Showing 24001 words to 27000 words out of 45162 words
Chapter 9 - HATSABIBIN TSIBIRI Littafin Yaki Book Complete .pdf
Unknown
25 Mar 2025
5229
mai so zai iya tuntubar number nan ta WhatsApp ko kira. 08132166848. Yarda ake
amfani da shi za a jik'a Lipton sai a d'iga man ayu a ciki a shanye da d'umi-d'umi za a iya zuba
zuma ko siga a ruwan Lipton d'in dan gudun d'aci haka za a iya zubawa a ruwan Tea a sha.
Masu asma da limoniya kuma zasu jajjaga tafarnuwa su matse ruwan su zuba ruwan d'umi da
man ayu su shanye. Masu Infection duk in suka wanke wurin da ruwan zafi sai su saka man ayu
haka masu kaikayin jiki idan sun fito wanka sai su shafa amma zasu sha da ruwan Lipton, Allah
ya ƙara mana lafiya Amin.*
[1/13, 12:05 AM] Mrsjmoon: HATSABIBIN TSIBIBI
By Mrsjmoon
Adabi Writer's Association (AWA)
https://arewabooks.com/book?id=63a2e3d8821822a8402d8eb1 follow me on Arewabooks í ½í¶•
*Ayimin Affuwa kwana biyu ina cikin hidima ce shi yasa ku ka jini shiru.*
Page 10.
Part d'in Mamie Fulani ta nufa ta shiga k'aton falon da sallama, Lailah ce ta amsa cikin dishewar
murya wacce ke zaune gaban Sadauki bisa alamu laifi tayi masa. Da sauri Maryam tayi nufin
juyawa ya daka mata tsawa.
"Ke!"
Tsak ta tsaya batare da ta juyo ba.
"Zo nan dama ina shirin kiranki."
'Nashiga uku Allah yasa dai ba masifa Lailah ta janyomin ba.'
Ta ambata a ranta ya yin da a fili ta juyo jikinta na rawa tare da furta "Ni?"
Shiru shi ne amsar da ta samu sai tasami kanta da ƙare masa kallo sanye yake cikin kayan
sarauta wanda yafi ta'amali da su domin kafin ka gansa da ƙananan kaya aiki ne sai ko suit
wanda da an gansa cikin shigar ke nuni da zaiyi tafiya ne sai kuma a filin motsa jiki inda ke
shigar sport wear.
"Please Maryam ki zo kiyi masa bayani wallahi ba ruwana da Muhib, shi ne ke takurani ke
biyoni gida."
"Keep quiet!"
Ya ambata a fusace.
"Sorry Yaya, dan Allah ka taimakeni ka saurari bayanin bakin Maryam domin ita, Neera, da
Zuhra ne shaiduna akan bayanin da nake yi maka, wallahi Allah ba ruwana da Muhib."
Kallo kin rainani ya auna mata sai ta fashe da kuka ta kama k'afarshi janye ƙafar ya yi tare da
mik'ewa ya nufo k'ofar fita saboda kukanta ya karya masa zuciya kuma a take ya yarda da
gaskiya take sanar da shi.
Maryam na ganin tasowarshi ta runtuma da gudu tamkar zata kifa sai lamarin ya bashi dariya ya
murmusa tare da juyowa ya ce da Lailah "Ki fita sabgar mara natsuwar yaron nan idan kuma
kina son mu sa k'afar wondo ɗaya da ke ne to in sake ganin ƙafarsa a cikin Masarautar nan
sannan in har kin san kin kamu da son shi to kiyi gaggawan cireshi a ruhinki domin kinfi ƙarfinsa
ta ko wani fuskan kuma ke mai tsarki ce dan haka ba zan bari ki auri mai cike da dattin najasa
ba, a bisa umurnina ki koreshi koro na har abada."
Ya kai ƙarshen maganar na runtse ido domin yanajin tamkar bayyiwa masoyan adalci ba.
Gyada kai ta yi tana share hawayen da ke zubo mata, ganin na kallonta sai ta motsa baki a
hankali ta ce "Nayi maka alk'awarin dakatar da shi daga zuwa Masarauta tare da nesantarshi na
har abada duk da dama shi ke haukansa ni bai isheni kallo ba."
"Da kyau."
