Showing 36001 words to 39000 words out of 45162 words
Chapter 13 - HATSABIBIN TSIBIRI Littafin Yaki Book Complete .pdf
Unknown
25 Mar 2025
5211
shigarta sashin. Tafiya ta cigaba dayi a hankali tana kallon taurari da suka k'awata sararin
samaniya lamarin da yasa bata ganin abinda ke gabanta domin kanta a amsa take tafiyar
hasken taurarin na sake haska ruhinta tana hasko kanta tare da Sadauki suna nishad'i cike da
tarin ƙauna. Karo da juna sukayi wanda sam bai lura da ita ba yayin da itama bata san da
zuwarshi ba. A tare suka sunkuya ita cike da tsoro shi kuma tunaninsa yaji mata raunine domin
kafadarsa ne ya doki kirjinta, gano bataji ciwo ba yasa ya tsare gira yana kallon cikin idonta ya
furta "Sannu amm me yasa bakya lura da abinda ke gabanki?"
"Haka ake bada hak'uri tare da tuhuma?"
Itama ta furta fuska a haÉ—e.
Kunninta ya ja ta saki ƙara ya saketa da sauri tare da mik'ewa ya nufi hanyar Part din Mami
Fulani yana cewa "Kingama rainani amma da Ammi zan haÉ—aki kuma kika turomin macizai
Allah sai na tsoma kanki cikin k'oramar Mungaye Garding kifin nan ya tsole idanun rashin
kunya."
Lumshe idanu tayi cike da jin madarar ƙaunarsa na kuma cika ruhinta, bata furta masa kalma
ba har ya b'acewa ganinta shima ya cika da mamaki jin bata tankashi ba alhalin yasan bata
barin ta kwana komin k'araminsa sai ta maida martani musanman idan akansa ne domin ya
gano tana d'agawa kowa ƙafa ban da shi marainin wayonta.
Zubkud'a shoulder yayi dai-dai sadda ya sanya kai a falon yana cewa "Nayi sake ta san gadon
barcinsa amma zan gyara kurena dana bud'e mata sirrina da ko Imam bai sani ba."
"Waye ita Babana? Kuma meye damuwarka da ka kasa sanar da Amininka amma ka sanar da
mace?"
"Mamina Funanin mai mar...
"Amsa naka Babana, wai me yasa ka mai dani kamar Hajiya Dadah ce?"
"Allah sarki grandma na kwana biyu ban lek'ata ba amma in sha Allah gobe zan d'auki mara
kunyar can tayimin jagora dan ban iyawa da sababin Hajiya Dadah, Neerah ce dai-dai da ita."
"Allah Babana zan saɓa maka idan baka kiyayarmin tsohuwa ba."
"Kaina bisa wuya Mamina."
"Amsamin tambayana, wacce ita?."
"Mami yawan bincike fa baida kyau, dan Allah ki bari dan ba hurimin kiji sa ba ne."
Idanu ta tsira masa cike da zargi ganin haka ya kariso ya russuna ya gaisar da ita bata amsa ba
sai binsa da ido takeyi ya ba'ata rai tare da nufar kujera ya zauna ya tallabe kumatunsa.
"Babana kada ka sake mace ta zamo abokiyar sirrinka idan har ba matar aurenka ba ce."
"To Mami."
"Ina saurarenka ka ce zamuyi magana akan Companies."
Gyara zama yayi cike da natsuwa ya soma koro mata bayanen cigaban da Companies d'in suke
kan samu sai motsa kai takeyi cike da alfahari da ɗan nata, a ƙarshe ta sanya albarka tare da
bashi shawarwari da zasu sake bunk'asa kasuwancin nasu zamowarta wacce ta sami ilimi akan
kasuwanci.
Gyaran murya Mami tayi ya kalleta da sauri ta jinjina masa kai tare da soma magana "Babana
kai ne tamkar Uba ga k'annenka a d'akin nan to ina baka shawara da ka guje aikin da
mutuncinka zai zube kar wata rana su k'i yi maka biyayya, kaga yanzu Junaid da Jabir sun taso
har sun kai minzalin aure domin a wannan lokacin Mai Martaba ya ce zasu fitar da mata, nan da
lokaci kaÉ—an Allah zai basu rabo ya zamo 'ya'yansu ne manya a maimakon naka, dan Allah ba
dan ni ba ka fitar da matan aure kayi tare da zama da su bisa igiyoyin shi tun ƙasa bai rufe
idanuna ba, kaji Babana domin aure shi ne matakin cikar kalama."
