Showing 6001 words to 9000 words out of 45162 words

Chapter 3 - HATSABIBIN TSIBIRI Littafin Yaki Book Complete .pdf

Unknown   

25 Mar 2025

6527

kaunar ta har abada mara
algus, Amin ya rabbi.*

Page 03

Wad'annan manya dokoki sunyi matuƙar tasiri wurin d'aukaka darajar TSIBIRIN ta inda
mutanen cikinta ke alfahari da kansu domin sukan sakko yin farauta inda suke razana
makiyaya su d'auka wasu halittu ne na daban ko aljannu ne suka bayya garesu inda zasu gudu
subar dukiyarsu sai su kame shanye tarw da tarkacensu ciki har da yaransu maza da mata
wanda basa iya gudu ceton rai, su dawo kan TSIBIRIN su sadaukarwa Sarki shi kuma ya d'iba
ya bar musu sauran su raba tsakaninsu domin lokacin basu da yawa sosai kome suka samo na
wadatarsu. Yara da suke rabosu da iyayensu kuwa suna zuwa Sarki ke tsaface zukatansu su
manta da danginsu su saje da jama'ar Tsibirin in suna da addini su koma marasa shi.

Shi yasa babban yare a Tsibirin Fulatanci ne sai yarensu na gado wato Dusanci sai ko tsillin
yaren Hausa domin cikin mafarautan da tsau-tsayi ya kan ritsa da su zuwa farauta yankin an
taɓa kamo Bahaushe inda ya zauna a fadar Sarkin zamanin tare da miƙami mai girma wanda
yanzu a cikin tsatsonsa ne Sarkin yaƙi ya fito wato mahaifin Jarumi Buda.
Jama'ar Tsibiri mafi aka sarinsu suna da hasken fata mai daukan ido musanamam matansu shi
yasa suke da kyau na ban mamaki ko da kuwa baƙin fata garesu to zaka gansu masu cika
idanun mai kallonsu ne dan haka maza da matansu masu d'aukan hankali ne ainun sakamakon
gauraya da jinin Fulanin usul da sukayi.
Suna da zumunci na ban mamaki tare da rufawa juna asiri, jimlatan sun kasance masu amfana
da kayan juna ne sam basu san k'eta da mugunta ga junarsu ba shi yasa suke zaune tamkar
Uwa É—aya Uba É—aya.

Tafiya ya yi nisa inda TSIBIRIN ya cika da 'ya'ya da jikoki inda duk a tsarin da Sarki GOMA ya
ginasu suke wato tsafi da kwace wanda tuni ya mutu shekaru masu yawa da ya shudewa, sai
babban d'ansa ya gajesa bayan ya rasu shima d'ansa ya gajeshi, haka dai suka cigaba da
rayuwa bisa gadon-gado tare da cigaba da gina mulkin zaluncin na fashi da makami gami da
sace 'yan matan Fulani su zamo uwayen Æ´aÆ´ansu sai dai ba wacce ake haikewa sai tare da son
ranta domin a zamanin wani sarki mai suna Numan babban bafadensa ya taɓa haikewa ɗaya
daga cikin wanda sukayo fashin dan nuna isarshi a fadar tunaninsa ya wuce ayi masa hukunci,
aikam yana gamawa Dodo ya kwalla ihu kafin ace kwabo jama'a sun taru gaban fadar Sarki,
ana haka cikin dakon jawabin da za a yi masu saiga Bafaden nan ya bayyana tsirara, batare da
duba girmansa gami da mikaminsa ba aka datseshi tare da jefashi a kogin sihiri tun daga ranar
jama'ar suka sake shiga taitayinsu suke gujewa aikata wannan zunubi.

A wannan karnin Sarki Barde ke mulkin TSIBIRIN wanda ya kasance jika ga sarki Gunu wanda
ya sauka mulki batare da ya mutu ba dalilin mutuwar magajinsa wato mahaifin Barde dan haka
ya nad'a jikinshi Barde dan shima ya kasance yana da halin zalinci amma yana kawo tsari mai
b'ullewa ga masarautar tamkar yarda Sarki na farko ya ke yi dan ba'a tab'a sarki mai kawo
mafita ga Tsibirin ba irin Sarki Goma sai kuwa yanzu da sarki Barde ke kamantawa amma duk
da haka suna da bambanci mai tazara domin shi Sarki Barde wani lokacin yana kamanta adalci
sab'anin Sarki Goma da zaluncin kawai ya sanyawa gaba tare da wad'anda suka biyo bayanshi
ciki har Kaka Gunu.

