Showing 3001 words to 6000 words out of 71023 words

Chapter 2 - ASHE KECE Complete By One Love .txt

One Love   

31 Jan 2025

4655

taimake su babu kowa a wajen a tsugune suke bi ta jikin ajujuwa har suka isa nasu ajin,lekawa khairat tayi ta hango malam anas a ciki,sunkuyawa tayi da sauri tace"shiga uku malam anas ne aciki",idanun iman da yake tafi kowa tsoro har ta fara hawaye,nan suka tsaya har aka tashi sannan suka biyo ayarin dalibai suka shiga daukar Jakar su.




Suna fitowa suka tarar da malam anas da malam Khalid a tsaye,sunkuyar da kai suka yi zasu wuce,da idanu suka bisu kafin malam anas ya jinjina kai yace"allah ya shirya",malam Khalid ya amsa da"ameen.






Suna isa gida suka sami yaya sadik a zaune,fuska a daure yace"Ku zo nan",iman da sauri ta karasa gaban shi,ikhlas kuwa baya ta fara ja,sannin cewa zata iya guduwa yasa da sauri ya mike ya janyo ta,hararar iman yayi yace"biyo ni",ikhlas kuwa hannun ta ya rike yana janta.






Dakin shi ya bude ya jefa ta ciki sannan ya dakawa iman tsawa yace"shiga kafin nayi kwallo Dake",cikin sauri ta shige jikin ta na bari.








Fuska daure yace"ku kama mini kunne",zaro idanu tayi tace"tab wallahi baya na ciwo yake",bakin ya buge ta tsandara ihu lips din ta ya kama ya hade ya matse da karfi,hawaye ta fara tana yarfe hannu,iman ma ta fashe da kuka tana bashi hakuri.






Kallon daya Mata ne yasa tayi saurin kame bakin ta ta tsugunna ta fara kama kunne,sakin lips din yayi yace"zaki tsuguna ko kuwa",da sauri ta tsuguna ta kama kunne,kwado yasa ta baya ya rufe kofar sannan ya fita domin yayi sallah.






Yana fita suka nemi waje suka zauna suna haki,ikhlas tace"wallahi allah ya isa kuma wallahi sai na rama.






Suna zaune suna fira,ikhlas ta mike tace "wallahi daya zo guduwa za muyi",iman tace"ta yaya?",murmushi ikhlas tayi sannan ta rada Mata a kunne.






Suna nan zaune suka ji alamun bude kofa,tashi ikhlas tayi ta matsa jikin kofar ita kuma iman ta tsaya ta dayan barin,kofar na bude iman ta zuba da gudu da wuce,kan ya ankara ikhlas ta tsugunna ta wuce ta kasa,tsayawa kawai yayi yana mamakin yaran kamar ana kada musu gangar shedan.








Su ikhlas kuwa a bakin kofa suka tsaya sai da suka huta sannan suka shiga gidan,gefe suka zauna suka rabe,iman da bata da juriyar yunwa ta marairaice tace"umma Dan allah kiyi hakur.......",kasa karasawa tayi saboda kallon da umman tayi Mata.










Ana sallar isha suka dauki buta sukayi alwala suka yi sallah,suna idarwa ikhlas tace"iman kinajin yunwa kuwa?",hararar wasa tayi Mata tace"nama fiki jin ta wallahi",murmushi ikhlas tayi tace"duk abinda nayi ki goyi bayana kinji",daga kai kawai tayi.




















💮💮💮💮💮💮💮💮
*ASHE KECE???*💮💮💮💮
(Hypocrite-love-sacrifice)






*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATON~💫💫💫*


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~❄we beare's of soon golden we writer's assiduously percieven No pain so magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Out worlds for it cause u np pain~*










*written
-by-
*Deeja one love*






*dedicated to
Maryam khamis*



005-006




Cikin sanda suka fito,ikhlas ta leka dakin umma ganin tana lazimi yasa tayi murmushi taja hannun iman suka zauna a zaure,ikhlas tana jin alamar tsayuwar mashi ta tabe fuska ta langwabar da kai,da sallama ya shigo,ganin alamun mutum yasa yace"waye nan a zaune",ikhlas harda nishi ta marairaice fuska tace"abba mune nan",Kara tayi kadan tana fadin "wayyo!Abba cikina zan mutu".




Cikin sauri ya karasa kusa da ita ya riko ta kara langwabewa tayi tana fadin Abba yunwa mu keji",da mamaki yace "bangane ba ina umman taku take?"ikhlas harda hawayen karya tace"wai Dan ta aike mu munje da layi shine muka dade shine fa ta hanamu abincin rana dana dare".








