Showing 15001 words to 18000 words out of 45162 words

Chapter 6 - HATSABIBIN TSIBIRI Littafin Yaki Book Complete .pdf

Unknown   

25 Mar 2025

6518

da ladabi.

"Ya Amintaccen Hadimina na fahimceka amma in kaga ban sanya Zoben nan ba to numfashina
na ne ya bar jikina sannan kada kayi kuskuren boyemin ganinsa domin na gano kana shirin
aikata hakan sannan ka sani son mulki a jinana yake dan ko da zan hau karaga da dak'ik'a
É—aya ne numfashina ya bar jikina sai na hau a sanya lissafin sunana cikin Sarakunan da suka
mulka Hatsabibin Tsibiri."

"Allah huci zuciyar Shugabata, nasara naki ce nabarki lafiya zan tafi hutu amma ki sani ban
shirya komawa ga Iyalaina ba."

"Sauka lafiya hadimin gaskiya, ka huta sosai bana tare da matsala."

Motsa kai yayi tare da komawa jemake ya fice daga kogon dutsen a guje.

Tsirawa hanyar da ya fice ido tayi zuwa can sai ta murmusa tare da cewa "Hadimi Tsidau mai
amana ne, kada ka yarda wani ya yi nasarar rabaka da halin kirkin nan."

Ta jima zaune tana hasko abinda ke taɓa mata zuciya wanda batajin zai bar ruhinta ya huta
domin a duk sadda ta kaÉ—ai ce lamarin ne k yae mamaye zuciyarta. Numfashi ta ja idanunta ya
kad'a ya koma jajur da sauri ta sunkuya ta tura hannu a cikin ruwan dake gangara, aikam take
duwatsun wurin suka b'ace sai wata kofa babba ta bude ruwa na tartsi daga cikinsa, ta fadawa
cikin ruwan kofar ta kulle duwatsun da suka b'ace suka dawo muhallinsu.

***
"Affuwan Shugabata ba zan taɓa tafiya na barci cikin tarin hatsari ba ina tare da ke bakin rai
bakin fama indai Zobe ne a jalinki ba zan taɓa bari ki sanyashi a yatsarki ba ko da kin
d'aukoshi."

Tsidau ya ambata bayan ya sauka a wani Tsibiri domin ganawan sirri da wani gawurtaccen
Ifiritun Bil'adam, shi É—in masanin warwaran lamura ne shi yasa ya taho gareshi duk da yasan
rashin imaninsa amma haka ya yi kasadan zuwa saboda bawa Lina kariya.

***
Lima na tura É—an sak'o dan ya nad'o mata abinda su Lina ke tattaunawa sai ta zarce gidan
shak'atawar jama'ar Tsibiri inda suke cin karensu ba babbaka tunda suna gudanar da lamarin
bisa son zuciyoyinsu ne shi yasa doka bata hawa kan Mazajen dake tayasu watsewar.

Tana shigowa hargowa da kid'an da ke tashi ya É—auke, hatta da wanda suka killace kansu suna
aikata shed'anci sai da suka yatsa cak, haka maja'ar wurin suka riƙa mik'o gaisuwa bata kula
kowa ba ta sami wuri na musamman ta zauna wanda tana shigowa aka tanadar mata, saida ta
É—auki tsawon mintoci goma da zama sannan ta bada umurnin a cigaba da abinda a keyi wato
kid'a da rawa tare da fasik'ancin da suke aikatawa a gaban kowa batare da alkunya ba domin
wurin daki É—aya ne a gefe wanda shima Lima ce ta bada umurnin gina mata tun sadda ta soma
kawo ziyara wurin dan more k'uruciyarta.

