Showing 42001 words to 45000 words out of 45162 words
Chapter 15 - HATSABIBIN TSIBIRI Littafin Yaki Book Complete .pdf
Unknown
25 Mar 2025
5205
nasararshi na shiga cikin Tsibiri. Yanzu haka Ifritun Baushe ya sami
kusanci da Hatsabibin Tsiri saura samun nasarar shiga cikinsa tunda ga su Lima can na cigaba
da lulawa cikin duniya ba tare da sun gano sihiri ke d'awainiya da su ba.
***
Masarautar Mungaye.
Cikin ikon Allah su Zuhrah har suka isa Clinic ba wanda ya gansu sai hadimai dake ta mik'o
masu gaisuwa. An wanke mata ciwon inda anan aka gano ƙarami ne tsabar rakine ke damunta
ta cika masu kunnuwa da ihu, a hanyarsu na dawo ne suka haÉ—u da Jabir inda ya gaisar da
Mamma cikin girmamawa ta amsa tare da yin gaba ta barshi da Zuhrah, shi kuwa ya tsareta da
tambayoyi akan sanadin raunin fuskanta batare da jin ko É—arba ta koro masa bayanin abinda ya
faru sai dai ganin ɓacin ran da ya nuna har saida tayi da ta sanin faɗan domin yarda ya rufeta
da masifa sai da tayi zaton dukanta zaiyi, ta ja da baya ya fizgo hannunta suka isa sashin
Mamma ya turata tare da rufa mata baya. Mamma dake zaune riƙe da robar ruwa tana sha ta
mik'e a firgice tana tambayar abinda ke faruwa.
"Mamma ki gyarawa Zuhrah tarbiyya saboda yaya Hud ba sa'arta ba ne, shin taya za'a ce kina
kallo ta gama rainashi? A gaskiya da sake, in sha Allah gobe zan sanar da Mai Martaba domin
a dauki mataki dan ko me yakeyi ya fi gaban raini a wurin k'aninsa sannan rayuwar dake ciki
ƙaddara ce wata rana zai zamo labari dan haka dole Zuhrah ta girmama shi a matsayinsa na
babban yaya a d'akinsu."
Ya sauke dubansa kan Zuhrah dake risgan kukan baƙin cikin anayi mata faɗa alhalin ita aka
zalunta. Ya nunata da yatsa cikin kaushin murya wanda ya koma irin na Sadauki sak ya ce
"Wannan shi ne rana ta ƙarshe da zan ji kin sake aibata yayanki mai ɗauke da matakin uba,
idan kuma kince wasa nakeyi to ga fili nan ga mai doki, kin sanni dai sarai magajin Abba
Chiroma ne, so be carefull kuma ki hanzarta bashi hak'uri, zan tambayeshi idan naji saɓanin
haka na lahira sai ya fiki jin daÉ—i."
Sai ya russuna gaban Mamma yayi mata sai da safe ta amsa jiki a mace, saida ya fice sannan
ta sauke ajiyar zuciya tana ƙara tsirawa hanyar da ya bi da idanu saboda zantukansa sun nusar
da ita wani kuskure da take aikatawa na sangarta Zuhrah ya zamo kaf yayunta bata ganin
girmansu saɓanin sauran yaran dake kan girmama yayunsu, ta dubi Zuhrah kafin ta furta kalma
ta buga ƙafa tare da fashewa kuka mai sauti, Mamma ta nufota ta zille ta fice da gudu tana
gunjin kuka, komawa Mamma tayi ta zauna ta dafe kanta cikin sake tsunduma nazarin kalaman
Jabir inda take hango cikakken gazawarta wurin tarbiyyan yaranta.
"Ƴaƴan Fulani dai masu hangen nesa ne, komin hassadan mutum ya zauna da su sai sun shiga
ranshi tare da ƙaruwa da su, Jabir nagode da tunatarwa amma duk da haka bashi ne zaisa na
janye ga son Hud ya zama Sarkin birnin Mungaye ba, ina nan akan bakana sai na salwartan da
Sadauki daga wannan nahiyar."
