Showing 21001 words to 24000 words out of 45162 words

Chapter 8 - HATSABIBIN TSIBIRI Littafin Yaki Book Complete .pdf

Unknown   

25 Mar 2025

5225

kai, ciwon baya, ciwon ƙafa, ciwon mara, kaikayin jiki dana
matse-matsi, yalwatuwar ni'ima tare da samun gamsuwa a turaka da sauransu, muna saida
É—aya ko sari mai so zai iya tuntubar number nan ta WhatsApp ko kira. 08132166848. Yarda ake
amfani da shi za a jik'a Lipton sai a d'iga man ayu a ciki a shanye da d'umi-d'umi za a iya zuba
zuma ko siga a ruwan Lipton d'in dan gudun d'aci haka za a iya zubawa a ruwan Tea a sha.
Masu asma da limoniya kuma zasu jajjaga tafarnuwa su matse ruwan su zuba ruwan d'umi da
man ayu su shanye. Masu Infection duk in suka wanke wurin da ruwan zafi sai su saka man ayu
haka masu kaikayin jiki idan sun fito wanka sai su shafa amma zasu sha da ruwan Lipton, Allah
ya ƙara mana lafiya Amin.*
[1/13, 12:05 AM] Mrsjmoon: HATSABIBIN TSIBIBI
By Mrsjmoon.

AWA.

Page 9.

Bata amsa ba ta cire wayar a kunninta ta mik'e da kyar tana rangaji cike da izzar mulki gami da
tarin damuwa.

Falo na musanman da suka saba sirri Umma tayiwa Mama Kilishi jagora suka zauna a saman
manyan kujerun alfarma da suka k'awata matdakaicin falon, bayan sun kulle k'ofa, Mama Kilishi
ta dubi Umma cikin son jin k'arin bayani domin ta zak'u taji abinda ke faruwa.

***
Sadauki

Motsawa ya keyi a saman lilon a hankali idanunsa lumshe, hannayensa zube saman goshinsa,
sanye yake cikin kayan motsa jiki sky-blue sun manne da farar fatar shi, iskan da ke busowa
daga bishiyon lambun ya taimaka wurin ƙara nutsawarshi cikin zurfin tunani, inda ya ke hango
kyaky-kyawar fuskanta da surarta tana jifarshi da shu'umin murmushin da ta saba amfani da shi

wurin birkita masa lissafi yaji kamar zai haukace a cikin buk'atuwa.

Daga nesa take hangoshi ta dauki mintoci biyar bata dauke idanunta akanshi ba zuwa can ta ja
siririn tsaki tare da watsa masa mugun harara wanda baisan tanayi ba, har ta zauna a inda ta
saba zama domin yin nazarin akan abinda ya shafi aikinta na kiyon lafiya sai kuma ta mik'e ta
nufo inda ya ke nan ma ta dauki mintoci uku tana kallonsa batare da ya sani ba, nazartowa da
tayi ya yi zurfi cikin tunani wanda tabbas zai iya zamowa barazana ga lafiyar yasa ta matsa
gabansa ta motsa yatsunta biyu suka bada sauti mai ƙara ya motsa cikin kamewa duk da ya
tsorata da jin sautin amma jarumta irin nasa ya hana tsoron baiyana a fuskanshi.

Kallo ɗaya yayi mata ya ɗauke kai tare da jan ƙaramin tsaki yana maijin tamkar ya rufeta da
duka saboda katse masa yanayin da ke ciki na shagaltuwa da kallon Aljana domin bad'ini da
zahiri sunar dake ambata mata kenan Aljana dan ta can-canci sunar dubi da yarda shi kaÉ—ai ke
iya ganinta.
Nuna halin ko ina kula da yayi mata ya tunzura Dr. Muneera inda ta yi nufin barin wurin cikin
zafin nama ya fizgota ta dawo gabanshi tamkar zata faÉ—a jikinsa ta yi nufin ja baya cikin
ambaton a'uziyya ya sake janyota gabansa yana auna mata harara.

Murmusawa ta yi domin ta gano abinda ya keson ji daga bakinta wato ban hak'uri dan zuwarta
wurin har ya zamo abin laifi.

"I'm sorry Yaya YS (Yarima Sadauki)."

