Showing 15001 words to 18000 words out of 71023 words

Chapter 6 - ASHE KECE Complete By One Love .txt

One Love   

31 Jan 2025

4661

ta kira gwaggo haka iman, shidai sadik abin farin ciki yake sashi domin yasan suna son dan da zai haifa, iman ita kullum tafi son mace, ita kuma ikhlas tace namiji, ita kam islam cewa take Allah dai ya sauke ta lafiya.










tunda taje bata da kawa ko guda daya har suka cinye first da second semester, suna cikin third semester ta hadu *nafeesert jibreel jasawa*ita amma yar kano ce hakan yasa daga gida takan zo makarantar.


Bayan sun fito daga lectures ikhlas tace"yauwa feenat muje jifatu dan Allah ina so nayi siyayya", nafeesa tace"babu komai muje kawai amma fa daga can gida zan wuce", ikhlas tace babu komai", ikhlas ke driving kasancewar tun tana bauchi suka koya a motar yaya hafeez.








Suna parking suka fito waya ce a hannun ikhlas tana fadin"bari na kira maman baby yau kwata kwata ban kira ta ba", dariya safeena tayi tace"ai kuwa ya kamata", amsar da tayi niyar bata ne ya tsaya saboda karo da tayi da mutum har wayar ta ta fadi shikuma ledar dake hannun shi ta fadi.






A tare suka tsugunna domin tattaro kayan, shikam kokarin daukar wayar tata yake yi, wanda hakan yasa tayi saurin fara tattara nashi, dakatar da ita yayi yace"am sorry ki barshi zan kwashe kawai"murmushi tayi tace"ok na gode", juyawa tayi suka shiga ciki.






Ikhlas kuwa siyayyar take tana tunanin wannan mutumin tabbas bafulatani ne daga ganin shi, domin fari ne kuma kyakkyawa,murmushi kawai tayi, suna gama siyayyar suka fito.




Abin mamaki a tsaye suka same shkenanjingina da motarshi yana danna waya, feenat tace"to ikhy gashi ki hau mota ki koma", kallon kin raina mini wayo tayi kawai ta cigaba da tafiya.






Tana fita bakin titi motar tayi parking a gabanta glass din ya sauke ya leko yace"princess muje ko", kamar zata ce wani abu sai ta fasa kawai ta bude ta shiga ", murmushi yayi yaja motar.






Sunyi nisa da tafiya ya dube ta yace"ni sunana saifullahi muhammad yunusa gimi muna zaune a kaduna anguwar rimi, aiki ya kawo ni kano kefa?, sai da ta numfasa sannan tace"sunana juwairiyya muhammad ni ina zaune ne a bauchi karatu ya kawo ni kano".




Murmushi yayi yace"which school? ", ta bashi amsa da"BUK,mass com dept",dariya yayi yace"ai ban tambaye ki ba", itama murmushi tayi tace"ai nasan tambayar gaban kenan". Har bakin hostel dinsu ya ajiye ta.




Fitowa yayi yace"to baki bani number din ki ba", fari tayi tace"ta siyarwa ce",dariya yayi yace"how much",it's very expensive that you can't buy it",ta bashi amsa, murmushi yayi yace "to ai nace ki gaya ne",juyar da kai tayi tace"ban shirya shan duka wajen madam ba".






Dariya yayi yace"ashe ma ke matsoraciya ce", juyowa tayi ta kalle shi sannan tace"ni ba matsoraciya bace zan iya baka amma kada ka bari ta gani", dariya kawai yayi ya miko mata wayar, number din tasa mishi, a take a wajen ya kirata yace tayi saving shi kuma ya shiga mota ya tafi.










Washe gari ta bawa feenat labari, dariya kawai tayi tace"ai dama na kusa gano haka sai dai kin san me? ", gurgiza kai tayi, safeenat tace"lecturer ne a makarantar nan ke matsayin doctor gare shi", zaro idanu tayi tace da gaske", daga kai tayi alamar eh.






Yanzu cikin iman yana da wata takwas, a lokacin kuma tsakanin ikhlas da dr saifullahi soyayya suke gudanarwa sosai.