Tana ambatar haka ta mik'e da sauri ta shirya ta fice zuwa sashin Umma domin kamma aikin da
suka soma na birne layun da Mai Martaba zai ambaci sunar Hud a matsayin magajinsa domin
Mamma mutum biyu take aikin a kansu wato Sadauki da Sardauna, ta kora Sadauki ya b'ace a
duniya shi kuma Sardauna ya nak'asa yarda mulki zaifi ƙarfin shi,a wannan gaɓar mai martaba
zai ayyana Hud, duk ta manta idan ba Sadauki da Sardauna a kwai wasu zaratan samarin
Junaid da Jabir.
***
Washe gari.
Neerah ce zaune gaban Mami Fulani, tambayar duniya tayi mata akan sanin gaskiyan ra'ayinta
akan Sadauki sannan ta umurceta da kada ta b'oye mata komi dake ranta, amma taki yin
motsin kirki sai shafar yatsun ƙafarta takeyi. Murmushi Mami tayi tare da umurtanta da ta tashi
taje ta karya tunda tak'i yin magana.
"Ina Azumi."
Ta ambata a hankali kuma cike da shagwaba'a.
"Masha Allah, ai namanta yau Alhamis, to Allah ya karb'a ya bada lada."
"Amin."
Shiru ya sake ratsa wurin zuwa can Mami ta kalleta a natse ta gano da maganar da take son
furtawa, kiran sunarta tayi "Muneerah."
"Na'am Mamina."
"Sanarmin da zancen dake ruhinki kada kiji komi, nayi miki alkawari kome ye shi ina tare da ke
sannan ki haÉ—a da bani amsar tambayar da nayi miki, shin kina son Babana ko takuraki yayi?"
Tafi mintoci biyar bata ce komi ba har sai da Mami ta dafa kanta cikin cewa "Sarauta gadonsa
kikayi ba haye ba d'iyata, idan baki zamo mai nazari kafin bada amsa ba tabbas baki cika d'iya
ga Sarki Abdul Hakim ba."
Dagowa tayi tana murje ido cikin turo baki ta ce "Mami kiran sunar Abbanmu tsirara fa kikayi."
"To Abban su Doctor Neerah, shi kenan na lullub'e?"
Dariya ne ya kufce mata domin bata taɓa jin Mami ta kirata da sunar irin haka ba.
"Tubarkallah, masha Allah, Allah Alhamdulillah da ya azurtani da d'iya mai kyau koda kuwa
kuka takeyi."
Kafad'ar Mami ta kife fuskanta tana cigaba da dariyan mara sauti.
"Tashi mugama magana domin yau yau ake da zama na musamman akan zaɓinku daga nan
sai a tsaida lokacin biki."
"Mami nifa ba zan ƙaryata yaya Yarima ba kawai duk abinda ya sanar da ke hakan ne, dama shi
ne abinda zan faÉ—a miki tun d'azun nake jin nauyi."
Tana gama ambata ta mik'e da sauri ta fice domin gujewa tambayoyin Mami wanda amsasu
zasu bata kunya matuk'a. Bayanta Mami tabi da kallo baki buÉ—e sai kuma ta tsare gira tamkar
an aiko mata da sakon mutuwa.
"Da sake bazan yarda da wannan gangancin ba na aurawa Babana jinin k'anwata ya ƙarasa
kunyatani cikin dangi."
"Mamina kada kiyimin haka, tunda dai kinji gaskiya to ki kai maganar ga Abba tare da sanya
mana albarka."
Tsirawa k'ofar shigowa falon tayi ido ba kiftawa har Sadauki ya iso gabanta ya zauna tare da
riƙe ƙafarta muryansa cike da rauni ya ce "Natuba Mamina, bazan sake aikata zunubin da ya
gabata ba, zan zauna da Muneerah har ƙarshen rayuwata domin ita ce sirrina, tasan waye Aliyu
sama da ku mahaifana sannan bazan taɓa baki kunya ba nayi miki wannan alkawarin, dan Allah
ki yarda da Babanki Mamina."