Ta kai ƙarshen maganar idanunta na cikowa da ruwa.
"Zanyi aure Ammi dan Allah kada kiyimin kuka, wallahi zanyi a cikin tsakanin nan, ni dai fatana
ki duba lamarin kada ki juyamin baya kinji Ammina."
"Ka sanja magana Babana domin ba zan amince da wannan maganar ba."
"Ammina na tuba, wallahi ba zan baki kunya ba."
Banza tayi da shi ya cigaba da yi mata magiya tamkar zaiyi kuka.
***
Neerah kam ta sami lokaci mai tsawo duk'e a inda Sadauki ya barta sai doka murmushi takeyi
tare da bitan karatun ruhinta tana ƙara dilmiya cikin kogin ƙaunarsa.
"Hey Sis Neerah dama ina nemanki ido rufe."
Kallonta ta sauke kan Zuhrah wacce taci uban kwalliya tamkar zata party. Numfashi ta sauke
tare da kauda kai gefe tana jin haushin ganinta saboda tunowa da tayi itama na son abinda take
so.
"Please Sister zaki iya taimakona?"
"Me ke damunki?"
Ta ambata tare da mik'ewa tsaye fuska a haÉ—e.
"Makahon so."
"Me kike nufi?"
"Ciwon so ya kamani kuma ke ce hanyar samun maganinsa."
"Like how?"
"Ki taimakeni badan na isa ba sai dan shaƙuwar da ke tsakaninku da wanda kaf yaran
Masarauta ba wanda ke sakewa da shi sai ke kaÉ—ai shi ne nake neman tallafinki da ki sanar da
shi sak'on karatun ruhina wato Yaya Sadauki cewa shi ne zaɓin ruhin Zuhrah mai cike da burin
mallakanshi ita kaɗai dan har na sanar da Mamma shi ne zaɓina dan haka idan ya sami labarin
ya amince na zamo abokiyar rayuwarshi ko da bai shirya sake yin aure yanzu ba nayi masa
alk'awarin zama da shi har ƙarshen rayuwata domin da sonshi na rayu, zamowarshi auri saki
bai dameni ba dan shi É—in nake muradin ganin na amsa sunar mijin Zuhrah."
Da taimakon a'uziyya da Neerah ta riƙa ja tun soma maganar Zuhrah a cikin ranta yasa
shedanin dake buga gangar kishin hauka a zukatan mata yasa bai rabeta ba, badan haka ba
tabbaas da ba abinda zai hana bata kwashe Zuhrah da maruka marasa irga ba.
Momyn Haske ne.í ¾íµ°
*Muna saida ingantaccen man ayu wanda ya zo daga Chad. Yana maganin Infection, asma,
limoniya, mura, ciwon basira ciwon kai, ciwon baya, ciwon ƙafa, ciwon mara, kaikayin jiki dana
matse-matsi, yalwatuwar ni'ima tare da samun gamsuwa a turaka da sauransu, muna saida
É—aya ko sari mai so zai iya tuntubar number nan ta WhatsApp ko kira. 08132166848. Yarda ake
amfani da shi za a jik'a Lipton sai a d'iga man ayu a ciki a shanye da d'umi-d'umi za a iya zuba
zuma ko siga a ruwan Lipton d'in dan gudun d'aci haka za a iya zubawa a ruwan Tea a sha.
Masu asma da limoniya kuma zasu jajjaga tafarnuwa su matse ruwan su zuba ruwan d'umi da
man ayu su shanye. Masu Infection duk in suka wanke wurin da ruwan zafi sai su saka man ayu
haka masu kaikayin jiki idan sun fito wanka sai su shafa amma zasu sha da ruwan Lipton, Allah
ya ƙara mana lafiya Amin.*
[1/13, 12:05 AM] Mrsjmoon: Hatsabiban Tsibiri
By Mrsjmoon.
Adabi Writer's Association.
14.
"Dan Allah Dr. Neerah ki taimakeni na sami amincewar yaya Sadauki domin shi ne muradina
mahad'an ruhina a bisa igiyar aure."
