Showing 30001 words to 33000 words out of 45162 words

Chapter 11 - HATSABIBIN TSIBIRI Littafin Yaki Book Complete .pdf

Unknown   

25 Mar 2025

5206

zai shiga fadar domin ganawan sirri da Ifritu Baushe akan
uwar gijiyarshi Lina.

Bai samo mafita ba ya jiyo ruguji a bayanshi bai waiwayo ba ya buÉ—e zafin hannunshi domin
sanin me ke faruwa, wani dutse ne ke fitar da wuta ya nufoshi irin dai wanda ya so halakashi a
fadar Kaka Gunu kwanakin baya. A gigice ya juyo tare da neman hanyan tsira sai dai ya
makaro domin dutsen ya cimmasa ya bangajeshi a take ya cillashi ƙasan tsaunin inda ke kai
inda farin hayak'i ke fitowa mai kama da tafiyar giragizai a sararin samaniya. Kafin ya sauka
ƙasa yaji anyo sama da shi wani iska mai ƙarfi ya nashe idanunsa. Bayan wuce mintinan da
basu wuce biyu zuwa uku ba ya ji an saukeshi ya zabura sai ya yi ido biyu da Ifritu Baushe, ya
bushe da dariya mai fitar amo tamkar cidan hadari ya jima yanayi kafin ya dakata ya soma yiwa
kan sa kirata...

"Sai ni Baushe mugun itace, Baushe mai hayak'in masifu, Baushe bai san na gida ba tunda ya

zamo ajalin ubanshi mahaifi, Baushe k'i sabo dan ko hadimansa bai d'awa ƙafa ba, ko ank'i ko
amso sai nayi mulkin sarkin sakakunar Aljanu da Mutane."

Ya dakata yana kallo Tsidau da ya koma tamkar d'an tsako a gaban giwa.

Momyn Haske ce 🥰

Muna saida ingantaccen man ayu wanda ya zo daga Chad. Yana maganin Infection, asma,
limoniya, mura, ciwon basira ciwon kai, ciwon baya, ciwon ƙafa, ciwon mara, kaikayin jiki dana
matse-matsi, yalwatuwar ni'ima tare da samun gamsuwa a turaka da sauransu, muna saida
É—aya ko sari mai so zai iya tuntubar number nan ta WhatsApp ko kira. 08132166848. Yarda ake
amfani da shi za a jik'a Lipton sai a d'iga man ayu a ciki a shanye da d'umi-d'umi za a iya zuba
zuma ko siga a ruwan Lipton d'in dan gudun d'aci haka za a iya zubawa a ruwan Tea a sha.
Masu asma da limoniya kuma zasu jajjaga tafarnuwa su matse ruwan su zuba ruwan d'umi da
man ayu su shanye. Masu Infection duk in suka wanke wurin da ruwan zafi sai su saka man ayu
haka masu kaikayin jiki idan sun fito wanka sai su shafa amma zasu sha da ruwan Lipton, Allah
ya ƙara mana lafiya Amin.*
[1/13, 12:05 AM] Mrsjmoon: HATSABIBIN TSIBIBI
By Mrsjmoon.

Adabi Writer's Association.

12.

" Ya kai Tsidau amintaccen bawan Sadauki GauÉ—u da Gimbiya Lina ni Baushe k'i sabo na san
buk'atarka sai dai ka makaro domin nima hanyar nake nema tsawon shekaru tun kafin a haifi
Uban mahaifin GauÉ—u domin Zoben na Kakan Uba na ne aminci yasa ya sadaukarwa Kakan
Sadauki GauÉ—u na huÉ—u, Ubana, ya yi bakin iyawarshi yaga ya mallako Zoben ya dawo a
halinmu saboda shi ne yafi k'ulafucin mallakan Zoben tun sadda ya sami labari a wurin aminin
mahaifinsa amma ya kasa hasalima ya kasa tun k'arar inda Zoben yake ajiye, da wannan baƙin
cikin ya rayuwa to bayan na girma na fahimci burin Ubana sai dai bincikena ya tabbatarmin sai
na kashe shi na sha jininsa sannan zan soma taka k'amshin mallakan sihirtaccen Zoben sai na
aikata hakan a wani dare da muka fita na koyar da ni sanin alk'alaman tsafi sai nayi amfani da
dmar na halakashi na shanye jininsa tare da nad'e duk alk'aliman tsafinsa. Dama ni kad'ai na
rayuwa cikin 'ya'yansa, Uwata ta mutu bisa cin amanarta da yayi inda ya sadaukar da ita duk
bisa neman hanyar Mallakan Zoben.