"Babana wannan daɗin bakin naka bai karɓu ba dan haka tashi ka bani wuri domin bazan taɓa
amincewa da wannan auren ba dan kafi kowa sanin wacece Nana Safiyya gareni, ni ce na saki
Nono ta kama to ba zan amince da wannan lamarin ba."
"Please Mamina am begin you, kada ki rabani da Muneerah domin ita ce zaɓin ruhina."
"Babana idan ka sake ambatar kalma É—aya tak a wurin nan sai ranka yafi dare duhu, oya! Maza
ka b'ace min da gani "
Maimakon ya tashi sai kawai ya kife fuskanshi a ƙafarta, tana jiyo saukan d'umin ruwa wanda
hakan ya tabbatar mata da kuka ya keyi amma hakan baisa ta janye daga dokin nak'in data hau
ba saima janye ƙafarta da tayi ta mik'e ta shige bedroom d'inta ta kulle k'ofa. Dafe goshinsa yayi
cikin jin kansa na sarawa yanayin da baya so na son kawo mashi ziyara, a hankali ya mik'e ya
shige dakin Lailah inda ya sami Neerah daren jiya, ya zauna a saman Cushing tare da d'an
zamewa ya kwnta ya d'aga kansa sama ya tsirawa ceilling ido, abin mamaki sai ya ji barci na
ziyartansa amma idonsa yaƙi kullewa. Fitinannen k'amshinta ya jiyo yasa ya sake ware idonu na
kallon fuskanta da ya bayyana a saman fankan da ke juyawa, hannu ya daga ya nunata cikin
cewa "Har a sashin mahaifiyata sai kinzo kin tozartani?"
D'age masa gira tayi cikin jifarsa da shu'umin murmushi sai kuma ta bayyana zaune gefenshi,
ƙafa yasa ya hankad'ata sakamakon tuno makarkin da yayi jiya tamkar a irin haka abin ya soma
kafin ta rikid'e masa zuwa sifar Neerah, ya haik'e mata ba d'igon imani.
K'irjinsa ne ya harba tuno baya, a mugun fusace ya mik'e ya nunata da yatsa cikin amo mai
amsa kuwa ya ce "Kina taɓani na rantse sai na kasheki!"
"Ka taɓa ganin inda Aljani ya mutu?"
"Za a fara akanki, azzaliman banza kawai,mara addini!!."
Ya kai ƙarshen maganar cikin buɗe murya bai ko tunanin Mami zata iya jiyo shi.
"Kai ka koyamin zalincin ya kai Yarima Aliyu Sadauki takwarar mafarin Mungaye Malam Aliyu
Malle kuma takwarar Baffan mahaifiyar shi Fulanin Sarki Abdul Hakim."
"Ya isheni haka nan ya ke banziya!."
"To nayi shiru amma in kamanta zauna in tuna maka zalincin da ka aikata wanda ya janyoni
bibiyan farin cikinka."
Kafin yayi yunkurin magana ta turashi zaune ta hanyar hura masa iskan bakinta ya lumshe ido
ya bude cikin jin mutuwar jiki, ta nuna bango da yatsa sai ga gidansa na dajin Tekun Kabobo ya
bayyana, ya ware idonu ta gyaÉ—a masa kai cikin cewa "Ka tuna zalincin da kayi a wannan
gidan?"
Bai amsaba illa kallon gidan dakeyi cikin wani yanayi mai wuyar fassaruwa.
"Nayi alkawarin sai ka ambatawa Masarauta aika-aikan da kayi da bakinka a gaban dubban
Jama'a kuma a yau ɗin nan saboda aikina na daf da zuwa ƙarshe."
