Showing 1 words to 3000 words out of 45162 words

Chapter 1 - HATSABIBIN TSIBIRI Littafin Yaki Book Complete .pdf

Unknown   

25 Mar 2025

5207

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na
https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake
yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta
don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin
littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta
whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda
ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura
maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi
amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga
dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including
your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not
charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free,
any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending
novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our
site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or
TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[1/13, 12:05 AM] Mrsjmoon: HATSABIBIN TSIBIRI.
By Mrsjmoon.

Adabi Writer's Association (AWA)

https://arewabooks.com/book?id=63a2e3d8821822a8402d8eb1

(Hatsabibin tsibiri kagaggen labari ne, ba'ayi shi dan wani ko wata ba in anci karo da abinda ya
yi daidai da rayuwarka/ki alkalami ne ya zo da salon. Labarin zaiyi nutso ne cikin wata rayuwa
mai ban al'ajabi na matsafa tare da wata ƙasaitacciyar masarauta da magajinsu ya shigo da
salon da tun ginuwarta tayi hannun riga da lamarin. Duhu, Haske, Ƙarya,Gaskiya, Zalinci,
Tausayi, Halarci,Butulci, Sadaukarwa, son mulki bakin rai bakin fama gami da tasirin riƙo da
Addini duk na ƙunshe cikin tafiyar Mrsjmoon a cikin wannan labarin na Hatsabibin tsiri.

Ya Allah ka lamuncemin na rubuta abinda zai amfani al'umma. Allahumma Amin.

*Littafin baki dayansa sadaukarwa ce ga aminaina masu dubun karamci a gareni wato Khadija
Candy da Rahma Kabir, Allahu ya ja wannan zumunta har zuwa gidan Aljanna mu zamo
makwaftan juna Alfarman sayyidul sadati Manzon Allah S.A.W. Amin.*

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai, Allah ka karo dubun salatai marasa irga ga masoyinnan
naka, shugaban Halittu baki ɗaya abin alfaharin salihan bayi, jagoran mabudin alkhairai, Abul
Fad'imatul Zahra'u Sayyiduna Muhammadur Rasulullah S.A.W.

Page 01

Tekun Kabobo.

Teku ne mai faɗi da tsawo wanda ya ke cikin k'ungurmin dajin da ke yammacin Hatsabibin tsiri
kuma gabashi da Masarautan birnin Mungaye.

Ruwan Tekun na da abin al'ajabi domin da safe zuwa rana kalansa blue ne amma idan marece
ya shiga sai ya koma fari k'al wanda mai gani kan iya hango halittun da ke rayuwa a ƙasanshi
na shawagi dan k'asansa na dauke da halittun da ke rayuwa a ruwa nau'ika daban daban, kama
daga Kadoji, Kifaye da sauransu haka yashi da tsirrai koraye duk suna bayyana a fili ga duk
wanda ke iya kawo ziyara da yamamcin.

Duk wannan girma da Tekun ke da shi gami da yawan ni'ima ya zamo hange daga nesa ga
Fulani makiyaya domin basa iya isa gab'an shi balle tsautsayi ya kai dabbobinsu su shan
ruwansa, hasalima basa biyo hanyar sai bisa makuwa inda suna farga da dimuwan da sukayi
zasu sanja hanya tare da kare hanyar da dabbobin zasu isa zuwa gab'an Tekun domin jugewa
samun asara dan duk wanda ya yi kuren isar bisashensa bakin Tekun zasu afka ciki tamkar
waɗan da aka tura. Hatta da mafarauta ba kowa ke shiga dajin Tekun ya dawo lafiya ba sai in
har ya kai kwaro wurin tsafi tamkar irin tsirarun jama'ar Hatsabibin Tsibiri. Sai kusan shekaru
biyu da ya gabata Gimbiya Lina d'iya ga Sarki mai mulkin Hatsabiban Tsibiri ta maida Tekun
muhallinta shi ya janyo matsafan sukayi nesa da Tekun domin girmama muradin mafi soyuwar
Gimbiyarsu.

***
Guguwar iska ce ta turnik'e sararin samaniya dajin ya koma bak'ink'irin tamkar ruwan sama na
daf da sauka domin ba sautin da ke tashi sai gunjin fitar iska wanda guguwar ta ke kad'awa da
mugun k'arfi gami da tashin duk abin da taci karo da shi zuwa sararin samaniya, abin mamaki
har da ƙananun duwatsu iskan sama ta ke yi da su tamkar ledoji. Ƙara gami da rugugi kawai ke
tashi abinda ya haddasa rud'ewar tsun-tsayen da ke saman bishiyoyin da suka kewaye Tekun
soma neman wurin tsira.

