Showing 18001 words to 21000 words out of 45162 words

Chapter 7 - HATSABIBIN TSIBIRI Littafin Yaki Book Complete .pdf

Unknown   

25 Mar 2025

6521



Ya furta cikin shak'ewar murya gami da matse cinyoyinta.

"Your wife."

Ware idanu ya yi ta kyalkyale da dariya gami da huro masa iskan bakinta wanda ke dauke da
wani k'anshi na musanman, shi ne ke kuma haukatashi matuk'a. A gigice ya nufeta hankalinsa
a tashe cikin son kasancewa da ita ko ta halin k'ak'a. Ta shi ta yi ta soma ja da baya ya kai mata
cafkota ta zama haske ta b'ace tana cigaba da yi masa dariya wanda ke sake hautsina masa
lissafi, toshe kunnuwansa ya yi amma sai yaji dariya makar sake ƙaruwa ya keyi sai ya cire
hannun cikin furzar da iska mai huci ya ce "Na rantse idan kika sake shigowa hannuna a karo
na biyu sai na illata miki rayuwa ba aljana kike ba ko ifritiya ce ke sai na gana miki a zaba mai

rad'ad'i fiye da wanda kike kan ganamin."

Ya k'are furucin cikin kaiwa iska naushi, ta saka ihu cike da tantiranci, ya ja tsaki mai ƙarfi ya
nufi bathroom tamkar zaki ya sakarwa kansa ruwan sanyi, ya É—auki mintoci ashirin tsaye ruwan
da dukanshi sannan ya fito jikinsa na digan ruwa dan ko kayan jikinsa bai cire ba ya nufi firij ya
zuba ruwa a cup ya ciko k'aramin spoon da gishiri ya juya a ruwan ya matse lemon tsami a kai
ya daga ya shanye domin ko yasha tablet ya kan jima kafin ya dawo dai-dai amma wannan
had'in take yanke ke samun natsuwa, yana jin kak'oshinsa tamkar zai tsage amma haka nan ya
jure.

'Wata rana zaka sami matsala game da lafiyarka Aliyu.'

Jinjina kai yayi alamun ya sanda da hakan ta hanyar bawa zuciyarsa amsa.

***
Sardauna da Sadauki tagwayen ne ga mai martaba Professor Abdul Hakam duk kuwa da ba
d'umin ciki É—aya suka sha ba dan an haifi Sardauna da hantsi da marece kuma aka haifi
Sadauki wanda faruwar haka ya so tada k'ura inda Umma ta ce Sadauki shegene girkinta
Mamie Fulani ta ci dan haka bashi da gadon sarauta domin a wanna lokacin Mai martaba ya
soma samun haihuwar 'ya'ya maza. Hajiya mai babban zaure ce ta tsawatar wato mahaifiyar
mai martaba sannan ta kafa dokar duk ranar da Umma ta sake ambatar wannan kalman a
k'arshen zamanta a matsayin matar d'anta, aikam ta shiga hankalinta inda ta kame bakinta har
zuwa yau bata sake furta kalmar ba amma ta raini zuciyar Sardauna akan son mulki bakin rai
bakin fama dan ta kance da shi ko zai hau karagar mulkin da second ne ya koma ga Allah sai
ya hau kujerar sarautan Mungaye.

Umma irin matar nan ne masu fuska biyu inda cikin dubara take cutar da duk wanda ta tsanani
ganin warwalanshi batare da makusantarshi sun gano ba.

Momyn Haske ce 🥰
[1/13, 12:05 AM] Mrsjmoon: HATSABIBIN TSIBIBI
By Mrsjmoon.

AWA.

Page 8

Umma ta wargaza zaman lafiya tsakaninta da Mamie Fulani cikin salonta mai wuyar ganewa,
duk da ita Fulanin bata kulata tana bata girmanta amma hakan baisa ta kame kanta ba wurin
maida k'aramin abu zuwa babba a tsakaninsu ta hanyar makirci kala-kala wanda kafin mai
martaba ya farga Mamie Fulani ta k'unsa bak'in ciki har ya kaita ga kamuwa da hawan jini sai
dai bisa amincin Allah Mai martaba ya gano tungun Umma batare da ita Umman ta san hakan
ba wanda shima mahaifiyarsa ce Hajiya babban ta haska mashi fitila a take kuwa ya warke

makanta da ke ciki ya yiwa lamarin tubkan hanci ta siyaya ba tare da nuna fifikon da zai janyo
tashin hankali ba inda maimakon Umma ta gyara sai ta sake k'aimi cikin fito da sabon salo.

