Showing 12001 words to 15000 words out of 45162 words
Chapter 5 - HATSABIBIN TSIBIRI Littafin Yaki Book Complete .pdf
Unknown
25 Mar 2025
6520
a jikinsa, akan haka Mai Martaba ya ce ya gama samo masa matar aure. Bayan
watanni Mamie Fulani ta matsa sai ya amince da auren 'yar aminiyarta inda ya amince bisa
takurashi da tayi saidai shima auren kwanarshi daya ya bata sallama inda kafin ta isa cikin
Masarautar da labarin ya tsere gidanshi da ya gina a b'oye da ke dajin Tekun Kabobo wurin da
ba wanda ya sani sai amininsa Imam da turawan da sukayi aikin. Bayan wasu watanni ya dawo
ya sha faÉ—a tamkar Sarki zai dukeshi ya yi ta basu hak'uri, anan suka rutsashi sai ya sanar
masu da matsalarshi Amma yak'i magana akan dole suka rabu da shi, daga nan bai sake aure
ba sai wata É—aya da ya wuce inda Na'ibin Sarki ya bashi sadakar d'iyarshi mai wadataccen
ilimin addini sai dai yana jin labarin ya hankalinsa ya tashi inda Mami Fulani ta rufe shi da faÉ—a
tare da gargadi akan kada ta sami labarin ya saki yarinyar inko ya kuskura ya aikata mai rabata
da shi sai Allah wannan kalma ya hura wutar jin rabuwa da Sakina wacce a ranar da aka kawo
mashi ita ya bata saki wanda faruwar haka ya saka Masarauta shirya taron zama na
musamman akanshi a karan farko tun soma wasa da auren da keyi gami da son zubar da
Martaban Masarautar su domin lamarin na taɓa ran manyan masarautar musanman Baba
Chiroma da yafi kowa zafi haka ansha mamaki da har zuwa lokacin bai nemi ganawa da
Sadauki ba shi yasa yanajin sakon kiran da yafito daga bakin sa sai ya gudu mab'oyarshi tare
da gargadin Imam akan kada ya sake ya tona inda ya ke. Sai da ya sami wata É—aya da kwana
biyar wato sati biyar kenan sannan ya dawo inda ya ke kan fuskantar fushi daga mahaifanshi ya
yin da dan uwanshi Sardauna ke yi masa shagub'e na kiranshi da kalman mai auri saki mara
godiyar Allah, duk da kalaman nayi masa ciwo amma ko kallo bai isheshi ba balle ya tsaya
bashi amsa wanda ke kallo a matsayin bata lokaci sannan duk da hakan kauanrshi ga Jama'ar
gari bai rage komi ba wannan lamari ya rage masa damuwar da ke ciki na fushi da mahaifanka
keyi da shi. Duk da b'oye halin da ke ciki da ya keyi amma kallo É—aya zakayi masa ka gano
yana cikin matsanancin damuwa wanda Amininsa Imam ke aikin bashi baki.
***
Aliyu Sadauki.
Tsaye ya ke a bakin window dake bedroom dinsa inda ke kallon kai da kawon hadimai bisa
alamu manyan baƙi ne zasu halarci Masarautan. Bushe-bushen da aka soma ne ya sashi barin
wurin ya koma saman sofa ya kwanta idanunsa na kallon sama zuwa can ya tashi zaune ya
furzar da iska mai huci tare da kaiwa k'irjinsa duka ya rintse ido da hanzari jin yarda zafi ya
ziyarci wurin da ya duka. Ya juya kai cikin furta "Why ta zamemin masifa a rayuwa? Shin aina
zan sake ganta? Shin ita din mutum ce ko aljana? Me yasa na aikata mata haka? Shin har sai
yaushe zan fita daga wannan rayuwar na fitinuwa da son kasancewa mace amma ko ta zo
gareni sai naji banda mak'iya irinta?"
Kwalla ne ya taru a kwarmin idanunsa ya kai hannu ya goge tare da tsirawa ruwan hawayen ido
da ya shafo.
"Narantse duk ranar da na sake ganinta sai na wulak'antata fiye da yarda take kan wulak'antani
yarda zatayi jinya tare da shiga damuwa sama da wanda ta jefani ciki."
"Wacece ita Aliyu?"