Sabbin zantukan Zuhrah suka dawo da Neerah hayyacinta, sai da ta saita kanta kafin ta soma
magana cike da kamewa "Kiyi hak'uri, Muneerah bata cikin sokayen matan da so ke kaisu aikin
zubar da k'ima dan haka kai tsaye bazan iya taimakonki ba, hausawa suka ce iya ruwa fidda
kai, tunda kin iya kamuwa da ƙaunarsa ai banjin tunk'ararsa domin fayyace masa karatun
ruhinki zai zamowa abin wahalarwa ba da har sai kin kama ƙafa da ni saboda tsaban kin
rainamin hankali, foolish girl, mitcheww!."
Ta kai ƙarshen maganar ranta a mugun b'ace tana maijin tamkar zuciyarta zata faso k'irjinta
saboda zugi da takeyi maka.
"Hey Malama me ye na b'ata rai har da zagin cin mutunci daga neman alfarma."
"Kanki a jeji sokuwa kawai kuma wallahi kada ki sake tarana da wannan maganar banzan idan
kuma kina son ranki ya ɓaci ne to ki sake jaraba tarana da maganar."
Daga haka tayi gaba, duk da Part dinsu taso tafiya amma sai ta nufi Part din Mami Fulani tama
haÉ—a hanya domin bata ganin gabanta sosai. Ita kanta mamakin zafin da ta É—auka akan
maganar Zuhrah takeyi, anan ta sake gasgata ƙaunar da takeyiwa Sadauki. Tana shiga suka
d'ago suka zuba mata ido da sauri ta sauke kai ƙasa ta iso gaban Mami ta zauna gefen ƙafanta
ta riƙo hannunta tana sauke numfashi da sauri da sauri.
"Lafiya kike kuwa Muneerah?"
"Mami ina s...
Sai kuma ta fashe da kuka ta mik'e da sauri ta nufi d'akin Lailah, ta faÉ—a saman gado tana
cigaba da rera kuka tamkar wacce akayiwa dukan tsiya domin tanajin idan batayi kukan ba
jininta zai iya hawa.
"Babana jimin wani shiri-rita dai."
Shafo sajensa yayi cikin jin rashin daÉ—in ganinta a damuwa, ganin Mami na dakon cewarsa sai
ya saita kanshi ya tab'e baki ya ce "Ita ta sani ai, tunda ita ba yarinya ba ce sannan tafi kowa
sanin illar jefa kai a damuwa dan haka ki barta har sai ta sakko da kanta tanemi kiji damuwarta
amma dan Allah kada ki saka kanki a sokancinta hawan jininki ya motsa."
" A she baka da imani Babana?"
Da sauri ya kalleta ta zabga masa harara zaiyi magana ta d'aga masa hannu "Gara da hakan ya
faru na gane waye kai, daga yau Jabir ko Junaid zan soma kira baya goya marayu, Ubannin
k'annensu ba kai ba."
"Mami wai me na...
"Sai da safe Babana zan tafi jin damuwar d'iyata yanzu bazan fahimci tatsuniyar nan naka ba."
"Innalillahi wa inna ilaihin raji'un, wai me nayi da zafi ne haka Mami?"
Tashi ta yi ta barshi da baki buÉ—e. Sosa goshinsa yayi cike da mamakin zafin da Mami ta É—auka
akan abinda bai kai ya kawo ba. Maimakon ya tashi sai ya gyara zama ya jingina da Cushing
d'in da ta tashi sautin kukan Neerah nayi masa amsa amsa kuwa a cikin kunni hakan ya ƙara
dagula masa lissafi inda ya tashi da sauri ya nufi wurin da zuciyarsa keyi masa jagora, tura
k'ofar yayi a hankali idanunsu ya sarke da juna wacce take lafe a kafad'ar Mami na taping
bayarta da ido yake tambayarka me ke damunta tura baki tayi tare da lumshe ido, k'ofar ya É—an
buga saboda ya lura Mami b'ata san da shigowarshi ba dan ta bama k'ofar baya.
"Babana ko maciji ka zama ka shigo a silale kana tunanin ba zan san da isowarka wuri ba ne?"
"Mami affuwan na janye kalamaina."
"Ya wuce Babana amma ga kanwarka nan ka tabbatar da ta sanar da kai abinda ya sakata
kuka."