Sakinta ya yi ya koma yarda ya ke ya cigaba da motsa lilon. Kasa tafiya Dr Neera tayi ta gyara
tsayuwa ta kafeshi da manyan idunta na gado domin zuri'ar Masarautan k'alilan ne basa da
manya idanu masu burgewa.

"Kina son ranki ya b'aci ko Doctor N?"

"No."

"To b'ace a wurin nan."

"Saboda me?"

BuÉ—e idanu yayi ta rausayar da kai ya tsare gira tare da cewa "Ina buk'atar kaÉ—aici, zaki iya
tafiya domin ban nemeki ba, shin ko nazo ganin likita ne?"

Bata amsa ba illa takowa da tayi ta zauna gefensa ta rike ƙarfen lilon da kyau saboda
zamowarka mai tsoron hawa Lilo tun tana ƙarama. Ta soma motsa lilon a hankali kamar yarda
ya keyi, sake lumshe ido Sadauki ya yi yana jin wani yanayi na ziyartanshi zamowar kusancin
da sukayi da juna dan jikinta na gogan dantsen hannunsa da ya ke abude ga kuma k'amshin

turarenta mai tada hankali da ya fahimci ya kame jikinta.

"Yaya YS ka natsu ka san cewa rayuwarka ba kai kaÉ—ai take amfanarwa ba har da dubban
jama'a daga cikin Masarauta zuwa wajenta dan haka ka kori damuwa ka maye gurbinta da
nishad'i sannan ka k'ok'arta wurin cikawa su Mai martaba burinsu na zama da mata bisa igiyar
aure mai tsauri kada ka sake aikata laifin da ka aikata a baya domin hakan zai taimaka ka
samawa su Mamie sanyin idaniyarsu kafin ƙasa ya rufe idanuwarsu wato abin cikin kwai."

Shiru ta yi tana murmushi cike da tsokana, ganin baida niyyar magana saita sauka akan lilon ta
yi dan taku biyu zuwa uku sannan ta juya ta fuskanceshi duk da tana da tabbacin ba kallonta ya
keyi ba ta ce "Karfin sha'awarka na son kaiwa matakin da zaka kasa mallakan kanka har sai ka
fitar da shi wanda bana fatar ka haik'ewa kuyangi ko k'adangarun bariki ka goga mana bak'in
fenti, laifin da bamusan yarda aka aikatashi ba ya bibiyemu mu shiga uku."

Tar ya buÉ—e idanunsa amma sai ya ci karo da bayanta domin tana gama ambata ta juya ta nufi
wurin zamanta da sar-sarfa. Bai daina kallon bayanta ba har saida yaga ta zauna tana shirin
d'agowa sai ya maida idanunsa lumshe amma yana hangota dishi-dishi.

"Miskili kafi mahaukaci ban haushi, ai na gamu da wahala kam."

Ta ambata a saman lips dinta.

"Amma me ye damuwarshi? Yana da lafiya irin haka ya ke sakin matarshi sannan duk ba wacce
ya aikata sunna da ita, kai anya ba Aljana ta aureshi ba? A'a Wanda Aljana ta aura baya jin
feeling kamar yarda yaya YS ke ji, wallahi da lauje cikin nad'i a game da rayuwarsa, shin ta ina
zan san bakin zaren?
Murmusawa ta yi tare da murza goshinta ta furta wata kalma a can k'asan mak'oshinta wanda
ita kaÉ—ai taji kayanta.

***
"Ina jin damuwa da lamura ki Dr. Muneera tun kuwa baki san kanki ba."

Sadauki ya furta a hankali yana mai jin yanayin da ke ciki na ƙara tsananta gare shi. Sauka ya
yi ya nufi k'oramar da ke ƙarshen lambun ya shiga ya nutse cikin ruwan tsawon mintoci biyar
sannan ya taso yana girgiza sumarsa ruwa na tartsi,ya sake komawa ƙasan ruwan wannan
karan ya shafi mintoci ashirin sannan ya d'ago rik'e da kan narkeken kifi yana zile-zillen son
kufcewa. Bakin k'oramar ya fito ya zauna saman kujerar roba ya tsirawa cikin ruwan ido abin
mamaki ita ce take nink'aya cikin sutura masu bayyana halittanta fili, ware idanu yayi tare da
sakin kifin ya koma cikin ruwa aikam ta cafeshi ta cillo masa ya fad'o jikinsa lamarin da ya shi
sakin siririn ƙara cikin fitar sauti saboda ya dukar masa cinya da ya yi, aikam ƙaran sai a kunnin
Neera ta nufo hanyar da zai sadata da wurin a guje, jin takunta yasa Sadauki komawa ruwan
tare da kifin domin baya son ta ganshi a yanayin bayyanar halittunsa fili dan shiga ruwar da yayi

ya sanya kayan sun mamme a jikinsa surarsa ya fito fili.

