Showing 39001 words to 42000 words out of 45162 words
Chapter 14 - HATSABIBIN TSIBIRI Littafin Yaki Book Complete .pdf
Unknown
25 Mar 2025
5209
Zuhrah ya faÉ—a saman Cushing yana sunbatun sai ya illata rayuwar Zuhrah tunda ta
rainashi, daga haka barci yayi gaba da shi.
"Mamma jijiyar idanu zasu tsinke kiyi wani abu kada na rasa idanun gani, wayyo! Na shiga uku
na lalace, walalhi ba zan yafewa É—anki mara amfanin can ba."
A gigice Mamma ta kamota tare da tara d'ankwalinta a goshin tana zabga salati gami da toshe
mata baki dan ta daina aibata É—an uwanta tare da gudun kada wani ya jiyo.
"Mamma kaini Mungaye Clinic kada in rasa idanu cikar ado da k'walliyar duk kan mutane
musanman mata."
Bata da zaɓi zai fito da ita zuwa Clinic duk da bata so hakan ba saboda bata son labari ya fito
cewa Hud ne ya jima shalelenta ciwo domin a bayyane nakasu ne gareshi akan burinta na
ganin ya haye karagar mulkin Mungaye.
***
Tsibiri.
Iskan bai tsaya a É—auke masu gani ba har da halaka jama'a, a cikin abinda bai wuce mintoci
biyar ba ya halaka mutane masu yawa. Tsibiri ya hautsine da iface-iface na neman dauki, cikin
fushi Sarkin yaƙi wato mahaifin Buda ya aika sak'o cikin aikin alk'aliman sihiri zuwa ga Abun
akan su dawo Tsibiri zai kama da wuta sannan ya soma ƙoƙarin tsaida guguwan cikin kwarewar
tsafi sai dai lamarin ya sha ƙarfinsa, suka taru suka haɗa ƙarfi kamar yarda sukayima na farko
nanma bata sanja zani ba sai kawai suka soma neman matseta tare da bawa jama'a taimakon
wurin b'uya.
Rugugi ne ya doso Tsibirin abinda ya sanya iskan nan lafawa, tamkar k'iftawar ido iskan ta
ɓace, zuwa can Lina ta bayyana fuska a daure, kafin su ankara ta soma huro sanyi wanda ke
fitowa daga bakinta na shiga jikkunar Jama'a inda ke warkar masu da raunin da suka ji tare da
tashin wanda suka jikkata, ta É—auki tsawon mintoci goma tana huro iskan kafin ta dakata tana
kallon al'umman da duk suka samu natsuwa suka sakata a tsakiya suna yi mata kirari da
Gimbiyarsu mai tausayi.
"Kuyi hak'uri da matsalar da 'yar uwana ta janyo muku, yanzu ku tafi ku kauda wanda suka
mutu tare da cigaba da harkokinku zanyi bakin iyawata wurin kare lafiyarku domin wannan shi
ne burina kuyi rayuwar 'yanci wata rana."
"Mungode shugaban gobe, Sarautar Tsibiri naki ne Gimbiya Lina."
Suka ambata a tare cikin daga murya.
Jinjina kai tayi ciki da alfahari da su. Suna watsewa Abun ya bayya tare da Buda, Lina na jin
alamun takunsu ta ɓace ta bayyana cikin Bukkan Kaka Gunu inda ta sami Lima sunkuye kan
Mah tana aikin ceto ranta.
"Sakacinki ya janyo Mah zata mutu, wannan bak'ar ranar nake jiye mana har na umurceki da ki
kula da ita amma saboda son zuciya irin naki kin kasa zama da ita kin taho neman cikar burinki,
to ki zauna a nan tare da ita domin fitowarki kiran ajalinki ne domin Jama'an Tsibiri sun fusata
da kashe masu dangi da kikayi sanadi sannan Abun yana farautanki kamar yarda yake
faraunata da Mah."
"Me kike nufi da Abun na farautanmu? Alhalin mu ne kaÉ—ai sanyin idanunsa."
"Lima yanzu Abun ya sanja dan shi ne ke wasa da rayuwar Mah domin ya samu hankalina ya
dawo kanta inda zai hilace ni ya mallaki Zoben da ke hannuna wand zai bashi damar samun
ƙarfin tsafin da ya zarce na kowa dake zamanin nan haka ya fiki burin son mallakan Ruwan
Albarkan Kaka Gunu domin shima na É—auke da sirrika masu girma akan tsafi da cikar mulki, ki
sani a yanzu mu ne damuwarshi akan haka ya kudiri halakamu baki É—aya indai zamu kawo
masa tangarda a samun tsawon rayuwa akan mulki."
