Showing 54001 words to 57000 words out of 71023 words
tashi iman da gwaggo wannan ba sabin abu bane, idan aka yi la'akari da urin son da suka yiwa juna da shakuwar su.
Ikhlaa ita tafi to mishu da kaya ya saka, sannan ta kawo mishi abinci, zuba mishi tayi,da murmushi ya debo ya miko mata a baki.
Dariya tayi tace"kai yaya na girm......... ",ba ta karasa ba saboda abincin daya zuba mata a baki.
Sai da ta hadiye sannan ta bata rai tace"yaya meye haka ne yaya yanzu fa inada da, ko ince 'ya'ya".
Gaban shi ya fadi, da sauri ya kalle ta yace"ban gane ba, kinyi aure ne? ",murmushi tayi yace"harda yara guda uku".
Sunkuyar da kai yayi kasa, yace"ina mijin da yaran? ",hannun shi ta riko suka fito falo ta nuna asp abdallah tace"kaga mijin yaran kuma suna kano mun bar su wajen maman shi".
Zuciyar shi ke bugawa da karfi,jingina yayi da jikin bango a zuciyar shi yana karanta"innalillahi wa'inna ilaihir raji'un".
Su dai yan falon kallon su suke yi,su beelert da suka san gaskiya suka zuba mata idanu, su gwaggo kuwa har sun yarda.
Hafeez ya kalli asp abdallah yace"masha allah ka auri mace ta gari, bani da haufi akan ikhlas", duk da shima zuciyar tashi bugawa take.
A sanyaye yaya sadik yace"meye sunan yaran ne? ",dariya tayi tace"babban sunan ka ne, wato sadik,sai mustapha ana kiran shi da muhsin sai ya ma dayan".
Ta fada tana duban iman, iman tace"bansani ba ai", ikhlas ta kalli beelert tace"meye sunan yarinyar hannun ki ne? ".
"Yauwa ikhlas, nama tuna, sune yaran nawa", ganin wasa take mishi yasa ya biyo ta inda ita kuma tayi waje tana dariya.
Kwaikwayar yadda yayi take yi, idan taga zai kama ta sai ta juya da gudu tana dariya, shima dariyar yake yi.
Ganin idan yayi wasa ba zai kamata ba yasa ya fara gudun,taku daya biyu ya cafko ta, tana dariya ta fara bashi hakuri.
Kallon cikin idanun ta yake yana fadin"wa na kama? ",rike kunne ta tayi alamar ban hak'uri".
Dariya yayi yace"zo ki bani labarin abinda ya faru dake".
*maman farouk*😁
💮💮💮💮💮💮💮💮
*ASHE KECE???*💮💮💮💮
(Hypocrite-love-sacrifice)
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
✍✍✍✍✍✍✍
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION~*
✍✍✍✍✍✍✍
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
*written*
-by-
*Deeja one love*
*🏆JAKADIYAR GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION*🏆
*Dedicated*
-to-
*Maryam khamis*
Allah sarki my sis *hassana tafarki* d writer of *ilham* , Allah ya baki lafiya yasa kaffara ne.
Godiya gare ku, Group din aunty Fatee hausa novels ku sani, Sakonnin ku suna zuwa gare ni sosai da sosai.
Dan haka na ba kowanne members na wannan group din wannan page din.
Sumaimah kina daya daga cikin masoya na.
Farida Atiku naga sakon ki ameen na gode sosai da sosai.
To fa! Yan group din aunty Fati hausa novels Zainab musa habib tace tayi muku anko ku duka dan haka sai ku sako mu tafi bikin *Saifullahi da Hafsat*.
*Sanaz* d writer of *direban gidan mu* tnxs for your support.
Kuyi hakuri masoya, wallahi yanzu na zama lazy ne na rasa me yasa hakan na kasa dinga muku koda one page ne per day, na sani da kyar kuke samun three to four pages ma a week, ku kara hakuri insha allah zan yi kokari na gyara kada ku manta ni daku *one love*😘.
59-60
Sosai suka sha fira dan har dare suna tare,cin abinci duk tare suke yi sallah kawai yake zuwa yayi ya dawo.