Cikin tashin hankali yace"bangane ba wane kalar horo ne da yunwa,mu shiga gidan",da sauri ikhlas tace"a'a Abba muje ka fara siyo mana wani abu muci",ledar da ya shigo da ita ya mika musu cikin sauri suka amsa tsire ne a ciki da zafin shi suka fara ci.








Anan ya tsaya har suka cinye tas hollandia ya mika musu suka bude suka shanye roba daya tas,gyatsa suka yi sannan yayi murmushi yace"mu shiga ciki".






Da sallama suka shiga,umma tace"wa'aikumus salam daman yanzu nake cewa abban ikhlas ko lafiya",Abba yace"lafiya lau wallahi",mikewa tayi ta kawo mishi abinci,kallon ta yayi yace"zauna muyi magana umman ikhlas meya sa kika hana yaran nan abinci?".






Ajiyar zuciya tayi tace"ai dama tunda na ganku tare nasan sun kulla abinda suka saba,yanzu abban ikhlas yarda kayi da yaran nan?",Abba yace"to eh mana idan ba haka ba me yasa suka je zaure suka zauna?.






Umman kasa cewa tayi komai girgiza kai kawai tayi tace"Dan allah kayi hakuri",murmushi yayi yace"komai ya wuce",dariya umma tayi tace"wuce kuje kuci abinci akwai a kitchen".










Turo baki ikhlas tayi tace"ai mun riga da mun koshi",murmushi umma tayi tace"to yayi kyau",daga haka bata kuma cewa komai ba.








Sai da suka tabbatar da gwaggo tayi barci sannan suka lallaba suka kwanta,ikhlas na can karshe yayin da iman ta makale a jikin gwaggo.










Washe gari da safe bayan sun tashi sun yi sallah,komawa suka yi suka kwanta suna sharar barci.






Karfe takwas Sadik yayi sallama ya shigo,gwaggo dake wanke-wanke ta dago ta amsa cikin sakin fuska.






Cikin fara'a yace"gwaggo ina yaran suke suka barki kina wanke-wanke da kanki?",gwaggo tace"ina zasu zo suyi aiki suna can suna barci kamar mai danye",tashi yayi cikin fushi ya nufi dakin,da kallo ya bisu,tsabar barci yayi dadi ikhlas ta yaye cinya har pant ana iya hangowa.






Cikin sauri ta kawar da kanshi,iman kuwa dankwalin ta kawai ya fita yana gefe itama tayi gefe,tsaki ya sannan ya dauko carbin gwaggo ya caulawa ikhlas a cinya.






Wani razanannen ihu tayi ta mike a guje janyo ta yayi ya Kara zuba mata a jiki,rudewa tayi ta fashe da kuka,iman kuwa da ihun ikhlas ya tashe ta tuni tayi waje da gudu.






Kuka take tana fadin"Dan allah yaya sadik kayi hakuri",kamar ba dashi take ba,sai da yayi Mata dukan tsiya sannan ya kyaleta.




Yana fita ta fada gadon gwaggo ta cigaba da rera kukan ta,a haka har barcin wahala ya dauke ta.






Iman kuwa yana fitowa tayi hanyar waje,kallon daya yi Mata yasa ta fara hawaye,cikin kuka tace"wallahi yaya ba laifi na bane laifin ikhlas ne",daure fuska yayi yace"amshi wanke wanken ki karasa mata",jiki na rawa ta amsa ta karasa,share gidan tayi ta wanke bayi sannan ta shiga dakin a kwance ta sami ikhlas tana barci.






Taba ta tayi cikin sauri ta bude idanu tana fadin"wallahi yaya bazan kuma ba kada ka dake ni",a sanyaye iman tace"ikhlas nice fa",jin muryar ta yasa ta galla Mata harara tace"ai inda nice koda yaya ne sai na Cece ki amma ni shine kika gudu kika barni ko?.






Dafa ta iman tayi tace"am sorry wallahi na tsorata ne,yanzu tashi kije ki gasa jikin ki kinji",babu musu ta mike ta shige bathroom ta dade tana gasa jikin ta sannan tayi wanka ta fito.




Ko kallon gwaggo bata yi ba ta wuce daki,itama gwaggon bata damu ba.




Tana shafa mai sadik yayi sallama ya shigo juyowa tayi ta Kalle shi kawai ta juya ta cigaba da abin da take yi.