Daga nan ban koma gida ba na nausa cikin daji na yi ta neman ilmomin sihiri kuma duk wanda
na k'aru da shi to nine a jalinsa a haka na haÉ—u da gawurtaccen matsafi wanda ya haskamin
amfanin da Zoben sihirin zaiyimin kana ya riƙe ni tsawon shekaru har zuwa sadda aka haifi
uban Sadauki GauÉ—u daga nan ya mallakin duk kan tsafinsa tare da hadimansa dangin
hatsabiban aljannu da mutane wanda suka maidani Ifritu na zamo k'wan jimina gagara É—aukan
Shaho, na gagari har da su kansu hatsabiban shed'anun alhjannu da mutane na zamo tamkar

ba zan mutu ba domin bana jin zan bar Duniya sai an hura k'aho tamkar yarda aka halicci aljanu
haka nake jin kaina domin naga zamanai na matsafa daban-daban, ni kuma an kasa ganin
nawa "

Ya bushe da dariya wacce bishiyoyi suka soma rangaji suna busar da iska mai ƙarfi.

'Hak'ik'a Baushe yafi ƙarfin hilata dole na samo mafita domin tsira da rayuwata kada na ƙare a
yi masa bauta.'

"Tabbas Tsidau daga yau kazama hadimina, dole kayimin bauta tamkar yarda wanda suka fika
komi suke k'asan ikona in kuma ba haka ba dole ka amince da sharad'ina akan shugabanka
Gimbiya Lina."

"Sanarmin inji me ye sharad'in? Dan ba a yoni domin bautawa azzalimi irinka ba."

Wani dariya ya sake bushewa da shi domin abu mafi yi masa daÉ—i shi ne a ambata masa
kalman zalinci.

'Duk da nayi biyayya ga zantukanki Gimbiya da ban kasance a wannan wuri mai cike da hatsari
ba.'

"Ka natsu Tsidau domin zantukan zuccinka ba zai amfaneka da komi ba."

"Ina sauraren sharad'in naka."

"Idan na ambata dole sai ka amince da shi, kai ko ban ambata ba amincewarka wajibi ne."

"Ina sauraronka ya Sarkin Sarakunar Aljannu da Matsafa."

Ya ambata cikin ladabi.

"Hilarka ba zaiyi tasiri a wannan Fadar ba ya kai Tsidau garama ka ajiye kalaman yaudararka
wata k'ila gaba za suyima amfani."

"Sanar dani buk'atarka ya Ifritu Baushe."

Wannan karan cikin rashin tsoro ya ambata.

"Da kyau Sadauki Tsidau, to maza buÉ—e masu jinka ka saurari bayanina wato kawomin Lina
fadana tare da Zoben sihirin dake tare da ita, a daidai lokacin da ta sanya ya zamo nine mutum
na farko da zanyi ido biyu da ita bayan kai."

"Ko zan san dalilinka na neman hakan?"

"Cikar ikona ba zai samu ba sai Gimbiya Lina ta zamo É—aya daga cikin Matana ta haifamin
yarinya mai kama da ita na sha jininsa to daga ranar burina zai zamo tabbatacce ita kuma zan
kasheta da hannuna bayan na sha jinin 'yarta a gaban idonta."

"Ba zan yarda a kashemin uwar d'aki a irin wannan kisan wukak'ancin ba domin nayiwa Jarumi
Gauɗu alk'awarin kula da ita har ƙarshen rayuwata, dalilin da yasa kenan na zo Fadarka samun
wani ilimi da zai bani damar hanata saka Zoben sihiri saboda sakashi mutuwarta ne ya
kusanto."
"Tabbas ni ne ajalinta kuma wannan bayanin shi ne ya buÉ—e maka kake hango mutuwarta
sannan tunda ka saurari manufata cikamin aiki dole ne ko in É—auko iyalanta na halakasu a
gaban idonka, in na ce iyalanka ina nufi kaf zuri'arka zan tiso k'yeyarsu."

'Tirk'ashi na kawo kaina gidan jafa'i da masifa."

