Showing 33001 words to 36000 words out of 45162 words
Chapter 12 - HATSABIBIN TSIBIRI Littafin Yaki Book Complete .pdf
Unknown
25 Mar 2025
5210
cikin takon dake
motsa ƙasa zuwa can ya d'aga sama tamkar tsuntsu ya b'ace cikin gajimare.
Lima da duk abinda da ya afku akan idonta ta shiga mamakin lamarin sai kuma ta saki
murmushi tare da shigewa d'akin Mah ta isa gaban bangon da Mah ke hira da Lina ta shafa
take kuwa Lina ta bayyana cikin shigar yak'i fuskanta babu d'igon annuri lamarin da ya razana
Lima domin bata taɓa ganinta cikin ɓacin rai irin wannan ba tun tasowarsu.
"Me ke faruwa 'yar uwa?"
Lima ta jefo mata tambayar a rikice.
"Ya wuce É—aukan tunaninki Lima, ni dai ina son ki kulamin da Mah, kada sakacinki na yawon
zuwa mashaya ya janyo na rasa Mah, domin in hakan ya faru na rantse da ruhin Sadauki
GauÉ—u sai na illata rayuwarki ki zamo baki da mamora balle ki sami damar zuwa timb'ele a
mashaya."
"Kada kiyimin barazanar da har abada nafi ƙarfin sa kawai ki sanar dani abinda ke faruwa ko ina
da halin taimakawa akai."
"Ki kula da Mah shi ne kaÉ—ai taimakon da zaki iyayi."
"Kin san shirin Abun kenan?"
"Eh wanda hakan na nuni da rayuwarsa na daf da zuwa ƙarshe."
"Me kike nufi?"
"Zan tafi idan na dawo zan sanar da ke komi batare da kin tambayeni ba."
Sai kin dawo amma ki sani ba zan zauna gadin Mah ba tunda ba dan shi na zo duniya ba."
"Shi kenan na barki lafiya amma ki kwana da sanin rasa Mah tamkar nak'asarki ce, wata ƙila
makanta, kurumta ko gurgwanta sai kiyi nazarin abinda zai fish-sheki domin tabbas sakacinki
yasa na rasa farin cikina wallahi kema kinyi ban kwana da naki farin cikin. Ki kula da Mah shi ne
ƙarshen umurnina gareki Lima."
Kafin Lima ta yi magana bangon ya dawo yarda yake tamkar komi bai wanzu ba a mugun
fusace ta fice batare da ta kula kiran da Mah ke yi mata na kula da ita ba dan ta shiga rud'anin
kalaman Lina har tayi da ta sanin k'in binta da tayi.
Bukkan Kaka Gunu Lima ta nufa ta shige batare da samun tangarda ba.
"Zannuna miki ni ce shugabanki Lina kuma magajiyar karagar Tsibiri, a yanzu banjin ko Abun
zaifini ƙarfin iko balle ke 'yar tsako abar tausayi."
Ta na rufe baki dutsen dake Bukkan ya dare biyu wata gawurtacce mikiya ta bayya ta iso
gabanta ta zube tare da rikida zuwa mutum maiji da Sadaukantaka ya russuna cikin cewa
"Barka da zuwa magajiyar Tsibiri shalelen mai gida Gunu, raina fansa ne gareki ya ke uwar
gijiyata."
"Waye kai?"
Ta ambata cike da izza duk da tana kokwanto ko Tsidau ne ya sanja salon yaudara.
"Ki kwnatar da hankalinki ba mayaudari Tsidau ba ne a gabanki wannan amintaccen Hadimi ne
sunana Mutuwa babban hadimin Kaka Gu...
Ai kafin ya k'arasa zancensa Lima ta fice Bukkan a guje lamarin da ya janyo Mutuwa ya bushe
da dariya a take Bukkan ya soma motsi tuno illar da dariyarsa zai iya haifarwa ga Tsibirin sai
yayi gaggawan tsuke bakinsa amma duk da haka saida wata dunk'ulalliyar Guguwa ta fice ta
rufawa Lima baya ya so bin guguwan ya dawo da ita amma ya kasa saboda aikinsa iyaka kula
da cikin Bukkan ne da kuma tulun ruwan albarka.