"Ta ya zan yarda da gaskiya kike sanarmin ba yaudarar da kika saba yimin ba ne? "
"Ifritu Mutuwa zai gasgatani."
"Tabbas zantukan yar uwanki Lina ba ƙarya duk da itama tana son shan ruwan albarkan domin
ta sake finki komi dan hawa karagar mulki, ko ba haka ne manufarki ba ya ke Gimbiya Lina?"
"Tabbaas haka ne kuma har a yanzu ina cikin muradin rigaki mallakan ruwan albarkan sai dai
ba yanzu shi ne a gabana ba domin haka kaima Mutuwa dole ka dakata da taimakonta na
mallakan Ruwan har sai na kammala da abinda ke gaba in yaso sai kayi mana k'uri'a duk
wanda ya ci shine mai mallakin gadon Kaka Gunu."
"Baki isa ba Lina, ni ce ke da gadon Ruwan Albarkan Kaka Gunu dan haka ki fitar da ranki
akansa."
Murmusawa Lina ta yi batare da ta furta kalma ba ta isa gaban Mah da ke shimfida tamkar
gawa ta sunkuya ta shafi fuskanta wani haske ya sauka a fuskan zuwa ilahirin jikinta aikam sai
ta soma tari tana kiran sunar Abun da ya zo ya taimaketa.
"Mah kina tare da 'yan biyunki kuma bisa kulawarsu kika tsira daga baƙin iskan da Lima ta yi
jagoran shigowarsa cikin al'umma, yanzu zan barki a wannan Bukar ta Kaka Gunu Lima zata
kula da ke zuwa sadda zan dawo na maidaki inda duk ƙarfin tsafin matsafi yayi kaɗan ya iya
zuwa wurin."
"Ki dawo lafiya Ruhin Sarki Goma ya baki kariya."
Motsa kai tayi tare da mik'e ta kalli Lima da ta tsare giran sama da ƙasa ta hurama fuskanta iska
kan dole ta murmusa saboda tunowa da lokacin baya da take azabtar da Lina da iskan bakinta.
"Yawwa kin tuna muguntarki na baya ko? To ki natsu kiji me zan sanar da ke, ki zauna a nan
kamar yarda na sanar da ke a farko, ki kulamin da Mah, Ifritu Mutuwa zai kula da ku sannan zan
batar da Bukkan Kaka Gunu a idanun Abun wanda ke nufin isowa bada jimawa ba."
Lima zatayi magana Lina ta daga mata hannu tare da cewa "Kada kiyi yunkurin barin Bukkan
nan dan zuwa watsewarki domin yin hakan wasa da rayuwarki ne domin kina fita zaki tsinci
kanki a akurkin sihiri ko na Abun ko na Ifritu Baushe kuma ki sani bana da lokacin taimakonki
saboda lamarin Mah d'ita ya fiyemin komi, in kinji gargad'i ruwanki, ni zan wuce ba zan jima ba
zan dawo dan bana son na wuce kwanaki biyu rak ban kammala abinda naje yi ba."
Kafin Lima ta furta kalma Lina ta zama farin hayaki ta b'ace kallonta ta sauke kan Ifritu Mutuwa
sai ya jijjiga kai tare da bude tafin hannunsa saiga wurin ya sanja, ya dawo dauke da kilisai
masu laushi da makeken gadon alfarma, jinjina tayi masa ya gyaÉ—a kai tare da b'acewa, ta
doshi gadon ta hau ta kwanta ba jimawa barci ya dauketa cike da burin sai ta fita wurin nan taga
abinda zai faru. Mah itama gadon ta hau cike da tarin damuwa.
Lina na fitowa ta jiyo takun Dokin Buda sai ta zama balbela ta haye saman bishiya suna
wucewa ta sakko ta watsa haske a baki É—aya Bukkan ta lula sararin samaniya.
