Showing 27001 words to 30000 words out of 45162 words

Chapter 10 - HATSABIBIN TSIBIRI Littafin Yaki Book Complete .pdf

Unknown   

25 Mar 2025

5208

d'iga man ayu a ciki a shanye da d'umi-d'umi za a iya zuba
zuma ko siga a ruwan Lipton d'in dan gudun d'aci haka za a iya zubawa a ruwan Tea a sha.
Masu asma da limoniya kuma zasu jajjaga tafarnuwa su matse ruwan su zuba ruwan d'umi da
man ayu su shanye. Masu Infection duk in suka wanke wurin da ruwan zafi sai su saka man ayu
haka masu kaikayin jiki idan sun fito wanka sai su shafa amma zasu sha da ruwan Lipton, Allah
ya ƙara mana lafiya Amin.*
[1/13, 12:05 AM] Mrsjmoon: HATSABIBIN TSIBIBI.
By Mrsjmoon.

Adabi Writer's Association (AWA)

https://arewabooks.com/book?id=63a2e3d8821822a8402d8eb1 follow me on Arewabooks 🖕

Page 11.

Su Lailah na fita wajen Masarauta Neerah ta doshin Mungaye Garding maimakon gidan Dada
da ta ce zasu.

"Dr. Ya dai?"

"Nafasa zuwa can muje Lambu saman Lilo."

"Lilo kuma? Yau ke ce ki ke ambatar hawa Lilo?"

"Eh Ina son tuno da wani yanayi ne da ya wuce."

"Ikon Allah, anya ba soyayya kika faÉ—a a gofce ba Sister?"

Bata amsa ba ta tura hancin motar cikin garding dogarawa masu gadin gate É—in suka soma
mik'o gaisuwa hannu suka d'aga masu kawai suka wuce. Can kusa da filin motsa jiki ta yi
parking suka fito zuwa wurin Lilo sula hau suna motsawa a hankali. Neerah ta yi lum idanu
lumshe fuskanta cike da murmushi, ita dai Lailah da kallo take binta cike da mamakin sauyin
yanayinta daga mara walwala zuwa mai walwala daga hawa saman Lilo.

"Uhm in tayi wari maji."

"Me ne?"

"Komi da kike b'oyemin."

Wani murmushin ta sake cika fuskanta da shi, Lailah ta kaiwa cinyarta duka ta buÉ—e ido da sauri
tana shafa wurin batare da tayi yink'urin ramawa ba, cike da mamakin hakan Lailah ta kamo
hannunta tana cewa "Me ke faruwa Neerah da za a yi miki abu ki hak'ura batare da kin rama
fiye da yarda akayi miki ba?"
Bata kula ta ba illa ta sake lumshe ido tana motsa Lilon da É—an sauri

***
"Imam ina cikin damuwa domin a yau ina jin k'aunar d'iya mace sama da komi sai dai k'alubalen
da na ke hangowa na son dakushemin k'warin guiwar da nake da shi na tunk'arar yarinyar."

"BuÉ—e min lamarin bana son wannan kwane-kwanen Malam."

Rintse ido Sadauki ya yi tamkar ba zaiyi magana ba zuwa can ya buÉ—e ido yana fuskantar Imam
cikin serious tare da yin ƙasa da voice kana ya ce "Ita ce nake hangowa zata iya hak'uri da
lalurata, ita ce zata b'oyemin sirri, ita ce jinin jikina gaba da baya dan haka ina jin k'aunarta
domin zamowarta mai bani kariya tun sadda na fuskanci ina da lalurar haka ita ce ta fi kowa
fahimtar lamuran da na aikata ƙaddarata ce ba son zuciyata ba, shin me wannan karamcin
gareni da me ta dace a wurina?"

Shiru Imam ya yi domin bai É—auka jiran amsarshi Sadauki ke yi ba.

Duka Sadauki ya sauke mashi a arm ya kalle shi da sauri yana shafa wurin.

"Uhm answer please."

"Au wai tambayata kakeyi daman? Ai nazaci duk cikin tsarin salon labarin ne."

"Wato ka maidani mai zancen kihayoyi ko? Thank you."

Yana ambatar haka ya mik'e ya shige bedroom ya bar Imam da baki buÉ—e.

"Anya Sadauki baida shafan aljannu kuwa?"

