Showing 39001 words to 42000 words out of 71023 words
yin aure dan tasan bata da iyayen da zasu d'aura mata auren.
To! Idan ma tana dasu,waye zai bar dan shi ya auri yarinyar da bata da asali, wannan bazai yiwu ba, dan ko saifullahi bata taba sawa aranta zasu yi rayuwar aure dashi ba.
Hawaye ta goge tana fadin"Abba kabeeru duk kai ka ja mini wannan".
Runtse idanu tayi wasu magan-ganu na dawo mata kai
_haba ikhlas kamar ba musulma ba baki yarda da kaddara bane,ko kin manta kowa sai ya mutu ne,ki daina fadan haka addu'a ya kamata ki rinka mishi ba wai kuka ba,dan ta hakan ne zai gane cewa ya bar 'ya ta gari da take mishi addu'a"_
_kayya meya kawo haka kuma haba ikhlas da bakin ki kike fadin haka ne,kamar baki yi karatu ba,kin manta kowa da kaddarar shi ne,kada ki manta ke musulma ce_
kuka ta fashe dashi domin tabbas tayi rashin mai mata nasiha,ganin kukan bazai yi mata bane yasa ta mike ta dauro alwala ta fara sallah.
Wanka yayi cikin sauri ya shirya, wayar shi ya dauka, cikin sauri ya danna wasu numbers, ana d'agawa yace"manager ina so ka kori ikhlas ahmad daga shoprite din ku".
Jim yayi kafin yace"amma yallab'ai kan wane dalili? ",cikin fushi yace"oh! Tambaya ta dalili kake yi?".
Cikin sauti yace"yi hak'uri yallab'ai zamu sallame tan",be ce komai ba ya kashe wayar.
Murmushin mugun ta yayi yace"zan ga kuma dame zaki dinga tak'ama dashi,filthy bitch".
A tare suka fito,maleek yace"good morning lovely",dariya yayi yace"morning lily".
A tare suka jera har suka fiyo falo, kamar kullum suna zaune suna kallon masu shiga da fice.
Saifullahi ya gaishe da hajiya shi kam maleek yace"ah! Hajiya barka da hutawa,har an fito kenan? ",harara ta galla mishi.
Cikin rawar baki bintu tace"ina kwana yaya maleek",be kalle ta ba ya bata amsa da"lafiya", sannan yace"lovely ka taso muje kada muyi late mana".
Nan fa hajiya ta dasa"wato kai ga mara mutunci, yayan ka shi da yake yasan darajar na sama dashi ya tsuguna ya gaishe ni amma kai baza ka iya gaishe dani ba, kaga maleeku ka kiyayeni".
Suna shiga falon mummy ta karaso, harara ta gallawa maleek da yake gaishe ta kafin tace"tun da na fara jiyo muryar hajiya a sama na san ka taho, wato kai baza ka dena tsokanar ta ba ko".
Kwantar da kan shi yayi a jikin mummyn yace"to ai itace mummy ta fiye sa ido wallahi, har fa tazo ta zauna a falo tana kallon masu shige da fice".
Mummy taja hannun shi ta kai shi kan dinning ta zaunar dashi,cikin sauri -sauri suka yi breakfast din sannan suka fice".
haka nan yaji kawai yana so yabi hanyar,yana isa kofar gidan motar ta na fitowa daga cikin gidan dan haka kawai ya rufa mata baya.
Sai da ta sauke baby a makaranta yana kallon ta sannan ta wuce,a bakin shoprite din tayi parking shima gefe yayi yana jiran fitowar ta.
Ikhlas kam bata ma lura dashi ba,tana shiga kamar yadda ta saba ta fara gaishe dasu, manager ya dube ta bayan ta gaishe dashi.
Yace"ikhlas ahmad nasan kina da hakuri, ki k'ara akan wanda kike dashi,ga wannan dan allah kiyi hak'uri bani da yadda zan yi ne shiyasa sak'o daga can sama kan na kore ki".
Murmushi tayi tace"kada ka damu manager, haka Allah ya ruboto mini", tana gama fadin haka ta amshi kudin sannan ta mike ta fito.
Tana fitowa kamar daga sama ta ganshi, hade rai tayi ta nufi motar ta, karasowa yayi yace"ya dai 'yan mata,an fito daga wajen maular ne ko kuwa yau maular ta kare a nan ne? ".