***
Abun tsaye a turakansa yana kai da kawo cikin tarin damuwa zuwa can ya ja iska ya fesar tare
da zama akan k'ok'on kan Giwa ya na cije lebe, ya sharce Gumin da ya feso masa a goshi tare
da mikewa a fusace ya kaiwa bango duka cikin ambatar "Ƙarya ne, saina Mallaki Zoben
hannunki Lina sannan yar uwanki zata kasheki a gaban mahaifiyarki, a yanzu bana da abokiyar
gaba sama da ke, zan nuna miki ta yaro kyau take amma bata k'arko, ki sani ba zan barki ki
Mulke ni ba alhali ina rayuwa, tabbaas a yau na musanta kalman cewa bazanyi fito na fito da ke
ba haka na gasgata kalamin Kaka Gunu da ya ce samuwarki cikinmu masifa ce domin zaki
karya k'adarinmu ki sanja tarihinmu ki watsa mana Martaban Tsibiri hak'ik'a dana sani na bashi
dama a can baya ya sanya kinbi rariya ya zamo Lima kawai zata zo duniyarmu."
Momyn Haske ne í ¾íµ°
*Muna saida ingantaccen man ayu wanda ya zo daga Chad. Yana maganin Infection, asma,
limoniya, mura, ciwon basira ciwon kai, ciwon baya, ciwon ƙafa, ciwon mara, kaikayin jiki dana
matse-matsi, yalwatuwar ni'ima tare da samun gamsuwa a turaka da sauransu, muna saida
É—aya ko sari mai so zai iya tuntubar number nan ta WhatsApp ko kira. 08132166848. Yarda ake
amfani da shi za a jik'a Lipton sai a d'iga man ayu a ciki a shanye da d'umi-d'umi za a iya zuba
zuma ko siga a ruwan Lipton d'in dan gudun d'aci haka za a iya zubawa a ruwan Tea a sha.
Masu asma da limoniya kuma zasu jajjaga tafarnuwa su matse ruwan su zuba ruwan d'umi da
man ayu su shanye. Masu Infection duk in suka wanke wurin da ruwan zafi sai su saka man ayu
haka masu kaikayin jiki idan sun fito wanka sai su shafa amma zasu sha da ruwan Lipton, Allah
ya ƙara mana lafiya Amin.*
[1/13, 12:05 AM] Mrsjmoon: Hatsabibin Tsibiri
By Mrsjmoon
Adabi Writer's Association.
https://arewabooks.com/book?id=63a2e3d8821822a8402d8eb1 Follow me on Arewabooks.í ½í¶•
15
Ya kai ƙarshen zance cikin ɓacin rai, yana jin tamkar ya dawo da baya ya goge samuwar Lina a
cikin zuri'arshi.
"Da girman mulkinka ya mai Tsibiri, ya kamata ka fito dan jajantawa Jama'a masifar da ta afku
wanda Gimbiya Lima ta janyo faruwarshi."
Sarkin yaƙi ya ambata daga bakin kofa kansa sunkuye.
Cikin ɓacin rai ya nuna Sarkin yaƙi bakinsa na fitar da tiririn masifa ya ce "Yau she mulkin Tsibiri
ya kai ga lalacewar da Sarki mai ikon juya kowa da ke Tsibirin nan zai fito bawa Talakawa
hak'uri abisa afkuwan lamarin da ya zamo cigaban Mulkinsa ne, to ka tuna idan ka manta ne
Tsibirin nan bai ginu bisa Tausayi ba haka ba zai taɓa haɗa hanya da shi ba, ka ƙara sani, nai
alfahari da afkuwan masifar nan domin samun cikar burina na mallakan ababen da ke hannun
'ya'yana sai da zubda jini k irin wannan, lallai aikikinki na kyau Gimbiya Lima, a kullum ina
alfahari da zamowarki gudan Jinina tabbaas ke ce magajiyar Tsibiri na sake gas-gata kalaman
Kaka Gunu na cewa nasaranmu naga hawa karagar mulkinki ne duk da ina da wani buri akanki
amma ba zan k'i yaba miki."
"Ya shugabana ka natsu mu fuskancin masifar da wannan zubda jinin zai haifar domin Dodo
yayi fushi ya bar Tsibirin domin Guguwan ta rainata masa mata yanzu haka ya killace kansa a
Kogo yana shirin yak'ar Lima shin idan baka fito ka jajantawa Jama'a ba me kake tunanin yi
wanda zai sakko da Dodo akan dokin nakin na ya hau?"