Sai after eleven sannan ta wuce wajen kwanciyar ta, A zaune ta tarar da Beelert, Feenert kuma tana waya.
Beleert tace"sai yanzu an gama soyayyar ne? ",Ikhlas tayi dariya tace"Ki dena fadin haka mana kada Iman taji".
Haka suka kwanta cike da farin ciki,Domin dai fiye da shekara biyar bata kuma yin kalar wannan ba, Yanzu dai abinda take addu'a shine Allah ya bayyana mata Umman ta.
Hajiya ta dubi Baffa tace"Yanzu dan Allah ga Sadiya ga Shamsiyya amma aka kasa hada daya daga cikin su da Saifullahi sai wai Hafsat.
Baffa yace"Rabi'atu kenan kada ki manta su Shamsiyya bamu muke da iko akan su ba,Tunda mahaifin su na nan da rai, Haka ko baya nan yan uwan shi na nan da rai".
Hajiya rabi ta tabe baki tace"shikenan ai Allah ya sanya alkhairi",Baffa yace"Yauwa abinda ya kamata ki fada kenan".
Bata ce komai ba ta mike ta tafi,A daki ta tarar da Bintu da Sadiya wacce take zaune tana kuka, sai Shamsiyya dake danna waya.
Hajiya rabi tace"kema jarababbiya haba, Kamar shi kadai ne namiji duniya, Ki nemi wani mana".
Sadiya cikin kuka tace"Hajiya ni wallahi shi nake so,Kuma shi kadai zan iya aura",Shamsiyya ta tabe baki tace"Wahalalliya kawai".
Hajiya tace"kema dai kya gaya mata haba kamar mayya ana kyamar ki kina mannewa".
Bintu dai bata ce komai ba, domin kuwa itama hakan ta faru dashi.
Sosai abin ke damun sadiya sai dai tasan babu yadda zata yi hakan yasa ta wartsake domin ko ta nuna damuwar ta babu wani amfanin hakan.
Ikhlas ke zaune kusa da gwaggo ta tankwashe kafar ta tana faman zuba rok'o,tace"dan allah gwaggo ki bari mu je tare".
gwaggo ta mike ta dauko carbi,gaba daya dakin aka fashe da dariya,cikin mamaki tace"gwaggo da waye zaki daka da wannan? ".
Gwaggo tace"ke mana, kiji ja'ira",dariya ta kuma yi tace"haba gwaggo da da yanzu da bambanci yanzu idan aka ce ki dake ni sai ki dake nin? ".
"Kwarai kuwa mara kunya, ke wallahi ki kiyaye ni, ja'ira kawai",sadik ya mike yace"kai gwaggo tunda har ba zaki je ba, mu zamu je".
Tabe baki gwaggo tayi tace"a gayas Allah ya raka taki gona",duka suka amsa da ameen.
Washe gari,ikhlas, iman, feenerh, beelert, yaya sadik, yaya hafeez sai asp abdallah suka dauki hanyar adamawa.
Bangaren abba kabeeru kuwa hankalin shi ya tashi sosai ganin babu beelert,sai dai ya rasa waye ya fitar da ita.
Ganin zai dami kan shi yasa yace"sai wani damun kai na nake, ai tunda takardun suna hannu na shikenan na san babu mai zuwa yace zai amshi wannan.
Beelert kam farin ciki fal ran ta, duk da an fara wasu events din basu nan hakan be sa ta damu ba, ita dai tun da suna hanya shikenan.
Shi kan shi saifullahin sai da ya gaji ya tambaye ta"wai amarya ta wannan wane irin farin ciki ne haka? ".
"Wallahi wasu baki zan yi daga bauchi", jin ta ambaci bauchi yasa gaban shi faduwa saboda tunowa da yayi da ikhlas.
"Meya faru ne? ", ta kuma tambayar shi,"babu komai kawai na tuna wani abu ne, anyway Allah ya kawo su lafiya", ta amsa da ameen.
Su ikhlas basu suka shigo garin yola ba sai bayan isha'i,gidan bashi da wuyar kwatance, domin yana bakin titi.
Suna shigowa harabar gidan,suka tabbatar da ana biki, domin wasu maza ne sanye da kayan fulani, suna ta faman rawar al'adar su.