Kallon Imam ya yi wanda bisa alamu ya jima tsaye bai sani ba.
Ganin da Imam ya yi ba zai sami amsar tambaya ba sai ya tako ya zauna gefenshi ya kamo
hannunsa cikin sanyin murya ya soma magana "Please Sarkin gobe ka daure kayimin bayani
yarda zan fahimta wanda zai fitar da su Mamie Fulani daga zargin sihiri akayi maka wanda ba
dare ba rana suke mik'a kukansu ga mai warware k'ulli batare da gajiyawa ba akan abinda ke
jikinta ya fita ka yi aure ko saga jininka kafin su koma ga mahalicci su."
Shiru bai tanka ba saima kwanciya da ya yi yana jin mararsa na kartawa tamkar yarda ya saba
ji duk in ya shiga tunanin sanin wacce ke alak'anta silar rashin zamanshi da matarsa na aure.
"Yar gidan waye? Me ta ke tak'ama da shi? Shin zan iya samun wadannan tambayoyin daga
bakin Aliyu Abdul Hakam?"
"No."
"Why?"
"Imam ban santa ba haka ban san me zance maka akanta ba."
"Ikon Allah, wato ta tabbata Aljana dai kenan?"
"Ina tunanin hakan."
"To aina ka gamu da ita?"
"A Barci."
Ya samu kanshi da ambatar hakan alhalin ya san ba hakan ba ne.
Shiru Imam ya yi na kallonshi ya yin da shi kuma ya kauda kai gefe,murmushi ce ta kufcewa
Imam har da zarcewa da guntun dariya lamarin da ya fusata Sadauki ya mik'e ya nuna masa
kofar fita sai kawai ya kulle bakinsa da tafin hannunshi ya cigaba da dariya har da fitar kwalla.
"Na haukace ko Imam?"
"No Brother kawai dariya k'aryar da ka yanko ne ya bani domin k'arara ka tona kanka ba
gaskiya ka ambatamin ba."
"Me kake nufi da kalamanka?"
"Nothing, but sit and tell me the truth, dan wallahi ba zanyi kaffara ba, ba gaskiyan kenan ba."
"Nagode da maidani mak'aryaci da kayi kuma ka fice alamarina, bana son sake ganinka kusa
da ni, yes na amince na rayu cikin kaÉ—aici kamar yarda Mamie ta furtamin, Abba ya bawa sokon
danshi mulkin Mungaye, Umma ta cigaba da kirana mara amfani."
"Innalillahi! Sadauki yaushe Umma ta ambata maka wannan mugun kalman?"
"I said get out! Malam."
Ya ambata tare da jan hannun Imam ya mik'ar ya soma ja har zuwa bakin falonshi sannan ya
sakeshi ya koma saman Cushing ya zauna ya rik'e kanshi gam wanda ke jin tamkar zai fice
daga muhallinsu.
"Affuwan A...
Hannun da ya daga masa yasa Imam gintse ban hak'urin da ke nufin bashi.
Tsawon mintoci uku ba wanda ya yi magana sannan Sadauki ya mik'e ya doshi hanyar bedroom
saida ya tura kofar sannan ya yi magana cike da izza ya ce "Ka shirya idan anyi sallah zaka
rakani sake bawa su Abba hak'uri a turakarshi dan yau Mamie ke da girki kamar yarda Lailah ta
sanarmin."
"Ok Allah ya kaimu."
"Amin."
Ya amsa can ƙasar mak'oshi wanda ko Imam bai jiyoshi ba.
***
Durk'ushe suke gaban Mai Martaba Abdul Hakam da Mamie Fulani. Imam ne ke ta ban hak'uri
ya yin da Sadauki yake ciccira hawaye nayi masa zarya na bak'in cikin jin kalaman da Mamie
Fulani ta ambata sadda ta ganshi gabanta.
'Ban son sake ganin fuskanka Babana domin k'unci nake shiga a duk sadda ka ziyarceni dan
haka kada ka sake zuwa inda nake na rok'eka.'