A kawo sauyi ga Jama'ar Tsibiri Sarki Barde ya sanya mutanensa sun soma Noma da kiwo a
gefen Tsibirin inda duk wani makiyaya da suka jiyo k'amshinsa zasu bi bayansa su yake shi su
mamaye dajin baki É—aya. Da yaga sun tara abin duniya sai ya hanasu fashi da makami sai bisa
lalura ta rashin abinci sannan ya nad'a mutum uku da zasu rik'a kaikawo a tsakanin jam'ar
TSIBIRIN.

Sai ya killace TSIBIRIN ta inda ba mai iya fita gefenta da zarrar sun cire amfanin gona face
mutum uku sun amince masa, kome mutum ya keso a nan TSIBIRIN zai samesa domin ya
bud'e musu kasuwa na cinikayyan kayan abinci da sutura dan yanzu suna saka kaya sab'anin a
baya da suke saka ganye da fatu. Na mijin da ke da aure zai saka dogon wanda da rigar 'yar
shara mara aure kuwa gajeren wando zai saka da rigar sak'i na Fulani, mata kuwa da mai aure
da mara aure zani da riga na sak'i suke sakawa su nad'e kansu da bak'in sak'i sai dai 'yan
matan sunfi saka godayen riguna na farin yadin karen miski da ratsin ja.

Su wad'annan mutum ukun da Sarki Barde (Mai Tsibiri) ya wakilta sun had'a da Sarkin Noma
wanda alhakin kula da kayan amfanin gona ke hannunshi shi ne ke fitarwa da Sarki kasonshi
kafin mamoni ya soma amfana da kwayar hatsin da ya noma haka shi ke hada-hadar sai da
musu da kayan ya kawo musu kudinsu ba cuta ba cutarwa. Sai na biyu shi ne mai dawa wato
sarkin mafarauta wanda shi ne ke kula da abu-buwan da ke faruwa a dajin da kewayen Tsibirin
gudun samun tangarda mahara su kawo samame duk da Tsibirin na kewaye da alk'aluman tsafi.
Sai mutum na ƙarshe shi ne Sarkin yak'i wanda shi ke sanya ido a kai da kawon kowa dake
cikin Tsibirin da shirin ko ta kwana idan mai dawa ya yi nisan zango zuwa farauta.

Musanman Sarki Barde yasa aka farauto driver da motarsa, ya sami wata biyar yana ko yawa
mutane uku nan mota bayan sun kware ya korashi daji inda Namun daji sukayi watanden
namansa bayan ya turawa 'yan matan Tsibirin sun gama zuk'e masa ruwan jiki da jarabarsu
daga nan labarinsa ya zamo tarihi. Sarkin ya sama musu motoci uku lafiyayyu inda suka soma
shiga cikin gari suna mu'amala da su ta hanyar fitar da amfanin gonansu su siyar su siyo wanda
basa shukawa tare da sutura irin tasu sai dai duk in zasu shiga gari sukanyi shiga irin na
makiyayan usul wani zubin kuma suyi irin na kabilun da suke hurd'a da su shi yasa abokan
huld'an kasuwancin nasu basu gano daga inda suke fitowa ba balle su zama abin tsoro.

Duk wannan lamari da ake ciki Tsibirin baida magaji domin matar Sarki Barde bata taɓa yin bari
ba, ganin haka sai ya dukufa yin tsafi akan ya samu haihuwa inda kakanshi Gunu ke tausarshi

da cewa zai haihu da zarar lokaci ya yi. Kwatsam bayan shudewar wasu shekaru matar sarki ta
sami rabo inda ta haifi 'yan biyu dukansu mata masu kama d'aya tamkar an tsaga kara, ranar
suna anyi bidiri na gaban kwatance daga bisani aka sanya musu suna Lina da Lima inda suka
ci gaba da girma bisa kulawan mahaifansu da kakan mahaifinsu wato tsoho kaka Gunu.
Sai dai tun suna tsumman goyon suka taso da bambancin ra'ayi inda Lina mai tausayi ce Lima
kuma muguwa, hakan yasa basa ga maciji da juna.