Abin ya birge ikhlas sosai da sosai, don sakin baki tayi tana kallon ikon Allah.
Bata yi aune ba taji an rungume ta,tana juyowa suka hada idanu da hafsat,sosai suke murna kafin su shiga gida.
Kasancewar asp abdallah shima jikan gidan ne yasa ya kai su yaya hafeez masauki.
Ikhlas tace"kai hafsat gidan ku gidan yawa ne sosai, gaskiya familyn ya birge ni".
"hmm dan ma baki gan su duka ba kenan,ai sai ranar daurin auren tukunna", hafsat ta fada.
Yauwa ikhlas ku tashi mu tafi wajen gyaran kan,"to ina zuwa bari na dauko waya na",ikhlas ta fad'a tana juyawa zuwa bedroom din daneji.
Suna tsaye suna jiran ta,saifullahi da maleek suka shigo,hafsat tayi murmushi, shima murmushin yayi mata yace"sai yanzu zaku tafi? ".
"Eh yanzu zamu tafi,am yaya ga feenert, wannan kuma iman, ga beelert kuma, kuma dukan ku ga angon saifullahi, wannan kuma kanin shi ne abdul maleek".
saifullahi yayi murmushi yace"barkan ku dai, manyan baki ai tun kan ku iso labarin ku ya iske mu".
Maleek kuwa kallon su yayi yace"nice to meet you",daga haka be kuma magana ba.
Feenert kuwa kallon saifullahi take tana mamaki,domin abin ya daure mata kai, ganin be gane tana wajen ba yasa ta fuske kawai.
Maleek ya kalli yayan nashi yace"yaya pls let's go mana",saifullahi yayi dariya yace"kai lily muje to, sai kun dawo",daga haka suka wuce.
Ikhlas ta fito tace"sorry for keeping you waiting,muje ko", jiki sanyaye feenert ta bisu.
Asp abdallah ya kai su, waje ne mai tsari da kyau, hafsat tace"shiyasa nace ba zan zo gyaran kai ba sai kun zo domin zan fi jin dadi".
Sai bayan magrib sannan suka dawo, wanda a lokacin wanka suka yi sannan suka yi sallah,aunty meenat(matar daddyn adamawa wato mahaifiyar asp abdallahi) ta shigo.
Gaishe da ita suka yi sannan tace"hafsat kizo umman ku tana neman ki", tashi tayi ta fita.
Ikhlas tace"ni dai wallahi dole mu gwan-gwaje a bikin nan,feenert what happened? ".
"Me kika gani ne cat eyes",feenert ta fada,beelert tace"nima tun da muka hadu da ango naga fuskar ta ta canza".
Feenert tayi ajiyar zuciya tace"wallahi kawai kai na ke ciwo", daga haka ta mike.
Ikhlas kam kwanciya tayi domin barci take ji,beelert tace"feenert wai dan allah meya faru ne?".
"Hmm nabeelert abinda na gani yafi karfin ji na, kin san angon da hafsat zata aura shine saurayin ikhlas wannan da take kira da zuman ta".
Zaro idanu beelert tayi tana fadin"feenert are you serious shine? ",daga kai feenert tayi tace"wallahi shine".
Beelert tace"yanzu abinda za'a yi shine kija bakin ki kiyi shiru, domin na tabbatar idan hafsat taji zata fasa wannan auren".
"Dama sai kin gaya, haka kawai ace ni na kashe aure babu ruwa na",daga haka suka canza fira.
Washe gari aka yi sister's eve iya yan mata ne da samari, sosai wajen ya kayatar,zuwan ikhlas kenan jikin ta sanye da orange din material da ratsin milk.
Ta hadu sosai hakan yasa duk wajen kallo ya koma kan ta, iman ta iso wajen cikin sauri tace"sister ga babyn ki can yana zazzabi".
A rude ikhlas ta bita, samarin wajen sai faman cizon yatsa suke domin sun so su dan taya.
Ikhlas kuwa jiki na rawa ta nufi cikin gida,tun kan ta karasa har ta fara hawaye,karo suka yi da umma da aunty meenert wacce suka fito tare.