Murmushi tayi ya maida mata da martani ya juya, har ya fice ya dawo ya ce "Saura ki haÉ—a baki
da wancan mara kunyar ku turomin macizai saman gadona kamar yarda kuka saba aikatawa
idan anyi maku faÉ—a."
"Allah yaya ba ruwana Neerah ce da aikin kasan bana yin Ofi sai da babban dalili."
"Nadai sanar dake kada inga maciji a muhallina."
Sunkuyar da kai ta yi tana murmushi domin tsayawa zancen nan na nufin ya huce kenan.
"Humm zan gyara maku zama ne musanman ita da ta rainani."
Ya ambata yana barin wurin.
"Ka soma gyara kanka Babana domin kai da su duk kanwar ja ce wani fanninma kafisu tsorata
mutane da Macizai wai lamarin har kan Mai Martaba dan ya sanar da kai gaskiya."
Da sauri ya dawo falon ya rik'o hannun Mamie yana k'ifta mata ido, alamun tayi shiru.
"Yes, ka soma gyarawa kanka zama kafin ta zo kan wasu wanda basuyi kwatan-kwacin laifin da
kake kan aikatawa ba."
"Wayyo Mamiena me na yi kuma?"
"Babban zunubi na auri saki da kuma tsoratar da Musulmi ta hanyar fito da macizai su razanasu
akan laifin da baikai ya kawo ba, kwanaki Mai Martaba har kusan fad'uwa ƙasa ya yi dan tsoro,
tabbaas da ba dan ina kusa ba da anji mugun labari sakamakon macizai da suka cika
turakanshi marasa kyan gani sannan tamkar almara suka b'ace, ganin anyi binkice ba agano
komi ba sai na tabbatar kaine ta turosu, anya Babana hakan ya kamace kuwa?"
"Mamie ya wuce fa."
Ya furta cikin tsare gira ganin Lailah na k'unshe dariya.
"Bai wuce ba, mai jin magana kawai kada a fad'i É—ayan."
"Please Mamie ki manta da lamarin, ai natuba da jimawa."
"Anya Babana kai kaÉ—ai ne kuwa?"
"Me nayi kuma Mamiena?"
"Watsi da cikar kamala wato aure sunnar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam.
"Ayya Mamie ki bar maganar auri sakin nan domin yana daga cikin zanen ƙaddarar shi wanda
bawa bai isa kufce masa ba saboda rubutacce ne daga Allah."
Duk kallon bakin falon sukayi a tare, Dr. Muneerah ce tsaye idanu jajur bisa alamu kuka tayi.
"A'a Likita bokon turai, lamarin Babana ko da ƙaddara to son zuciya ya soma yi masa jagora
domin ba sau É—aya ko biyu ya aikata laifin ba har fa sau hu...
"Mamiena ya tuba ai ba zai sake komawa ga zunubin ba ko yaya Yarima?"
Kafeta da idanu ya yi batare da ya amsa ba.
"Yes Neerah yaya ya yi tuba na gaskiya da yardan Allah ba zai sake komawa ga wannan laifin
ba, zaiyi aure ya zauna lafiya da iyalinsa wannan a rubuce yake."
Lailah ta amshe da sauri tana kallon idanun Sadauki.
"Au, in na fahimta kuna bayan iya shegen da yarik'a aikatawa kenan?"
"A'a fa Mamie amma dai tunda ya wuce to abar d'aga zancen gudun ɓacin rai kinsan abu kaɗan
ke sanyashi cikin tunani ya soma wasan b'uya da kowa kuma hakan kan jefashi cikin kaÉ—aici
sannan hakan bai kamata ba yana Sarkin Gobe na fuskantan matsin rayuwa."
"Muneera wai nawa Babana ya biyaki ne?"
"Na me fa Mamie?"
"Na campaign mana."
Ware ido ta yi Sadauki ya murmusa tare da russunawa gaban Mamie ya yi mata rad'a wanda ita
kaÉ—ai tajiyo abinda ya ambata aikam ta sauke masa dundu tana furta "Allah ya tsare, ya kare,
can ga su gada wai Zomo yaji kid'an farauta, wallahi a kul É—in ka da wannan lamarin kadaiji na
sanar maka in ba so kake mu koma gidan jiya ba."
"Allah Mamie na zama kurna akan lamarin sam banji me kike cewa ba."