Hassada gami da kishin Umma ga Mamie Fulani ya samo asali ne akan tazararsu da juna tun
daga kan Ilimin addini dana boko zuwa dukiya wanda idan bata zarta mai martaba ba to zasu
iya zuwa kunnen doki dan mahaifinta mai tarin arziki ne wanda kowa ya shaida a cikin birnin
Mungaye da wajenta, ya rasu ya bar musu gado wanda ita da yayanta na miji É—aya da
k'anwarka suka gada sannan tun kafin ta auri mai martaba tana kasuwanci wanda ke kawo
mata kuÉ—i domin tun kafin ta shiga Jami'a ta mallaki restaurant na kanta wanda a yanzu shi ne
wurin cin abinci mafi girma da k'ayatuwa a cikin birnin Mungaye. Wannan ya tsole idon Ummu
duk kuwa da tana amfana da shi ita da 'ya'yanta dan Mamie Fulani mai kyauta ce bata taɓa
nuna bambanci tsakanin 'ya'yan Umma da nata, ko me suke so ta kanyi musu domin kusan ita
ta raini Sardauna da Sadauki tare da Imam shi yasa duk fitsarar Sardauna baiyi mata sai dai ya
k'are a kan Sadauki marainin wayonshi wanda ke d'aga masa ƙafa ba dan tsoro ba sai dan koyi
da halin fiyayyen halitta Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam inda ya ce da mu zamo masu
yawan hak'uri.

Har izuwa yanzu Umma tana kan sanya rashin jituwa tsakanin 'ya'yanta dana Mamie sai dai ba
dukansu ne suke bayanta ba, tafi samun kan Sardauna sama da kowa, shi yasa take ji da shi
tamkar kwai duk da shima Sardaunan a cikin Masarauta ne ke nuna mugun halin da tsanarshi
ga Sadauki amma da zarar sun fita wajenta tamkar babu komi tsakaninsu ke nunawa wannan
halin ya aroshi ne dole ya yafa saboda gargadin mai martaba dan ya tabbatar masa duk ranar
da labari ya zo masa ya wulak'an 'yan uwarshi a bainar jama'a to ya tabbatar da ya bar masa
Masarauta bari na har abada, ba Sardauna ba hatta da Umma gargad'in ya ratsa
kwa-kwalwanta sai ta d'orashi a tsarin fitowa a mai fuska biyu irin yarda take yin takonka shi ne
dalilin da Imam kan ambata masa kalman a wasu lokuta in har ya taɓa Sadauki sai ya zamo
Imam ne abokin karawarshi amai makon Sadauki.

Kaunanr Sadauki da Imam ya samo asali ne tun yarinta inda aka kawoma Mamaie Fulani yayen
Imam ta haÉ—ashi da su Sardauna ta raina har zuwa sadda sukayi hankali kowa ya koma gaban
mahaifiyarshi sai dai har kwanan gobe Imam yana yiwa Mamie Fulani daukan uwa tamkar
wacce ta tsuguna ta haifeshi shi yasa ba'a yi masa shamaki da shiga shashin mai martaba a
duk sadda ya nemi hakan.

A b'angaren 'ya'yan Mamie Fulani kuwa ba ruwansu da rashin d'a'a ga Umma domin Mami
Fulani ta horesu da kada su sake su shiga faÉ—ar da babu ruwansu ciki. Sai dai duk wannan
zaman lafiyar da Mamaie Fulani keyi ga kowa a masarautar hakan bai hanata gamuwa da
mak'iya ba wand'anda suke takewa Umma baya irin matar Sarkin Fada dama wasu kamar dai
yarda mafi akasarin gidan Sarauta aka sanshi bai rasa 'yan bani na iya, ma hassada da 'yan
birne-birne asirai duk dan ganin bayan wanda ya fi su samun Ni'imomin rayuwa har da wurin
Mahalicci domin duk wanda yafika tawakkali na yarda da ƙaddara khairan ko kishiyarta to ya
fika samun duk kan Ni'imomi wurin Ubangiji Allah Subhanahu wata'ala.

(Allah ka ƙara cire mana tsa-tsa a zukata domin alfarman Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam Amin).