Imam ya furta cikin tsirawa k'ofar d'akin da Sadauki ya shiga ido. Ba jimawa ya fito cikin sport
ware ya d'ora alkyebba saman su ya wuce ta gaban Imam cikin takun k'asaita.

"Uhm sarauta ba k'arya ba magajin Gobe."

Jiyowa ya yi cikin tsare gida ya motsa lips a hankali ya ce "Mu haÉ—u a filin motsa jiki inkaga
dama."

"In kuma ban gani ba fa?"

Cije lips Sadauki ya yi kamar zaiyi magana sai kuma ya fice da sauri.

"Aliyu rigima, ai sai ka sanar da ni abin da ke damunka tunda A har zuwa Z, ina sane nake nuna
ban gane yarenka ba, fatana Maryam ce kakeyiwa wannan k'aunar tabbas dana tayata murnan
na dakon k'aunarka da tayi tsawon lokaci."

Mik'ewa yayi zuwa dakin barcin Sadauki ya sanja kaya zuwa na motsa jiki kalan da Sadauki ya
saka wato white da rashin red, ya sako jallabiya mai hula akai ya fito sai ya sami Sadauki tsaye
a bakin k'ofa yana jiranshi dukan wasa ya sauke masa a kafad'a ya dalla masa harara aikam ya
kawo hannu kamar zai tsole idon ya yi saurin kauda kai.
"Au ashe Sadaukantakar na bogi ne tunda har d'iya mace ta iya raunata hamshak'in basarake
kamar Aliyu Baban Mamie Fulani shalelen Mai Martaba Professor Ab...

"Malam ya isheka wannan shiriritan in zaka zo muje, kaji damuwata kazo in kuma neman
magana zaka tsaya sai ka sami wurin zama ga guzirin paper can a saman bola ka d'auka kayi
ta rubutu."

"Wato na zama mahaukaci kenan?"

"Kusan haka."

"Ni dalla muje kada Matana ta nemeni."

Wani mugun kallo Saduaki ya wurga masa ya ko kwashe da dariya domin ya rama mai dashi
mara aikinyi da ya yi cikin sauk'i.

"Inaga zanyi hijira daga Masarauta domin samo mafita da kaina batare da masu mata sun
tsomamin baki ba."

"Sorry Aliyu muje naji damuwarka da fatan ina da mafita."

"Malam na fasa sanar da kai zan nemi mafita da akai ko wurin Muneerah."

"Haba Yallab'ai yaushe kafara shawara da k'annenka kuma mata?"

"Tun sadda ka zama mai iyali."

"Oh ya rabbi affuwan Sadauki kafahimceni ba da wata manufa na ambata maka hakan ba sai
dan in rama abin...

"Is ok nasani wasace, oya wuce muje Aminin sirri tun yarinta."

"Nagode Sarkin Gobe."

"Allah ya amince hakan É—an uwa."

"Amin."

"Mubi ta baya bana son bi ta babban gate su dameni da kirari."

"Ok amma ka sani matsayinka ne ya kai."

Bai kula ba uka jera Imam natayi masa magana cikin rad'a shi kuma na gyad'a kai tare da
murmusawa, zuwa can Sadauki ya kawo masa naushi ya yi saurin tarewa, jinjina Sadauki ya yi
masa cikin sake faÉ—ad'a murmushinsa.

"Yes jiya ba yau ba boss, ko ka manta mun halarci makarantar koyon dambe a b'oye da muke
Japan?."

"Imam ina jin wata rata sai kayi sub'ul da baka ka tona mana asiri a Fada, mu shiga uku da
masifar Abba Chiroma."

"Kai Allah ya tsare wannan rana na shigarmu karejin haƙoran Abba Chiroma."

"To Amin dai."

Suka murmusa tare da shigewa garding, batare da b'ata lokaci ba suka yi shirin soma buga
wasan basketball.

"Za'a ga wanda yafi zira k'wallaye araga, idan har ka wuce ni ko da tazarar É—aya ce to ka
can-canci sauraren damuwata inko na wuceka da good 5 goal to Muneerah ce zataji damuwata,
do you agree?"

"Yes."

"Ok let start."