Daga haka ta fice, da ido suka raka bayanta sannan suka kalli juna na seconds, Sadauki ne ya
d'age mata hira cikin tambayar kurame na meye damuwarta. Harara ta cilla mashi tare da
hayewa saman gado ta rufe jikinta da bargo har saman kanta.
"Kin hutar da ni yanzu zan tafi in sanar da Mami kishin wanda baisan kina dakon son shi ba
kikeyi."
Ai kafin ya rufe baki ta diro daga gadon ta cukumeshi ta baya tare da fashewa da sabon kuka
mai sauti wanda ya janyo hankali Mami ta shigo a hanzarce ganinsu haka sai ta nuna Sadauki
da yatsa cikin gargad'i batare da ta furta kalma ba. Murmusawa yayi ya janyo Neerah ta dawo
gabanshi ya kalli Mami dake cillo masa harara ya kauda kai tare da cewa "Kiji tsoron Allah
Doctor N ki sanarmin da gaskiyan damuwarki in har ba akan kishi ba ne"
Duka ta soma kai masa a k'irji ya kalli Mami ta watso masa dak'uwa tare da barin wurin ganin
Neerah bata lura da wucewar Mami ba sai ya saki Murmushi mai sauti tare da janyota ya jefa
cikin k'irjinsa ya matse da ƙarfi dan ji yake tamkar ya tsaga k'irjinsa ya tura ta cikin zuciyarsa.
"Wash! my boobs."
Ta ambata tana mai son kubcewa.
Sassauta riƙon yayi mata ta zame ƙasa ya bita suka zauna saman rug, ta tura kanta tsakanin
cinyoyinta sai lamarin ya bashi dariya, ya kai bakinsa daf da kunninta ya hura mata iska ta
zabura ta mike tsaye ya nunata da yatsa nayin dariya mara sauti mai bayyana cikar kamalarshi
a fili.
"Yaya Yarima me ye haka? Allah bana so."
"I love you so much Dr. N, do you love me?"
Idanu waje take kallonsa ya tsare gira tamkar bai taɓa dariya ba ya sake maimaita tambayeshi
cikin dakon jin amsarta, tayi tsit kanta sunkuye tana miƙa godiya ga Allah na jin furucin bakinsa.
"Baki so na saboda na zamo mai sauri saki ko?"
Da sauri ta d'ago ta zuba masa idanunta har lokacin ta kasa furta kalma, girgiza kai yayi cike da
damuwa kana ya mik'e da sauri ya fice tare da bugo k'ofar da ƙarfi.
"Your are stupid Neerah."
Ta ambatawa kanta hakan tare marin fuskanta cike da takaicin barin damar da ta samu ya kufce
mata.
"Amma ai kunyarshi naji."
"Kunyar Babana ko saurayin da kike kishi?"
A firgice ta kalli Mami ta gyaÉ—a mata kai cikin rashin walwala tare da shigowa d'akin ta kamo
hannunta suka fito ta nufi É—aya daga cikin d'akunar barcinta.
"Shiga kiyi wanka ki fito mu kawo ƙarshen maganar munafuncin nan taku."
"Kaina ciwo Mami kuma barci nake ji kuma walalhi bamuyi munafuncin komi ba ki yarda dani
Mamina."
"To kwanta zuwa gobe mayi maganar kuma ki tabbatar da gaskiyan ruhinki zaki sanarmin domin
ta nan ne zan gane abinda ya kamata inyi akai duk da ba'a son raina lamarin ya zo a haka ba."
Kai ta motsa tana kulle ido sanyin ac na son saukar mata da zazzaɓi sannan ruhinta cike yake
da tambayoyin inda zantukan Mamu Fulani suka dosa na abinda take ambata da ba a son ranta
zai faru ba.
Ac Mami ta kashe tare da rage mata hasken wutan dakin ta fice, ajiyar zuciya ta sauke
natsuwar ruhi na rab'arta saboda yarda kalaman ina sonki sosai Dr N, shin kina so na? Ke
amsa kuwwan a cikin kunnuwarta, juyi tayi tare da furta "I love you too Yaya Yarima."