***
Washe gari a makare Sadauki ya tashi dan ko masjid bai sami zuwa ba lamarin da ya bak'anta
masa rai ya k'arajin tsanar budurwan Aljanar domin ita ce silar makarar shi dan bai samu barci
ba sai wuraren ƙarfe uku na dare wanda ya yisa cike da mafarkan daji mai duhu yanata neman
hanyar fita ya rasa a ƙarshe ita ce ta bayyana cikin guguwa ta d'aukeshi sukayi sama. Lamarin
da ya kasa b'acewa a kwakwalwar shi ganin taimakon da ta yi masa alhalin ita d'in azzaluma ce.

"Mitcheww! Hak'ik'a ina cikin damuwa matsananci, shin aina zan sake gamuwa da ita?"

'Aliyu ko dai fansa take É—auka?'

"No! Banyi mata komi ba sai bisa tsautsayi wanda ita ta janyo afkuwanshi."

Ya ambata cikin bawa zuciyarshi tabbacin shi mara laifin ne duk da wani shashi na zuciyarsa na
ƙaryata hakan amma kaso mafi rinjaye bashi gaskiya keyi. Wanka ga gabatar sannan ya yi
sallah ya koma saman gado ya kwanta dafe da k'irjinsa ya fad'a kogin karatun wasik'ar jaki
wanda bai amfanarsa da komi sai sake shiga damuwa. Babban damuwarsa yarda yake kasa
neman tsari da yarinyar haka yanzu bai iya tashi raya dare da nafil-fili kamar yarda ya horu da
yin hakan a baya, jin bak'on lamarin na son sake ziyartanshi sai ya soma hailalah zuwa can ya
tashi ya shirya cikin shigar sarauta har da yin rawani wanda ya k'ayata fuskanshi ya fito a Mai
Martaba sak.

Siyayyar da yiyowa su mai martaba ya É—auka ya bar na k'anninsa. Yana fitowa da Saudauna ya
haÉ—a idanu yana zaune a daf da shiga babban falon sashin Mai martaba, cikin nuna kulawa ya
karasa gabanshi ya miƙa mashi hannu tare da ambatar sallama, k'eme-me Sardauna ya k'i
amasawa balle bashi hannun dan musabaha, shanye ɓacin ransa Sadauki ya yi ya doshi shiga
falon Sardauna ya kara masa ƙafa ya daka tsalle gefe k'iris ya rage bai faɗi ba, kallonsa ya yi
tamkar zaiyi magana sai kuma ya gintse ya shige falon cikin sar-sarfa.

"Sarauta dai sai gani ga masu gani"

Sadauki na jiyo kalamamshi wanda ya soki zuciyarshi domin yana son Sarauta tamkar rai da
ajali, a hasashenma ya fi Sardauna kaunar zamowa magajin mahaifinsu.

Mai martaba ya samu yana ƙaryawa ya tako a sannu ya russuna ya kwashi gaisuwa sannnan
ya zauna sosai cike da ladabi kansa ƙasa yana wasa da yatsun hannunsa.

"Aliyu Saudauki Baban My Fulani, ina godiya."

Mai martaba ya furta yana janyo jakan da Sadauki ya ajiye a gefenshi.

Motsa kai Sadauki ya yi yana murmushi domin lamarin mahaifin nasu game da ambatawa
Mahaifiyarsu kalma mai nuni da tsan-tsar kaunarsa gareta ya daina bawa kowa na gidan kunya
domin a gaban kowa ambatarta ya ke da My Fulani ko my Queen.

Gyaran murya Mai martaba ya yi yasa Sadauki maida hankalinsa kanshi tare da gyara zama ya
tsira masa ido.

"Aliyu ina da magana da kai mai mahummanci a game da abin kunyar da kake aikatawa wanda
lamari ne da ya taɓa martaban Masarautarmu domin auri saki babban zunubi ne a tarihin
kafuwar Masarautan Mungaye dama cikin addinin musulinci. Domin ba'a taɓa samun wanda ya
taɓa sakin matarsa ba har sai mutuwa ce ta rabasu sai yanzu akanka dan haka ina mai sanar
da kai hukuncina na ƙarshe akan lamarin shi ne duk ranar da ka sake sakin matarkata ta
sunnah wallahi kaji na rantse bani ba ...

