Showing 3001 words to 6000 words out of 45162 words

Chapter 2 - HATSABIBIN TSIBIRI Littafin Yaki Book Complete .pdf

Unknown   

25 Mar 2025

6511

jini na zuba a gefen kanta zuwa can itama Lina ta bayya dafe da
kafad'arta jini na bin hannunta, a tare suka kalli juna ko wacce ta shafi inda taji ciwo a take ya
koma babu alamun rauni suka sake kallon juna ko wacce taja tsaki tare da sauyawa zuwa
halittar tsun-tsaye suka sula sararin samaniya.

Lina ta nufi kudu, Lima ta nufi yamma sai dai bayan wucewar mintoci uku Lima ta dawo saman
tsaunin ta talli wata bishiya take ta tsage ta rabe biyu, ta bushe da dariya cikin cewa "Na san
zaki dawo wurin nan Lina ni kuma na yi alk'awarin gano sirrinki tare da gano uban da yayi miki
ciki kika b'oye bayyanarshi balle Kadojin kogin sihiri su sami abin kalaci kud'in shigar Tsibiri ya
bunk'asa dan ina jiyowa da karfi ya ketaki sannan na yi alk'awarin bawa Kadoji jinin wannan
mutumin domin barinsa a raye barazana ce ga lafiyar tsibirinmu mai dogon tarihi da ya barranta
ga haik'ewa mata da ƙarfi."

Tana ambatar hakan ta yi girgiza ta dawo yarinya karama cikin takun hawainiya ta isa gaban
bishiyar da ta tsage ta shige ta koma ta kulle tamkar wani abu bai faru ba.

Daga can saman girgije Lina ta huro iskan bakinta zuwa kan bishiyar take kuwa ta b'ace b'at
sannan ta sakko ta tsaya tare da kama k'ugu ta ce "Ni walkice daidai k'ugun kowa Lima, ki farka
barci lafiya tare da mance kin ganni a zahiri domin nuna miki na wuce da saninki, yanzu ba da
ba ce da kike shugabana a sanin alk'aluman sirihi da mugunta, ni yanzu shugabar kowa da ke
HATSABIBIN TSIBIBI ne hatta kuwa da mahaifanmu nasha gabansu balle wancan basamuden
banzan Buda wanda ke kan wahalar da kanshi, burina na daf da cika domin ba da jimawa ba
zan kawo sauyi a tsibirinmu, Gimbiya Lina nan ta fe gareku ya ku jama'ar Hatsabibin tsibiri da
samuwar cikar 'yancin da kuke burin wanzuwar shi."

Tana ambatar haka ta lula cikin girgije tamkar walk'iya bata sauka a ko ina ba sai saman Tekun
Kabobo.

"Lina!"

Sautin kiran sunarta ya karad'e yankin bata waiwayo ba saboda ta gano muryan mai kiran nata
sai kawai ta yi girgiza ta zama babban kifi ta yi nutso cikin Tekun daga can saman tsaunin Buda
ya zaburi sihirtacce dokinsa ya daka tsalle zuwa cikin Tekun wanda yana fad'awa ruwan Tekun
ya sanja kala zuwa launin yellow a maimakon fari k'al. Faruwar haka da seconds halittun cikin
Tekun irin kifaye da kadoji suka soma fitowa suna yada zango a gefen Tekun wasu kuma na
tseren hawa saman dutsen da ke tsakiyar Tekun.

A take kuwa Ruwan Tekun ya soma maik'o yana taruwa wuri d'aya tare da yin tsiri na feshi
zuwa jikin bishiyoyin da ke kewaye da shi.

Mrsjmoon ce.

Ku daure ku buɗe Arewabooks👇

*YADDA AKE BUÆŠE ACCOUNT A AREWABOOKS*

Bayan kaje play store ka É—akko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form É—in kamar haka: -

*Enter your name:* (Cikakken sunanki)

*Enter your mail:* (Email É—inki)

*Enter an username* (Sunanki)

*Enter your password:* ( misali 12341234)

*Confirm password:* (misali 12341234)

Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks.