*Muna saida ingantaccen man ayu wanda ya zo daga Chad. Yana maganin Infection, asma,
limoniya, mura, ciwon basira ciwon kai, ciwon baya, ciwon ƙafa, ciwon mara, kaikayin jiki dana
matse-matsi, yalwatuwar ni'ima tare da samun gamsuwa a turaka da sauransu, muna saida
É—aya ko sari mai so zai iya tuntubar number nan ta WhatsApp ko kira. 08132166848. Yarda ake
amfani da shi za a jik'a Lipton sai a d'iga man ayu a ciki a shanye da d'umi-d'umi za a iya zuba
zuma ko siga a ruwan Lipton d'in dan gudun d'aci haka za a iya zubawa a ruwan Tea a sha.
Masu asma da limoniya kuma zasu jajjaga tafarnuwa su matse ruwan su zuba ruwan d'umi da
man ayu su shanye. Masu Infection duk in suka wanke wurin da ruwan zafi sai su saka man ayu
haka masu kaikayin jiki idan sun fito wanka sai su shafa amma zasu sha da ruwan Lipton, Allah
ya ƙara mana lafiya Amin.*
Momyn Haske ne í ¾íµ°
[1/13, 12:05 AM] Mrsjmoon: HATSABIBIN TSIBIBI
By Mrsjmoon
Adabi Writer's Association.
13
Guguwar ta wuce Lima ta nausa cikin Tsibirin inda ta soma b'arna domin duk wanda taci karo
da shi nad'eshi takeyi ta yi yaga-yaga da namansa ta watsar. Kafin 'yan mintoci tayi mugun
b'arna musanman ga tsoffi da ƙarfinsu ya ƙare. Kuru-ruwan da ke tashi ya cika ko ina a Tsibirin
yasa Mah fitowa domin ganin abinda ke faruwa saidai bisa tsau-tsayi Guguwan ta yi karo da ita
wacce ta juyo domin komawa inda ta fito bisa arangamar da tayi da matsafan Tsibiri suka haÉ—u
suka dakushe tasirinta shi ne ta juyo a fusace sai Mah ta faÉ—a komarta. Cikin kiftawar ido tayi
awon gaba da Mah, ganin haka ya sanya Lima kwalla ƙara da ya haddasa zubowar ganyan-yaki
daga jikin bishiyoyi, a take suma suka rikid'e zuwa guguwa mai karfi wanda ya doke wacce tayi
barna, suka watsu cikin al'umma suka soma illata ganinsu.
***
MUNGAYE.
"Sadauki banda Ofi da ka gada zamowarka Gambon 'yan biyu har da tsafi kake haÉ—awa?"
"Imam tafi wurin iyalinka am not in good mood gobe zamuyi magana."
"Kasan Allah ban wucewa sai ka amsamin tambayata."
"Nacinka yayi yawa Imam."
"Naji kome zaka kirani, ina dai jiran amsarka."
Tsaki Sadauki ya ja tare da dukan goshin Imam da ƙarfi aikam ya sunkuya ƙasa da sauri dafe
da wurin yana sakin ihu mara sauti.
"Ragon maza kawai kana ambatar Brother Sardauna da rago a she kaima layin kake."
"Sadauki tafi kawai nafasa jin amsar."
Yana ambatar haka ya nufi Part dinsa da sauri har da haÉ—awa da gudu, dariya mara sauti
Sadauki ya raka bayarsa da shi yana mai furta "Bana tsafi aminina amma ina iya yin wasu
ababe tamkar mai sihiri duk a sanadin zamowana Gombon 'yan biyu kamar yarda ka ambata
sannan tare da taimakon Aljanar can mara mutunci."
Yana ambatar haka ya tsare giran sama da ƙasa ya doshi part d'insa rai b'ace tamkar bashi ne
ke nishad'i yanzu ba.
***
"Neerah idan muka tafi gidan Dadah kafin mu dawo dare yayi kinga Mami b'ata son tukin dare
ga su yaya balle garemu mata, haka Abba zai hukuntamu domin kinfi kowa sanin dokarsa a kan
'yan matan Masarauta."
"Kaini gate din gidan ki juyo kawai Sister."
"Kina son janyowa kanki magana ko Doctor?"
"Gidan Dadah zan kwana ba wani wurin da banba Malama."
"Umurnin Abba ne dole kowa ya kwana gida in har ba gari mutum ya bari ba ko aiki irin naki ya
riƙe mutum."