Toshe kunnuwansa ya yi tuno kalaman, ya d'ago kanshi hawaye wani na bin wani duk da
zamowarshi mara saurin kuka amma kalaman Mami ya sakashi kasa jurewa. Ya sarrafa cikin
sarsarfa ya isa bagan Mamie Fulani ya sauke kanshi a saman k'afafunta yana furta "Ki yafemin
Mamiena wallahi ina cikin iftila'in rayuwa ne domin fushinki guba ne gareni dan ba zan tab'a
sake yin tasiri ba har abada."
Sai ya fashe da kuka mai sauti wanda rabon da ya yi irinsa ba zai tuna ba. Ganin haka sai
Imam ya tashi ya fice da sauri yana goge hawayen tausayin Amininsa.
Momyn Haske ceí ¾íµ°
[1/13, 12:05 AM] Mrsjmoon: Hatsabibin Tsiri
By Mrsjmoon.
ADABI WRITER'S ASSOCIATION (AWA)
https://arewabooks.com/book?id=63a2e3d8821822a8402d8eb1 Follow me on Arewabooks.í ½í¶•
Page 5.
Kuka Tsidau ya fashe da shi abin da ya sanya Lina dakatawa daga rikiÉ—an da ta so yi zuwa
tsun-tsuwa domin komawa inda ta fito, ta zuba masa idanu shi kuma bai saurara da kukan ba
lamarin da ya karya mata zuciya taji kwalla ma ciko mata ido sai ta lumshe idanu gami da ware
hannayenta zuwa can ta nuna Tsidau haske ya sauka saman kansa tamkar walkiya sai gasu a
wani fada mai cike da shimbud'u na alfarma ta dubi Tsidau da ya É—auke kukan ta ce "Samo
mana abinci mai rai da lafiya kana na saurari matsalarka da ya sanyaka kuka daga jin ka kusa
samun 'yanci zuwa ga iyalenka."
Motsa kai yayi ta murmusa cike da Izza tana mai fesar da iska daga bakinta, kafin kiftawar ido
Tsidau ya bacewa ganinta, gyara zama ta yi a saman kilisan ta ɗauki kwalban turare ta ɓalle
murfunsa ta kafa a bakinta, tas ta shanye tamkar ta sami ruwan roba, ta cillar da kwalban tare
da tsirawa gefen hagunta ido zuwa can ta mik'e da sauri ta kaiwa iska cafka saiga wata
budurwa riƙe ba hannunta, suka zubawa juna ido kafin Lina ta furta kalma budurwan ta zama
ƙatuwar Kura ta ja baya tana sakin haniniya, ita kam ko motsi ba tayi ba illa zubawa Kuran ido
da tayi tana mai nazarin abinda take nema a gareta da take bibiyan duk takun sawayenta
tsawon lokaci. Tsidau ne ya bayya dauke da abinci mai rai da lafiya kafin kwabo Kuran ta ɓace.
'A sannu zan gano abinda kike nema a gareni.'
Ta ambata cikin ranta tana mai wadata fuskanta da murmushi.
***
Abun da Lima.
Sunyi tafiya mai tsayi sannan Abun ya kalleta yaga hankalinta baya kanshi sai ya daga
dafadarta ta saki ajiyar zuciya gami da kafeshi da ido.
"Ya ke 'yata mafi soyuwar gareni, hak'ik'a ina sonki so matsananci shi yasa na ke son
taimakonki domin kina fita na shiga taskan bincikena aikam na ci karo da isowar yar uwanki
Lina tare da binciko manufar zuwar Tsidau shi ne na taho a hanzarce na tasheki domin inda ban
iso ba a haka zaki wanzu cikin barci tsawon lokaci ko sadda zaki farka Lina ta gama mallake
gadonki domin a yanzu shi ne babban burinta."
"Abun zan kashe Lina!."
Ta mabata bakinta na fesar da hayak'i saboda ɓacin rai.
"Kul! Na sake jin wannan kalami mai cike da abin kunya na fita a bakinki."
"To ka dakatar da ita daga shigamin gona."
"Zanyi wannan domin idan mukayi sake ta mallaki Tulun ruwan albarkan to ba ke ba har ni zan
fuskanci matsala ta hanyar mallake min Tsibiri duk da ina hango wani babban kalubale da zata
fuskanta bayan ta samu cikan burinta lamarin da nake jin ban son ya afku gareta."
"Me ye shi Abun?"
"Binciken da zan shiga kenan na tsawon kwanaki uku dan haka ina baki umurni da kada ki sake
komawa Bukkan Kaka Gunu har sai na fito."