*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google
za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

*Register* - Shine cike form domin buÉ—e account a ArewaBooks.
[1/13, 12:05 AM] Mrsjmoon: HATSABIBIN TSIBIBI
BY MRSJMOON

ADABI WRITER'S ASSOCIATION.
https://arewabooks.com/book?id=63a2e3d8821822a8402d8eb1 Follow me on Arewabooks.🖕

*Shafin sadaukarwa ce ga kafatanin member na Adabi Writer's Association (AWA) Allah ya ƙara
dankon kauna mara algus, Amin.*

Page 02

Juyi Lima ta yi cike da jin daÉ—in barcin sai ta jita a k'asa tim! daga saman gadon da ya ke da
wani launi na daban da sauran gadajen da jama'a suka saba gani. A razane ta tashi zaune tana
sosa bayanta cikin son tuno abin da ya faru amma ta kasa kamo komi tsaki taja ta dubi bangon
d'akin tare da hura iskan bakinta sai ga Lina ta bayyana tana zabga murmushi yamutsa fuska ta
yi tare da mik'ewa ta ja hannunta tana cewa "Nagaji da wannan wahalar narantse duk inda kike
sai na nemoki domin hakan ya tauyemin jin dad'in rayuwata na tabbata Lina kin aikata min
hakan ne dan murgunamin tare da hanani fita holewata amma duk ranar da na yi ido biyu da ke
bazakiji da daÉ—i ba."

Duk yarda taso jin basaja fushin da ke fuskanta ya koma irin murmushi fuskan fake Lina ta kasa
saboda yau ta fusata sama da kullum, ga shi Abun bai nemeta ba taji son zuwa gareshi. Wani
tsakin ta kuma ja tana dokawa dake Lima harara ita kam sai murmushi dake dokawa abinta.

"Wallahi ba dan rabi ruhina da ke nanne jikinki ba da yau na kasheki na huta."

Gurnani tajiyo a bayanta ta juyo cike da masifa amma bataga komi sai sake jan tsaki zuciyarta
na ƙara shiga ƙunci.

Fadar mahaifinsu ta nufa kai tsaye, tana shiga fadawan suka soma mik'o gaisuwa cike da tsoro
ba wanda ta kula ganin haka suka watse aka barta da mai Tsibiri. Ta iso ta sunkuya gabanshi ya
mik'a hannu zai dafata ta tashi da sauri tana dariya fake Lina da ke bayanta duk'e itama ta tashi
tana dariyar girgiza kai Dattijon ya yi tare da kaiwa wani tulu duka a ta ke dake Lina ta nufi jikin
Lima ta shige suka zama a bu d'aya, ya kalleta ta sunkuyar da kai ya nuna mata hanyar fita
cikin fushi sai ta iso gabanshi ta zauna tare da kamo hannunshi.

"Kada kice komi Lima na jima da gano Lina bata wannan tsibirin sai dai tsawon lokacin na kasa
gano inda ta b'oye duk da bincikena yana nunamin tana rayuwa cikin walwala da 'yanci amma
na kasa samun natsuwar ruhi akan inda ta ke da dalilin aikata mana wannan munafuncin
sannan ina hango wani haske mai son maidani makaho a tare da ita amma a yau Buda ya gano
mab'oyarta a k'asan Tekun Kabobo kamar yarda bincike ya bayyanarmin mintoci biyu kafin
shigowarki, yanzu haka ina dakon isowarsu ne duk da ina shakkar isowar sa tare da ita."

"Saboda me Abun kake shakka?"

"Lina ta soma bani tsoro da gaske ba wasi-wasi."

"Abun me ya razanaka da ita haka, alhalin ko tsun-tsun Tsibiri bata iya kamawa saboda
sokancinta da rashin amfani?"

"Kayya Lima, ki bi a sannu domin wannan sabuwar Lina ce mai cike da sadaukantaka ta
fannoni da dama haka bincikena ya haskomi halin nan nata na tausayi shi ne zaiyi sanadin
kawo k'arshen Hatsabibin Tsibiri mai dogon tarihi domin ba'a gina shi dan adalci da tausayi ga
bak'i ba amma ita ce ta farko da zata shigo mana da sauyin da dole mu amsa kamar yarda taso
yin nasara a baya."

"Ta ina hakan zai sake faru Abun?"