"Sarkin yaƙi ka rufemin baki tun fushina bai sauka kanka ba sannan Dodo zai dawo bakin
aikinsa kuma fushin-shi na rashin samun damar san Jinin jama'ar da baiyi ba ne, ba wai na
nak'asar matarsa ba, shin ko ka manta bata da lafiya a cikin ko wani lokaci zata iya samun
rauni, tunda ta saci jiki taje ta sha Jinin wani dan Fulani shi kuma ya soma bin hakkin jinin
Ɗansa lamarin da yaso shafar ƙarfin ikon Tsibiri, shin ko mutuwa tayi ai bamu da asara."
"Haka ne ya mai Tsibiri, tabbas na tuna da wannan masifar da muka kasa samun maganinsa sai
da k'yar."
"To Dodo fushin karya ya keyi sai dai bazank'i ta bakinka ba zamu É—auki matakin kare kai kada
ya kawo mana matsala saboda ya soma nuna rashin amana wanda hakan zai haifar masa da
rasa rayuwarshi ba damuwata ba ne."
"Me zamuyi masa?"
"Cin amanar tun kafin ya samu nasarar cin tamu, wato samo hanyar halakasu cikin dibara."
"Ya mai Tsibiri Dodo ya wuce da saninmu domin ya rayu tun farkon Sarkin da ya raya wannan
Tsibirin, yana da nindarai kala kala sama da dubbunnai dan haka shawara mafi samun mafita
shi ne anjima da dare zanzo mu tafi wurinsa mu rarrasheshi ya dawo mu cigaba da zaman
amana amma ka janye batun halakashi saboda gudun matsala."
Jim Abun yayi daga bisani ya gyada kai alamun aminta da zancen, Sarkin yaƙi za ku saka
magana Abun ya d'aga mashi hannu tare da nuna kofar fita, ya ko juya da hanzari ya fice yana
mai cike da farin cikin hayewa matakin farko daga cikar burinsa.
Abun d'akin bincikensa ya shige yana mai jin rashin yarda da zantukan Sarkin yaƙi na zuwa
muhallin Dodo sai dai burin son nemo hanyar da zai ladaftar da Lina har ya mallaki Zoben
hannunta ya shafe binciko abinda Sarkin yaƙin ke shiryawa, sai ma watsar da lamarin da yayi
saboda zuciyarsa na bashi tabbacin aminci dake tsakaninsu da juna.
A gafen Sarki yaƙi kuwa gidansa ya nufa inda ya sami ɗansa Jarumi Buda zaine na dakon
isowarshi. Yana isa ya rungume Buda yana kyal-kyalan dariya sai da yayi mai isarshi sannan ya
tsagaita ya doki kafadan É—an nasa yana mai koro masa yarda sukayi da Abun, yana dasa aya
Buda ya amshe da cewa" Ya Baba ina guje mana afkawa tarkon Lina dan zuwa yanzu na soma
tsorata da lamarinta kada garin halaka mahaifinta mu É—in mu halaka a banza saboda bata bari
kayi nasarar halaka mahaifinta ba, ni dai da zakaji shawarata da mun hak'ura da son mulkin nan
mu kare namu da muke da shi na Sarkin mayak'a."
Yana rufe baki wani taurari suka gifta a maganansa sakamakon marin da Sarkin yaƙi ya zabga
mashi. A gigice ya durk'ushe gami da kwalla ihu wanda yayi amsa kuwwa a Tsibirin lamarin da
ya sake gigita Al'umma suka soma fadawa mahallinsu suna kare kai ta hanyar tsaface kansu da
'ya'yansu domin tunaninsu wata masifar ce ta dawo. Ihun Buda ya sauka a kunnin Abun dake
tsaka da bincike, tsak ya tsaya yana nazarin abinda ke shirin faruwa sai dai jin takun isowar
Lina Tsibirin yasa shi barin komi ya soma shirin tunkararta tun kafin ta hayo, burinsa ya halakata
kowa ya huta da ganinta.
Sarki yaƙi yaji rashin jin daɗin abinda ya aikatawa ɗan nasa sai yayi ƙasa da murya yana mai
cewa "Kayi hak'uri ya kai É—ana amma ka sani burin mahaifina kenan mu gaji mulkin Tsibiri
hakan bai samu ba saboda Kaka Gunu ya katange hanyar shi yasa na rayuwa da burin kawo
karshen mai Tsibiri ko da hakan na nufin rasa raina zanyi dan haka kada ka sake ambatamin na
ja da baya tunda kai baka son hawa mulki to ni zan hau duk da na soma tsufa."