"Idan an tambayeki kice ina asibiti ina da tiyatan dare."
"Ba zanyi ƙarya ba."
"Shi kenan bani motar ki tari napep ki koma."
"Wannan isar ne kuma bakiyi ba sai dai ke ki hau Napep É—in."
"Lailah ke É—in ciwon kai ce wallahi, dan Allah ki barni na huta badan na isa ba."
"Bakiga hutu ba tunda kika bari ƙaunar abinda zai iya tarwatsa rayuwarki yayi miki kamun kazar
muku."
"Kina cikin yan adawa kenan."
"No, but ina takaicin lamarin."
"Why?"
Sai da ta fesar da iskan bakinta sannan ta amsa "Yaya Sadauki nawa ne zanfi kowa murna da
aurenku amma ɓacin ran da zai biyo baya shi ne bana son ji da ganinsa dan haka ki hak'ura da
yaya ki kama na gaske mai yi miki ƙauna mara algus."
Lafewa Neerah tayi a seat tamkar mai barci, batare da Lailah ta kula da hakan ba ta cigaba da
cewa "Mami zata shiga damuwa sannan Abba zaiyi fushi da yaya in har ya aureki ya saki kamar
yarda yayiwa su Mubina kuma mu...
"Ina sonshi a hakan, in yaso ranar da aka daura mana aure ya sakeni, ni kuma zan nuna masa
zama da shi yanzu na soma aurenmu mutu ka raba takalmin kaza."
Ta katse Lailah cikin ɓacin rai.
"Neerah ki dawo hankalinki kada so ya rufe miki ido ki kasa gano aibun lamarin, wallahi nafi ki
son aurenku amma su...
"Da kata da motar Malama!"
Gefen hanya Lailah ta gangara ta tsaya, Neerah ta nemi ficewa ta yi saurin kulle motar baki
É—aya.
"Buɗe ni ko ranki yafi nawa ɓaci."
"Ina dakon duka tunda daga faÉ—ar gaskiya sai ya zamo aibu."
"Lailah rayuwarki ko nawa?"
"Yours."
"To ki zuba ido zaifi miki."
"Ank'i zuba idon wallahi ko kina so ki ba kya so sai na sanar da ke illar zawarci dan haka bazaki
auri yaya Sadauki ba ga yaya Najib nan ya mutu a da ƙaunarki dan haka shi ne zaɓinmu domin
munga abinda zai iya ba dan mutuwa tayi masa yankan ƙauna ba da yanzu suna da albarkan
aure."
"To Ammi sai ki É—aukeni ki kaini dakinsa da wannan zantukan banzan kuma ki fita harkata tun
raina bai ɓaci ba."
"Macizai ne turosu muga wanda zai afka ɓacin rai ni da ke domin kinfi kowa sani a fannin
tankasar muke."
Shiru Neerah tayi tana sauke murmushin yak'e.
'Kai wallahi Lailah fitina ce bata tsoron a mutu.'
"Yes bana tsoron a mutu domin mai tsoron a mutu shege ne."
Idanu waje Neerah ke kallonta jin ta bata amsar zancen da tayi a zuci.
Harara ta zabga mata tare da tada motar da juya zuwa Masarauta, Neerah na kallonta bata
tanka mata ba saboda duk tarin rigimanta Lailah ta damata ta shanye. Suna isowa bakin gate
Sadauki na fitowa zuwa masjid, tsayawa Lailah tayi tana hararan Neerah dake doka murmushi.
"Daga ina Sisters?"
Ya ambata idanunsa na kan Neerah ba yabo ba fallasa.
"Hanyar gidan Dadah wannan yar rainin hankalin ta juyo bisa dalili mara tushe."
Neerah ta amsa a shagwabe.
Hancinta ya ja cikin sake d'aure fuska, ta saki ƙara ya janye hannunsa yana zabgawa Lailah
harara ganin ta yi kamar bata a motar.
"Sorry Yaya bana jin daÉ—i ne."
Ta ambata da sauri.
"Saboda kina cikin 'yan adawa ba, kin san Allah kada inji kada in gani idan kuma kince wasa ni
da ke ne mara kishin d'an uwanta kawai."