Zama tayi ta kafe ruwan da ido tana mamakin yarda ke iya jimawa a ƙasan ruwa kuma yafito
lafiyalau. Takalmansa ta dauka tana juyawa dan ta soma gajiya da zaman jiran fitowar na shi.
Ruwan ya motsa da ƙarfi, ta kalli cikin k'oramar gami da ware ido saboda hango k'atuwar Kada
na shawagi alhalin ta san babu ko kadangare a cikin tsafta-tacciyar k'oramar, murmushi ta yi
tare da jifarta da takalmin hannunta aikam take ta ɓace.

Tafi ta yi tana furta "Haba yaya YS ba twins yayan gambo zaka gwadawa Ofi ba balle ka bani
tsoro, wallah sai dai ni na baka tsoro da macizai."

Tana rufe baki babban kifin nan ta fado kusa da ƙafarta ta daka tsalle tare da kwalla ihu, kafin
kobo ta bar wurin a guje domin Allah ya jarabceta da tsoron manyan kifaye shiya ko su Lailah
na kallon chennel É—insu bata zama a wurin.

Fitowa ya yi yana murmushi ya zauna saman dutsen gefen k'oramar na sharce ruwan gashin
kansa.

"Doctor Muneerat manya aida kin tsaya kin nunamin ke 'yan biyu ce da ni kuwa na gwada miki
Gambo sha gaban 'yan biyu ne a Ofi."

Ya jima zaune a bakin k'oramar yana wasa da kifin inda ke kiranshi sai ya taho a juye idan zai
kashi sai ya zille ya daka tsalle ya koma ruwa inda zai watso a fuskanshi, da ya gaji ya dawo
saman kujera ya zauna ya daga kai sama yana kallon tsuntsaye da ke ta shawagi a saman
bishiyar mango zuwa lokacin har kayan jikinsa sun bushe sakamakon iskan da ke kad'awa,
yana ta mamakin yarda akayi Aljanan ke son yi masa wasa da hankali. Kiran sallar a Zuhur
yasa ya mik'e ya nufi filin motsa jiki ya É—auki jallabiyasa ya saka ya fito cikin takun k'asaida
wanda ke ƙara fito da kwarjininsa a fili. Bayan an fito sallah suka hadu da Imam suka nufi cikin
Masarauta gidan su Imam suka nufa suna shiga Neera na fitowa da gudu Maryam biye da ita,
tsak suka tsaya kafin Neera ta yi magana Sadauki ya tareta cikin cewa "Kun girma ba kusan
kun girma ba to aure za'ayi muku ku tafi can suyi ta haukan da mazajenku."

"Aikam da ka kyauta mana dan naga kamar an manta da mu ne gashi mun balaga da jimawa."

Kallon Neera ya yi idanu waje yana lek'en bayanta sai yaga bakowa a wurin sai shi da ita dan
Imam wucewa ya yi ciki.

"Kin rainani ko?"

"A'a kawai banji daÉ—in kalman haukan da ka kiramu da shi bane kuma ina son magana da kai."

"Banda lokaci."

"Zakayi ne idan ciwonka ya sha k'arfinka."

"Neerah!"

Ya ambata da sauti.

"Yaya YS me nayi kuma?"

Ta furta a shagwab'e.

Sauke numfashi ya yi ganin Momy ta fito ya russuna ya gaisheta tare da juyawa ya fice.

"Muneera me yasa kika raina Sadauki ne?"

"Momy wallahi ban rainashi ba."

"Shi ne zai ambaci sunarki cikin fushi."

Sosa tsinin hancinta ta yi ta furta "Mahaukaciya ya cemin na ce masa aljanin ruwa domin
wallahi d'azun a Garding ya dauki kusan awa É—aya a cikin ruwa bai fito ba kuma har da bani
tsoro ya yi."