Lima ta soma cutar da 'yar uwanta Lina tun kafin su san kansu sai Mahaifiyarsu wanda suke
kira da Mah ta maida kulawarta ga Lina shi kuma Abun ya maida nasa kulawan kan Lima inda
Tsoho Guna ya mara mashi baya. Sadda suka soma tasawa sai Kaka Gunu ya killace Lima ya
soma koya mata dabarun tsafi da yak'i ya yin da itama Lina ke amsar horon wurin d'an sarkin
yak'i Buda a b'oye batare da sanin kowa ba wanda ya kamu da sonta batare da ta san yanayi
ba, dalilin da ya k'udiri aniyar horar da ita kenan domin yana sane da wariyar da Kaka Gunu ke
nunawa tsakaninta da yar uwanta sai dai abinda bai sani ba horarwan baiyiwa Lina amfanin
komi saboda kafin ta dawo gida Kaka Gunu zai lalatashi idan ta dawo nanma mahaifiyarta kan
cigaba da koya mata tsafi domin tasan ilimin sosai wanda shi ne ke amfanarta domin Kaka
Gunu bai lalatashi bisa wani dalili nashi na daban.

Ganin sun soma taka makakin girma sai burin Sarki Barde ya koma kan tagwayen 'ya'yan dan
yana aiyana wata rana d'aya daga cikinsu zata jagoranci jama'an Tsibirin domin su kad'ai ya
mallaka saidai burinshi yafi karkata akan Lima saboda muguntarta da k'arfinta tamkar babban
sadaukiya sabanin Lina da ke da sanyi tare da gudun zalinci dan lokacin suka shiga shekaru
goma sha É—aya a duniya amma a haka Lima ke iya dambe da manyan sadaukai kuma ta samu
nasara akansu. Tunanin mai Tsibiri daya dana Kaka Gunu duk da a tarihin Tsibirin mace bata
taɓa jagorantar su ba.

Lokacin da suka taka matakin cikakkun 'yan mata sai rashin jituwar su ya k'ara tsanani
sakamakon ganowa da Lima ta yi Sadauki Buda na son Lina wanda ta ke ganin bata isa kaiwa
matsayin ba alhalin gata wacce ta tara abin so fiye da ita kamar k'arfi da tarin ilimin tsafi,
wannan dalili ya tunzurata ta ƙara k'aimi wurin murguna mata ya zamo bata jin dadin zaman
Tsibirin kwata-kwata, sai ta soma keb'e kanta tana rayuwa ita d'aya inda Lima zata binciko wurin
taje ta mallake a cewar ita ce ke da ikon mallakan wurin hutawa sama da Lina.

Tsananin Lima ya soma kai Lina bango gashi bata son suna fada da juna, sai kawai ta koma
duk in ta fita rangadi sai ta ajiye kuyanginta a bayan gari ta zama tsun-tsuwa mafi gudu cikin
tsin-tsaye ta nufi biranen da ke da nisa da su inda zatayi ta ganin ababen al'ajabi musanman
bauta da taga jama'a na yi a killatattun d'akuna masu kyau abin da yafi bata mamaki shi ne
ganin yarda suke gudu idan ana magana a abin fitar sauti (Kiran sallah kenan) sai ta lalace
wurin kallonsu gami da sauraren muryan da ke fitowa (Karatun Qur'ani kenan) ta kan b'ata
lokacin tana saurare tare da son shiga wurin amma sai ta riƙa jin hucin zafi na dawo da ita baya
inda zatabar wurin a d'imauce amma idan ta nemi shiga dayan ginin da ake kida da rawa gami
da wak'a sam bata jin hucin zafi sai tafi maida hankali a wurin inda zatayi ta binsu suna tikan

rawa batare da ta bayyana masu fili ba balle su koreta har ta soma ƙaunar yaren da suke
magana da shi ta soma fahimta kaÉ—an-kaÉ—an. Wani zubin kuma in ta shigo birnin sai ta tare a
makarantun boko inda wannan ya bata damar jin yaren turanci managarci har take fahimtar
abinda ake koyarwa a d'akin da ake yin rawa da wak'a.
Sosai ta sami ilimin boko batare da sanin kowa ba sai mahaifiyarta wacce bata boye mata duk
abin da ta aikata, sannan tana halarta Masarautu kala-kala tana naÉ—o salon mulkinsu domin
wata rana ta shimfida a Tsibirin su da take da burin mulkansa ko da hakan zaizamo ajalinta ne.