A daidai wannan lokacin Gimbiya Lina na zaune a saman ruwan Tekun Kabobo ta hard'e
kafafunta saman kujera mai ruwan zuma tamkar ta hau saman dutse kamar yarda wurin da ta
ke zaunen ya nuna babu alamun ruwa mai motsi balle igiyarshi ya wuce da ita ta zamo abin
kalacin halittun ruwan.
Ga dai shi ruwan Tekun na tsiri gami da kumfa na gudu cikin murd'ewar igiyoyi sai dai kafin ya
iso inda ta ke zaune ya ke sanja hanya ya zagayeta ya nausa gaba inda ke isa tsakiyar Tekun
ya rufe dutsen da ke tsakiyarshi ruf zuwa wasu sakonni dutsen ya bayyana tamkar ruwan bai
tab'eshi ba.
Murmushi ta saki cike da nishad'in ganin yarda ruwan Tekun ke wasanninsa, jin rugugin ya ƙi
ƙararewa sai ta d'aga kai ta tsirawa sararin samaniyar ido na tsawon sekon goma sannan ta
sauke kallonta kan fatar jikinta da ya ke bud'e ba sutura sai walwali ya ke yi cikin d'aukan ido
tamkar jikin tarwad'a, sake kallon giragizan ta yi da suke k'ara yin duhu sai ta shafi fatar dantsen
hannunta na hagu tare da kallon halittan k'irjinta masu ban sha'awa da cika domin ita kanta in ta
kallesu suna burgeta saboda zubin da Allah ya yi musu na kyawu gami da jan hankalin duk
wanda ya yi arba da su. Shafosu ta yi da hannun dama idanunta lumshe sumar idanunta na
d'igar da ruwa na bin saman kuncinta. Girgiza kai ta yi sumar kanta ya yi tsiri sama ya fesar da
ruwa sannan ya dawo ya rufe mata fuska zuwa saman k'irjin, ta yaye sumar da hannunta na
hagu tare da sake kallon sararin samaniya a tak'aice ta kauda kai gefe cikin had'e fuska.

"Lima kenan, tabbas neman maganarki ya yi yawa, sam bakya son a zauna lafiya, kin addabi'a
al'umma tsibiri kin kuma hanani watayawa a can, to ai shi kenan mu zuba mugani, domin jiya ba
yau ba, Gimbiya Lina ta tumbatsa matuk'a, zata baki mamaki dan haka bari in nuna miki kaɗan
ya ke Gimbiyar da bata kai a ambata mata sunar ba."
Ta furta a hankali tare da jan tsaki mai sauti ta nuna guguwan da tafin hannunta wani haske ya
soma fita daga tsakiyar hannunta na nufar iskan, aikam tamkar kiftarwar ido sai ga sararin
samaniyar ya washe tangaras, ta sauke numfashi tare da share gumin da ya tsats-tsafo mata a
saman goshi sai ta mike a saman ruwar ta yi nutso cikin Tekun, kujerar da take zaune ya zama
walk'iya ya b'ace haka ruwan da ke sanja hanya a inda take zaune ya samu damar biyowa na
kai da kawon shi.

Bak'ar tsun-tsuwa ce mai yarfin ja a fuska-fuskanta ta baiyana gefen Tekun zuwa can ta bud'e

fuka-fukan ta soma shawagi a saman Tekun zuwa kimanin 'yan mintoci sai ta zama bak'in
hayak'i ta b'ace.