Girgiza kai Momy ta yi tana murmushi, bayanta Neera tabi tana cewa "Hajiya Momy bani
sakwarar in kaiwa Ammina."

"Ita dama zan haÉ—a miki da kaina dan nasan Hajiya Safiyya tunda ta ce inyi mata kowa ya saka
hannu zata iya ganewa na k'i ci."

"Ai Momy lamarin Ammie mamaki ke bani ita ba twins ba amma tafi twins tsirfa da gano abin da
aka b'oye mata."

"K'ila ke da Sadauki kuka sammata Ofi."

"Nikam Momy ban da komi sai dai ko shi."

"Baki da shi kike hukunta duk wanda ya dukeki da macizai sadda kuke yara?"

"To ai Momy lokacin muna yara ne yanzu kuwa girma ya zo dole na watsar da shiriritan nan."

"Uhm Allah yasa haka ne kuma ki rage biyewa Sadauki dan tsaf Hajiya Safiyya zata hukunta ki
inta gano kin raina mata shalele."

"Uhm nikam Momy ban raina shi ba kawai ina son ganin yana magana ne kamar kowa sam ban

son ganinsa cikin shiru domin yin maganar zai taimaka wurin rage masa damuwa."

"Shi ya sanar miki yana cikin damuwa?"

"A'a Momy amma a kallo É—aya zakayima yaya YS ka gano na tare da damuwa duk da b'oyewar
da ya keyi."

"Oh ni Hauwa kulu ina ganin wani salo a wurin Likita alhalin ita ba karatun sanin halayyan d'an
Adam ta yi ba."

"Kai Momy, kawai damuwana da lamuransa ne yasa nake saurin ganowa in har yana cikin
yanayi mara daÉ—i."

Dariyar da Momy ta sanya ne yasa Neera sunkuyar da kai ƙasa, sai kuma ta juya ta fice da
sauri.

"Ja'ira bisa alamu iska na wahalar da mai kayan kara."

Momy ta furta tana jinjina kai fuskanta É—auke da murmushi.

Suna hira da Maryam Momy ta fito da kwando da sauri Neerah ta mik'e ta amsa tana mai furta
"Allah ya rubu ce Momy."

"Amin Doctor."

Har Neera ta kai bakin k'ofar falo ta tsinkayi magana Momy inda take kiranta tazo suyi lunch.

"Momy zan shiga Asibiti nan da awa É—aya amma a haÉ—a dinner da ni dan anan zan kwana
saboda haka Maryam ki dafamin abinda na fi so dafatan kin gane."

" 'Yar rainin hankali sai dai ki kwana da yunwa domin jirgi É—aya ya kwasomu kinfi kowa sani ba
son shiga kitcken nakeyi ba"

"Kinji Momyna ki dafamin abu mai daÉ—i kuma Allah ba wanda zaici."

"Ko yaya Saudauki ne?"

Maryam ta ambata tana kallon idanun Neerah.

Ficewa falon ta yi da sauri Maryam ta kwashe da dariya, Momy ta yi mata dak'uwa ta gintse
dariyar.

"Aikam gara da kika ambata mata haka yaya Maryam domin daga ke sai shi Yaya Neera ke

sakemawa in ancire mahaifanmu nasha jin ana gulmanta domin har 'yar k'waya naji ana ambata
mata."

"Ke Baby Nanah ban son k'arya."

"Allah kuwa yaya Maryam, naji yaya Sardauna na faÉ—awa abokinsa wai k'waya yaya Neerah
take sha shi yasa bata ganin kowa da gashi dan kawai ta dawo a gajiya ta wucesu yana yi mata
magana bata kulashi ba sai hannu ta d'aga mashi."

"Autana taho muci abinci kuma ban son na sake jin kin bada wannan labarin gudun haÉ—a fitina."

"To Momy amma dai zan sanar da yaya Neera saboda ta dauki mataki kada jama'a su soma yi
mata wak'ar 'yar maye."

"Autana kada ki sanar da ita sannan 'yar k'waya da Sardauna ya ambatawa Muneera ba nufinsa
tana shaye-shaye ba, nufinsa tafiye rashin son magana da kuma takawa ko waye burki in ya
tab'ota."

"Oh Momy na gane yanzu amma ba kowa ne zai fahimci haka ba."