A kwana a tashi Lina na nad'o labarai na samun 'yanci sai watsam ta soma aiwatar da
manufarta cikin dibara inda ta kawo sauyi a tafiyar mulkin Tsibiri inda ta soke tsarin hana
jama'ar Tsibirin fita lamarin gabansu sai da izini wanda ba dan mahaifin nata ya so ba ya
amince rok'onta sai dan manufar da ta gina maganar akai mai amfani ne na abar kowa na fita
shan iska duk inda suka so da harkan cinikaiya da kansu saboda ta nan zasu kara wayewa na
daga abin da basu sani ba sannan tanan za su iya ƙarowa Tsibirin sanin da bata da shi ta
fannoni da dama. Ganin ta samu nasara a nan bayan wani lokaci ta sake wargaza wani tsarin
inda nanma ta sauya musu shigar sutura ta kawo tsarin 'yan gidan sarauta dole su bambanta da
jama'ar da basu da sarauta inda ta ce suna da damar saka suturun da suka so a duk sadda
suka ga dama kuma mai tsada da burgewa irin wanda yayi daidai da ra'ayinsu musanman ga
'ya'ya mata ababen ado da kwalliya su kuma jama'ar gari ta ce suna da damar saka sutura
masu rufe jiki duk kalan da suka so amma banda irin na gidan Sarauta. A nan gefen ne tasha
wuyar janyo hankalinsa har ya amince da tsarin inda Lima ta yi ta fushi wai Lina na son juya kan
mahaifinsu son da keyi mata ya dawo kanta sai da kyar ya iya shawo kanta ta janye ik'irarin sai
ta yi yaƙi da Lina.

Jama'ar Tsibiri kam sun ji dad'in wannan sauyi dan a take suka soma bata girma sama da
wanda suke bawa Lima dan killace su a wuri É—aya yayi mugun takurasu basa da bakin magana
ne kawai ya sa dole sukayi biyayya ga abin da iyaye da kakanninsu suka wanzu a cikin shi.

Mrsjmoon ce🥰

Ku daure ku buɗe Arewabooks👇

*YADDA AKE BUÆŠE ACCOUNT A AREWABOOKS*

Bayan kaje play store ka É—akko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form É—in kamar haka: -

*Enter your name:* (Cikakken sunanki)

*Enter your mail:* (Email É—inki)

*Enter an username* (Sunanki)

*Enter your password:* ( misali 12341234)

*Confirm password:* (misali 12341234)

Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks.

*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google
za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

*Register* - Shine cike form domin buÉ—e account a ArewaBooks.
[1/13, 12:05 AM] Mrsjmoon: HATSABIBIN TSIBIBI
By Mrsjmoon.

ADABI WRITER'S ASSOCIATION.
https://arewabooks.com/book?id=63a2e3d8821822a8402d8eb1 Follow me on Arewabooks.🖕

Page 04.

Sai dai abin da basu sani ba Lina ta yi yaƙin k'wato masu 'yanci ne domin kanta saboda gudun
kada mahaifinsu ya gano tanayin nisan zango zuwa wani yanki batare da saninsa ba haka tana
da burin shiga ta alfarma kamar yarda take ganin a masarautun da take zagayawa da ke birane
daban daban sannan tana da burin samo ilimin tsafin da zai bata kariya daga zalinci Lima tare
da samun damar shiga fadar da jama'a ke turu-ruwan shiga musaman ranar juma'a suma taga
wani kalan bauta sukeyi tare da iya yarensu mai ratsa zuciya. (Masallacin Juma'a da karatun
Alqur'ani Lina take magana)

Burinta ya cika inda ta cigaba da fita yawo duk inda taga dama a kuma sadda ta so dan har ta
kan kwana a can amma bata wuce kwana É—aya zuwa biyu duk tanayin tafiyar ne bisa
amincewar Abun tare da neman albarkan Mah.