"To Abun amma ina son ka bani dama na tafi Tekun Kabobo na dakaceta zuwa sadda zaka fito."
"Na yarje miki wannan ya ke yata mafi soyuwa gareni."
"Godiya nake Abun."
"Kafin ki tafi ki shiga wurin Mah domin tana bukatar sanyaki a ido."
"To."
Ta amsa da sauri. Kanta ya shafa tare da shigewa turakanshi tana ganin shigewarshi ta rikida
zuwa bak'ar tsun-tsuwa ta tashi sama da gudu ta nufi inda Abun ya ce kada ta koma sai ya fito
daga bincikesa.
Lima na isa bakin Bukkan Kaka Gunu ta samu yana ta cike hanyar shiga ta ja da baya cike da
fushi ta watso wuta sai dai yana sauka ruwa ya taho da mugun gudu ya kasheshi, iska mai ƙarfi
ta turo daga bakinta shima yana isa guguwa ya maida iskan baya ya tafi da ita gefe ta zube
ƙasa, numfashi ta sauke da karfi ta mike ta tunkari bukkan da dukkan ƙarfin sihirinta sai dai bisa
mamakinta sai ta ga Lina Zauna a saman kujera bata sama bata ƙasa ta kare hanyar shiga
Bukkan, kallon kallo suka yiwa juna na sokonni sannan Lina ta sakar mata murmushi tare da
mik'a hannu container ya bayyana cike da farfesun kayan ciki sai fitar da turiri keyi, ta kalli Lima
cikin izza tare da sake sauke mata murmushi tamkar zata furta kalma sai kuma ta gintse ta
maida hankali wurin cin farfesun hankali kwance.
Iya fusata Lima ta yi sai kawai ta ja baya ta dunk'ule ta zama k'aton dutse mai fitar da hayaki ta
nufo Lina gadan gadan saidai kafin ta isa Jarumi Buda ya bayya cikin gaggawa ya ture dutsen
tare da kai masa naushi a take Lima dawo sufarta ta tashi tsaye tana murmula goshinta da ya
kumbura sakamakon naushin da ta sha, kalonsa ta yi cikin mugun fushi kafin ta furta kalla ya
iso gabanta shima a fusace ya kwasheta da mari yana mai cewa "Me yasa baki san ciwon kanki
ba ne? Shin idan kika shiga Bukkan a wannan yanayin kin san kalan barnan da zakiyi? Ko ance
miki fadar kaka Gunu wurin wargi ne? To maza ki bar wurin nan har sai Abun ya fito daga
bincikensa kamar yarda ya bani umurnin zuwa dakatar da ke daga aikata barna wanda zai iya
zanyowa Tsibiri nak'asu."
"Ka bani hanya Buda na illata Lina domin gata nan tanayimin dariya dan ita nake son kaudawa
a doron ƙasa dan ta gane bakin rijiya ba wurin wasan yaro ba ne haka faɗa da Giwa bana 'yan
kuikuyo ba ne, burina ta gane ni babban goro ne mai taɓani ya kwana lafiya sai wanda ke
neman turb'aya ta kulle maganenshi na har abada."
"Karya kike Lina bata zo nan ba sai dai in gizo idanunki keyi miki dan haka ki ɓacemin da gani
tun ban aikata miki mugun aiki ba."
"Buda na rantse da kabarin Kaka Gunu Lina na tare da mu dan haka ka kaucemin a gaba ko in
sauke fushin a kanka wanda ya wuce naka fushin da kake karad'in cika baki a kai."
"To nunamin ita domin na hukuntata akan wani rainin hankali da ta yimin wanda ya janyomin
rasa sihirtaccen Dokina Mardu."
Da hanzari ta tureshi daga bakin Bukkan sai dai abin mamaki ta nemi Lina ƙasa ko sama ta
rasa alhalin ko sadda take maganar ta ganta zaune bayan Buda.
"Tabbas Lina ta koma Aljana."
Ta ambata da fushi hucin hayaki na fita daga bakinta saboda tsabar masifa.
"Tare kuka zama ai."
"Buda!."
Ta kira sunarshi da ƙaraji.
"Lima!."
Shima ya maida mata martani.