Gimbiya Lina da ta nutse cikin kogin sai da ta sami kimanin mintoci goma sha biyar sannan ta
taso sama ta soma tafiya tamkar tana taka turb'aya dan yarda k'ura ke bin bayan takalmi idan
ana tafiya a kan sa to haka ruwan ke tartsi na bin diga-digan Gimbiya Lina, wanda suke farare
sol tamkar yarda fatar jikinta ya ke.
Tafiya ta keyi tamkar wacce ke filin gasar sarauniyar kyau dan cikin k'asaita ta ke takun abin da
ya bawa mazaunanta da ke cikin siririn pant damar motsawa tamkar ba ita ce mamallakinsu ba
dubi da yarda take mara k'iba su kuma gasu da fad'i gami da cika tare da fitar da shape na
musanman tamkar wacce aka zana su a jikinta.
Ta yi tafiya har zuwa tsakiyar Tekun sannan ta tsaya jikin k'aton dutsen ta bud'e hannayenta
tamkar walk'iya ta rikid'a zuwa balbela fara sol ta tashi sama zuwa wani tsauni da ke kusa da
Tekun tana sauka ta yi girgiza ta dawo halittarta na Bil'adam ta yarfe yatsunta biyu saiga sutura
ya baiyana a jikinta cikin shigar doguwar rigan yadin karan miski fari da ratsin ja tare da
takalmin fata half cover mai launin Sarauta shima fari ta mik'a hannu jan gyale mai yarfin fari ya
baiyana saman tafin hannunta ta nad'e kanta da shi ya zauna d'as, ta sake mik'a hannu
kwalban turaren Company mai daraja mai suna LOST IN YOU ya baiyana ta fesa tare cilli da shi
sama ya b'ace wani kwalban turare fari sol tamkar ruwa ya bayyana ta kai bakinta ta b'alle
murfin ta kafa a bakinta ta shanye tas tare da cilli da kwalban ya zama walk'iya ya b'ace ta
had'a hannayenta wuri d'aya ta manna a saman goshinta tare da kulle ido tana wani surutai
saiga wata budurwa mai kama da ita sak tamkar an tsaga kara ta baiyana cikin shiga mai
kamanni da nata, suka tsirawa juna ido kowa da karatun da ruhinsa ke kitsawa masa.

Gimbiya Lina ce ta kawo k'arshen shirun da cewa "Ba kya jin magana ko Lima? Shin wai har sai
yaushe zan daina yi miki gargad'i akan shigomin yanki batare da neman izininta ba?"

"Baki isa ba Lina kuma bazaki tab'a isar ba, yankinki ko yankina? Ko kin manta ne in tuna miki?
Ni ce mai k'arfin iko sama da ke dan haka kada ki sake yimin tsaurin ido domin zan hukuntaki
tamkar uwar gijiya da baiwarta, dafatan kin tuna tazararmu da juna na sanin alkaliman sihiri."

"Oh rigimar na ki ta nan ya b'ullo? To zan barmiki nan amma ki sani duk ranar da kika k'ara
binciko inda na ke sai kin raina kanki domin yanzu ba da ba ne, na ga ba ya yi ga ba na baya
kam sai tsintar hula sannan ina baki shawara ki koyi yarda ake magana da shugaba kada ki
sami matsala nan ba da jimawa ba domin Gimbiya Lina ce gabanki sarauniyar Hatsabibin Tsibiri
lokaci kaɗan mai zuwa."

"Haka zalika nima Gimbiya Lima ce a gabanki wacce kowa na tsibiri ke tsoron karo da ita domin
bata san wargiba aiki da cika ne takenta ko da kuwa ga jininta ne sannan magajiyar karagar
Hatsabibin Tsibiri batare da wasi-wasi ba."

"Na yaro kyau take bata karko amma bari in barki ki gama cika bakin naki sai 'yar nanuniya ta
nuna shugaban wani a tsakaninmu ba da jimawa."

Dogon tsaki Lima ta ja tare da kaiwa kafadar Lina duka cikin cewa
"Ke dalla ni rufemin baki ki zauna ki sanarmin da inda kikayi b'atan dabo na tsawon shekara
d'aya da rabi, kika barni da jidalin rabuwa biyu duk in Abun ya nemi ganinmu a lokaci d'aya
domin bana son b'acin ranshi idan ya gano bakya Tsibiri zai iya sauke fushin a kaina."

"Binciken ki ya bayyana miki inda na je tunda bazaki fita sabgata ba kamar yarda ba ruwana da
naki sannan baruwana da fushin Abun dama Mah kika ce to na duba lamarin."

"Idan kin isa ki cire hijabin da kika sanya a tafiyar naki kisha kallon tonon silili kamar yarda na
tabbatar cikin jikinki da kika tafi da shi d'an kwanaki talatin da bakwai wanda kika b'oye
haihuwarsa kuma fushin Abun ya dad'e bai dameki ba idan kinso kice ba shi ne
makyen-kyashinki ba daga sama kika fad'o."
Jim Lina ta yi tana kallon 'yar uwarta zuwa can ta motsa labba ta ce "Lima sharrin da zakiyimin
kena, na Haihuwa? A she tsanar naki har ya kai haka? Ni ce fa Linar da ta tsani ak'idarki na
bilayi a gidan hutu, shin me yasa zaki jefeni da lamarin da kika san ban taɓa sha'awar aikatawa
ba?"
Kinfi kowa sanin ban iya sharri ba domin abin da nake da tabbacin shi na kanyi zantuka a kansu
sannan kin fi kowa sanin ina kan gaskiya, tabbas kin bar Tsibiri da ciki dan haka maza sanarmin
ko ranki ya b'aci, yanzu na aikaki gaban Abun ba sutura ki fuskanci hukunci."