A daure yace"ku shirya zamu je gidan abba kabiru yanzu,"murguda baki ikhlas tayi tace"babu inda zan je",murmushin Mugun ta yayi yace"har kin manta dukan kenan",cuno baki tayi ta juya,dariya kawai yayi ya juya.








Cikin sauri iman ta mike ta shiga wanka,zama ikhlas tayi ta dauko kaya ta saka domin ita kwalliya bata gaban ta.






*ASALIN SU*


*IKHLAS*
'Ya daya da Abba da umma suka haifa,ainihin Abba haifaffen garin biu ne dake borno mahaifiyar shi shi kadai ta haifa sai dai yana da yan uwan ta bangaren matan mahaifin shi,yana da shekara takwas mahaifiyar shi ta rasu,haka ya taso tsakiyar yan uba,dakyar ya samu yayi karatu akan business admin,ya hadu da umma ne a adamawa daya je service din shi,an kai ruwa rana kafin suka yarda dashi har ya auri yar su sai dai mahaifin umma yace"matukar shi take so to kada ta sake wani abu ya faru tazo wajen shi,haka ta yarda.






Shima bangaren abba haka ta kasance domin da kyar mahaifin shi ya yarda sai dai fa maganar tana ta a dangi.






Haka dai akayi aure amarya ta tare a bama,zama ne na hakuri tayi domin Abba dai be samu aiki ba sai dai ya koma kasuwa siyar da yadika.






Bayan wata goma umma ta fara fuskantar gorin haihuwa daga gare su,duk da haka umma ta cigaba da hakuri domin mace ce mai hakuri.






Shekarar su biyu da aure sannan umma ta sami ciki,kowa kuma sai yaja baki yayi shiru,lokacin haihuwa nayi ta haihu sai dai yaron kwanan shi daya ya koma,haka su umma suka dauki kaddara.






Tunda lokacin umma takan samu ciki amma data haihu yaran basu dadewa suke mutuwa,tofa!daga nan sai dangin Abba suka cigaba da cewa ya auri me wabi,nan dai gori ya dawo sabo.




Ana haka wata rana umma ta kuma samin ciki,Abba yayi farin ciki sosai da sosai,lokacin haihuwa nayi umma ta haifo yarinyar ta kyakkyawa sai dai fa a ranar kuma mahaifin abba allah yayi masa rasuwa,aifa tashin hankali da ba'a sa mishi rana,domin yan uwan abba cewa suka yi dole abba ya bari su kashe umma da abinda ta haifa domin kuwa yarinyar data haifa mayya ce,wasu kuma suce aljana ce,Da kyar aka samu aka daidaita suka hakura.






Wani abin al'ajabi shine yarinya tun ana Kira Mata mutuwa har akayi bakwai shiru,nan fa yan uwan Abba suka fara cewa"dama ai ta dauki wanda take so ta kashe dole ita ta rayu.






Yarinya dai taci suna ikhlas,koda ta fara Wayo kyawun ta karuwa yake yi haka tsangwamar yan uwan mahaifin ta.










Bayan wani lokaci aka zo aka raba gado,a wajen abba yace"shidai idan da Wanda zai siyi nashi to ya siya amma yana so yabar garin bama.






Budar bakin babban wansu sai cewa yayi"alhamdulillahi zamu rabu da jafa'i da wahala.




Wannan magana ta yiwa Abba da umma zafi,haka kuwa akayi wani a cikin yan uwan nashi ya siya.






Washe gari kuwa suka sauka bauchi,gida suka kama mai saukin kudi,anan suka sami su gwaggo domin sune makotan su.






Nan abba ya cigaba da siyar da yadika yana samin na rufin asiri a haka har allah ya taimake shi ya siyi gidan da suke ciki.








*sadik kuwa daya daya ne tilo ga alhaji mustafa ibrahim azare,mahaifin shi mai kudi ne tun yana karami gwaggo(kanwar mahaifin shi)ta raine shi,hakan yasa koda yayi kudi yasa ya dauko ta daga azare ya maida ta cikin garin bauchi.






Shekarar su tara da aure sannan suka haifi sadik,kwallafa rai da mahaifiyar sadik tayi akan ya mace gashi allah be basu ba yasa alhaji mustafa yaje gidan marayu ya dauko iman tana da shekara uku a duniya.








Lokacin data kai shekara bakwai,kasancewar sadik yana boarding,yasa gidan daga ita sai su mamie,ranar tana kwance taji harbi.






Cikin tsananin tsoro ta kara kudundune kanta cikin bedsheet,kofar aka turo da sauri,mamie ta Tashe ta cikin sauri tace"iman barayi sun shigo mana gida nasan da wuya su barmu da rai dan haka yasa na dauko wannan.