Sunkuyar da kai ta yi tana hasko wani lamari da ke yi mata wasi-wasi akan sabon halayyar
Buda wanda sam a da bai daga mata murya hasalima miskili ne mai takama da Izza a kan Lina
kawai ke zamowa soko saboda kaunar da keyi mata.
"Maza wuce muje ki huta, tunaninta da kikeyi ne ya ke son maida ki sokuwa har ta soma yi miki
gizo."
"Kaine Babban soko amma bani Gimbiya Lima ba."
'Lallab'ata ta wuce tun kafin ta hargo jirgin.'
Murmushi ya sakar mata jiyo abinda Lina ta ambata masa a kunni. Ya gyara tsayuwa cikin tsare
gira ya ce "Biyoni kawai ta salama Basarakiyar gobe."
Bata musaba ta rufa masa baya cike da sake nazartan halayyar da ya aro da rana tsaka
sannan a gefe kuma ta ci alwashin hukunta shi haka komin rintsi da sa idonshi kafin mahaifinta
ya fito daga dakin bincike sai ta mallaki Tulun gadonta domin batajin zata raba gadon da kowa
hatta kuwa da shi Abun.
***
Suna barin wurin Lina ta bayyana gaban Bukkan ita da Hadimi Tsidau inda keyi mata fifita da
fatar kunnin Giwa fuskansu dauke da murmushi.
"Uwargijiyata kina da kaifin basira duba yarda na koma Jarimi Buda na tasa miki keyarta cikin
lumana sai dai marin da naushin danayi mata zai bar baya da k'ura domin ta rikeshi hanyar
fansa akan Jarumi Buda kuma kinsan shi É—in ba kyalle ba ne barinma da yanzu ke cike da
haushin ajalin dokinsa da kikayi sanadi."
"Bar soko ai da gangar nayiwa dokin illa saboda na gano shi ke hasko masa lamuran dana
boye."
Shugabana kina ƙara kutsa kanki cikin ayyuka masu hatsari domin kin haɗa Lima faɗa da Buda
lamarin da zai iya haifar da É—a mara ido a Tsibiri bayan burinki zaman lafiya ya wataci yankin
naku."
"Bana dana sanin komi akan hakan dan kome zatayi matsalarta ce haka zalika Buda ya wuce
da saninta hasalima baida lokacinta na tabbata kome zatayi mashi ba zai daga kai ya kalleta ba
ko ni da nayi masa babban laifi ba zai kulani ba dan na tabbata ita ba za tayi masa mai munin
wanda na aikata mashi ba."
"Haka ne Shugabana, kin gini hango gaskiya."
"Mu bar zancen haka Tsidau, yanzu zan tafi domin dauko Zobe na."
"Uwar gijiyata mu bar yankin nan na baki shawara mai b'ullewa domin na jiyo kamshin tahowar
dan leken ashirin tsibirin na tinkaro inda muke cikin alk'aluman sihiri bisa umurnin Lima domin ta
gano makircinmu."
Yana rufe baki suka b'ace b'at inda suka sauka a saman Dutsen dake tsakiyar Tekun Kabobo
suka shige wani rami inda cikinsa ruwa ne ke kwaranya fari k'al, duwatsune masu suffar kujeru
sun zagaye ruwan akan É—aya daga cikinsu Tsidau ya zauna ita kuwa Lina kujerarta ya bayyana
na zauna cikin mulki ta kalli Tsidau ya sunkuyar da kai tare da soma magana "Shugabata bana
son ki d'auko ajalinki da hannunki domin ina jiyo amon sautin fitar ruhinki daga muhallisa shi ne
d'azun ya sakani zub da jirwaye(hawaye), wannan hatsarin ya sanya Shugaba GauÉ—u ya birne
shi a ƙasan Teku dan haka kema ki barshi a inda yake inma da hali ki fita sabgarshi har abada
dan bala'in da ke cikinsa yafi nasarar da kike hange."
Shiru ya ratsa wurin na tsawon mintoci goma sannan Lina ta sauko saman dutsen kujerar da
take zaune ya b'ace ta tsomo kafafunta cikin ruwar dake da mugun sanyi ta lumshe ido kana ta
bud'esu tar akan Tsidau da ya sake sunkuyar da kai ƙasa cike