Lumshe ido yayi yarda lamarin ya kasance ya soma dawo masa a idanu tiryan-tiryan, kafin
kwabo yaji tamkar gashi a bakin Tekun Kabobo da mafarin lamarin ya soma, wani iziyar ruwa ya
zashi zuwa cikin Tekun duk yarda ya so kufcewa halaka ya kasa sai ya hango Neerah a tsakiyar
Tekun na d'ago masa hannu ya zabura da ƙarfi, Mami ta zabga salati sai ya kalleta a razane,
idanunsa sun sanja kala zuwa jajur, cigaba da karanto addu'a tayi tana tofa mashi ya ritse ido
na jiyo amsa kuwwan ihunta, da hanzari ya toshe kunnuwanshi, Mami ta sake zabga salati,
muryanta na rawa take cewa "Kada kayimin haka Babana indai akan aurenku da Muneerah ce
kake son haukacewa walalhi na amince, Allah ya tsare afkuwan abinda nake tsoro, ya baku
zaman lafiya da zuri'a masu albarka."
Komawa kwance yayi najiyo dariyarta a daf da kunninsa kana daga bisani tace "Na tayaka
yaƙin samun cikar burinka na auren masoyiyarka saura samuwar nawa wanda ya ke nak'asu
ne ga ci gabanka domin Birnin Mungaye baza su amshi azzalimi matsayin jagoransu ba, na tafi
kada mamanka ta ƙarasa konani da gatan addinku wanda kake da sani akansa amma na haka
su amfane ka."
Yanajin iskan tafiyarta ya juyo ya tsirawa Mami ido sai a lokacin yaga a she harda Abba, da
Neerah a d'akin, bai lura ba sai yanzu. Runtse ido yayi tare da tura hannayensa a cikin
sumarshi. Jan hannun Mami mai martaba yayi suka fice batare da Sadauki ya sani ba saboda
ya amincewa kansa Sadauki na tare da shafan Junnu.
"Yaya Yarima."
Kollonta yayi ta sakar masa murmushi tare da matsowar ta zauna a hannun kujeran da ya ke
kwance ta soma bashi labarin abinda ya faru cikin natsuwa.
"Ina fitowa daga falon Mami na hango zaka shigo sai na b'oye sai da ka shige sai na samu
kaina da biyo bayanka, na jiyo duk yarda kukayi da Mami shi ne na biyo bayanka domin sake
samun tabbacin kalaminka na cewa ni É—in sirrinka ce sai na samu kana ta magana kai kaÉ—ai,
sam na kasa fahimtar abinda kake faÉ—a ga daishi da yaren da nasani kake maganar amma
harshenta yana sark'ewa ta yarda maganar bai fitan da za'a fahimta, ganin kamar baka
hayyacinka shi ne na kira Mami, tana zuwa ta soma tofa maka addu'a ganin abin na son fin
ƙarfinta sai ta kira Abba inda yana shigowa ka dawo hayyacinka lamarin kamar shafan Aljannu."
'Innalillahi wa inna ilaihin raji'un.'
Ya ambata cikin rashi yana maijin harbawan halittarshi da ƙarfi wanda ya haddasa masa zabura
tare da kai hannu gabanshi cikin dibara gudun kada Neerah ta gani saidai ita sam bata lura da
sanjinsa ba, saima tambaya da ta jefo masa.
"Yaya Yarima wasu kalan mafarkai kakeyi? In da hali ka sanar da ni irin wanda kayi jiya tunda
na zama sirrinka kuma zan cigaba da kasancewa sirrinka na har abada."
Kallonta yakeyi cikin jin wani kalan sha'awa na taso masa na daban da yarda ya saba shiga,
sam bai fahimtar zantukan da takeyi.
Jin bai amsa ba sai ta kalleshi, mik'ewa tsaye tayi jikinta na rawa dan a take ta tuno mafarkinta
na jiya mai wuyar sha'ani, ware idanu tayi a kansa tare da tsirawa inda hannayensa suke ido, ya
cire hannun cikin dibara, suka tsirawa juna ido ba k'iftatawa, a take Neerah ta gano halin da
yake ciki wanda a irinsa ta ganshi a barcinta na daren jiya, sai dai tuno abinda ya faru
tsakaninsu yasa ta nemi barin wurin saidai ta makaro dan a zafafe ya damki dantsen hannunta
ya jefata a k'irjinsa ya matse, yana sauke numfashi da sauri da sauri tare da jin harbawan
halittarshi cikin salon da bai taɓa samun kansa ciki ba, sai ya sami kansa da ware ƙafa ya
matse guk'unta gam.