"Ban sani ba Lima amma ina lalibo hakan a lokuta da dama tun kuwa kuna tsumman goyo shi
Kaka Gunu ya keb'eki ya rik'a nuna miki sanin ilimin tsafi fiye da ita ya kuma raini ruhinki da
rashin tausayi wanda kika rik'a wahalar da ita mahaifiyarku na yi miki kashedi kina watsi da
kamarin saidai a yau na hango alamun ta samo sanin alk'aluman tsafi fiye da wanda kike tare
da shi dan na kalli artabunku na d'azun duk da ta yi dubarar b'oyewa cikin iskan guguwa dan ta
san zan gani sai amma ta makaro dan komi ya bayyana gareni tamkar kuna gabana."

"Abun dama ba mafarki na yi na had'u da Lina ba har muka goge raini?"

"Eh ba mafarki ba ne, tabbaas kin had'u da Lina wanda hakan ya bawa Buda damar gano inda
ta ke ta bayan b'atan dabon da ta yi na tsawon shekara d'aya da watanni ta hanyar jiyo

k'amshinta wanda ta nan mafi akasarin jama'ar Tsibiri ke ganeku.."

"Abun me kake son sanar dani akan 'yar uwata Lina?"

"Babu komi 'yata illa hatsarin da Lina zata zame mana musanman ke domin zuciyarta ya ginu
da tausayi ne ya yin da na ki ya ginu da tsabar mugunta, Kaka Gunu ya sanarmin d'abi'unki na
kamanni da kakan-kakanninmu wanda shi ne silar samuwar Tsibirin nan wato Sarki Goma na
farko."
"Abun rabani da wannan zantukar gaibun na Kaka Gunu yanzu babban damuwata shi ne sanin
gaskiyan abin da Lina ke b'oyewa."

"Nafiki son gano lamarin da ta birne wanda bokayenmu suka kasa gano shi hatta kuwa da ni
sarkinsu kuma jagorar wannan tsibiri."

"Abun, shin yanzu Lina tafika k'arfin tsafi kenan?"

"Bata isa ba Lima."

"To meye yasa ka kasa gyara Mata zama?"

"Har abada bazan tab'a fito na fito da ita ba saboda ina son 'yata haka itama bazata tab'a yin
gaba da gaba da ni ba domin girman da ta ke ganina da shi ya wuce tunaninki tana kawai nuna
miki tafi damuwa da mahaifiyarku ce kamar yarda kika fi nuna damuwa da ni sannan zan baki
aiki wanda na san akanshi kike wato na son gano lamarin Lima baki dayanshi na tsawon tafiyar
da ta yi."

"Ina saurarenka Abun."

" 'Yata Lima a yanzu nake son ki shiga bukkan Kaka Gunu kiyi wannan binciken."

"Abun yau da kanka ka amince in shiga taskan sirrin Kaka Gunu wanda ya ke kulle tun bayan
mutuwarshi?"

"Eh na baki damar shiga ya ke 'yata, dama can gadonki ne dan ya tabbatar min ke kad'ai ya
mincewa shiga bukkar amma bisa babban bincike shi yasa na baki umurnin shiga dan gano
mana abin da Lina ta b'oye da kuma wanda ya koyar da ita dabarun ilimin sihirin da ya ke son
doke wanda muka gada Kaka da kakanni."
"To Abun kasan da wannan wasiccin ka barni ina ta wahala tsawon shekara d'aya da rabi akan
wancan sokuwar yarinyar?."

"Akul Lima! 'yar uwarki ce bana son wannan tsanar da kike nuna mata wanda na yi imani shi ne

silar b'oye miki sirrikanta ga shinan zai wahalar da ke a banza."

"Abun bana sonta tunda Mah ta nuna da ita take yi ba ni ba."

"Lima kin sanfa an raba ne ke ce nawa ita kuma na Mah É—in ku."

"Na barka lafiya Abun gobe da safe zan taho maka da bayanai wanda na amince tono sirrin
Lina ce kaf d'inshi."

Ta ambata tare da mik'ewa bayan ta subbaci bayan hannunshi.

"Baburdo ya taimakeki 'yata."

"A'a Abun ruhin Kaka Gunu ya bani sa'a zakace domin Baburdo Dodon gadin Tsibiri ne bai isa
bani taimakon komi ba saima ni ce keyi masa alfarma na shaƙar ni'imar Tsibirin."

"Haka ne Lima to ki fito lafiya cikin kiyayewar Ruhin Kaka Gunu."

"Amin."