Wata jaka ce mai kyau,mikawa iman tayi tace"documents din daddynku ne a ciki ki rike a hannun ki kada ki bawa kowa idan yayan ki ya dawo daga makaranta ki bashi kinji ko?.






Daga kai kawai tayi,hannun ta taja ta baya kofar baya ta bude ta tura ta,tana kallon ta tana murmushi har ta bace.






Gudu sosai iman tasha kafin ta kawo bakin titi babu mota hakan yasa ta nemi wata rumfa ta makale,duk da bata da hankali sossai amma tasan da wuya iyayen nata su sha.




Tana nan tsaye wata mota ta taho da gudu,tsaya wa tayi gaban ta,cikin tsananin tsoro ta kara makalewa a wajen.




Fitowa suka yi dukan su da mask a fuska,daya daga cikin su ya cire fuskar,rufe baki iman tayi,hannun shi ta duba wata katuwar scorpion aka zana.






Kallon na gefen yayi yace"hazard mu wuce kawai,komawa suka yi suka shiga.motar suka tafi.






Anan iman ta kwana sai da safe ta karasa gidan gwaggo,kafin taje labarin mutuwar alhaji mustafa da matar shi ya baza garin bauchi.




Haka aka dauko sadik daga makaranta sai kuka yake gwanin ban tausayi,sai da aka natsa sannan iman ta bashi documents din,yayi kuka sosai da sosai.








Haka yasa suka zauna a wajen gwaggo wannan yasa iman da ikhlas suka shaku sosai.






Shima sadik zaman shi yayi a wajen gwaggon,sai dai idan suna bukatar kudi suje wajen abba kabiru(PA din alhaji mustafa)su amsa kudin da suke bukata.




Yanzun ma iman da ikhlas sun zana common entrance shi yasa sadik zai je domin ya amshi kudi ya sasu secondry.




*WANNAN KENAN*




iman ta shigo dakin da sauri ta fara shiryawa,zama tayi ta tsantsara kwalliya kamar wata babba sannan ta saka kaya,less ne a jikin su golden da zanen filawa milk,dinkin Kala daya aka musu domin komai Kala daya suke sakawa.




















💮💮💮💮💮💮💮💮
*ASHE KECE???*💮💮💮💮
(Hypocrite-love-sacrifice)






*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATON~💫💫💫*


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~❄we beare's of soon golden we writer's assiduously percieven No pain so magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Out worlds for it cause u np pain~*










*written
-by-
*Deeja one love*






*dedicated to
Maryam khamis*





007-008




Suna fita suka hau mashin a jahun 2 suka sauka bakin wani gidan dankarere,sai da suka bubbuga get din sannan aka bude musu,da sauri suka shiga suna ihun murna,itama da sauri ta fito suka rungume juna.








Ikhlas tace"ke Islam baki zuwa inda muke sai dai mu muzo ko?",langwabar da kai tayi tace"ayya ikhlas wallahi daddy ne baya bari na kuma kinga makaranta itama kullum busy.






Harara sadik ya galla musu yace"kun tsaya ne baza Ku wuce muje ba",ikhlas sai da ta murguda mishi baki sannan ta ja hannun su suka wuce",murmushi yayi ya shafa fuskar shi sannan ya bisu a baya.






A falo suka sami duka yan gidan,da sauri abba kabiru ya mike ya karaso inda suke,cikin farin ciki yace"barka da zuwa yara na,ina gwaggon ku?",sunkuyar da kai Sadik yayi yace"tana lafiya tace a gaishe Ku,idan ta sami lokaci zata shigo ma.








Hannun shi Abba kabiru ya ja ya zaunar dashi yace"yauwa registration na riga da na gama muku kai da Dan uwanka hafeez,Dan haka nan da sati biyu zaku koma school.






Murmushi sadik yayi yace"Abba an gode allah ya saka da alkhairi,sai maganar su Iman",shafa kanshi yayi yace"na riga da na musu komai da komai yanzu abin da ya rage shine shopping kawai zaka yi musu.








ATM ya ciro ya mika mishi yace"gashi kaje ka siya musu komai da komai da ka San zasu bukata",hannu biyu ya sa ya amsa yana godiya,Abba kabiru yace"kada ka damu sadik ka dena mini godiya,firar mu ta karshe da alhaji shine kada ka bari yara na su tagayyara kada ka bari su dena karatu",kwalla sadik ya goge yace"allah ya jikan ka Abba na",duka suka amsa da ameen.