"Innalillahi wa inna ilaihin raji'un, na mutu Mamina, dan Allah Yaya Yarima karufamin Asiri."
Abinda Neerah ta iya furtawa kenan cikin ƙaramar murya saboda tana gudan kada tayi ihu su
Abba su dawo su gansu a haka Sadauki ya kunyata lamarin da zai iya kawo nak'asu ga samun
damar mallakan junarsu a matsayin ma'aurata tare da hawa karagar mulkin Birnin Mungaye.
Jikinta ne ya soma rawa cikin jin shiga matakin da bata san ta inda ya afku ba wato feeling da
take cikawa su Lailah bakin bata cikin mata masu motsawar sha'awa, duk in suka nutsa cikin
hiransu na 'yamma, inda zasuyi ta tsokanar da cewa bata cika mace ba ne shi yasa.
Juyatan da Sadauki yayi zuwa ƙasan shi cikin fita hayyaci yasa ta dawo ɗan tunanin da ta afka,
sai dai ta makaro wurin kwatar kanta domin ya saka mata ƙarfi yana kaimata summba a zafafe
a duk inda bakinsa ya sauka.
*Alhamdulillah.*
This is the end of free pages.í ¾í´©
Affuwan idan na b'atawa masu jiran shi a kyauta, hakan ya faru ne saboda wahalar da rubutu ke
da shi gami da kashe lokacin ayyuka.
Pay 300 only to 0468069082, Haruna Safiyya GTbank. Send the evidence via 08132166848.
*Yanzu labari ya soma.*
*Ga dai Sadauki da Dr. Neerah, shin ko ya zasu ƙare? Wani Zalinci Sadauki ya aikata da ya
zamo kalubale a rayuwarshi? Wacce Aljana ce wannan? Shin burinta na wulakanta Sadauki a
cikin fadar birnin Mungaye na samuwa kuwa? Waye Sarkin Mungaye cikin Sadauki, Hud,
Sardauna da É—an dogarai Salis? Burin Mamma da Umma na samuwa kuwa? Sannan ga Tsibiri
can na shirin kamawa da wuta. Wa zai kawo masu É—auki? Shin ta ina Gimbiya Lina zata soma?
Burinta na hayewa karagar mulkin Hatsabibin Tsibiri tare da kawo canjin mulkin Aldalci na cika
kuwa? Shin itama Lima na samun damar mulkan Tsibirin? Me ye sirrin da Lina take b'oyewa?
Shin ta yaya Hadimi Tsidau ke kub'uta? Waye Sadauki GauÉ—u da dalilin mallakawa Gimbiya
Lina sirrukanshi na tsafi? Shin Ifritu Baushe na yin nasarar É—auke Mah tare da mallakan
Gimbiya Lina kuwa? Buda na samun cikar burinsa na auran Lina da hawa kan mulkin? Ya Abun
zai ƙare? Shin na mallakan tulun ruwan albarka da Zoben sihiri kuwa?*
WaÉ—annan dama wasu bayanen duk suna tafe cikin cigaban labarin HATSABIBIN TSIBIBI(
labari mai É—auke da sashi biyu) A cikin farashi mai sauk'i #300 kacal. A turo ta asusun banki
kamar haka 0468069082 Haruna Safiyya GTbank, sai a turo shaidan biya ta wannan layin
wayar: 08132166848.
Thank you so much my fans. I said kada ku bani kunya dai.í ½í¸Š
Momyn Haske neí ¾íµ°
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na
https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake
yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta
don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin
littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta
whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda
ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura
maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi
amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga
dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including
your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not
charge for our services
Note