Ya cillawa Imam ball É—in, ya ko cafe suka soma wasan cike da k'warewa. A cikin mintoci k'alilan
Sadauki ya yiwa Imam 5 one. Cikim dariya ya dakata yana cewa "Ina baka tazarar biyar ka tashi
daga aminin sirrina Dr Neerah zata maye gurbinka, right?."

"No Aliyu mu bar wasan da ba zai fish-shemu ba, taho muje bakin k'orama ka sanar dani
damuwarka kuma na yi alk'awarin fitar da kai hanya mai b'ullewa tamkar dai yarda na saba."

"A'a taho mu cigaba da wasa ina jin nishad'in buga kwallon."

"To ni na gaji sai kayi kai kad'ai ko ka kira Doctor Neerah sabuwar Aminiyarka."

"Eh gani a kusa ai zan tayashi tafi kayi hutawarka Yaya Imam."

Neerah ta ambata tana mai buge ball d'in a hannun Sadauki ta rungume.

Idanu suka zuba mata ta rausayar da kai tare da zare ƙaramin hijab ta cillawa Lailah sannan ta
b'alle abayarta, ta bayyana cikin best iyaka cibiya da gajeren wando da ya matseta wanda ya
tsaya iya guiwarta, ta ajiye ball É—in ta tubke gashinta sai reto yakeyi saboda tsayinsa sai ta fito
tamkar yar wasan na zahiri.
"Oya taho mu soma na baka tazara fiye da wanda ka bawa Yaya Imam."

Ta ambata cikin ja da baya ta soma buga ball d'in cike da k'warewa.

Kallon Imam ya yi yaga ya tsira mata ido, wani harbawa k'irjinsa ya yi ya zabura yayo kanta a
fusace, aikam sai ta zille da ball É—in kafin ya kamota ta daka tsalle ta cilla sama ya zabura ya
buge balla din tare da hannayenta tayi baya zata fad'i ya tarota ya jefa a cikin k'irjinsa ya
matseta da k'arfi, ihunta ya fito tare da nashi inda shi ya furta "Bani rigarta Lailah!"
Kafin Lailah ta d'auko Imam ya miƙa masa ya fizga tare da rufa mata sannan ya sake ta ya juya

baya ya kare ta yana mai bata umurnin ta suturce jikinta. Jikinta a sake ta sanya sannan ta iso
gefensa ta tsaya ya kalleta idanu jajur lumshe nata ta yi sannan ta juya ta soma tafiya ya riko
hannuta ya matse ta kallo ƙara ya kalleta cikin kaushin murya ya ce "Wannan shi ne karo na
farko da zan sake ganin kina bayyana tsiraicinki tunda baki da tunani sokuwa kawai."
Ya cillar da hannun ya nufi inda alkyabbarsa ya ke ya saka ya nufi bakin k'orama ya faÉ—a ciki
tunjim!!.

Duk suka zabura saboda sautin ya razanasu.

"Nima abinda zan sanar da ke kenan dan Allah kada ki sake aikata hakan Neera, ko ba komi ki
tuna matsayinki na 'yar Masarauta kuma mai tarin sani ga addini."

"Baza ta sake ba Yaya Imam."

Lailah ta ambata a hankali. Motsa kai ya yi ya nufi bakin k'oraman cike da tarin tambayoyi game
da abinda Sadauki yayi wanda bai taɓa aikata kwatan-kwacinsa ga d'iya mace ba wato
rungumarta cikin nuna tsan-tsan kishi.

***
"Muje ko?"

Girgiza kai ta yi.

"To me zaki tsaya yi tunda giyan k'aunar ya kaiki aikata abinda baki taɓa yi ba."

"Me na yi Lailah"

Neerah ta furta cikin rawar murya mai nuni da tana daf da fashewa da kuka.

"Ni taho muje kada ki sake bada kanki har ki shafamin."

"Ya gane ina son shi wai?"

Tafi Laila ta sanya gami da fashewa da dariya lamarin da ya dawo da Neerah hayyacinta ta dafe
goshinta cike da takaicin fallasar karatun ruhinta.

"Nagano karatun ruhinki Sister sai dai abun da kamar wuya wai gurguwa da auren nesa haka
fagen da 'yan hamayya sai kin nemi makaman ya k'i domin Zuhra da Maryam na cikin filin
dagan."

"Maryam? Wacce Maryam?"

"Maryam tamu k'anwar yaya Imam d'iyar Momy da Abba Sarkin Fada."