"Zan hau Babana domin nima ina da burin mulkan jama'armu."
"Da kyau É—ana, ina alfahari da kai."
Kauda kai Buda ya yi yana mai buÉ—e k'ofofin hancinsa sai kuma ya mik'e a hanyarca, Sarkin
yaƙi ya rik'oshi cikin alamun tambayar inda zaije.
"Babana Gimbiya Lina na daf da shigowa Tsibiri kuma ina jiyo alamun zata gamu da matsala
dan haka zan kai mata É—auki."
"Ta mutu mana ina ruwanmu."
"Ina sonta Babana, ka amincemin na kai mata ɗauki saboda sai da ƙarfinta zan samu damar
hawa karagar mulkin Tsibiri."
"Kana hauka ne Buda? Lina tafi kowa son mulkan Tsibiri dan haka zan amince maka kaje
gareta bisa aniyar kasheta ka riga mai Tsibiri mallakan Zoben da naji yana magana akai wanda
ke hannunta."
"In haka ne Baba kaga kenan taimakonta zansoma akan duk abinda ta sanya gaba idan ta
aminta da ni cewa masoyinta na gaskiya ne sai na yaudareta na amshe Zoben daga nan sai mu
fito mata da manufarmu na yak'arta mu kaudata cikin sauk'i."
"Da kyau fasihin ɗana Buda, tafi gareta da albarka Takobin yaƙina, kai ne ke da nasara kan
Gimbiya Lina."
"Godiya nake Babana."
Daga haka Buda ya fice ya doshi inda yake jiyo K'amshin Lina wanda ya kaishi ga fita yankin
Tsibirin baki É—aya. Shima Abun ya nausa wajen Tsibirin inda ke jiyo takon Lina har lokacin kuma
ya kasa cimma ta sai ya ƙara k'aimi domin riskanta akan lokaci.
Sai dai abinda ba su sani ba shi ne duk kansu bayan Lima suka biyo wacce ta fice ta bar Mah
na barci, lokacin da zata fita Ifritu Mutuwa ya so hanata amma tuno zaman cika umurninta
yakeyi sai ya kyaleta ta fice cike da muradin son ganin abinda zai faru akan fitar nata, mutuwa
ce ko rayuwa, nasara ce ko rashin nasara, ita dai burinta yin ido biyu da kalaman Lina domin ji
take idan bata fito wajen Tsibiri ba to Lina ta gama samun nasara akanta na zamowa
shugabanta tunda gashi nan ta bata umurni kuma ta bi.
Abun, Buda tare da Lima sunata yin nisa da Tsibiri a bisa hanya É—aya batare da sun gano hakan
ba domin Ifritu Baushe ne ya shiryo musu sihirin ficewa daga Tsibirin ta hanyar kusanto masu
da takun Lima gami da k'amshinta da ya sauya da irin na Lina sak, saboda Hadimi Tsidau ya
sanar masa indai suna cikin Tsibirin to ba zaiyi nasarar shigowa ya É—auke Mah ba wacce ke son
yin garkuwa da ita domin Lina tazo yankinsa da kanta inda zai mallaketa tare da Zoben sihirin
hannunta daga bisa ya sadaukarwa da Dodonsa jinin Mah a gaban idanunta, kana yayi mata
ciki ta haifa masa d'iyar da zai sha jininta duk akan idonta ya tabbatar da ganan labarinta ya zo
ƙarshe dan ko bai halakata da hannunsa ba ya san bak'in ciki zaisa ta had'iye ranta.
Tunda Tsidau ya farka da barcin da ya kwashe shi sai ifrutu Baushe ya adana shi yana gana
masa azaba kala daban daban domin ya fahimci makirci ke son shirya masa ya gudu dan ba zai
taɓa kawo mashi Lina Fadar sa ba, yanzu haka yana can kurkukun tsafinsa da ke k'ark'ashin
ƙasa cikin tsaron wasu bak'ak'en rindunar Aljannu suna aikin azabtar da shi, wuya yasa shi
sanar da Baushe hanyar da zaibi domin samun nasarar shiga cikin Tsibirin har ya samu cikar
burinaa wato sai ya kora su Abun sunyi nesa da Tsibiri domin yawan yin nisansu da Tsibiri shi
kuma yawan kusanci ga