"Haka ne kam Autana mai kaifin basira."

Murmushi Nana ta yi cike da jin daÉ—in yabon da a kayi mata alhalin kashe bakin bada labarin
Momy tayi zamowarta mai gudun fitina.

Bayan sun gana cin abinci Momy ta kira Maryam suka shiga bedroom d'inta ta dubeta ta ce "Me
ke tsakanin Muneera d Sadauki?"

"Wallahi ban sani ba."

"Ban son wasa Maryam sanar da ni abinda na ke zargi."

"Momy a gaskiya Neera na son yaya Sadauki tun kafin ya soma auri saki karatun da takeyi yasa
bata nuna masa alamu ba har zuwa yanzu tana son shi duk da hatsarin da ke cikin aurensa
baisa ta sadduda ba sai dai in banda ni ba wanda ya sani hatta kuwa Lailah da Zuhrah ba
wanda ya gano k'aunarta gareshi jama'a na ɗauka ƙarfin zumuntar da ke tsakanin su ne ya
janyo suke shiri da juna dan kema sheda ce kaf 'yan matan Masarauta ba wanda yaya Sadauki
ke sakewa fuska har ta gaya masa maganar da taga dama sai Neerah."

Numfashi Momy ta ja tare da cewa "Zanso Sadauki ya furta yana sonta."

"Saboda ne Momy?"

"Saboda duk wanda ya aura ya saki haÉ—a su akayi wata k'ila nuna ra'ayinsa akan auren wacce
ya ke so zai kawo ƙarshen auri sakin."

"Momy yaya Sadauki na da matsala a fara neman masa magani kafin a sake yi mashi aure."

"Kema kinyi magana anan domin muna tattauna maganar neman masa magani da Mamie
Fulani "

"Yawwa hakan dai yafi."

Sai abu na gaba shi ne maganar fitar da miji, shin wa kika tsayar cikin namemanki?."

"Miji fa Momy?"

"Eh Dadynku ya umurceni da in tambayeki saboda ya daina yarda da auren had'i sannan Mai
martaba ya soke auren had'i amma in kun haÉ—a kanku ba ruwansu zasu sanya albarka."

"Momy wani abu na faruwa ne wanda bamu sani ba har akan ya faru?"

"Ko É—aya kawai Mai martaba ne da kansa kwanaki ya tarasu ya sanar da su soke auren had'i
amma ina jin bai rasa nasaba da abin kunyar da Sadauki keyi na sakin matar da ake bashi."

"Momy bana da gwani saboda ina tsoron abin da ya sami yaya Khadijah ya sameni domin har
yau tana begen Mahmud bayarda zatayi ne dole ta karb'i yaya Sardauna duk kuwa da yana kan
cutar da ita."

"Ban tambayeki wannan labarin ba sannan tunda baki da gwani sai Dadynku ya zab'a miki ko
cikin dogarai ne."

"Momy dogarai kuma?"

"Eh tunda na zama abokiyar wasanki ba."

"Sorry Mum zamuyi shawara da su Neera."

"Ke dai kika sani kuma ina baki shawara da kiyi nazari banda biyewa shawarar zuciya wanda ke
haifar da dana sani."

Ganin ta faÉ—a tunani Momy ta fice daga d'akin cikin yi mata addu'ar samun k'warin zuciya akan
duk abinda ta sanya a gaba.

Maryam ta kwanta a saman gado, matsanancin damuwa kwance a fuskanta.

"Yaya Sadauki."

Ta furta a saman lips d'inta tana mai lumshe ido tare da nazarin kalaman Momy na ƙarshe.
Zuwa can ta zabura tamkar wacce a sokawa Allura ta fito, ganin ba kowa a falon sai ta dauki
hijabin sallah ta fice da sauri, Hadiman da ke kai kawo a tsakanin sassan Masarautar suka
soma jero mata gaisuwa amma ba wanda ta sami zarafin amsawa.
Momyn Haske ce 🥰

*Muna saida ingantaccen man ayu wanda ya zo daga Chad. Yana maganin Infection, asma,
limoniya, mura, ciwon basira ciwon kai, ciwon baya, ciwon ƙafa, ciwon mara, kaikayin jiki dana
matse-matsi, yalwatuwar ni'ima tare da samun gamsuwa a turaka da sauransu, muna saida
É—aya ko sari

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login