Wani dum taji, jiri ya ziyarceta tayi baya zata fad'i, daidai Hud ya iso wurin sai ya tareta da sauri
yana ambatar sunan Allah, lumshe ido tayi tana nanata sunar Maryam aminiyarta itama na son
Sadauki domin sam jin Zuhrah na ciki bai d'aga mata hankali ba.

Ruwar da taji an fesa mata a fuskan yasa ta buÉ—e ido tana sakin ajiyar zuciya, tundaga saman
sumar kansa ta soma kallonsa har ta dire a fuskanshi wanda ke d'igan ruwa.

"Yaya Yarima."

Ta furta a saman lips d'inta tana sake lumshe idanu.

Harara ya zabga mata tare da fizganta daga hannun Hud ya nuna mata hanyar waje "Maza ku
b'ace min dagani tun ban karya ku ba kuma daga yau na haramta muku sake shigowa lambun
nan sai da izinina, idan kuma kun isa in sake ganin sillayen ƙafafunku cikinsa."

Da sauri Lailah ta ja hannun Neerah suka fice, wacce jikinta yayi mugun sanyi.

"Malam ba da haka ake nuna k'auna ba ka natsu mu buga game d'in duk da ba ni kad'ai ke cikin
'yan wasan ba, Ni, kai, Sardauna wata k'ila har da d'an korenka Imam na ciki ko da yake na san
kai baza ka haye ba saboda warin kashin kajin dake manne da kai na auri sa...

"Ya isheka Hud bama son rashin tunani, dan haka ka kiyaye kalaman da zai sake fitowa a
harshenka."

"In ank'i fa?"

Kafin Imam ya bashi amsa Sadauki ya janyo hannunsa na girgiza masa kai alamun kada ya
sake magana, tsaki ja tare da nuna Hud da yatsa alamun gargad'i sannan ya biyo Sadauki na
bambamin faÉ—ar bai son hanashi gogewa masu kawo masa raini hadda da keyi.

***
"Aikin banza da wofi wallahi sai na zama sarkin Mungaye ko da hakan zai zamo fansa ne ga
ruhina."

"A she muna da yawa masu fansar da ruhunan namu akan hawa karagar mulkin Masarauta
Mungaye."

A razane Hud ya kalli inda maganar ya fito ya yi raba da Salis d'an Babban Dogari kuma d'a ga
Jakadiyan sirri.

"Ai wai cin dank'o har da su Kaza?"

"Eh sai dai na wuce Kaza sai Jimina."

"To mu zuba shege ka fasa."

"Tam zaka sha mamaki kuwa."

Saboda takaici Hud bai sake magana ba ya bar wurin, Salis ya rakashi da harara daga bisani ya
É—auki Basketball d'in ya soka bugawa shi kaÉ—ai cike da nishad'i.

***
Nagaji Imam! Nagaji na ce! Wallahi zanyi hijira, zan tafi inda ba wanda zai sake jifana da
kalman auri saki sannan auren ma na fasa yinsa, ka zamo shidata insha Allah ni da aure har
aba...

"Kul! Baban Mamie, kada ka sake ka shiga hurimin Ubangiji, auri saki na cikin zanen ƙaddarar
ka dan haka kada ka yanke k'auna daga samun rahamar Ubangiji, ka sama ranka zakayi aure
kuma zaka rayu da matarka batare da saki ya shiga cakaninku ba."

"Banjin hakan zai tabbata gareni ba Imam."

"Na ce ka saka a ranka zakayi aure ka yi rayuwa tamkar yarda kowa keyi."

"Ta yaya hakan zai faru, alhalin wancan shed'aniyar na bibiyan bad'ini da zahiri na, shi yasa zan
koma inda babu mutane na k'arasa rayuwata hankali kwance."

"Aliyu ka dawo hankalinka, wai me ke damunka ne?"

"Damuwa mai tsanani."

"Nasar da ni Please."

"Not now Imam domin baka da abin magancemin shi."

Yana ambata ya mik'e ya shige dakin barcinsa ya murza key.

Cike da tarin damuwa Imam ya fice domin tunda yaga Saudauki ya kulle kansa ya tabbatar ba
zai taɓa saurarensa yanzu ba dan haka cikin Masarauta ya nufa, direct turakar Mai Martaba ya
nufa yana addu'ar samun nasara a k'udirinsa wanda ke hasko samun yayewar damuwa ne ga
Amininsa.