Wasu samari ne kyawawa guda biyu ba kaya jikinsu sai gajerun wando suka taho gabanta suka
zube, ta fesar da iska cikin Izza sannan ta yi masu nuni da kafad'arta suka tashi da hanzari
suka soma matsa mata zuwa hantsen hannayenta, sai miƙa take saki cikin 'lumshe idanu cike
da jaraba bajimawa wasu 'yan mata suma kyawawa suka zauna gabanta ta É—ora kafafunta a
saman cinyoyinsu suka soma matsawa suna ja mata yatsu ta tana lumshe ido cike da jin daÉ—in
yanayin abinda ya gusar mata da kaso mai yawa na damuwar da ta iso wurin da shi. Sun sami
kusan awa É—aya suna aikin yi mata tausa sannan ta dakatar da su ta mike zuwa dakin da yake
tilo a wurin samarin suka rufa mata baya suna masu zame gajerun wandunarsu tun kafin su
shiga d'akin yayin da 'yan matan kowa ta kama gabanta, sautin kid'a da ihun banza ya sake
hautsina wurin ganin Lima ta basu wuri su baje hajarsu son rai saboda duk wanda ke wurin a
buge ya ke domin antanadi giya na musamman domin nishad'i a wurin kowa zuwa yake ya sha
yarda ya so ba mai yi masa iyaka, sai hauka sukeyi suna shiga jikin juna tamkar dabbobi.

***
Abun kuwa duk abin da ya faru yana kallo a madubin tsafinsa illa shigar su Lina cikin kogon
dutsen ne lamarin ya b'oye masa sai halin da Lima ke ciki a wurin shak'atawa ya baiyana a
madubin, cikin fushi ya mike tsaye sannan akaran farko kunyar abin kunyar da Saurauniyar
Gobe keyi a gaban jama'ar da zata mulka ya k'ona masa rai, ya ja tsaki yafi sau shurin masak'i
a ƙarshe ya koma zaune ya tsirawa allon tsafinsa cike da burin son gano abinda Lina ke b'oye
masa musamman bayani akan Zoben sihiri. Hankalinsa ya kasu biyu ya rasa da wanne zai
soma.

"Hak'ik'a yanzu nafi ku son dauwama a karagar mulki Tsibiri, zan jajirce dan ganin nayi tsawon
rayuwa fiye da na Kaka Gunu yarda zanga mutuwarku batare da kunga nawa ba."

Ya furta cikin kaiwa wata batta duka a take ta fashe wani bakin ruwa ya malale ƙasa ya kai
hannu ya kwalfe ya shanye sai ga kamanninsa ya sauya sai ya bushe da dariya na kaiwa
k'irjinsa duka cike da gadara.

***
BIRNIN MUNGAYE.

Masarauta ce da ta kafu shekaru aru-aru wacce ta fara daga daji zuwa yanzu da take a
matsayin babbar birni mai yalwan al'umman Barebari, Fulani da Buzaye, su ne manyan yarukan
da suka kafa Masarautar domin Aliyu Malle da ya zamo tushen kafuwar Birnin babarbare ne, shi
ne ya soma yada zango a dajin saka makon matsin 'yan uba da suke son ganin bayanshi sai ya
baro garinsu ya dawo cikin dajin , ya cigaba da rayuwar kadaici, abokanansa su ne namun daji
inda ke farauto na halal ya samu abinci. Yana a wannan rayuwa ce wata raba ya haÉ—u da 'yar
Fulani da ta yi makuwa ya fitar da ita hanya daga nan fa ya sami wurin zuwa hira rigarsu har ya
zama tamkar d'an gida, suka shaƙu da Fulanin matuƙa inda in ya kwana biyu bai zo ba zasu
biyo sahun shi zuwa dajin Mungaye wanda a da yake gagaran su shiga kiwo saboda miyagun
namun dajin dake halakasu.

A hankali Fulanin suka soma yo hijira suna dawowa sansanin Aliyu Malle inda suka nadashi
Limaminsu domin shi ne silar musuluntarsu dan ya samesu kara zube ne basu san abin
bautawa da gaskiya ba. Zamowarshi mai tarin ilimin addini sai ya riƙa fad'akar da su a ilmance
har mafi akasarinsu suka amshi gaskiya, suka gane Allah subhanahu wata'ala É—aya ne tilo
baida abokin tarayya.

Momyn Haske ce🥰
[1/13, 12:05 AM] Mrsjmoon: HATSABIBIN TSIBIBI
By Mrsjmoon

AWA.

Page 07

"Is ok my son, stop crying, mun huce Allah ya tsare gaba."

Mai martaba ya ambata cikin taping bayarshi ammsa sai ya girgiza kai ya sake dank'e k'afar
Mamie Fulani yana sake fitar da sautin kukanshi tamkar ƙaramin yaro.

"My Fulani say something please, bana son jin sautin kukan nan."

Mai Martaba ya sake ambata cikin sigan rarrashi.