Ikhlas kam bama ta tsaya ba, umma ta bita da idanu duk da kan ta juyo tayi nisa hakan be hana gaban ta faduwa ba kamar zata tuna wani abu.
Suna zuwa sai faman rawar sanyi babyn yake yi,yana jikin mahaifin shi yana faman shafa mishi ruwan sanyi.
Tana zuwa ta amshe shi ta rungume tana kuka tana fadin"baby ka tashi pls kada ka tafi, kada ka mutu ka bar ni, dan allah ka tashi, baby".
Kuka take ciki da tashin hankali,kowa na wajen sai da ya tausaya mata,asp abdallah ya matso ya dafata yace"calm down mana ikhlas baby ba zai tafi ya bar ki ba, ki mika shi a kula dashi".
Da kyar ta mika ma asp abdallah,hakan yasa ya amshi towel din ya cigaba da goge masa jiki.
Sosai zazzabin ya ragu hakan yasa ya sami barci, ikhlas zama tayi kusa dashi, hannun ta sarke da nashi, tana zubar da hawaye.
Iman tace"to tun da ya sami sauki ku zo mu koma wajen eve din",ikhlas ta kalle ta ta kauda kai tace"kuje ni baza ni ba".
Duka suka fice suka bar ta a zaune,fuskar shi ta shafa tana murmushi.
Can wajen amarya kuwa, lokacin da ango da sauran abokanan ango suka iso waje ya sake cakudewa,ganin babu ikhlas ba iman yasa ta janyo hannun feenert.
Kusa da kunnen ta ta matsa tace"ina cat eyes ne da iman? ",feenert tace"naji ance baby bashi da lafiya shi yasa suka tafi".
Mikewa hafsat tayi tana fadin"bari naje na duba shi",da sauri feenert da ango saifullahi suka maida ta zaune wanda har lokacin be gane ta ba.
Feenert tace"kada ki damu jikin da sauki",ba dan ta so ba ta zauna,saifullahi ya kalle ta yace"lafiya kuwa?, ina zaki je? ".
"Wallahi babyn cat eyes ne bashi da lafiya hakan yasa nake so naje naga jikin shi",hafsat ta bashi amsa fuskar ta dauke da damuwa.
Murmushi saifullahi yayi yace"ni na lura kina damuwa da wannan cat eyes din sama da kowa, anya bazan fara kishi da ita ba kuwa? ".
"Ai kuwa da kana da aiki, domin ina jin ta a jiki na kamar wata yar uwa ta ta jini,sannan kuma tayi mini komai a rayuwa wallahi".
"To ai ni ban taba ganin ta ba,kuma yanzu naji ina so na gan ta",hafsat ta bude baki zata yi magana ta fasa sakamakon mutane da suka fara isowa wajen su.
Haka aka tashi sister's evening ba tare da ikhlas ba,ana gamawa amarya hafsat tayi saurin nufar cikin gida duk mutanen dake mata magana basu dame ta ba.
Umma ta janyo hannun ta tace"haba hafsat kina ji ana miki magana kuma kina tafiya? ".
Fuska cike da damuwa tace"wallahi umma dan wata kawata ne wacce ta zo daga kano shine beda lafiya nake so na dubo shi".
Umma tace"ayya allah ya bashi lafiya, muje na dubo shi",tare suka jera har bakin kofar.
Hajiya hassana(maman amarya)ita ta riko umma tace"suwaiba zo muje wajen abban ammar(baban amarya) wai yana neman mu.
Umma ta kalli hafsat tace"ki shiga ciki,allah ya kara sauki, bari muje wajen mahaifin ki".
Da sauri suka wuce ita kuma hafsat ta shige ciki,a zaune ta sami ikhlas din kan kafar ta kuma baby ne tana bashi abinci.
Da sauri ta karasa tana taba jikin shi tace"ayya ya jikin kuwa, nama ji babu zafi sosai".
"Eh gaskiya zazzabin ya sauka yanzu, dazu jikin yafi zafi baki ji ba kamar wuta, kiyi hakuri ban yi attending eve din ba".
"Kada ki damu babu komai, ai lafiya tafi komai",suna zaune suma su iman suka shigo.