Tana rufe baki taji motsin tafiyar wani abu a jikinta daidai saitin zuciyarta ta lalibo da sauri sai ga
ƙatuwar kunama jajur da ita, ta tsira mata ido sai kai da kawo takeyi tsakanin tafin hannunta
zuwa tsin-tsiyar hannunta ba tare da tayi mata illar komi ba, murmushi ta yi tare da matseta da
ƙarfi tana jin yarda bugun zuciyarta ya k'aru, ta lumshe ido tana mai furta "Where are you Yaya
Yarima? Dan nasan kana kusa da ni tunda ga kayanka a hannuna."
"Yes I'm here my Doctor."
Da sauri ta kalli bakin k'ofan cikin hasken da bai wadaci d'akin ba, shi ne tsaye yana kallonta
fuskansa ba d'igon annuri, murza idanu tayi dan tabbatarwa sai taga wayam ba kowa komawa
kwance ta yi ta tsirawa kunaman nan ido da ta koma jikin bango tana ta shawagi sai sanja color
takeyi from black to red, yellow, blue, brown and so on dan wani color d'in bata taɓa ganinsa ba
tsawon rayuwarta. Murmushi kawai take binta da shi, har bata san sadda barci ya É—auketa ba ta
kife ruf da ciki barcin da su Mami ke yak'in ta daina yi saboda rashin alfanunsa ga Bil'adam.
***
'Na yarda da zancen Bokanki Mamma hak'ik'a ya sanar da ke gaskiya cewa ina da kishiya a
kusa da ni, in ko haka ne wallahi sai dai kowa ya rasa Yaya Sadauki domin bazanyi kishi da ke
Neerah ba kamar yarda nasan kema bazakiyi da ni ba saboda girman zumuntarmu ya wuce
wasa, kai bama zai yiwu hakan ya kasance ba, tabbaas kai nawa ne Yarima Aliyu, ruwa da iska
banga mai yimin shamaki da aurenka ba, Neerah wahalar banza kikeyi, ke da Yaya Sadauki sai
zumunci na yan uwantaka da Allah ya haÉ—amu.'
Duk cikin zucci Zuhrah keyin zantukan idanunta na kan sashin Mami Fulani tana auna masa
mugun kallo tamkar shi ne Dr. Neerah. Cin tayar mota da akayi yasa ta kalli wurin a hanzarce
hango Ƴaƴanta Hud cikin maye yasa ta buɗe robar ruwar hannunta wanda ke da sanyi ta
nufeshi a fusace ta watsa masa ya saki a jiyar zuciya yana kallonta idanu jajur sake juye masa
ragowar ruwan tayi a fuska aikam ya rarumota ta kwasa da gudu ya rufa mata baya yana huci.
"Mamma kizo danki mara amfani zai illata miki ni."
Abinda take ambata kenan tana
maimaitawa sadda tayi nasarar shiga falonsu, Mamma ta fito zani na kufcewa dan tunda tajiyo
kalaman Zuhrah ta san ita da Hud ne wanda tayi imani ya koma ruwane na shigowa Masarauta
cikin maye lamarin da Zuhrah ke adawa shi kuma hakanne yasa tayi mugun rainashi duk da ba
ita ce sak'onshi ba domin a kwai mutum biyu tsakaninsu kafin ita.
"Me yasa ne Hud? kamanta tijarar Abbanku Chiroma ko? Shin kana ganin wannan gaulancin
zai kaika zuwa ga hawa karagar Sarautar Birnin Mungaye?"
Da sauri Zuhrah ta anshe da "Ina kuwa domin wallahi ko ni sai na yi sanadin rashin hawarsa
domin mu ba 'yan maye ba ne balle ya hau ya maida giya ruwan fanfommu duk mu lalace,
kanmu ya kwance kamar yarda nasa yake a kwance."
Tama rufe baki ta k'wallah ihu domin a fusace ya jefota da zobbesa mai kama da k'ashi, ya ko
sameta a goshi a take jini ya wanke mata fuska, Mamma ta yi kanta tana rafka salati fadi take
"Hud kiramin Dr Neerah ta bata taimakon gaggawa domin ban son Masarauta susan wannan
abin kunyar da ka aikata."
"Sai dai ta mutu wallahi Mamma indai sai na kira an bata taimako ne."
Ya ambata cikin rabewar murya irin na 'yan maye.
Wani a shar Mamma ta mulmulo ta antaya masa ko ajikinsa sai ma ya kwashe da dariya ya tura
kai d'akin