"Amsa naka Sadauki, Allah kada naji ko na gani kuma nan da sati biyu ka kawo mana matar
aure ko ranka yafi dare duhu da fatan katuna maganar Mai Martaba."
"Mamiena dan Allah ki ami...
"Nagama magana Babana sannan kada na sake ganin ka tasa k'anninka a gaba da zancen
baka son suna zance tunda ba jik'asu zamuyi mu sha ba."
"Mamie da dare zan dawo muyi maganar a gaban Abba domin a wannan gab'an banjin zan ja
da baya ba."
"Na zama abokiyar wasarka ko Baba Ali?"
"Tuba na ke Fulanin Mai mar...
"Gidanku na ce Sadauki."
Girgiza kai yayi tare da sumbatar hannunta da ke riƙe da shi tun dazun kana ya saki ya iso daf
da Neerah ya rage murya ya ce "Iyayi kawai to ban gode ba."
"Gobe ma rana ce da Muneerah kake zancen É—an Samari."
"Mamie 'yarki ta rainani fa."
Ya ambata cikin kawo mata duka ta gofce.
Banza Mamie ta yi masa sai ya fice yana cije lips gami da nuno Neerah da yatsa cikin salon
wasa ya yin da ita kuma keyi masa gwalo. Murmusawa Mamie Fulani tayi domin abinda ke
saurin sakata farin ciki shi ne ganin walwala a fuskan Sadauki Aliyu.
"Ke kuma taho naji damuwarki da kika tahomin da idanu kamar jan nama."
"Ciwo sukemin Mamiena."
"Kika sake ambatarmin k'aryan nan sai na saɓa miki."
"Affuwan Mamie kaina ke ciwo kuma kin san ban da juriyan ciwo ko kaÉ—an, shi ne nayi kuka
Ammi ta koroni wai na dameta da jan hanci kada in saka masu mura ita da yaranta."
"Ayya sannu, kyale Nana ai ciwo na kan kowa, taho kisha magani domin na san halinki na gaba
da magani wai kina Likita amma kina gudun magani, Allah ya kyauta kam."
Cikin murmushi ta iso ta zauna gefen Mamie tare da manno jikinta da ƙafarta, sai ta dafa kanta
cike da kulawa take yi mata sannu kana daga bisani ta bawa Lailah umurnin É—auko mata
maganin ciwon kai a d'akin barcinta, cikin dibara Neerah ta gudu kafin Lailah ta dawo ta nunawa
Mami a biyota da shi dakin Lailah saboda abinda Neerah ta tsani shansa shi ne magani.
***
Hajiya Umma ta ya kika yi wannan waftar na fed'ewa Sardauna biri har wutsiya shin kin manta
waye shi akan gaba da bin bokaye? To wallahi tun wuri ki dawo hayyacinki ki sanja dabara
domin ina da tabbacin bazamu taɓa samun haɗin kansa ba tunda kinayi waftar sanar da shi
gaskiyan lamarin da muke kai."
"Ki bari kawai Hajiya Kilishi wai a zatona in yaji Aljana na tare da Sadauki zaifi yin farin ciki tare
da bamu haÉ—in kai har mu kai ga nasara."
"Kin manta har kwanar gobe suna fita rangadi tare domin ginuwar ƙaunarsu kuma ƙaunar da
mai Martaba ya dasa a zukatansu bai taɓa gogewa sai dai zan sanar da ke hanyar gaskiya
domin kawo nak'asu a ƙaunarsu shi ne sai mun tashi tsaye mun sa an raunatashi yarda zasu
zamo basa ga maciji ko kaÉ—an shi ne zamuyi nasarar É—ora shi akan turban da muke so haka
game da son kud'insa sai anyi mana aiki ta yarda kome kika nema ya baki batare da kai ruwa
rana ba tunda yana da dukiya kuma ba mai amfana da shi sai makirar matarshi da uwarta ke
kuwa sai hange daga nesa to sam hakan ba mai yiwuwa ba ne, yarda kika sha wahalar
haihuwar sa gami da rainon sa dole ya zamo ke ce ta farko da zaki mori dukiyarsa tare da sanin
duk kan bayanen ƙaddarorinsa."