Lima hankalinta ya tashi sadda ta fahimci yawon da Lina ke fita wani sabon ilimi take samowa
wanda nan gaba zai iya zama bara zama a gareta, sai itama ta soma yin nisan zango saidai ita
ilimin zalunci take sake koyowa inda zata dawo tayi ta azabtar da bayi tare da jama'ar gari
hakan kuwa na faranta ran Kaka Gunu domin alamomin gadar karagar mulki na ta ƙara
bayyana a gareta, sai ya ƙara mara mata baya tana cigaba da zalintar wanda basu ji ba basu
gani ba, har saida Abun ya tsawatar mata tare da nunawa Kaka Gunu illar hakan ya ce a bari ta
hau mulkin zaifi wannan kalamin nasa ya fusata Kaka Gunu har ya ce ba wanda ta gaji ruwan
tulun albarkansa sai Lima sai Abun ya rokeshi da ya b'oye zancen zai cika masa wannan
wasiccin.

A cikin wannan tsakani Kaka Gunu ya mutu, Abun ya tafi dan mallakan Ruwan Tulun da sauran
sirrikan tsafi amma ifritan da ke gadin Bukkan suka hana shi da ya matsa sai suka nemi
halakashi kan dole ya hak'ura amma yana cike da burin mallakan wannan ruwa na albarka.

Bayan wasu shekaru burrin Lina ya cika domin ta samo ilimin da take burin mallaka wato tsafin
da ya doke na Lima wanda yanzu take shirya fito na fito da wanda ya nemi kawo mata cikas a
cikin manufarta na zamowa magajiyar karagar kujerar HATSABIBIN TSIBIBI domin shimfid'a
mulkin adalci gami da samar masu da abin bauta su daina zama kara zube, su sami ilmomi
mabambanta haka tana burin ganin wayewar su ya zarta na biranen da take shiga tana ganin
cigaba da suke tare da shi mai burgewa haka babban burinta shi ne su sakko daga kan Tsibirin
(Tsauni) su gyara dajin ya zamo birni mai zaman kan shi tare da kayan more rayuwa in yaso
saman tsibirin ayi masa gyara ya zamo wurin shakatawa na musamman da jama'a daga birane
daban-daban zasu riƙa zuwa yawon buɗe ido kuɗin shiga na halal na samuwa ga Tsibirin daga
nan ƙarshen zalincinsu ya zo su kowa rayuwar 'yanci mai cike da farin ciki tare da zumuncin ga
kowa, baƙi su zamo abar karramawa a tsibirin. Tarihin Hatsabiban Tsibiri da Sarki Goma ya gina
ya zamo ya tarwatse sai wanda ta ingana da kanta, sunarta ya zagaye Duniya da tambarin
Adalci. Saidai a gefen Lima duk kishiyar burin Lina shi ne nata wanda a kullum da shi take
kwana da tashi.

*Wannan shi ne asalin labarin Tsibirin da rayuwar jama'ar cikinsa gami da burikan tagwayen
Gimbiyoyin.*

Cigaban labari.

***
Lima a Bukkan Kaka Gunu.

Ta tura kai cikin Bukkan bayan ta yi amfani da alkaliman sihiri k'ofar bukkan ya buÉ—e, cikinsa
katon wuri ne da ya cika da k'okunar kan namun daji kala daban-daban a can daga nesa wani
kilisa ne mai daukan ido samansa da kujerar na alfarma ce, wurin Lima ta nufa ta hau saman
kujeran ta zauna tana fesar da iska cikin nuna izzar jinin sarauta.
"Barka da isowa uwar gijiyata, me ke tafe da ke?"

Kallon tsamurmurin tsohon ta yi cike da mamakin bayyanarshi ba neman iso daga gareta.

"Affuwan uwar gijiyata na kasance zaune a wannan bigire shekaru masu yawa domin tun sarki
na biyu nake a matsayin hadimisa sannan nine sirrin dukkanin sarakunan da suka shude dan
haka kema nine idonki akan komi umurninki kawai nake jira yanzu kiga aiki da cikawa."

"Me ye sunarka?"

"Tsidau uban yan binciken wannan fada."

"Madallah, yanzu na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login