Idanu waje suke kallonshi ya ja siririn tsaki ya wuce da kallo suka raka shi har ya haye stairs na
masallacin. A tare suka sauke ajiyar zuciya gami da tsirawa juna ido.
"Doctor ke ce kika bashi labari ko?"
"Tunda gani aljana ba."
"Be serious dear Neerah me yasa zakiyimin haka?"
Tsaki ta ja tare da bude kofar ta fice da sauri Lailah ta kunna motar ta zo ta wuceta zuwa
ma'adanar motoci ta ajiye ta fito ta cimma Neerah dake daf da shiga falon Momy, hannunta ta
fizgo suka kafe juna da ido.
"Sakeni to Uwata."
"Neerah me yasa kika bashi labari?"
"Kin san wallahi zan shuka miki rashin mutunci in kika ƙara zargina da gulma alhalin tare muke
ko kira ban amsa ba balle tura sako."
"To ya akayi ya gane ina adawa da ƙaunarku?"
"Ki tambaye shi zaifi da wannan ihu cikin dokar dajin da ba bil'adam balle dabbobi, sannan bai
san ina sonshi ba."
"Haka ne kuma fa amma anya yaya baida aljannu?"
"Layinku É—aya tunda kema kina jiyo zancen zucci."
Hannunta ta matse ta ko kwalla ƙara bashiri ta saketa tana dariya tare da cewa "Ke dallah
d'azun zancen zuccinki ne ya fito fili batare da kin sani ba."
"Kanki akeji dai, ni kinga tafiyata inyi dinner da Momy ."
"Uhm da kuma kishiyarki ba, 'yan wahala kawai."
A fusace Neerah tayo kanta ta kwasa da gudu zuwa Part din Ammi tana kyal-kyala dariya. Fasa
shiga part din Momy ta yi sai ta sami kanta da nufar Part din Imam kirjinta na harbawa da sauri
da sauri. Da Imam taci karo ya fito a gaggauce zai tafi masallaci, koda ta gaisheshi a hanzarce
ya amsa ya wuce bayansa tabi da kallo tana son aminta da karatun da ruhinta ke biya mata na
fallasa sirrin ruhinta gareshi ko tasamu ya yi mata jagora wurin mallakan Sadauki cikin sauk'i.
'Ki kame kanki Muneerah, namiji baida tabbas.'
"No, daina sanarmin da wannan zancen domin Yaya Yarima mai tabbaci ne."
Ta bawa zuciyarta amsa tare da turo k'ofar falon, Hafsat ta samu na shirya Mimi ganinta yasa ta
tsaya tsak ta zuba mata ido cike da mamakin ganinta a sashinta domin shigowar Neerah na
biyu kenan tun aurensu, na farko barkan Mimi tazo sai kuwa yau.
"Aunty Hafsat ya da kallo kamar na sanja miki?"
"Borin kunya ko Dr. Neerah?"
"No Aunty nidai bana son kallo ne sai duk naji na muzanta."
"Uhm to sannu da zuwa mai zumuntar ganin dama domin ba zance ni kaÉ—ai kike yiwa haka ba
dan har da su Aunty Hassana saboda nasha jin korafinsu akan rashin zumuncinki."
"Ayimin affuwa daga yau zan gyara shi yasa na soma da ke wacce ke kusa da Masarauta."
"To Allah ya nufa hakan."
"Amin."
Ta É—auki Mimi da ke ta mik'o hannu saboda bata da k'yuya. Cillata sama tayi tako kyal-kyale da
dariya sai lamarin ya taimaka wurin sanya Neerah nishad'i ta biye mata sukayi ta wasa, sosai ta
yabawa Hafsat wurin tsafta ganin yarda gidanta ke ta k'amshin tare adana komi a muhallin da
ya dace ga diyarta mai kyau cikin kamhi mai daÉ—in shak'a.
"Kawota kije ki ci abinci gashi can na shirya miki."
"Sallah zanyi Aunty."
"Ok shiga bedroom kiyo alwallah, ga k'ibla can."
Motsa kai tayi tana mai bin inda ta nuna mata da kallo. Bayan ta idar da sallah saita dawo cikin
falon ta zauna saman Cushing ta lafe tare da lumshe idanu tamkar mai barci.
"Kina tare da damuwa ko Doctor?"