Itama girgiza kai tayi cikin b'oye fuskanta a lafayar da yazame daga kafadarta sakamakon jijjiga
k'afarta da Sadauki keyi wacce itama kukan takeyi cikin b'oye fitar saurinsa hakan yasa ta kasa

furta kalma.

A fusace mai martaba ya janyo Sadauki ya jefashi cikin k'irjinsa ya matse ya soma magana a
kausashe.
"Me ye haka Aliyu? Shin a haka kake son zama sarkin Mungaye? To maza ka dawo natsuwarka
bisa wannan sokanci dan baka gajeshi ga kowa ba, kai jarumi ne, Sadaukin babban Masarauta
irin Mungaye domin tun kana yaro ka ci sunar Sadaukantaka dan haka ganinka cikin wannan
raunin sunar zai iya b'atan dabo daga kanka zuwa wurin autar my Fulani Mu'allim."
Ya ƙarasa maganar cikin raha irin ta uba mai son farin cikin 'ya'yansa.

D'ago kanshi ya yi mai martaba ya jinjina masa kai sai ya maida yana mai goga tsinin hancinsa
a k'irjin mahaifin nasa cike da jin natsuwar ruhi domin alamun hucewa ne hakan da ya yi masa.

"Abba fushinku ne ke son mai dani ragon maza, dan Allah a gafarceni na tuba ba zan sake
maimaita kuren ba."

"Tuni ya wuce a gareni Aliyu domin ko wani bawa da kalan zanen ƙaddarar shi, to kai naka a
auri saki ya fad'o."

"Godiya na ke Abbana."

Ya ambata cikin sake kafewa a k'irjin Mai martaba."

"Sake ni kada ka kadawa My Fulani miji."

Da sauri Sadauki ya janye jikinsa yana murmushi cike da farin cikin sakewar da Mai Martaba ya
yi masa, ya dawo gaban Mamie ya langabe kai, tsare gira ta yi ya kalli mai Martaba cikin
alamun ya sa baki sai ya zunkud'a kafada tare da kauda kai gefe sai ya tura baki tare da maido
hankalinsa kan Mamie ya kamo hannunta ta janye cikin cewa "Kalli idon mai kuka kamar na É—an
yaye."

Murshi ya saki tare da saukewa bayan hannunta sumba ya furta "Nagode sosai Mamiena."

Shafo kansa tayi cike da kulawa, sai yaji malolon da ya tsaya masa a kak'oshi da faÉ—a ciki a fili
ya furta "Ya Rabbi Alhamdulillah."

Ya mik'e dan nufin ficewa Mamie tayi masa nuni da ya koma ya zauna, lankwashe ƙafafu ya yi
gami da tsira mata ido cikin neman sassauci, hancinsa ta ja ya saki numfashi tare da sake
narkewa zuwa kalan tausayi.

"Yallab'ai a kira mai rukiyya ayima yaronka domin lamarinsa yayi kama da mai shafan
shed'anun junnu."

"Aikam hakan za'ayi My Fulani domin nima mafarkaina na haskomin yana da Junnu."

"Wallahi bana da komi, ku yarda ina cikin azal ɗin ƙaddara ce."

Ya ambata cikin hanzari yana sake kama hannun Mamie Fulani.

"Babana ta ya zamu gamsu da hakan? Alhali ka bijirewa raya sunnar Manzon rahma, bayan
kaima ta nan ka zo duniya."

"Zanyi aure Mamie, wallahi zanyi, kudai cigaba da yimin addu'ar had'uwa da zab'in ruhina."

Had'a idanu Fulani da Mai martaba sukayi suka jingina kai domin hasashensu ya tabbata kenan
Sadauki bai son auren had'i kamar yarda suka ruk'a yi masa.

"Har zuwa yaushe zamu ga zab'in naka Babana?"

Shiru ya yi tsawon lokaci baida niyyar amsawa.

"Ok tashi ka tafi gobe da safe ka zo ina son ganinka nasan zuwa lokacin ka samo amsar
tambayar Fulani dan nima ina dakon jin lokacin bayyanar zab'in ruhin naka Aliyu."

Godiya ya yi masu tare da mikewa natse ya fice sai dai kallo É—aya zakayi masa ka hango jikinsa
a sanyaye ya ke. Karo sukayi da juna kowa ya dafe goshi inda suka bugu, suka zubawa juna
manyan idanunsu da suka gada wurin Mai martaba Sarki Abdul Hakam.