"Ko baka kawo kanka ba za'a kawomin kai domin na soma gadinka tun sadda Sadauki GauÉ—u
suka soma faÉ—a da Ubanshi akan Zoben."

"Ko zan san abinda yasa tun a lokacin baka nemo Gimbiya Lina ba?"

"Bata da abin so ne sai sadda Sadauki GauÉ—u ya sadaukar mata da tsafinsa to a lokacin ta
shigo cikin k'omata dama ina jiran zuwar ranar domin tun kafin a haifeta nake da tabbacin a
hannunta zan sami cikar burinsa."

"Shugabata ba zata zo fadarka ba domin nasha jin tana ambatar tsanar azzalimi, tana adawa
da mulki irin naka hatta kuwa da irin mulkin Babanta, tabbaas tana da burin kawo ƙarshen irinku
a doron ƙasa dan haka ban san ta yarda zan faɗa mata ta zo gareka ba."

"Dole ka zamo maci amana idan zaka yimin aiki dan bana harka da masu gaskiya gami da
tausayi ko Lina domin zan amfana da ita ne amma da yaƙi ne zai rabani da ita duk da ina hango
wani al'amari na tun ƙarota wanda ya b'oyu gareni dan haka zan barka ka huta ga abin more
rayuwa nan sai wanda kaga damar amfani da shi zan dawo gareka bayan kwanaki biyu sannan
a lokacin zaka tafi kazomin da Gimbiya Lina ko ta wani hali sai ka wanzu cikin nemo mafita ina
sake sanar da kai cin amana shi ne matakin tsirarka daga hannuna."

Daga haka ya b'ace Tsidau ya fad'a kogin tunani daga haka wani barci ya sureshi wanda
rabonsa da yin barci har ya manta domin baya cikin jinsin aljannu masu barci.

***
Lima ta fito daga gidan shak'atawa bayan ta halaka samarin da suka d'ebe mata kewa ta kuma
b'atar da su tare mantar da jama'ar mashaya lamarin wanda ta saba aikata hakan duk wanda ya
kusanceta to bai kai labari sannan ba wanda zai sake neman d'ansa wannan sa'ar ta sameshi

ne daga Kaka Gunu domin duk wanda ta b'atar yana zamowa arzikin Masarautar ne inda kuÉ—i
zai ƙara taruwa a baitul mali sannan mafi ƙarancin mutanen da ta ke halakawa a duk sadda ta
ziyarci mashaya to mutum biyu zuwa uku ne saboda zamowarta mai ƙarfi sha'awa, wannan hali
nata na ciwa Gaimbiya Lina tuwo a k'warya har da shi ya zabura da ita ta fita nemo ilimin tsafi
domin kawo ƙarshen k'adarin 'yar uwan nata.

Cikin Izza Lima ta cigaba da tafiya tana fatahi da duk wanda taci karo da shi a hanya, kafin ta
isa gida ta raunata jama'a masu yawa ciki harda tsoffi, shi yasa ba wanda ke son yin karo da ita,
ƙaunarsu naga Gimbiya Lina. Muhallin Mahaifiyarsu ta nufa tana ƙara haɗe rai. Ta sami Mah
zaune gaban bangon É—akin tana hira da Gimbiya Lina wacce ke kwance saman ruwan Tekun
Kabobo, jikinta babu kayan kirki, fatarta sai É—aukan ido keyi mai nuni da hutu ya gama ratsata.
Mah na ganin Lima ta shigo ta kirawota da hannu ta iso gabanta tana gabgowa Lina harara
yayin da ita ke murmushi cike da nishad'i.

"Lina ga Lima ku sasanta bana son rabuwar kanku kunji 'yan biyuna, farin cikina?"

"Ni kam Mah ina sonta ita ce bata sona."

Lina ta ambata a hankali.

"Eh bazan taɓa sonki ba, munafuka kawai, mai fuska biyu."

"Kin jita ko Mah?"

"Kiyi hak'uri Lina, 'yar uwanki mai zafi ce komi zai wuce zanyi magana da ita domin yaÉ—uwar
kanku nake buƙata sama da komi yanzu."

"To Mah ni na wuce zan tafi ceton rai a wani kogi, ga jirjin ruwa can na shirin faÉ—i da mutane
ciki."

"Nasara na tare da ke ya ke 'yata."

"Godiya nake Uwa abin farin 'ya'yanta.