'Tuni na jima da sanin kana tare da aljannu, In banda aljana ta aureka taya zaka riƙa zancen
ganinta a zahiri d bad'ini, kai wallahi da sake ba wanda ya isa taɓamin amini ya kwana lafiya ko

da kuwa Aljan ne.'

Shigowar sak'o a wayarshi yasa ya katse masa zantukan zuccin da keyi ganin daga Sadauki ne
sai ya waigo ya kalli volcany ya hangoshi tsaye hannaye rungume a k'irji sai ya maida kallonsa
ga sak'on.

"Ban amince ka sanar da Abba komi ba domin baza su fahimta ba, ka tafi wurin iyalinka zaifi
maka."

Kallon inda Sadauki ya ke ya sakeyi har lokacin na nan tsaye sai ya girgiza masa kai tare hawa
barandar sashin Mai Martaba, wayarshi ya soma ringing sai ya maidata silent ganin Sadauki ne
ke kiranshi, yana zama gaban Mai Martaba ko gaisar da shi baiyi ba sallamam Sadauki ya doki
kunninsa waigowa ya yi a razane domin bai isa ya iso da hanzari haka ba duk kuwa saurinsa.
'Anya aljannu ba su maidamin da Amini jinsin su ba?'

"Imamundeen ya dai kake kallon k'ofa?"

Murza idanunsa ya yi babu Sadauki tamkar yarda ya gansa cikin 'yan sakonni da suka wuce.

"Uhm kana lafiya kuwa?"

Ya katse masa tunani.

Maido kallonsa kan Mai Martaba ya yi kafin ya furta kalma ya jiyo Muryan Sadauki na gaisar da
Mai Martaba.

"Au ka ce tare kuke shi ne ina magana kana kallon k'ofa tamkar warkewar makanta."

"Abba anyi lafiya?"

Ya sami kansa da furtawa.

"Alhamdulillah Imam."

Ya amsa tare da mik'ewa ya nufi d'akin barcinsa ganin su Imam nata mazurai ya ce idan sun
shirya magana da shi su sameshi a ciki dan bai shirya kallon shirmensu na fama ba.

"Kai Sadauki ban son iskanci wato Ofin naka har kanka amininka zai sauka?"

Imam ya ambata cikin fushi.

"Tashi muje ko ranka ya b'aci."

"Ban zuwa sai na bada labarinka da Aljannu."

"Zakuwa ka zama bebe nan bada jimawa ba, tunda baka ji magana."

"Aliyu me kake aikatawa a b'oye? tsafi ko me?"

"Amsa wannan mara jin magana kawai."

Aikam kafin ya ankara wani dum ya shiga kanshi ya tafi luw zai fad'i Sadauki ya tare shi zuwa
jikinsa tamkar walk'iya suka suka b'ace daga falon. Tun Mai Martaba na dakon shigowarsu har
ya gaji ya tashi ya shiga toilet ya d'auro alwalla ya zauna gabatar da azkar d'in marece cikin
rashin damuwa da lamuran shiri-ritansu domin sunar da ya bawa lamarin kenan.
***
TSIBIRI.

Tsidau ya sauka a wani tsauni mai yalwan bishiyoyi wanda suka taimaka wurin ƙara duhun da
tsauni ke da shi, amfani ya yi da haskensu na junnu ya cike tsaunin da haske sannan ya samu
hango Tsibirin da ke nema wato fadar Ifritu Baushe wanda ya zamo Bil'adam amma yafi Aljani
shed'anci ta ko wani fuska shi yasa ake yi masa lak'abi da sunan mugayen Aljannu wato Ifritu.
Tsibirin sai fitar da bak'in hayak'i keyi hakan ya ƙara munana dutsen da ya zamo fadar Baushe,
ƙasan dutsen kuwa wuta ne ke ci cikin fitar koren harshe, da ganin wurin zuwarsa sai an shirya
baga Bil'adam ko Ajani ba.

"Lallai ka ci sunarka Baushe domin ko a itatuwan daji, itacen Baushe ba mai saukin k'onawa ba
ne kamar yarda na ke hango shiga fadarka ba mai sauk'i ba ne."

Tsidau ya ambata yana nazarto yarda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login