"Kai makahon inane da kake tafiya baka kallon gaba ka?"

Sardauna ya ambata cikin kaushin murya domin jin labarin zuwar Sadauki turakar mai martaba
ya daga hankalinsa dan burinsa su cigaba da fushi da shi abinda zai bashi damar hawa karagar
mulkin Mungaye hankali kwance domin ya gama cika sharudd'an zama Sarki tunda nada aure
da albarka auren wato haihuwa, yayin da Sadauki yake fanko a wannan fannin.
Rab'e shi Sadauki ya yi ya wuce batare da ya tanka masa ba domin tankawarshi naushi ne
lamarin da ke gujemawa faruwarsa dan in har ya sakawa Sardauna hannu sai ya suma wannan
lamarin ya samo asali ne tun suna yara duk in faÉ—a ya haÉ—asu to Sadauki sai ya sumar da
Sardauna da zarar ya kai mashi duka.
"Mara amfani mai auri saki kawai, mijin Aljana!."

Kalaman sun k'ona ran Sadauki amma duk da hakan bai sa ya waiwayo ba.

"Kai! ne mara amfani, wawa mai fuska biyu kawai."

"Kai! Imam ka taka a sannu ko in antayo k'anwarka gida a satin nan na angwance da mata huÉ—u
a lokaci É—aya."

"Wanda ya fasa antayota ya raina kanshi da mai dattin d'ankwalinsa."

"Umman kake zagi saboda baka da hankali?"

"Gaka nan babban mara hankali, gab'on banza mara amfani."

Sardauna ya nufo Imam a fusace shi kam ya gyara tsayuwa na jiran ya shigo shi ganin haka sai
Sardauna ya ja baya ya juya ya nufi sashin Umma na aiki bambamin faÉ—a. Dariya Imam ya
kwashe da shi ya furta "Matsoraci kawai kuma ka sani lusari irinka ba zai tab'a zama jagorar
babban Masarauta irin ta Mungaye ba."
Jiyowa ya yi cike da baƙin ciki aikam Imam ya yi masa gwalo sai ya watso masa dak'uwa, Imam
ya zabura kamar zai biyoshi, Sardauna ya kwasa da gudu ya b'ace. Dariya Imam ya sake
kwashe da shi har da tafawa, Sadauki dake hangen abin da ya faru shima murmushi ya yi yana
Allah wadai da sokancin d'an uwanshi Sardauna.
"Ga daishi a fuska da cikar zati kamar jarumi amma saidai ko wata macen tafishi k'wanjin iya
kare kai."

"Ka bari kawai Sarkin gobe, shi yasa na ke bak'in cikin bashi auren Khadija da akayi domin
tafishi komi na jarumta, ni dai Allah yasa kada yaransu suyi gadon mugun abu na zamowa
sokaye a cikin tsararrakinsu kamar yarda ubansu ya kasance."

Duka Sadauki ya kawo ma Imam cikin cewa "Baka da dama fa Brother."

"Uhm ba za ka gane haushin da nake ji ba ne na wannan had'in auren da akayi da sokon can."

"Kaganka da neman magana, nikam taho muje nayowa su Mamie siyayya."

"Da kyau mutumina bisa alamu an karb'i tubanka."

Murmushi kawai Sadauki ya yi mai nuni da bashi tabbacin hasashen shi, aikam cikin jin daÉ—i
Imam ya rungumeshi daga bisani ya sake shi suka jera zuwa inda ake ajiye motoci cikin
nishad'i.

Sai da suka hau kan titi sannan Sadauki ya kalli Imam cikin rashin wasa ya ce "Ya kamata zuwa
yanzu kai da Sardauna ku dawo natsuwarku kudaina abu kamar yara dan kun zama iyaye ko ba
ma haka ba sirukan juna kuke tunda kamar yarda ke auren k'anwarka haka kaima kake auren
k'anwarshi to Please Aminina kadaina biye masa kuna raba hali ka zamo tamkar ni yarda sam

baya gabana kome zaiyimin ban tankashi dan bai kai matsayin na tsaya b'ata lokaci da shi ba,
haka ka rik'a duba girman dangartakanku da juna na zamowa daga tsa-tso É—aya."