Ta fice cikin sauri tana yarfe hannaye cikin salon mugunta inda yarfin ke fitar da iska na watsar
da mutanen da duk ta ci karo da su a kan hanya wasu tsoffi ne da yara k'anana ya yin da masu
ƙarfin tsafin ke kare kansu tun kafin ya iso inda suke, ganin jama'a na neman wurin buya
saboda giftowarta sai tayi amfani da wuta da kunna a tsakiyar Tsibirin a take mutane suka soma
kulle gidajensu masu sana'a suka tsere wutar ta soma bin kayansu tana lashewa, sai hakan ya
wadata k'irjinta da nishad'i tayi ta zabga murmushi, batare da ta kula da illar da wutar takeyiwa
jama'ar ba tayi gaba abinta tana dariya.

Ruwan ƙanƙara ne ya sauko a cikin minti ɗaya ya kashe wutar tare da ɗaukewa batare da sanin
Lima ba hakan ya afku, jama'a suka dawo bakin kayansu suna tsinewa Lima a cikin zukatansu.

Tafiya mai tsayi Lima ta yi kafin ta isa bakin bukkan da ke cikin kogon wani dutse duk a saman
Tsibirin.

WAIWAYE A DON TAFIYA.

*Asalin Tsibirin da mutanen da ke rayuwa a cikinsa.*

Hatsabibin Tsibiri, Tsibiri ne mai dogon tarihi domin sarakuna masu dama ne suka shud'e a
cikinsa kuma dukkannunsu abisa turba d'aya suka ginu wato tsafi da kafurci domin basa da abin
bauta balle wurin bauta, gasu nan dai kara zube domin ko Dodo Burda da ke TSIBIRIN basa
bauta masa dan a mai gadi suka ajiyeshi ta hanyar yin bishara idan bak'o ya shigo ko samun
wanda ya karya doka na yiwa mata fyad'e dan duk da wannan duhun da suke ciki suna

kyamatar ketawa mata haddi.

Mafarin TSIBIRIN ya samu ne bisa jagorancin sarkin farko mai suna GOMA wanda aka ci shi da
ya k'i inda ke mulkin al'uma masu yawa, sakamakon rashin nasarar da ya yi ne ya yi hijira da
iyalansa ya yada zango a Tsibirin lokacin wurin sansanin miyagun namun daji ne da suka kashe
dajin mafarauta da makiyaya suke tsoron haurowa samansa,.
Saukan sarki Goma ya sa suka koma gefen TSIBIRIN suka kewayeshi cikin yi masa mubaya'a
domin k'arfin tsafinsa kad'ai ya isa zamowa bara zana ga rayukansu.

Sarki GOMA ya yi nasarasar k'awata TSIBIRIN cikin alk'aluman sihiri yarda kowa ya keto cikinta
sai ya burgeshi kuma ya zamo ganimansa in ya so ya maidashi bawa in kuma ya so ya
kasheshi musanman idan ya bincika yaga mai addini ne. A haka ya cigaba da shimfid'a
mulkinsa tamkar yarda ya keyi a birninsa da yayo hijira sai dai ya k'ir-k'iro wasu ababe ya sanya
su doka mai zaman kansa wanda d'aya da ga ciki shi ne sanadin yo hijiransa wato dokar ita ce
ta hana mazaje haik'ewa Mataye wato yi musu fyad'e amma bai hana zinace-zinace ba abisa
ra'ayin juna amma ayiwa mace da k'arfi wannan babban laifi ne domin duk wanda ya aikata
hakan kafin macen ta kawo k'ararsa fadar Sarki Dodon Burda zai yi kuwwa mai razanarwa
kuma a take kowa zai halarta gaban faÉ—ar Sarki inda wanda ya aikata laifin zai fito da kansa
tsirara mahunta lamarin su sanya takofi mai kaifi su datse masa al'aura tare da d'aukansa zuwa
wata muguwar k'orama da Sarki GOMA ya k'irk'ireta na musaman domin hukunta masu laifi mai
suna k'oranar sihiri, su jefashi ciki, wacce ba komi cikinta sai ruwa mai rai da lafiya tare da
manyan Kadoji wanda abincinsu ya zamo manyan namun daji da mutane masu laifin aikata
fyad'e da masu hayowa tsibirin dan ganin k'wam. Haka duk sarkin da ya hau sai ya k'ara
inganta wurin da salon muguntarshi na daban inda kudin shigarshi zai sake ninka na sarkin da
ya gabata.