Yau ma suna tare tace"zumana nifa ina so muyi changing of course nida feenat kuma inaso ka sama mini gida a wajen makaranta ka kama mini", murmushi yayi yace"an gama princess wane course kuke so? ",kashe ido tayi tace"course din da kake koyarwa wato business admin mana", dariya sukayi gaba daya.






Yau sukayi hutu inda da sun dawo zasu shiga 200level, murna kawai ikhlas takeyi, feenat tace"yanzu ke zamu rabu sai murna kike yi? ", ikhlas tayi dariya tace"kada ki damu wallahi kina raina sai dai inaso naje naga baby ne", rike haba feenat tayi tace"wai ke dan Allah kamar wani babyn da yazo duniya? ", ai ya kusa zuwa insha Allah.








Dr saifullahi ya kalleta yace"yanzu princess tafiya zakiyi ki barni", murmushi tayi tace"kaima fa zumana nan da one week ne fa ka tafi kaduna ", juyar da kai yayi yace"ko naje kaduna princess lily baya nan ai babu dadin zama", dariya tayi tace"wannan lily ina son ganin shi kullum sai anyi maganar shi", yace"ai naso na hadaku shi yaki yarda wai yafi so yazo ya ganki da kanshi", dariya tayi tace"Allah ya kawo shi lafiya", ameen ya amsa.






A motor park ya ajiye ta kallon ta yayi yace"nace ki bari nasa driver ya kaiki gida kin ki yarda ko ai shikenan ", shiru tayi kamar bata ji ba ta fita, shima fitan yayi sai da ya sama mata mota ya biya sannan ya juya.










Da murna ta shiga gidan, rungume gwaggo tayi tana fadin"gwaggo gani na dawo", hannun ta gwaggo ta rike tace"yauwa yar albarka sannu da dawowa, ki shiga kiyi wanka kizo ga mutumin ki", cikin farin ciki ta shige daki, jaka kawai ta ajiye ta cire kaya ta shiga wanka.






Tana fitowa ta samu gwaggo ta ajiye mata komai in need zama tayi da sauri ta bude kwanon, murmushi tayi tayi wa gwaggo thumb up ๐Ÿ‘alamun jinjina.








Zama tayi taci lafiyayyen dambun da yaji kayan ganye tana gamawa tasha hadadden zobon da gwaggo ta hada mata me sanyi.






Sai da ta huta sannan tace"gwaggo bari naje naga baby, kin ga tun dazu maman shi ke damuna da kira.








Gwaggo kam dariya tayi tace"wannan da yana da iyaye masu yawa allah ya fito dashi lafiya", da ameen ta amsa sannan ta fice.




Tafiya take wanda duk inda ta gifta sai an kalle ta barin ma idan ta juya grey eyes din ta, wasu ma basa iya hakuri har sai sun tanka.








Da sallama ta shiga, iman da ciki ya tsufa da kyar take daga kafa ta karaso da sauri tace"ayya sisto sannu da zuwa ya makaranta? ", sai da ta yamutsa fuska sannan tace"lafiya lau wallahi amma fa akwai wahala ", iman ta janyo ledar da ikhlas ta ajiye ta bude, yalo ta dauko guda daya ko wanke wa ba tayi ta daba baki.






Tace"kinga wallahi baby ita ta hana ni cigaba amma da yanzu nasan ina na dosa ", dariya ikhlas tayi tace"Allah sarki my baby Allah ya fito mini da kai lafiya ", harara iman ta balla mata tace wallahi baku isa ba", zaro idanu ikhlas tayi tace"to idan allah ya bamu ba sai ki hana ba", firar su suka cigaba gwanin sha'awa.








Iman tace"ke baki ga kayan da yaya hafeez suka kawo ba na baby wai amma fa na maza", dariya ikhlas tayi tace"wallahi koni wanda nake siya na maza ne",iman ta harare ta tace"wato ni kadai kuka bari dana mata kenan har fa darling kayan maza yake siye", dariya kawai ikhlas tayi.










Tunda ta dawo kullum sai taje gidan iman, yau ma barci me yayi awon gaba da ita shiyasa bata tafi da wuri ba.