"Ok in sha Allah zan jaraba d'auke kai amma fa Aliyu ka sani yayanka baida tunani dazunfa
cemin yayi wai zai antayo Khadija gida ya angonce da mata huÉ—u rana É—aya."

Karya ya keyi domin na sami labarin ko Khadija hak'uri takeyi da ragwantarshi kawai ya ambata
ne dan ya b'ata maka rai kuma yayi nasarar hakan tunda gashi nan ka biye masa kunyi
shiririta."

"Kai Yarima yaushe ka sami labarin Sardauna rago ne a turaka?"

"Kai dai zauna nan ana batun arziki kana can kana shiririta."

"Ban son rainin hankali fa Sadauki, shin kai da ba mata ba gareka ba ta ina aka zauna tattauna
lamarin masu iyali da kai?"

"Zancen kake so na bar maka to."

"Allah baka isa ba sai ka fitar da ni duhu nan."

"To tafi ka tambayi Mamie gaskiyan zancen domin a bakinta naji in shima musamin zakayi to
bissimillah."

Idanu waye Imam ke kallon Sadauki yayin da shi kam ya tsare gira ya cigaba da tuk'insa hankali
kwance.

"Shin kana nufin ita Khadijan ta iya zuwa gaban Mamie da zancen bata gamsuwa da mijinta?"

"Kai kada fa ka dameni da zancen banza tam na kwanciya tam."

"Ai wallahi baka isa ba tunda ka takalo zance baka isa ka waskewa ba sai ka fed'emin biri har
wutsiya."

"Ai zaka iya shak'eni in na jiyo k'amshin barzahu na ambata maka gulman da kake son ji."

"Kaga malam dawo hankalinka ina saurarenka."

"Kaga Imam zan ci maka mutunci, sannan in kaima ragon ne ai sai ka sanarmin mu tafi neman
magani kafin matarka ta raina ka."

"Allah ya tsareni mugunji da gani."

"Ina tayaka murna da ka tsalle sharrin basir."

"Sadauki da magana a bakinka Please tell me."

Banza Sadauki ya yi masa har suka isa babban mall din dake dauke da tambarin Fulani store
wanda wurin ya zamo mallakin Mamie Fulani. Duk nacin Imam akan sanin gaskiyan labarin
Sadauki ya yi kunnen shegu da shi.

Suna shiga ya juyo ya aunama Imam mugun kallo a take ya tsuke bakinsa domin jinin sarautan
ya motsa kan dole ya yi mubaya'a duk da shima ba baya bane wurin nuna mulkin sai dai Toron
Giwa ya take na Rak'umi.

Turaruka masu tsada ya daukan musu kowa set huÉ—u sannan ya zarce wurin lafaya ya zab'ama
Mamie Fulani masu kyau kana ya dawo wurin takalma ya daukanma Mai martaba kalan na
sarakuna itama Fulani ya siya mata daga nan ya soma zab'ama k'anninsa duk abinda kowa ya
fi so suka fito tare da barin kayan a kai mashi gida. Yawo Sadauki yasomayi da su a birnin
baiko duba dare sakamakon birnin ya cika da hasken Soler ta ko ina, sannan duk inda suka
ratsa sai masoya sunyi masa kirarin da Sarkin Gobe mai Mungaye da yardan Allah, inda Imam
zai fito ya yi masu yayyafin kuÉ—i sannan su wuce, a k'arshe suka dawo Masarauta da misalin
k'arfe É—aya da rabi na dare, har bakin gidan Imam ya kaishi yaga shigarshi ciki sannan ya nufo
sashinsa cike da jin barci, a gajiye ya faÉ—a saman kushin yana maida numfashi zuwa can ya kai
hannu saman maranshi idanunsa lumshe yana yamutsa fuska dan hakan ya gujemawa shi yasa
ya yi ta gara-ranba da su har dare ya tsala a she a banza ya yi fitinar na nan mak'ale da shi,
tsaki ya ja yana mai tausayin kansa.

Tamkar ko yaushe ta bayyana cikin shigar daukan hankali ta zauna gabanshi tana jifarshi da
shu'umin murmushi. Motsawa ya yi ya tashi zaune da kyau ya tsira mata ido cike da buk'atuwar
ka sancewa da ita duk da a ƙasan ranshi baya maraba da lamarin amma gangar jikinsa ya kasa
bashi haÉ—in kai.
"Who are you?"

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login