Da sauri ta juyo ta kalle shi, d'aga mata gira yayi yace"ma'ana an kore ki ko, kada ki damu",shafa fuskar ta yayi yace"kada ki damu ga charity".
Hannun ta ya saka mata, sannan ya matsa daidai kunnen ta yace"na san kina bukata ko dan saka wannan dan shegen da garin yawon bar........ ".
Saukar marin da yaji yasa shi kasa karasawa,idanun ta yayi ja alamar bacin rai tace"don't dare say that again,duk wulakancin da za kayi ya tsaya kaina, idan ya tsallaka kan baby bazan taba iya d'auka ba".
Hannun shi ta bude ta saka mishi kudin shi sannan tayi murmushi tace"kora ta da ka saka akayi kayi a banza wallahi, domin bazan rama wannan a kan ka ba akan yayan ka zan rama, sannan charity kai kake bukata domin siyawa yayan ka panadol".
Tana fadin haka ta bude motar ta ta shige ta bar shi a wajen kamar statue.
*kuyi hakuri da wannan masoya insha Allah zaku iya samun wani page din anjima na gode*
*anan nake cewa nida ku one love*๐
๐ฎ๐ฎ๐ฎ๐ฎ๐ฎ๐ฎ๐ฎ๐ฎ
*ASHE KECE???*๐ฎ๐ฎ๐ฎ๐ฎ
(Hypocrite-love-sacrifice)
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
โโโโโโโ
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION~*
โโโโโโโ
*~โWe beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
Wattpad @13 deeja
Or
Deeja1love.blogspot.com
*written
-by-
*Deeja one love*
*dedicated*
to
*Maryam*
Ina kike my princess *princess mazadu* ga naki page din kamar yadda nayi miki alkawari yau na cika, dan haka ga 'yar k'anwar ki tana gaishe ki.
43-44
Da karfi ya daki motar yana mai jin haushin yadda tayi mishi,ga mutane a wajen wanda kowa yasan waye shi, cike da jin haushi ya hau motar shi ya bar wajen.
Ikhlas kam tana driving tana share hawaye domin bata taba tunanin zata shiga wannan matsalar ba.
Gida ta wuce kawai, tana parking ta shiga ciki,magan-ganun da ya gaya mata shi yafi b'ata mata rai,"lallai dole ta dauki mataki".
"U re mistaken maleek, zaka yi dana sani na abinda kayi mini",wayar ta ta dauka ta kira saifullahi.
"Zuma na ya ko nema na baka yi ba", ta fad'a cike da shagwab'a, ajiyar zuciya yayi yace"haba Princess nasan zaki shirya ki tafi wajen aiki kuma yau na d'an makara ne".
"To yanzu dai ina buk'atar ganin ka, ya za'a yi? ",cikin sauri yace"duk yadda kika ce Princess ",to kazo gida yanzu".
"Baki je wajen aiki bane",eh ban je ba, pls kayi sauri kaji", an gama gani nan zuwa yanzu kuwa", katse wayar tayi ta wuce bedroom.
Maleek kuwa fasa zuwa asibitin yayi, *KADUNA STATE UNIVERSITY* ya wuce, yana bude office din suka yi karo.
Da saauri yace"yauwa lily muje ka sauke ni a wani waje",be ce komai ba ya juya hakan yasa ya bishi.
Suna tafe yana nuna mishi hanya, ganin gidan da suka yi parking yasa ya daure fuska,saifullahi yace"fito muje".
Be kalle shi ba yace"kaje dai zan jira ka anan",girgiza kai saifullahi yayi ya wuce ciki.
A zaune ya same ta tana dannan waya, d'agowa tayi ta kalle shi fuskar ta ba zaka tantance wane yanayi take ciki ba.
Iska ya hura mata a fuska da sauri ta dawo hayyacin ta suna had'a idanu suka ui murmushi.
"Princess meye matsalar ki? ",ya fad'a yana kallon fuskar ta.
"Ni fa na ajiye aiki saboda na gaji",ta fad'a tana ya mutsa fuska.
"To dama bake kika mak'ale kina so ba,amma yanzu tun da baki so ai shikenan ni mai taimaka miki ne".