Tana cikin shiri sai gasu sun shigo, dariya tayi tace"Allah yaya ka hutar dani", murmushi yayi yace"ikhy nasan bani da matsala dake amma duk da haka ga amanar baby nan da kuma maman baby din", kallon shi tayi tace"meya faru", zan tafi wajen wani mutum ne da abba kabiru ya aike ni wajen shi can niger state zan kwana biyu kinga kuma be kamata na barta a can ba dan watan haihuwar ta ya kama kar nakuda ta kamata ita daya", ya bata amsa.






Cuno baki tayi tace"kai yaya maimakon ka bari naje ina tayata kwana", dariya yayi, gwaggo tace"wai *kwamacala*sunan wani littafi na maman mamy, ke din za'a bari da ita me kika sani? ", kara hade fuska tayi tace"wai gwaggo me kika mai da nine? Amsar haihuwar dai", ja can matsa ki bani guri








Dariya sukayi gaba daya, sai da ikhlas ta kawo mishi abinci yaci sannan ya mike yace"to gwaggo zan tafi, ikhy ga amana nan na bar miki", dariya tayi tace"insha Allah yaya zaka dawo ka sami amanar ka kamar yadda ka bar ta", juyowa yayi ya kalle ta yace"harfa suna na bar miki zabi dan baby dan ki ne halak malak fatan zaki kula dashi sosai ko", daga mishi kai kawai tayi.






Iman ita ta raka shi har waje sannan ya tafi, da yamma suna zaune ikhlas tana faman yanka albasa domin zata sawa dan malele da iman tasa tayi mata, fira suke yi da gwaggo dake gyara wake.






Ikhlas ta juya ta kalli iman tace"yadai maman baby naji kinyi shiru? ", ajiyar zuciya iman tayi tace"wallahi sisto, gaba na yake ta faduwa gashi na kira darling be daga ba tun dazu", jinjina kai kawai ikhlas tayi tace"may be aiki yayi mishi yawa.








Haka har akayi sallar magrib, iman ta kalli ikhlas tace"sisto number din yanzu bata shiga", ikhlas tace"kai sisto wannan soyayya haka, kin san fa niger fa aka ce", amma nasan idan ya isa zai kira......", maganar tace ta tsaya domin shigowar abba kabiru bayan shi yaya hafeez a hargitse.








Cikin tashin hankali islam ta shigo,rungume ikhlas tayi tana kuka tace"sister baby ya zama maraya", fincike jikin ta tayi bude baki tayi domin yin magana amma ina kaswa tayi domin jiyo abinda abba kabiru yake gayawa gwaggo.




Gwaggo cikin matukar gigicewa tace"ashe ajali ke kiran ka abubakar allah ya jikan ka yasa ka huta ", ihun taji a bayan ta, da sauri suka juya ita da islam ita kuma gwaggo ta fito da gudu, zubewa a wajen iman tayi, da gudu suka yo kanta wanda juyawar da ikhlas zata yi jiri ya kwashe ta ta zube a wajen..........








๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ
*ASHE KECE???*๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ
(Hypocrite-love-sacrifice)






*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATON~๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ*


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~โ„we beare's of soon golden we writer's assiduously percieven No pain so magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Out worlds for it cause u np pain~*




Wattpad @13 deeja


Or
Deeja1love.blogspot.com


*written
-by-
*Deeja one love*






*dedicated
to
*Maryam khamis*


Aunty nabeela ga page dinki na baki shi duka kiyi yadda kike so dashi.
19-20




Farkawa tayi taga islam a gefe tana yi mata fifita, shiru tayi tana so kamar mai tunani, tuna abinda ya faru yasa tayi saurin mikewa.






Islam ta rike ta tace"ikhlas ki tsaya kiji, kada ki fita a haka", juyowa tayi tace"wajen yaya sadik zanje nasan abinda aka fada ba gaskiya bane", dafata tayi cikin lallashi tace"ikhlas wanda ya mutu baya dawowa ", rufe kunne tayi tace"bana son ji islam ki dena gaya mini".








Ajiyar zuciya tayi tace"shikenan ikhlas yanzu koma ki zauna",kamar bata ji ta ba haka tayi kokarin fita take yi,islam tace"ina zakije?, bata juyo ba tace"wajen iman mana", ita ma islam binta tayi kawai.








Ganin babu kowa a gidan yasa ta juyo tan kallon islam,yake islam tayi tace"ikhlas iman tana asibiti tana labour tun dazu",harara ta galla mata tace"shine baki gaya mini ba tun dazu".