Daga haka ta b'ace daga jikin bangon Mah ta fuskanci Lima cikin tsuke fusaka ta ce "Daga yau
ban son nasake jin kin ambaci tsana ga 'yar uwanki idan kuma kika sake zan nunamiki wacece
ni sannan bana son zuwa mashaya da kikeyi shi ke janyo miki tsana ga Jama'ar Tsibiri domin
hatta da mahaifinku baya son abinda kike aikatawa, kiyo koyi da 'yar uwanki zaifi miki khairan
ko kya samu damar hawa karagar mulkin Tsibiri wanda ya ke babban burinki."

Sai a nan ta saki rai jin ta ambaci hawa mulkin Tsibiri ta dawo gaban Mah ta zauna tana wani
langab'ewa kana ta ce "In har kina sona da mulkin Tsibiri to kije d'akin Abun ki tsareshi kada ya
biyoni domin mallakan gadona na wurin Kaka Gunu."

"Kunfi kusa Lima ki rok'eshi ya bar maki kayanki."

"Ba zai bari ba Mah domin shima na burin mallakan Ruwan Albarkan."

"To ki gyara mu'amalanki da Lina na san zata taimakeki ki mallaka."

"Idan itama burinta na ta mallaki Ruwan ne fa?"

"Zata bar miki domin adala ce kinfi kowa sanin hakan."

"To zan nemeta mu sasanta."

"Haka na ke son ji 'yata."

Juya kai gefe Lima ta yi tana haskowa ruhinta wani mugun nufi akan Lina sai ta saki murmushi
tare da hayewa gadon Mah ta kulle ido ganin haka yasa Mah ta fice zuwa turakar mijinta
wannan damar Lima ta samu ta mik'e ta shafi bangon da Mah ke hira da Lina sai kuwa ga Lina
ta bayyana saman dutsen kogin Babobo iska na kad'a gashinta na rufe mata fuska tana
yayewa.

"Ya akayi Lima? Na san zaki nemeni shi yasa na tura Tsidau ya taimaki mutanen girjin na
dakata jiranki, ina saurarenki."

"Ki zo ki taimakeni na É—auko gadona a Bukkan Kaka Gunu."

"Zan zo amma ba yanzu ba sai Abun ya taho nemana dan haka ki nuna mashi kin hak'ura da
gadon hakan zai bashi damar barin Tsibiri a sirrance domin yanzu yafi buƙatar mallakan Zoben
dake gareni akan ruwan albarkan."

"To sai kinzo ina da abinyi."

Murmushi Lina ta yi tare da mik'ewa ta kalli Lima ta ce "Zan zo mu kwana tare yau sannan zan
baki labarin da kike nema na cikin jikina da wanda yayimin."

Cike da zumud'i Lima ta buÉ—e baki zatayi magana Lina ta d'aga mata hannu tare da b'acewa a
take bangon ya dawo yarda ya ke. Dafe kanta ta yi cike da takaicin b'acewar Lina. Ta fito zuwa
d'akinsu dake saman wani dutse daga gefen turakar Mahaifinsu.

***
Mah na shiga turkan mijinta ta fahimci yana d'akin sirri sai ta sami wuri ta zauna ta tsirawa wani
taswira ido wanda sai a yau ta ganshi a turakan sai ta shiga mamakin lamarin abinda ya É—auki
hankalinta har ta shagala da kallonsa sai ta soma ganin tamkar ta koma wani wurin ba turakan

take ciki ba, mik'ewa tayi dan isa gaban Taswiran sai taga haske na fitowa daga cikinsa da ta
matsa sosai sai taga hanyace ta buÉ—e daga cikin Taswiran sai taja da baya cike da tsoro amma
sai taji ana janyota sai ta soma tattaro tsafintata dan amfani da shi sai dai ya kasa tsiri wurin
bata kariya, ihu ta soma dan neman taimako amma sai muryanta ya daina fita illa ita É—aya
takejin fitar kayanta, tsawon lokaci ana son jefata cikin Taswira ita kuma tak'i shiga duk da
tsafinta ya k'i aiki sai dai tun can ita ɗin mai ƙarfi dantsen ne.

Mah ta jigata iya jigata har ta sare, ƙafarta na hagu ya soma shiga hanyar inda takejin hucin
zafin wuta na dokar ƙafar. Sauka wani abu taji dif!! Kafin ta tantance meye iskan guguwa ya
nad'eta ya jangota. A take Taswiran ya nad'e kansa ya b'ace b'at, bangon ya koma tamkar wani
abu bai taɓa zama ba.
" 'Yata Lina."

