabeeru kuwa bayan yaje wajen brr bashir yayi mishi signing yana fitowa ya kira hazard a waya ya gaya mishi number din dakin akan da dare suzo su kashe shi.
Sai dai sun makaro domin abba kabeeru na fita shima ya fice.
Koda ya koma office be ga hafeez ba hakan be dame shi ba,gida kawai ya shirya ya koma.
Washe gari da safe hafeez da islam suka shigo falon, kallon su yayi da murmushi, cike da dauriya kada ya gane komai hafeez ya mai da mishi.
Bayan ya fita office ne islam tayi tsaki tace"wallahi idan da wani ya gaya mini abba zai aikata hakan zan karya ta amma yanzu na yarda wallahi".
"Ai dama haka ne, yanzu abinda ya kama ta ki shirya mu wuce wajen ikhlas din".
"Aikuwa kamar kasan wallahi garin nan gaba daya haushi yake bani".
Wanda dalilin hakan yasa suka bi su ikhlas can azare,hafeez kam tunda yaji sadik yana da rai farin ciki ya mamaye shi.
Kallon ikhlas yayi da ta gama waya yanzu ya juya ya kalli su iman da islam dake ta faman fira.
Asp abdallah ya duba da shima suke fira tare da brr yayi tsaki yace"wai dan allah me yasa baku damu da ni bane, kowa kan shi ya sani".
Iman tace"kai yaya hafeez kowa ya damu da kai mana",kallon beelert yayi yace"to yau dai naga ko my love ta canza mini ina ga kuma kowa".
Feenert ta dauko baby ta zaunar dashi kan kafar shi tace"ga wannan fake din abokin naka kafin original ya dawo".
Rungume yaron yayi yace"ke kin iya iyayi da ywa kamar wata sardauna".
Yace"ke my aboki shine fake din",feeenrt tace"eh mana ko ba hakan bane".
Suna cikin fira,aka kwankwansa kofa, da sauri ikhlas da islam da hafeez suka mike,har rige-rigen zuwa suke.
Iman na bude kofa, yayi murmushi yace"wallahi na gaji, kinga duk na kosa na dawo na gan ki".
Iman tace"to ai shikenan ina muhsin din? ",miko mata shi yayi,kallon shi tayi da murmushi a fuskar ta tace"albishirin ka".
Lumshe idanu yayi yace"wannan wane iron albishir ne da ba za'a bari na shigo gidan ba".
Matsawa gefe tayi,da mamaki yake kallon su,su kuwa kokarin su su zo gare shi, ganin yana kallon su yasa duka suka tsaya.
Ajiyar zuciya yayi yace"iman kada kiyi mini irin wannan wasan mana",iman tace"ba wasa bane miji na da gaske duk wa'inda ka gani to tabbas sune".
Runtse idanu yayi yace"ya Allah kasa ba mafarki nake ba", hafeez ya matsa kusa dashu ya mare shi irin na wasa yace"yanzu ka farka".
Bude idanu yayi da sauri, suka rungume juna suna farin ciki, islam tace"yay sadeek ashe zamu sake haduwa bayan abba ya raba mu".
Hannun ta ya rike yana murmushi yace"tabbas kuwa islam, tunda gashi ma mun hadu".
Ikhlas kuwa babu abinda take sai hawaye,hafeez ya rike hannun shi yace"yanzu insha Allah babu mai raba mu".
Kallon inda ikhlas take yaga tana faman zubar da hawaye,a hankali ya bude hannayen shi, da gudu ta karaso inda yake suka rungume juna.
Bubbuga bayan ta yayi yace"haba beauty wannan kukan fa, wanda kika yi a baya ki bar shi iya wannan dan Allah dan wannan nauyi kike kara mini, dan nasan Allah sai ya tambaye ni amanar ki dana kasa rike wa".
Kowa a wajen hawaye yake yi, da sauri ta sake shi ta matsa ta janyo baby tace"yaya ga amanar ka".
Zubawa yaron idanu yayi yana murmushi yace "lallai beauty ke ta dabance na koyi darasi a rayuwar ki,duk wahalar da kika sha baki rabu da amanar da aka baki, amma ni kuwa na gaza".
Ya karasa yana hawaye, hannun shi ikhlas ta rike tace"yaya ba haka bane, komai kaddara ne, kuma be kamata ka dinga zubar da hawaye ba".
Rungume juna suka kuma yi yace"beauty dole na fadi haka, na gaza abba na gaza rike amanar da ka bani, umma ki gafarce ni kina ganin kamar zan iya rike amanar ki amma hakan bai yiwu ba".
Share mishi hawaye tayi tace"yaya baka gaza ba, kuma ni ban taba ganin gazawar ka ba, sai dai kowanne mutum da kaddarar shi".
.
Murmushi yayi yace"haka ne beauty yanzu bari nayi wanka sai na zo muyi fira",rike hannun shi tayi tace"muje to".
Tare suka jera suka tafi, duk yan falon kallon mamaki suke, ganin ga matar shi amma sun wani kule daki tare.
Amma hafeez da islam da matar