Hijab ta saka kawai suka tafi, a bakin asibitin suka hadu da yaya hafeez da abba kabiru dan haka a tare suka shiga.






Suna shiga nurse na fito da jariri, rigen-rigen amsa kawai ake yi,ikhlas ta kalli nurse din tace"ina uwar fa? ", murmushi tayi tace"kada ki damu tana lafiya, yanzu za'a gyara ta sai a fito da ita.








Hafeez ya miko mata yaron, hannu biyu tasa ta amshe shi, hawaye ya zubo mata domin tsantsar kamar da suke da mahifin shi, share hawayen tayi sannan ta mikawa yaya hafeez tace"kayi mishi huduba".






Kallon ta yayi yace"a'a ikhlas nasan sadik ke ya bari ki sa mishi suna",murmushin dole tayi tace"kada ka damu allah ya raya *abubakar sadik*,kuka ya kufce mata, tabbas tasan tayi asara, farko mahaifin ta daya rasu, na biyu mahaifiyar ta da aka neme ta aka rasa, na uku yaya sadik da shima ya tafi ya barta.








Dakin da aka kai iman nan suka shiga, tana zaune idanun ta yayi ja, suna hada ido da ikhlas suka fashe da kuka, islam ma hawaye kawai take yi.






Abba kabiru yace"ashsha! Me kenan waya ce muku kuka zakuyi, ai wanda ya mutu addu'a yake bukata ba kuka ba, dan allah ku dena yi mishi kuka haka, hakuri ya kamata kuyi domin komai zai wuce watarana",hafeez dake share hawaye yace"abba dole je mu damu kalli kaga burin sadik ya fito duniya a lokacin da shi kuma sadik din ya rufe idanu".










Gwaggo dai na gefe ta rasa me zata ce domin shi take gani take tunawa da mahaifin shi,hafeez yace"abba ya maganar gawar? ", ajiyar zuciya yayi yace"sai dai muyi hakuri domin ko ganin gawar ba'a yi ba".










Washe gari da safe aka sallame su, gidan gwaggo aka wuce da ita domin ko ta koma can babu abinda zata dinga yi sai kuka,abu ya hadewa ikhlas goma da ashirin domin duk wanda zata samu madafa dashi to kauchewa yake yi.






Gida fa ya koma kamar makabarta, domin baka jin sautin dariya ko fira cikin annashuwa, yau ma sai da hafeez yazo ya duba *aboki*domin sunan da yake kiran yaron dashi kenan.






Nasiha ya koma yi musu, sannan ya tafi, ikhlas na zaune tayi tagumi wayar ta tayi kara, duba me kiran tayi, ganin sunan yasa tayi saurin dagawa.






Ajiyar zuciya ya sauke yace"haka princess irin wannan shariya haka, wallahi duk hankali na ya tashi", kuka ta fashe dashi.






Kara rudewa yayi yana tambayar ta lafiya, cikin kuka tace"zuma na yaya sadik ya rasu",cikin kaduwa yace"innalillahi wa'inna ilaihir raji'uun! Ya maimata ya kai sau uku sannan ya dora da allah yaji kanshi", cikin sanyin murya ta amsa da ameen.










Washe gari da yamma tana yiwa baby wanka, gwaggo ta shigo tace"ikhlas kin yi baki a waje", mikawa gwaggo yaron tayi ta dau hijab ta fita tana tunanin su waye haka.






Turus ta tsaya tana murmushi, cikin sauri feenert ta karasa kusa da ita tace"haba cat eyes wannan irin kallo",hararar ta tayi kafin tace"to ku shigo daga ciki",su hudu ne,feenert kawai ta sani sai mamar ta amma sauran bata san su ba.










Suna shiga suka yi gaisuwa sannan maman feenert tace"oh allah yaji kanshi", duka suka amsa da ameen,jan hannun feenert tayi, su kuma sauran suka bisu.






Dakin su ta dire su,iman data shigo dakin tace"sisto waye wa'innan? ",murmushi feenert tayi tace"yanzu iman bata taba gaya miki sunana ba? ", daga mata kai tayi.