"Na'am Mah, kwanta ki huta nadawo Tsibiri bazan sake barinki ba ko da hakan na nufin ajalina
ne."

"Me ke faruwa Lina?"

"Mah cin amana yayi yawa, zalunci ya kewaye duniya ya zamo har da na jikinka za'a cuceka."

"Waye ya so aikatamin mugun abun nan?"

"Mah saninsa tarin damuwa ce gareki amma da sannu zaki san ko waye ke farautan rayuwarki
domin ya sami cikan burinsa na samun Duniya."

"Lina taho na runguneki."

Ba musu ta iso gaban mahaifiyar nata suka rungume juna, hawaye na zubowa daga ida uwarsu
na sauka a gadon bayan junarsu.

"Zan sanja miki wurin zama mai cike da tsaro Mah."

"A'a Lina ki barni a nan mahaifinku garkuwa ne gareni."

"Idan shi ne ke son halakaki fa?"

"Ba zai taɓa faruwa ba Lina, duk tarin zalunci mahaifinku ba zai taɓa sadaukar da abinda yafi so
sama da komi ba dan haka ki barni tare da shi tunda kin dawo ba abinda zai sameni."

Janye jikinsa Lina ta yi batare da ta sake furta kalma ba, ta soma zagaye d'akin zuwa can ta
tsaya ta dubi Mah ta ce "Ina da aiyuka a gabana wanda ban san adadinsu ba kuma ban san
mai taimakamin ba haka ban san ranar kammalasu ba."

"Ki sassautama kanki lamaura ya ke 'yata kada na rasaki."

"Mah banzo duniya dan samun hutu ba, ina cikin matsala tunda nace zan saka Zoben can mai
makon naga lamura nayimin sauk'i sai sake rikicewa sukeyi shi yasa nake neman amincewarki
da ki yarda na nesantaki da Tsibiri na wani lokaci in komi ya daidaita sai na dawo da ke saboda
zamanki anan barazana ne a gareni domin za'a taɓamin ke dan a sami galaba a kaina, Mah ki
amince na maidake saman Tekun Kabobo na killaceki ko kogon da gangan jikin Sadauki GauÉ—u
ke ciki nayi miki alk'awarin zuwa ganinki kullum dan É—ebe miki kewa haka komi kike so na
dangin abinci da bin sha zaki samesu."

"Lina kincemin fa kin dawo Tsibiri to me yasa zaki É—aukeni a cikinsa ke ki zauna."

"Na sanar miki da hakan ne dan hankalinki ya kwanta amma ban dawo ba."

"Lina ba inda zanje."

Tamkar zata fashe da kuka take duban Mah sai kuma ta zabura ta nufi k'ofar fita tana cewa
"Mah zan dawo anjima kada ki sanar da kowa zantukanmu ko da kuwa Abun ne ko Lima."

Kafin Mah ta yi magana ta fice a gaggauce, hawaye ne suka zubowa Mah na tausayin rayuwar
da 'yarta ke ciki domin tana burin rayuwa da 'yarta a kusa da ita tamkar yarda takeyi da Lima.

"Lina dole ki janye son hawa karagar mulkin nan ko na samu kusanci da ke kamar can baya."

Mah ta ambata cike da tarin damuwa.

"Mah."

Da sauri ta waigo Lima ce tsaye.

"Kin haÉ—u da 'yar uwanki Lima?"

"A'a, shin ta zo ne?"

"Eh."

"Me ta sanar da ke?"

Batare da tuno gargadin Lina ba ta sanar da Lima duk abinda ya faru tundaga zuwarta turakan
Abun har tafiyar Lina.

"Ina zuwa."

Itama ta fice da sauri tana fita ta yi girgiza sai ga Abun ya bayyana fuska a murtuke.

"Hak'ik'a Lina kina da wayau dole na san waye Sadauki GauÉ—u kafin na mallaki Zoben sirihin
hannunki ta wannan hanyar na basaja tabbas yanzu zanyi fito na fito da ke duk da ba hakan
raina ya so ba."

Ya ambata cike da ɓacin rai.

Ba jimawa Buda ya isa saman ingarman dokinsa Abun ya hau ya zabura

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login