"Na tuba Abbana, ku yafemin dan girman Allah, na rok'eka kada ka furta kalman da zai iya
zamemin matsala ko ya zamo ajalina."

Ya katse Mai martaba da sauri yana mai d'aga hannayensa sama alamun ban hak'uri.

Shiru Mai martaba ya yi yana kallonsa wanda har lokacin ke saman guiwoyinsa.

"Zauna da kyau ga kayan karin kumallo nan kayi."

"Na k'oshi Abba."

"Na soma wasa da kai ne?"

Girgiza kai ya yi tare da É—aukan kofi ya zuba kunun alkama ya soma kurb'a a hankali yana jin
gard'in Nono tare da madara da aka wadata kunun da shi na ratsa harshensa sai ya lumshe ido
zamowarshi masoyin duk abinda ke da alak'a da Nonon shanu.

Bayan ya kammala hira mai cike da fahimta suka b'alle da Mai martaba wanda a cikin dibara ke
tunasar da Sadauki mahimmancin aure ga baligi musamman wanda ke burin zama jagorar
al'umma. Sadauki na amsar nasihohin cike da alfahari da samuwar mahaifinasu a matsayin uba
mai tarin nagarta. Suna tsaka da hirar Sardauna ya nemi izinin shigowa Mai Martaba ya dama
ya shigo cikin ladabi ya zauna tare da mik'o gaisuwa ga Mai martaba da Sadauki suka amsa
daga nan aka É—ora hirar da shi har zuwa lokacin fita fadar Mai martaba ya yi ya sallamesu
Mamie Fulani ta shigo ta taimaka masa ya shirya ya fice ta rakoshi har daf da k'ofar shiga fada
da ke k'ofar sirri wanda Sarki ne kaÉ—ai ke shiga ta nan duk ranakun girkin Mamie Fulani domin
tana yi mara rakiya yayin da Umma ba ruwanta da bashi wannan kulawar dan tana kiranshi da
munafunci ne k'anin karuwanci.

Hak'ik'a a wurin kula da Mai martaba tundaga kula da cikinsa zuwa walwalanshi ya fi samunsa a
wurin Mamie Fulani dan ko ba ranar girkinta ba ne ya kan sanya ta yi masa girki tun Umma na
masifa har ta gaji ta bari domin mai martaba Abdul Hakam tsayayye ne akan iyalinsa yarda ya
ke shugaban al'umma haka ya ke shugaba a wurin iyalinsa sam bai É—aukan rainin hankali akan
abin da yake ikonsa. Shi yasa yake girmama duk abin da Mamie Fulani tazo masa da shi ko da
kuwa bai cikin tsarinsa zai amsa da hannu biyu ballema bata fiye zuwa masa da abin da bai
zamowa dai-dai da ra'ayinsa ba.

Soyayyarsa gareta ya samo asaline na kaunar da sukeyiwa juna tun kafin a aura mashi Umma
wacce ta zamo k'anwa gareshi domin da maifinsa da na Umma ubansu É—aya, ya ci burin soma
aure Mamaie Fulani a farko amma mahaifinsa ya ce a'a ga zaɓinsa da yake mai biyayya ne ya
amsa baki alaikum, shi yasa ko haihuwar fari Umma batayi ba ya auro Mamie Fulani sai dai
bata sami haihuwa ba har saida Umma ta haihu uku duka mata sannan Allah ya bata kyautar
'yan biyu suma duk Mata, a haihuwar Umma na biyar ne Mamie Fulani ta yiwa 'yan biyunta
gambo inda ta sami Aliyu, bayan shi ta sake haihuwar 'yan biyu maza Junaid da Jabir. Yanzu
haka Mamie Fulani na da set din 'yan biyu uku, mata uku maza uku saboda a set na uku mace
da namiji tayo, Saifullah da Lailah sai ta yi auta takwarar mai martaba suna kiranshi Mu'allim.
'Ya'yanta bakwai kenan, mata uku maza huÉ—u yayin da Umma ke da goma, mata takwas maza
biyu. A nanma Umma na cike da hassadar Mamie Fulani akan finta da 'ya'ya maza da ta yi, sam
ba ta gode Allah ba da ya albarkaceta itama da samun 'ya'ya mata jigon ginuwar al'umma.

***
Sardauna

"Umma dan Allah ki bar batun nan ban son jinsa, matata ta isheni rayuwa, ni bana cikin maza
masu ra'ayin tara mata duk da ina son mulki amma banjin zan iya ajiye mace sama da É—aya
ba."