Zubawa Hafsat manyan idanunta tayi fuska kwab'e, mai nuni da k'iris take jira ta fashe da kuka.
"Don't cry Sister, oya sanar dani damuwarki, it may be I have the solution."
"Aunty laifi ne idan ruhi ya samu abincinsa a lokacin da ya ke cike da yunwa?"
"Ba laifi ba ne Doctor domin samun cikar buri kenan."
"To me ya kamata a faÉ—a masa lokacin da yake burin cika tumbinsa da wannan abincin?"
"Abu biyu a lokaci É—aya su ne Ci a hankali domin kada ayi karo da tsakuwa wanda zai saka
abincin ya fita a ruhin ko kafin a Ci É—in a tabbatar da an duba babu wannan tsakuwa da zai iya
kawo cikas yayin kaishi ma'adanarsa."
"Karin bayani Aunty domin na kasa gano inda kika dosa."
"Manufata shi ne idan ruhi ya samu abincinsa to kada ya sake ya bawa abincin damar shiga
ma'adanarsa har sai ya tantance, wata kila zai iya illata shi dan haka ya san me ye nagartan
abincin tare da manufar cinsa gami da amfanin da zai samu idan ya ci domin gamsuwar ruhin
shi ne dace da abinci mai kyau da É—anÉ—ano da zai taimaka wurin tafiyar da lafiyar ruhin tare da
gangar jiki harma jama'a suyi alfahari da samuwarshi gareka ta hanyar yiwa ruhin fatan
dauwama tare da wannan abincin na har abada."
Shiru Neerah tayi tana nazarin zantukan kafin ta dawo tunanin ta tsinkayi muryan Hafsat na
ambatar "Allah yasa k'anwata ba soyayya ta faÉ—a a makance ba?"
Maimakon amsawa sai ta mike tana gyara zaman hijab d'inta tare da jan hancin Mimi wacce ke
lumshe ido tana son yin barci ta furta "Good night takwarar Mamina."
"Me kenan?"
"Zan wuce ai nayi miki hira insha Allah zan riƙa shigowa ko da a ƙarshen sati ne ina wasa da
diyata mai kama da Yaya Imam sak dan tafiki kyau da iya ado."
Yar dariya Hafsat tayi kana ta ja hannun Neerah zuwa dining tana cewa "Sai kinci abinci zaki
tafi."
Kan dole ta zuba ferfesun kayan ciki É—an dai-dai ta soma ci a hankali nata nazarin zantukan
Hafsa mai cike da fikrah.
'Lallai yaya Imam yayi dace da mata mai hangen nesa.'
"Hey Dr. Maida hankali ki daina karatun wasikar jaki wanda ba mai ganin ya rubutun ya ke sai
ruhi kaÉ—ai."
Murmusawa tayi tana mai sosa tsinin hancinta tare da gyaÉ—a kai. Taji daÉ—in ferfesun duk da
baya cikin abinci ta, ta kora da Apple juice zamowarta mara son drinks masu gas, sannan tayi
mata sallama ta rakota har bakin fita Part É—inta tana ta son jin gwaninta amma fir Neerah tak'i
bata haske sai zillewa zancen takeyi.
"Ai zanga Lailah ko Maryam nasan su zasu sanar da ni komi idan ke kin k'i buÉ—emin nayi fatan
khairan tunda kun sami yancin zaban abokanan rayuwarku da kanku ba irinmu ba da ko ka
zaba b'atawa kai lokaci kayi."
"Uhm nikam Aunty ban tashi yin aure ba yanzu dan haka bana da gwani."
"Samun wuri wato kunga an barku kun balaga kun balallage shi ne har da samun bakin salo?
Mu yaushe muka samu gatan nan, lallai Masarauta ta sami canji."
"Kai Aunty kuma fa saida kuka gama jami'a sanan kukayi aure dama dai su Aunty Hassana kika
ce su da secondary ma d'akinsu suka kammala."
"Eh da wannan kam amma dai kun fi...
"Good night Aunty yar jarida."
Ta katse Hafsat domin samun damar kufcewa zantukanta da ta lura basa da ranar k'arewa,
dukan wasa ta sauke mata a baya ta saki ƙara cike da shagwaba'a zata sake kai mata duka tayi
saurin ficewa da dan gudu tanajiyo dariyarta itama dariyar takeyi saboda ta sami nishad'i