"Tabbas kinyi gaskiya Hajiya Kilishi, zantukanki masu amincewa ne gareni, yanzu zan baki
wuk'a da nama ki zamo idanuna na kai da kawo tsakanin lamarin saboda yawan fitana a b'oye
nada hatsari dan idan Mai Martaba ya sani kashina ya bushe wata k'ilama aurena ya sami
tangarda tunda angama da shi bai kallona da daraja sai muguwar Fulanin can wacce ba zata
gama lafiya ba."
"Kibari kawai, gata bata jin Asiri."
"Kin manta waye Uwarta kenan? Ai Hajiya Dada cikakkiyar matsafiya ce domin maganar Malam
Sale kenan duk in ya buga ƙasa Uwarta na tsaye kanta shi yasa sai yarda tayi da Mai Martaba."
"Aikam na yarda Hajiya Dada na tsafi domin dubi zafin Chiroma amma a gaban Nana Safiyya
sai ya koma fulawa saboda laushi."
"Uhm ai ƙarshen su ba zaiyi kyau ba in sha Allah."
Allah ya amsa."
"Amin Aminiyata."
Murmushi Hajiya Kilishi tayi sannan ta maida hiran kan abinda suka zauna a kai, inda cike da
kisisina take cewa "Dama ina shirin yi miki wannan maganar fitar da kanki sai nayi nazarin a
wakilta Hud yana amsowa tare da sanya Sardauna amfani shi wanda ba sai ya zo hannunki ba
kinsan Hud da iya kalaman makirci na tabbata cikin sauk'i zai sakashi yin amfani da maganin
hankali kwance, kinga ko wanda zaici a abinci ne duk Hud zai bashi saboda in muna son ya
sami farin jinin jama'a sama da wanda Sadauki ke da shi dole sai mun hada na ci a abinci da
sha da wanka har da hayak'i."
"To ba matsala hakan za'a yi, zan turo maki sak'o anjima amma kada a amso na hayak'in nan
saboda zai harbo jirjinmu."
"To madallah, bari in koma kada mai gidan ya neme ni."
"Yau ke ce da turakar kenan."
"Eh fa."
"Ok tafi nima ina da baƙi anjima kaɗan."
"To na wuce, Allah bamu yinin lafiya."
Motsa kai Ummu tayi cikin lumshe ido dan kanta taji na ciwo, harara Hajiya Kilishi ta zabga
mata ta gefen ido tana zund'enta a fakaice sannan ta buÉ—e k'ofar ta fice cike sak'e-sak'en yarda
tsarinta zai tafi batare da samun tangarda ba na ganin d'anta Hud ya haye karagar mulkin
Mungaye tunda shima Babansa É—an Sarki ne yana da sarautar da zai iya Mulki ba sai lallai
'ya'yan Sarkin dake kan karagar mulki ba
"Wallahi bana son Sadauki domin tuni na kamla rabashi da Masarautar baki É—aya lokaci nake
dakon ya yi a nemeshi a rasa daga ganan Hud ya zamo Sarki mai iko domin bazan bari
Sardauna ya zame masa matsala ba a tafiyar ba."
"A'a Mamma ina mutuwar son Yaya Sadauki kuma shi nake burin gabatarwa Abba a matsayin
zab'ina kamar yarda kuke dakon jin gwanina sannan ina tare da ke kan zamowar yaya Hud
Sarki saboda lokaci ya yi da za a kawo sauyi ba lallai sai 'ya'yan Sarkin dake mulki ne zasuyi ta
gadon sarautan ba, duk da a gefe ɗaya ina jin kamar ba zai iya ba dan ban taɓa jin mashayi ya
hau karagar mulkin Mungaye ba."
A razane Hajiya kilishi ta dubi inda mafi soyuwar 'yar nata É—aya tilo mace cikin 'ya'yanta maza
huÉ—u. Gyara tsayuwa ta yi tare da jinjinawa mahaifiyar nata kai alamun bata tabbacin furucinta
tare da cigaba da cewa "Yes Mamma ina yin Yaya Sadauki kuma shi ne mijina da yardan Allah
dan na k'udiri aniyar d'aura d'amarar jure zama da shi a duk yarda ya ke, ni ce zan kawo
ƙarshen auri sakinsa insha Allah"
'Wata sabuwa inji 'yan ca-ca, hak'ik'a aiki ya sameni ni jikan Magaji.'