"Saboda kana ragon maza ba."

"Umma kema kin bi hanyar kirana da sunar da na tsana ko?"

"Eh nabi d'in kuma ba k'arya akayi ba, rago ne kai ta ko wani fuska, izzar mulkin kawai ka ajiye
gami da bak'ar zuciya amma a nuna k'wanji ko sakaryan mace ta fika katab'us."

"Umma wallahi zan bar miki falonki tunda hakan kike so."

"Gaskiya ne baka son a fad'a kuma sai na faÉ—a, sai dai kafi ruwa gudu. Wallahi ina kam takaicin
zamowarka mai tarin rauni a cikin 'ya'ya mafi soyuwa gareni, in dama a ce ana canji da bilahil
azim dana canjaka da autana Sayyid ya dawo kai ka koma shi ko burina ya cika na zamowa
uwa ga Sarkin Mungaye."
A fusace ya juya zai fice ta daka masa tsawa ya dawo ya zauna jikinsa na rawa saboda ɓacin

rai.

"Aifa kam a fushi nan kafi auki kamar wani jarumi."

"Umma Please stop saying such kind of things dan wallahi suna k'omanin rai, ina jin tamkar
zuciyata zatayi bindiga tayo waje ta tarwatse."

"Natsu! Sardauna, ka samu bani hankalinka nan."

Ta ambata cikin daka masa tsawa cike da takaici.

Idanu ya tsirawa Umma fuska a haÉ—e, murmusawa ta yi tare da cewa "Kaga Sarkin birnin
Mungaye ba, ta kawarka lafiya dan Sarki jikan sarki magajin Mai Martaba Abdul Hakam Hashim
Malle."

Murmushi ya yi tare kare fuskanshi da tafin hannunsa na dama cike da jin daÉ—in kirarin da ta yi
masa kuma a take fushin da ya ke ciki ya sauka.

"Ko kai fa Yarima, yanzu buÉ—e kunnuwanka ka saurari labarin fitar da na yi daren jiya cikin
b'adda kama."

"Duk kan natsuwata na tare da ke ya ke Ummata."

Muskutawa ta yi daga kishingid'en da ta ke ta soma magana cike da walwala bisa alamu
bayanin na faranta mata rai sai dai ga Sardauna abin bai yi masa daÉ—i ba domin sai tab'e baki
ya keyi tare da girgiza kai tana dasa aya kuwa ya mik'e tsaye rai a b'ace ya soma magana.

"No Umma bana son jin irin wannan shirmen na bokaye, shin in banda ya rainawa mutane
hankali ta ya zaici miliyan biyu da rabi ya tsaya yiwa Aljanu karyan wai suna bibiyan Sadauki
dan daukan fansa, k'ila Ubanshi ya turosu daukan fansa! To wallahi tun wuri ya dawo
hayyacinsa dan baici bulus ba dole sai yayo kashin kud'ad'en nan tunda ba da Kakan Uban
Ubanshi muka nemosu ba."

"Sardauna koma ka zauna ko ranka yafi nawa ɓaci kuma kada na sake jin ka zagi Malam Sile
dan ba sa'arka ba ne sannan duk wanda ya ce zai taimakeka ai fi gaban wulak'antawa."

"Nifa Ummu bai taimakeni ba ya dai taimaki kansa dan haka sai ya biyani dukiyana."

"Na ce ka zauna muyi maganar."

"Affuwan Ummu sai anjima zan dawo jin tatsuniyar rainin hankalin da sile ya yi miki domin na
gama kiransa da Malam daga yau."

Baki buÉ—e Ummu ta raka bayansa da kallo har ya fice falon, tashi zaune ta yi daga kishingid'en
ta dauko wayarta ta latsa kira ana dauka ta ce "Hajiya Kilishi maza ki zo in ban takuraki ba."

"Lafiya kuwa Hajiya Umma?"

"Ba lafiya Hajiya Kilishi."

"Innalillahi! To gani nan zuwa ta k'ofar baya ki fito ki buÉ—e min a sirrance kinsan munafukai sun
soma saka mana ido."

Momyn Haske ce 🥰

*Muna saida ingantaccen man ayu wanda ya zo daga Chad. Yana maganin Infection, asma,
limoniya, mura, ciwon basira ciwon

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login