"Zama bak'ar guguwar da kika zo a cikinsa ki b'acemin da gani ko in illataki sannan ki sani na
wuce gaban barazanarki, jiya ba yau ba ce Lima na sake sanar da ke wannan kalman kuma ki
saita harshenki kada ki fusatani na aikata miki abinda zai taɓa min domana ( rai)."

"Kome zakiyimin bazan kauce ba sai na san gaskiyan da kika b'oye kuma shi ne dalilin da yasa
na rufa miki asiri ban sanarwa Abun labarin bakya cikin Tsibiri ba domin ina son na soma
hukuntaki kafin ya yi miki
nashi."

"Saboda na zama karyan maza irinki ba, mara yiwa kanta amfani?"

"Lina in magana kike son faɗamin kin makaro domin kaf sirrikanki a tafin hannuna suke dan
haka ki biyoni mu koma tsibiri ko infasa kwai kowa ya san halin da kika kasance na yin cikin da
baida sahihin uba sannan da ƙarfi akayi miki kika b'oye wanda yayi saboda kina yiwa jama'a
bakin cikin samun ganimar jinin shi."
"Ko yanzu lokaci bai k'ure miki ba maza tafi ki tona asirin domin ban shirya komawa Tsibiri
yanzu ba ko wannan ganin da kikayimin wani dalili ya sanyani fitowa duniyar tsirrai dan haka

yanzu zan koma dausayin sanyi na cigaba da rayuwa tare da hallitun ruwa masu amana."

"Aikam kin gama komawa k'asan Tekun Kabobo Lina tunda ke ba aljanar ruwa bace haka ban
san ta inda kika haɗa dangi da 'yan ruwa ba."

Dariya Lina ta bushe da shi tare da zama a saman wata kujera mai haske da ta bayya gabanta
tamkar kiftarwar ido wanda haskenta ya kashewa Lima ido ta k'are da tafin hannunta tana ja
baya, hannu Lina ta kai ta rik'o hasken tamkar igiya haka ya shige tafin hannunta sannan Lima
ta samu damar dauke hannayenta daga saman fuskanta ta zubawa Lina ido wacce ke cin
kayan lambu da suka bayya gareta cikin wani container mai d'aukan ido shima.

"Lina banda tsafi da muka gada kin koma ruwa biyu ce?"

Bata amsa ba illa murmushi da take dokawa cikin jijjiga kai.

"Wani Aljani kika samu ya baki sa'a irin wannan? Ko shi ne wanda ya yi miki cikin?"

"Lima idan baki daina ambatar cikin nan ba zan sab'a miki."

"Zamu sab'awa juna dai Lina domin baki isa b'oyemin halin da kika fad'a ba kuma duk takunki
ban k'yaleki sai kinyimin bayanin inda kika b'oye ko rayuka su b'aci."

Kayan marmarin ta watso mata cikin fushi Lima ta yi sauri daga hannu suka tsaya cak batare da
sun iso inda ta ke ba haka basu sauka k'asa ba. Numfashi su sauke a tare sannan suka ja baya
ko wacce rai a haɗe zuwa can suka juya baya sannan suka juyo da makamai rik'e a hannunsu
cikin gaggawa ko wacce ta nufi 'yar uwanta da nufin halakawa. A ta ke k'azamin fad'a ya b'arke
tsakaninsu, guguwa ya turnik'e ya rufesu ruf baka ganin kowa cikinsu sai fitar sautin takubba
tare da walk'iyar hasken sukan da suke kaiwa juna. Bayan wucewar mintoci goma sha biyar
sautin ya d'auke gami da washewar guguwar, wurin ya koma babu su sama ko ƙasa.

Takun ingarman doki ne ya ratso saman tsaunin da ya sanya itatuwar tsaunin soma fad'uwa
ƙasa zuwa can wani gabjejen Sadauki ya bayya zaune a saman dokin ya iso ya tsaya a daidai
wurin da Lina ta zauna yana bud'e k'ofofin hansa sai kuma ya diro ya shafi dutsen gefen da ta
jingina da shi ya sunsuna ya soma waige-waige sai ya juya da hanzari sai ya kaiwa inda Lima ta
tsaya duka sauti ya fita dum! Ya ja tsaki sai kuma ya zabura ya hau saman dokinsa ya nausa
cikin tsaunin da mahaukacin gudu dokin na sakin haniniya wanda ya hargitsa k'ananun haluttun
tsun-tsaye.

***
Lima ce ta soma bayyana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login