Washe gari, aka daura auren *SAIFULLAHI MUHAMMAD YUNUSA tare da amaryar shi *HAFSAT SA'EED YUNUSA* akan sadaki dubu dari uku da hamsin.
Duk inda ka kalla jama'a ne wa'inda suka halacci wannan bikin,sosai hayaniya da kuje da algaitu ke tashi.
Ango kuwa duk inda ya bi mutane ke bin shi, shi kuwa wurga idanu yake inda zai gano dan uwan shi.
Daddyn adamawa ne ya damki hannun shi ya ja shi har gaban mahaifin nashi, sosai ya ga farin ciki a fuskar mahaifin nashi, haka daddyn abuja wato mahaifin amarya.
Cikin gida kuwa ana daura aure, guda ta fara tashi, sosai kowa ke murna domin wannan hadin zumuncin.
Gefe daya kuwa umma ta goge hawayen daya zubo mata, domin bata da tabbacin ganin tata yarinyar, waya sani ko tana raye.
zaune ne suka fara shigowa cikin gida domin gaisawa da iyaye da kuma daukar hoto na domin tarihi.
Bangaren maleek kuwa yana daki yana tunanin abinda ba zai fishshe shi ba,sosai abin ke bashi mamaki na yadda ya damu da kuma yin kewar ta.
Number din ta wacce ya dauka a wayar dan uwan shi ranar nan ya kuma dannawa a karo na barkatai amma still har ta gama ringing ba'a daga ba.
Saifullahi ya shigo ya same shi a zaune da waya a hannu, yana faman tunani.
"Wai me kake tunani ne ka fito muje muyi hotuna",saifullahi ya fada yana riko hannun shi.
Tashi yayi ya bishi jiki a sanyaye,tun da suka fita ake faman hotuna, su da mummyn su da sauran yan uwa.
Su bintu da tuni sun saje da yan uwa sai daukar hotuna ake dasu.
Beelert tace"pls ku tashi mu tafi",ikhlas ta dube ta tace"ni dai babu inda zani".
"Baki isa ba, in dai baza ki je ba nima to babu inda zan je", hafsat ta fada.
Feenert tace"bari na fada wa ango", tare da beelert suka fice.
Kusa da ango suka je suka fada mishi,hajiya hassana tace"wannan wane kalar shirme ne haka, muje".
Zuwan hajiya hassana yasa dole ikhlas fitowa, duk da haka sai da taja gyale ta rufe rabin fuskar ta.
Suna isowa gaban shi, su hafeez da sadik suma suka karaso.
A hankali hafsat tace"amm,cat eyes ga angon wanda dama kece baki hadu dashi ba".
Kallon saifullahi tayi tace"yaya ga cat eyes dina",saifullahi kallon ta yake yi gaban shi na faduwa.
Jin kamar idanu akan ta yasa ta dago a hankali,a tare shi da maleek suka furta *PRINCESS*!.
Ja baya ta fara yi tana fadin"ba zai taba yiwuwa hakan ba, wannan mafarki ne".
Umma da tun fitowar su ta kafa mata idanu, tana tantanma a ran ta amma shigowar su sadik da kuma daga gyalen ta da tayi ya tabbatar mata yarinyar ta ce wannan.
Da sauri ta dafata tace" *IKHLAS DINA, ASHE KECE DAMA??*.
jin muryar wacce bata yi tsammani ba yasa ta waigo, zaro idanu tayi cikin rawar murya ta furta" *UMMA NA! *.
A tare suka zube kasa.............
*up team saifullahi*
To allah yaji k'an ku ikhlas da umma yasa aljanna ce makoma 😀.
Readers ku amsa da ameen fa! Kada ku manta dai........... *babyn abdul ce haka kuma maman farouk da elham*.
💮💮💮💮💮💮💮💮
*ASHE KECE???*💮💮💮💮
(Hypocrite-love-sacrifice)
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
✍✍✍✍✍✍✍
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION~*
✍✍✍✍✍✍✍
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
*written*
-by-
*Deeja one love*
*🏆JAKADIYAR GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION*🏆
*Dedicated*
-to-
*Maryam khamis*
61-62
Maleek da Sadik ne ke rige-rigen isa wajen ta,