"Ok, na gode, wata k'ila nima nan da ranar asabar zan koma kano".
Zaro idanu yayi yace"me kika ce, oh no! Kada kiyi mini haka mana, haba princess sai da kika saba mini da ganin ki yanzu ma zaki sake guduwa ki barni".
"Sai ka sake komawa kano dama ai har yanzu suna so ka koma, amma zuma bazan iya cigaba da zama a kaduna ba".
"Wallahi ko me zan yi daddy da mummy ba zasu bari na koma kano ba, kiyi hak'uri ki zauna dan Allah, ke dai da baby ai bazai gagare ni ba".
"Bafa saboda haka zan koma ba,ni dai ina so na tafi idan yaso daga baya kazo koda bayan satittika ne".
"Wai me ya faru ne? Kike so ki tafi, idan da zaki hak'uri ki zauna, daddy yace mu fito da mata nan da wata biyu, kin ga da sai na kai ki nayi kusu bayani kawai".
"Saifullahi aure tsakanin mu bazai fa yiwu ba, saboda babu wanda zai amshe ni a matsayin sirika".
"Me yasa kike cewa hakane haba ikhlas, ni zan musu bayani sannan idan hakane ba sai ki koma wajen abba kabiru ba da zama har lokacin da za'a d'aura mana aure".
Kallon anya kan ka d'aya ta aika mishi sannan tace"hmm, baza ka gane ba kenan, kaima fa naga tafiya za kuyi fa".
Be bata amsa ba ya mik'e ya fice, rai a bace maleek na ganin shi gaban shi ya fad'i kada dai abinda ta fad'a take aikatawa.
Idan tace ta rabu da yaya ya zan yi?koda yake ma ai gwara haka ma dai kowa ya huta.
Katse mishi tunani yayi ta hanyar cewa"ka tada motar mu tafi mana",murmushi yayi wanda baza ka tab'a tantance wane yanayi yake ba.
Ikhlas kam yana fita tayi ajiyar zuciya tace"na shiga uku ni ikhlas yanzu wa zan nuna a matsayin nawa,umma ta b'ace,iman ta mutu, gwaggo ma haka, yaya sadik duka sun tafi sun barni ga abba na dana rasa tun farko".
Hawaye ta gige tana tausayin kan ta, dole ne ma taje daukar fansa, wayar ta ta d'auka tayi kira.
"Hell, company din ku nake so ka duba ka gani am fara barin share,idan ana bari zan turo maka da details na company din wata, ina so ka san yadda zaka yi baban ka ya yarda da company din shi kuma companyn zai siyi share".
Daga haka ta katse wayar, murmushi tayi tace"abba kabeeru yanzu zaka paying what you did".
Su kam a motar babu wanda yayi magana, saifullahi ya katse shirun"mu wuce gida kawai",a tare suka fito.
Kamar yadda suka saba, yan zaman falo na nan, maleek yayi murmushi yace"barka da hutawa hajiya"bata kula shi ba sai dai harara da ta dank'ara mishi.
Sadiya tace"ina wuni yaya? ", kallon ta yayi yace"har kun dawo daga school d'in",d'aga kai tayi tana bin saifullahi wanda ya kusa wuce falon.
Bintu da jikin ta ke rawa yake kallo da alamu abinda sadiya ta fad'a ba gaskiya bane, d'aga kafad'a yayi alamar ku ta shafa sannan ya bi bayan yayan shi.
Yana shiga ya tarar da saifullahi na zaune a k'asa mummy kuma na kujera da alamu magana suke yi.
Juyawa yayi da sauri mummy tace"maleek ina zaka je? ",cuno baki yayi yace"mummy naga kamar magana kuke yi".
Dak'uwa tayi mishi tace"gidan ku, wato kai baza ka zo ayi maganar da kai ba kenan, me ya sami d'an uwan ka? ".
Tab'e baki yayi yace"ni dai nasan na raka shi waken budurwar shi daga nan kuma....... ",shiru yayi saboda tin abinda yake fad'a.
Kallon mummy yayi ganin kallon da take mishi yasa ya tab'e fuska yace"haba mummy wannan kalar kallo haka".