"Momma muje nasan baki rasa shawarar da zaki bani akan auren sannan kada ki kushemin
zab'i a kan abinda ya ke zanen ƙaddararshi ne wato auri saki."
Dafe kai Hajiya Kilishi ta yi tana jin wani mak'ak'in d'aci na sauka saman harshenta.
'Tirk'a haka zakiyimin Zuhra? To wallahi ko zaki mutu ne ba ki isa hanani kora Sadauki duniyar
da bazai kuma waiwayen Masarauta ba.'
Ta sake ambata cikin ranta tana dallawa bayan Zuhra harara wacce take shirin shiga d'akin
barcinta.
***
"Hey Doctor Neerah, me ke faru ne har ya sakaki kuka?"
Motsa yatsunta Neerah ta yi tamkar zata furta kalma sai kuma ta tsuke bakinta tare da hayewa
saman gado ta juyawa Lailah baya.
"Dan Allah Muneera sanar dani damuwarki ko in had'a ki da Mamie nasan ita zaki sanar da ita."
"A'a Lailah kada kiyimin haka, yanzu taso muje ki rakani gidan Hajiya Dada."
"Asibitin da kikace zaki shiga fa?"
"Na fasa."
"No ki muje na rakaki domin ba kyau saɓa alƙawari."
"Na tura masu Dr. Hassana harma ta isa kinga sak'on da ta turomin yanzu."
"Ok amma gaskiya kada ki sake irin haka tunda kin san ke suka fi buƙata."
"In sha Allah."
Suka fito bayan Neerah ta gyara fuskanta ya yi kyau suka sami Mamie zaune hadimai kewaye
da ita suna yi mata hira cike da sakewa zamowarta mara girman kai irin na mafi akasarin matar
sarakuna. Bayan sun amsa gaisuwar hadimai sai suka sanar da ita inda suka nufa ta tsare gira
kafin tayi maga Neera ta rigata da cewa "Please Mamina gidanmu na biyu zan kai ziyara fa
Allah daga nan ba inda zamu wuce kinsan halinmu.."
"Muneera bana son yawo ne alhalin kuna 'yan manyan gida musanman yanzu da ake maganar
aurenmu"
"Mamie dubo fa sanyin idaniyarki zamuyi ba yawo ba sannan baza mu wuce awa biyu ba zamu
dawo in sha Allah."
"Ok to shiga kitchen ki wuce mata sak'onta dama Junaid yanzu zai kai mata kun hutash-sheshi
kam."
"A'a Mamie suyi tafiyarsu inyi tawa da Maryam dama na ce ta shirya zamuje gidan tsohuwar
Mamie ziyara.
"Mun huta kam."
Lailah ta ambata cikin murgud'awa Junaid baki, ya kawo mata duka ta koma bayan Mamie tana
dariya.
"Affuwa dai Yarima Junaid."
Kuyangi suka ambata cikin girmamawa kansu sunkuye.
Hannu Mamie ta d'awa su Neerah suka fice sunayi mata godiya yayin da Junaid ya dubi wata
kunyanga ya bata umurnin da ta d'auko masa sak'on a kitchen, ta wuce da sauri tamkar zata
kifa.
"Bi a hankali Dudu."
Mamie Fulani ta furta cikin kulawa saboda yarda ta ke daraja d'an Adam, ko zaman kuyangi a
sashinta na dole ne dan zamowarta matar sarki amma tafi son ta kasance daga ita sai 'ya'yan
dana al'umma sosai take tausayawa bayi shi yasa wad'anda ke sashinta suke jin daÉ—i fiye da
wanda ke sashin Umma da sauran matan masarautar kuma hakan ya ƙara mata k'ima a
idanunsu da zuri'arta dama duk wanda ya ziyarci sashin to zaka samu kuyangin na karrama duk
bukatun sa.
Momyn Haske ce í ¾íµ°
*Muna saida ingantaccen man ayu wanda ya zo daga Chad. Yana maganin Infection, asma,
limoniya, mura, ciwon basira ciwon kai, ciwon baya, ciwon ƙafa, ciwon mara, kaikayin jiki dana
matse-matsi, yalwatuwar ni'ima tare da samun gamsuwa a turaka da sauransu, muna saida
É—aya ko sari mai so zai iya tuntubar number nan ta WhatsApp ko kira. 08132166848. Yarda ake
amfani da shi za a jik'a Lipton sai a