Wannan doka na hana fyad'e Sarki Goma ya aiwatar da ita ce saboda 'yarsa d'aya tilo wacce ya
ke tsananin so da k'auna Gimbiya Aya da wani cikin jama'arsa ya yi.mata fyad'e lokacin da tafita
shak'atawa bayan gari a sanadin ta rasa ranta sai gawarta aka kawo masa cikin jini babu kyan
gani hankalinsa ya tashi ya bazama duban wanda ya aikata laifin sai ya baiyana d'an sarkin
yak'insa ne ya aikata a ta ke ya sanya aka kamosa ya datse masa kai da hannunsa a bainar
jam'a lamarin da ya haifar da k'azamin fad'a tsakaninsa da rundunar Sarkin yak'i inda
Sarakunan da suke yammaci da na kudanci suka taho suka marawa Sarkin yak'in baya suka
rufuma rundunar Sarki GOMA inda suka sami nasara akansa tunda ya fahimci kutunguilar da
suka shirya na su sami nasara akansa su maidashi bawa sai ya silale da kafatanin ilalansa
wanda suka had'a shi da matansa biyu da 'yayansa biyar dukansu maza dama Aya ce d'iya
mace tilo cikinsu. 'Yayan ba wanda ya yi aure sai mutum d'aya wanda matarsa ke goyon jariran
'yan biyu suma maza.

Cikin mabiyansa an sami wasu sun rufa masa baya sai ya sami nasarar tafiya da jama'a masu
d'an yawa.

Dukkan kulawan Sarki Goma akan 'yan biyun nan ne har suka samu isowa HATSABIBIN
TSIBIRIN da yaga dacewar ya zamo fadarsa amma akan hanya ya yo fashin zuk'a-zuk'an 'yan
mata guda biyar wanda suma sukayo gudun hijira bisa jagorancin wani Sadaukin mayak'i inda
ya amince zai tserar da su amma bisa sharad'in zasu zama matarsa a take kuwa suka amince
shi ne ya biyo hanya da su bisa gudunmowar alk'aluman tsafi sai kuma ya yi rashin sa'a ya
gamu da tawagar Sarkin GOMA ya ritsashi ya kasheshi ya kwashe 'yan matan inda ya
mallakawa 'yayansa suka angwance a lokaci d'aya bayan kammaluwar gyaran Tsibirin wanda
ya bashi suna da HATSABIBIN TSIBIBI domin bak'o bai tab'a shigowa TSIBIRIN ya fita ba fa ce
wannan Dodon ya kamoshi ya bawa wad'an nan Kadoji sunyi watanda da Naman shi ko a
maidashi bawa daga bisani ya zamo dan Tsibirin na har abada ya manta da Asalinsa balle burin
komawa garesu. Wannan zalincin yasa mafarauta da sauran ma'abota shiga daji basa bin ko
gefen TSIBIRIN duk kuwa sonsu da yankin saboda ababen tsoratarwa dake kewaye da Tsibirin
yafi ƙarfin ji da ganinsu har gara kafin bayyanar Sarki Goma sukanyi shiri na musanman su hau,
yanzu kam ba wanda ya san yarda TSIBIRIN ya koma balle ya bada labari dan duk wanda zai
bada labarin an halakashi ko ya zama ganimar Tsibiri.

Mrsjmoon ce🥰

Ku daure ku buɗe Arewabooks👇

*YADDA AKE BUÆŠE ACCOUNT A AREWABOOKS*

Bayan kaje play store ka É—akko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form É—in kamar haka: -

*Enter your name:* (Cikakken sunanki)

*Enter your mail:* (Email É—inki)

*Enter an username* (Sunanki)

*Enter your password:* ( misali 12341234)

*Confirm password:* (misali 12341234)

Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks.

*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google
za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

*Register* - Shine cike form domin buÉ—e account a ArewaBooks.
[1/13, 12:05 AM] Mrsjmoon: HATSABIBIN TSIBIBI
By Mrsjmoon

ADABI WRITER'S ASSOCIATION.
https://arewabooks.com/book?id=63a2e3d8821822a8402d8eb1 Follow me on Arewabooks.🖕

*Shafin na Mum twins ce Kawalliyata Billy Galadanchi, Allah ya bar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login