Murmushi tayi tace"yauwa baby na zo ka zauna", mak'e kafad'a yayi yace"wallahi mummy bazan zo ba".
Yana ganin ta mik'e yayi waje da sauri yana murmushi, juyawa tayi ta kalli saifullahi tace"wato yanzu kun saka shirme da shirirta a aikin ku ko?kai da nake ganin ka fishi hankali ashe ba haka bane".
Shi dai saifullahi hak'uri kawai yake bata, sai da ta gama yi mishi fad'a sannan tace"tashi ka fice ka bani waje", tashi yayi kawai ya fita.
D'akin maleek ya shiga, maleek na kwance ya bud'e idanu, saifullahi ya zauna yace"lily nazo muyi magana".
"Ina jin ka ai, meya faru kuma yanzu? ",ya fad'a yana gyara kwanciyar shi.
"Nazo akan maganar princess ne", da sauri maleek yace"ba princess ba karuwa dai",haba lily ya zaka dinga kiran ta da sunan daba nata ba, waya ce maka princess karuwa ce bata taba zina ba".
"Hmm, yaya kenan kada so ya rufe maka idanu, ka kasa gane abinda yake a fili,yarinyar da nasha gani a hotel da *k'dangarun bariki* zaka ce bata tab'a zina ba".
"Kai ma kada kishi ya rufe maka idanu ka kawo abinda babu shi, na yarda da ikhlas wallahi ni nasan baza ta tab'a abinda kake cewa ta aika ta ba".
"Lovely ka canza da yawa,yau akan mace kake k'arya tani, akan wata banzar karuwa muke samun sab'ani".
"Kai kaso a yi haka, yanzu dai yi hak'uri,zauna kaji me nazo dashi, princess ce ke gaya mini ta ajiye aiki zata koma kano".
"To sai me, hakan ma yafi ai, kaga zan dena ganin fuskar da nafi tsana a rayuwa ta".
"Lily ya kamata kasan me kake fad'a, ka dena aiban ta princess a gaba na".
zaro idanu yayi yace"lovely bari na bar maka dakin kada gaba ka mare ni akan karuwa".
"Lily ina maka gudun ranar da zaka yi nadamar abinda kake fad'a, sannan ka sani bana fatan ranar da zan mare ka har abada bana fata tazo".
Daga haka ya fice daga d'akin,maleek ya bishi da kallo, da mamakin wane kalar so yake yiwa wannan banzar.
Yau ikhlas ta tattara kayan ta domin komawa kano,saifullahi ya kalle ta yace"shikenan kafin mu tafi adamawa zan yi k'ok'arin zuwa".
D'aga kai tayi tana kallon maleek wanda yake jan tsaki,juyawa tayi ta shiga mota tace"na tafi sai ka zo".
"Shikenan allah ya kiyaye hanya, ya tsare hanya, dan allah kada ki manta dani",d'aga kai tayi tana fad'in "ameen".
Maleek ya shafa kan baby yace"yauwa my son maza shiga motar, ka dinga zuwa makaranta akan lokaci sannan kada ka dauki halin banza daga mutanen banza".
Murmushi ikhlas tayi domin tasan da ita yake,baby yace"daddy yaushe zaka zo? ",rik'e hannun shi yayi yace"tare da uncle zamu zo kada ka damu".
Peck yayi mishi a kumatu, shima ya mishi, ta madubi take kallon shi abinda yake hanata shuka mishi rashin mutunci kenan saboda yadda yake son baby, ita kuma duk me son baby to tana son shi.
gidan hafsa ta wuce, da murna suka tare ta, hafsat tace"Kin tafi kin dawo", dariya suka yi gaba d'aya.
Ikhlas tace"ai yanzu ma ba lallai na zauna ba, at any time zaku iya nema na ku rasa".
Feenerh tace"waya ga jirgin yawo, kamar sardauna๐ lek'e lek'e kamar b'era",dariya sukayi gaba d'aya.
Beelert tace"wai ke me yasa kika raina sardauna ne? ".
"To shine tunda yayi *matafiya uku* har yau be kuma wani ba sai dai aukin fowarding".
Ikhlas tace"ban san sharri bana ga wani ba wanda suka yi had'in gwiwa".
"Ke wannan kara sunan shi yayi amma bana shi bane, allah sarki sardaunan gauraye๐", feenerh ta fad'a tana dariya.