Iman bata ce komai ba ta mike ta nufi wajen kayan ta, murmushi ikhlas tayi kafin tace"sorry sisto duka course mates dina ne", da mamaki feenert ta dube ta, harara ta galla mata wanda yasa tayi shiru.








Iman bata ce komai ba, sai daukan sadik data yi zata fita,da sauri ikhlas ta kwace shi tace"malama jeki kawai wannan ai yarona ne",juyawa kawai iman tayi ta fice.






Bayan ta fita ikhlas ta dube su tace"yauwa ku amshi yaron mana",feenert ta dauki yaron,kallon ta ikhlas tayi tace"oya gaya mini su waye wa'innan din?".






Feenert tace"wannan sunanta nabeelert wannan kuma sunan ta hafsat,idan kin dawo kano zaki ji komai daga bakin su", daga kai tayi sannan ta mika hannu ta dauke shi domin kaiwa maman feenert din yaron.












Tana dawowa ta zauna suka cigaba da fira, wayar hannun ta tayi kara, cikin sauri ta daga.






Ajiyar zuciya yayi yace"ki fito gani a kofar gidan ku",amsawa tayi da to sannan ta harari feenert tayi waje.






Jingine a jikin motar shi ta same shi,yana ganin ta ya fara murmushi, itama murmushin tayi mishi a hankali ta karasa kusa dashi.








Cikin idanun ta ya kalla sannan ya juyar da kan shi yace"princess nace ki dena kallo na haka wallahi har tsakiyar kaina nake jin wannan idanun naki", murmushi kawai tayi ta juya fuskar ta.








Langwabar da kai yayi yace"princess ya hakuri", ajiyar zuciya tayi tace"mun gode Allah, "dan murmsuhi yayi yace"baki tambaye ni waye ya nuna mini gidan ku ba? ",juya idanu tayi tace"ai feenert ce na riga da na sani", dariya yayi yace"hmm kina da basira", lip din ta na kasa ta ciza tace"na riga da na san hakan, well mu shiga ka gaisa da gwaggo ta sannan kaga baby na, sai ka wuce dasu feenert".








Sai da tayi mishi iso sannan ya shiga, sun gaisa da gwaggo da maman feenert,gwaggo sai mata kallon tuhuma take, ta gane hakan yasa ta dena kallon gwaggon.






Hakama iman data fito suka gaisa,yaron ta amso a wajen su feenert ta bashi,a take a wajen yaji yaron ya shiga ran shi sosai, ya dan jima sannan ya mike ya fita.






Shiga dakin tayi tace"feenert ki fito ku tafi",mikewa feenert tayi tace"haba cat eyes wannan irin kora", kallon sauran tayi tace"ku taso mu tafi", su dai basu ce komai ba suka tashi.








Suna fitowa ya rinka bin t da kallo,kin yarda tayi su hada ido,tace"ka bude musu ka bar su suna jira", da sauri ya bude musu suka shiga.






Kallon ta yayi yace"na gode da kora ta da kike yi",murmushi tayi tace",zuma na ba haka bane,ka bari idan na dawo kano zamu hadu yanzu abinda nake so shine please kada ka dawo har na dawo kano",ajiyar zuciya yayi yace"ok as you wish", ya juya ya tafi.






Sai da taga sun bace sannan tayi ajiyar zuciya ta koma cikin gidan,daukan sadik tayi ta ringume tana jin soyayyar yaron har cikin ran ta.








Iman ta shigo ta dube ta tace"yanzu kin kyauta kiyi kawaye amma ki kasa gaya mini? ", murmushi tayi tace"taya zan gaya miki sisto bayan wannan abin daya faru", hararar ta tayi tace"eh ai haka dama zaki ce mana yar rainin wayo ni wallahi yanzu kallon stranger nake miki, ba'a gane inda kika saka gaba, always hidding something",dariya kawai ikhlas tayi ta cigaba da yiwa sadik wasa.












A yau kwanan sadik ashirin da mutuwa,islam tayi sallama ta shigo,binta da kallo suka yi,dariya tayi tace"ke miko mini baby na ganshi",mika mata ikhlas tayi.








Sun sha fira kafin ta wuce makaranta,suna zaune daddare iman tace"sisto wai meyasa yanzu baki da gaskiya ne, kallon ta ikhlas tayi for some seconds sannan ta cigaba da sawa sadik

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login