Kallon su yayi yace"Ku tashi mu tafi mana",cuno baki ikhlas tayi tace"haba yaya tun yanzu allah babu inda za muje",kafin yace komai mama tace"ka kyalesu anjima sai Ku tafi kai ma kaje wajen Dan uwan ka yana dakin shi",murmushi kawai yayi ya Tashi ya tafi.








Aifa ikhlas an sami abinda ake so gaba daya sai abinda suka yi babu mai kwabar su,nan suka wuni shirme da shiririta.






Sai yamma sannan hafeez ya kai su abubakar balewa shoprite anan yayi musu duk siyayyar daya kama ta.






Ikhlas ta Kalle shi tace"yaya me za kayi da kayan provision",murmushi yayi yace"Ku zan kai boarding",ihu ta zuba tana fadin "wallahi bazai yiwu ba tab bana so kada ka kaini makarantar boarding wallahi zamu dena abinda mu keyi",ko kallon ta beyi ba.






Bin shi take tana kuka,banza yayi da ita,duk inda suka bi mutane kallon su sukeyi,haushi yaji ya daka mata tsawa,jiki na rawa ta matsa harara ya galla Mata yace"kin bar nan wajen ko sai na make ki".






Hafeez yazo da sauri ya rike mata hannu yace"zo muje kinji kyale shi",hannun ta ta kwace tana fadin"ni ka kyaleni bana so",harara sadik ya galla Mata wanda yasa da sauri ta bi hafeez,.






Mota ya bude ya saka ta sannan ya zagayo ya zauna a driver seat,hannun ta ya rike yace"ikhlas kiyi shiru baki ga kuka beyi miki kyau ba",idanu ta lumshe tace"please yaya hafeez kace mishi bana son boarding school kaji?",shiru yayi be ce komai ba.






Da idanu take kallon shi kafin tace"yaya hafeez baza ka gaya mishi ba kenan?",hafeez yace"ikhlas ba haka bane kinga an riga an gama komai da komai kiyi hakuri Ku je kawai kinji",hawaye ya zubo mata ta bude kofar ta fito.




Hango shi ya taho bayan shi iman ce rabe kamar munafika,da sauri ta kauda kai ta juya ta bar wajen.




Sadik na kallon ta domin tunda suka fito hankalin shi na kan ta,bude boot suka yi suka zuba kayan,kallon iman yayi yace"wuce ki shiga",jiki a sanyaye ta bude motar ta shiga.






Hanyar da ikhlas ta bi ya bi,can jikin wata rumfa ya ganta a tsugune,tsayawa yayi ya zuba mata idanu yana kallon ta,ita kuwa bama san yana yi ba kukan ta kawai takeyi domin ita a duniya ta tsani boarding wato yasan da hakan shiyasa yake so ya tura ta can.






Hawayen fuskar ta taji ana goge mata da sauri ta dago idanun ta,murmushi yayi yace"meye na kuka ikhy bafa mutuwa zakuyi ba ba kiga yar uwar ki ta hakura bane".




Shiru tayi tana share hawaye,hannun ta ya murza yace"ya isa haka tashi muje suna jiran mu",babu musu ta tashi hannun su sarke suka nufi motar,da kanshi ya bude Mata kofa ta shiga,shi kuma ya shiga gaba,sannan hafeez yaja motar.






Ana parking ta bude ta fito,gidan gwaggo ta shige da kukan ta,gwaggo dake sallah da sauri ta sallame ta juyo tana kallon ta,ita kuwa ikhlas kuka take kawai,gwaggo tace"gaya mini meya faru ne kike bude baki haka",banza tayi da ita.








Gwaggo ta yunkura ta mike,carbin ta ta dauko zata caula mata,da gudu ikhlas ta mike,a bakin kofa suka ci karo da sadik,cikin sauri ya rike ta yana fadin "lafiya kuwa?",fincike hannun ta tayi ta fice daga gidan.






Gwaggo ya kalla yace"gwaggo lafiya kuwa?",gwaggo tace "Kai zan tambaya lafiya kuwa?"murmushi yayi yace"wai fa Dan zata tafi boarding shine take wannan aikin",gwaggo tace"alhamdulillahi ai gwara su tafi ko zamu huta".






Ikhlas kuwa na zuwa gida ta sami kayan jibge a dakin umma,iman kuma na gefe ta rabe kamar marainiya,turo baki tayi tana fadin"Abba Dan allah bana son boarding wallahi",harara umma ta galla mata,Abba kuwa janyo ta jikin shi yayi yana Kara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login