Ikhlas tace"ya isa haka, yanzu dai bari nayi wanka na kwanta", hafsat tayi murmushi tace"gobe zan tafi abuja daddy na nema na".
Duka suka amsa da "allah ya kaimu", daga haka firar su suka cigaba, ikhlas kuma ta wuce bedroom domin tayi wanka ta huta.
Yau satin ikhlas d'aya da komawa kano,zaune take bayan ta dawo daga d'auko baby.
Feenerh tayi sallama ta shigo, kallon ta ikhlas tayi ta fara dariya, tsayawa tayi tana duba jikin ta.
Beelert da ta fito daga d'aki ita ma tsayawa tayi tana kallon ikhlas da feenerh din, ganin tak'i dena dariyar yasa feenerh cire takalmi ta jefa mata.
Wayar ta tayi k'ara wanda hakan yasa ta dakata ta d'auki wayar.
"Assalamu alaikum, officer ya dai ka iso ne? ",banji me aka ce daga can b'ari ba sai dai ita data amsa da "to an gama,ba masa ba,to tana nan tana jiran ka".
Katse wayar tayi ta d'aga gira alamar lafiya tace"naga kun zubo mini ido ne, bafa wani bane zuma na ne yake kan hanya shi da wannan mata-mazan".
"Ah kice mu zo mu shirya, waya sani ko mata-mazan yace yana sona,beelert ta fad'a tana washe baki.
"Dama ai da bazawara ya dace,kin san sune suka cika zalama",feenerh ta fad'a tana dariya.
"Haba sai kace wata *maman mamy* zalama ai sai ita kamar zata kwace maka miji",dariya suka yi.
Beelert tace"wai na tambaye ki, naga sai fara'a kike ne? Anya kuwa? ".
"To yar sa ido, yau da farin ciki na tashi,kuma gashi kin gani", feenerh ta bata amsa.
"Ba wani dai d'azu muka yi waya da asp abdallah yace yana hanya shine dalilin farin cikin ta",ikhlas ta bada amsa.
Feenerh ta mik'e tace"bari kiga in wuce gida, dan umma tace yau kabeer zai zo d'aukar suhaila domin kai ta gidan su".
Daga haka ta fice,ita kam ikhlas mik'ewa tayi tace"bari na shirya kada zuma na yazo ya iske ni haka", Ciki ta shige ta bar beelert a zaune tana kallo.
Wanka tayi sannan ta zauna ta tsantsara kwalliya, atamfa ta saka blue da ruwan zuma sai ratsin milk colour doguwar riga fitted,tayi daurin *zahra buhari* turare ta fesa wanda ya bude dakin da k'amshi.
Mayafi mai ruwan zuma haka bracelet da fashion na d'an kunnen data saka,kafar ta blue din takalmi ne wanda yake high hill.
Tana fitowa beelert ta fara mata tafi,cikin washe baki ta fara wasa ta, juyi ikhlas tayi tace"ya dai nayi kyau ko? ".
"Ai bana jin zai gane ki yau idan ya gan ki",beelert ta bata amsa.
Wajen baby ta shiga, shima ya gama shiryawa domin yana farin ciki tun da yaji ance da daddyn shi za'a zo.
Dakakkiyar shadda ya saka blue colour,yayi kyau, "like father like son, baby akwai son gayu kamar mahaifin shi".
Kwab'e baki tayi ganin yadda yake wani feshe jiki da turare kamar wani babba, wayar ta ne yayi k'ara da sauri ta kalle shi tace"baby taho mu tafi gasu nan sun iso".
Daga haka taja hannun shi suka fice, a inda ta bar beelert ana ta dawo ta same ta,tace"yauwa bani mukullin falo d'in".
Mik'a mata tayi da sauri ta amsa.
B'angaren su saifullahi kuwa,babu abinda yake buri kalar ya hango ta, maleek kuwa dannan waya yake amma duk da haka hankalin shi yana kan hanyar.
Wani gefe na zuciyar shi yana mararin ya ganta,duk da wani gefen yana k'ok'arin danne hakan.
Hannun su s'arke dana juna suka fito, a natse suke takowa,duk yadda yaso ya daure kasawa yayi dole ya bar