Showing 9001 words to 12000 words out of 45162 words
Chapter 4 - HATSABIBIN TSIBIRI Littafin Yaki Book Complete .pdf
Unknown
25 Mar 2025
6526
zo ne domin sanin abin da 'yar uwata Lina ke boyemin game da tafiyarta
da duk abin da ya faru gareta tun kafin tafiyar har zuwa yanzu."
"Kwanta ki huta uwar gijiyata kina tashi na yi alkawarin bayyana miki duk abin da ya shige miki
duhu akan Gimbiya Lina."
"Tsidau bana jin barci domin bashi na zo yi ba."
"Dole kiyi shi uwar gijiyana."
"Kada ka kawomin wargi na hukunta ka y kai Tsohon wofi."
"Tuba nake Sarauniyar Gobe, fushinki kukan yaro."
Tana shirin sake magana ya hura mata iskan bakinsa a take ta zame daga kujerar kanta
langabe alamun barci ya É—auke ta, da yatsarshi ya nunata sai gata kwance saman kilisar ta yi
matashin kai da wani filo mai zanen fatar jakin daji.
"Shin ta ina zan soma boye miki sirrin abin da kika zo bincike?"
"Bar wurin don ka gama aikinka kafin ta farka na nade sirrin da aka barmata gado."
Muryan Lina ya ratso.
"Na barki lafiya Gimbiya mai jiran gado."
"Ko da yake kafin nan zauna da ita ya kai amintaccen hadimin Sadauki GauÉ—u bari in koma na
sallami wancan lalataccen kada maikon kogin da ya yi jagorar samar da shi ya halaka shi."
"A dawo lafiya ya ke adalar Sarauniyar Duniya."
Murmushi ta yi tare da b'acewa shi kuma ya gyara zama gaban Lima ya tsirawa hawa da
saukan numfashita ido tamkar mai irgawa. Rugigi ya ji a bayanshi kafin ya tantance dalilin
afkuwan lamarin Bukkan ya ɗauki rawa wani gaton dutse ya d'ago daga ƙasa inda ke zaune ya
nufo inda ya ke yana fesar da koren wuta, tamkar walkiya Tsidau ya b'ace a daidai lokacin Lima
ta farka a firgice sai dutsen ya koma mazauninshi tamkar bashi ba. Abun ne ya shigo a rikice ta
tashi da hanzari ta isa gabanshi ya rik'o hannayenta ya soma magana.
"Ya ke farin cikina wannan binciken yafi karfinki dan haka ki lamuncemin amsar gadonki domin
na samu damar taimakonki."
"Abun zan iya, kabarni da kayana."
"Bazaki iya ba tunda ga shinan an sakaki barci bisa hila wanda saninki da ilimin tsafi bai amfana
miki komi ba a wannan gab'an."
"Abun waye Tsidau?"
"Hadimin ne ga 'yar uwanki Lina."
Ware ido ta yi cikin cewa "Lallai Lina ta shiryawa taran aradu."
"Biyoni kawai domin sanin ta inda zaki bullowa lamarin."
Biyo bayanshi ta yi cike da zantukan zuccin wanda ta sanyawa ranta sai ta nemo sanadin
afkuwansu dan hatta Abun ta soma wasi-wasin a kansa.
***
Lina ce tsaye a saman ruwan Tekun Kabobo fuska a haÉ—e ta watsa wani haske da ya fito daga
babban yatsar hannunta na dama,a take maikon da ya b'ata ruwan ya soma tafiya har ya b'ace
amma launinsa na yellow bai sanja ba. Ta sake tsuke fuska tana fitar da huci zuwa can ta yi
gunji ta soma tafiya a saman ruwan a hanzarce har ta isa tsakiyarshi kujerarta ga gold ya
baiyana a saman dutsen da ke tsakiyar Tekun inda wasu halittun ruwan sukayi dandazo domin
gudun hijira daga halaka, ta zauna tare da tsirawa ruwan Tekun ido da ya ke sake komawa
yallow mai duhu, zuwa can dokin Buda ya taso sama ruwa ya yi tartsi tare da fitar haniniyarshi
mai firgitarwa inda halittu suka sake rudewa da neman mafaka sai kuma ya koma ciki tsundum!
Tamkar an janyoshi, kimanin mintoci biya ya sake tasowa sama wannan karan Buda na kwance
saman bayarshi tamkar Gawa, tafiya yasomayi a saman ruwan cikin jan ƙafa saidai kafin ya kai
bakin gab'a wani igiya daga kasan ruwan ya fito kamar walk'iya ya maidashi ciki sai ruwan ya
sake rukid'ewa zuwa bak'in-k'irin tare fitar k'ugi tamkar rugugin hadarin damina.
Lina da ke kallon komi ta mik'e tsaye da sauri tare da kulle ido ta nuna ruwan a ta ke dokin da
Buda suka taso sama ta tura hannunta gaba suka tafi a guje tamkar tsintsaye suka zube a
saman yashi da ke gefen Tekun. Ta sauke numfashi ta re bud'e hannayenta ta nuna ruwan ya
dawo launin shi fari k'al yana murdewa yarda ya keyi a tun farko, ai kafin kwabo Halittun nan
sun soma rige-rigen komawa muhallinsu, ido ta zuba musu tana sakin murmushi ta sunkuya
tamkar zata fad'a cikin ruwan sai kuma ta tashi tsaye tana mai shafan gefen fuskanta cikin cewa
"Na sami cikar burina na taimakon dabbobin ruwa tare da sokon can Buda, mulkin Adalci ya
soma sauka daga hannuna, godiya gareka Sadauki Gaud'u da kayimin komi na ganin na
mallaki ilimin tsafin da ya zarce na ko wani matsafi dake nahiyar nan harma da waje ta, hak'ik'a
zanyi aiki da Adalci tamkar yarda hakan shi ne cikar burinsa, ganinan tafe zuwa mik'o gaisuwa
ga ruhinka abar girmamawata, tabbas idan na zama Sarauniyar Tsibiri kogon da kabarinka ya
ke nan ne wurin bautarmu."
Tana kulle baki ta rikid'a zuwa k'aramar tsuntsuwa mai shegen gudu ta lula sararin samaniya ta
ɓace tamkar kibiya sai dai tana sauka a cikin kogon dutsen da kabarin Sadauki Gauɗu yake
idonta ya sauka kan Hadimi Tsidau kansa sunkuye cikin tsantsar ladabi ya soma magana.
"Uwar gijiyana ayimin gafara lamarin ne ya sha gabana domin na kusa halaka kuma a faruwa
hakan na gano ma'adanar tulun sirrin da kike burin mallaka sai dai zamowa mallakinki da kamar
wuya saboda manyan iffiritai ne ke gadinsa kuma mahaifinku shima na burin mallakan tulun ya
tura 'yar uwanki ne domin ta binciko Tulun sai ya tabbatar ta nemo sai ya taho ya amshe cikin
hikima saboda ya san iffiritan da ke gadin Tulun ruwan albarkan baza su yi mata komi ba
sabanin da in shi ne zai iya rasa ranshi dan ya taɓa jaraba mallakansa ya sha da k'yar."
Numfashi Lina ta sauke tare da buÉ—e idanunta da suke kulle tun soma maganar Hadimi Tsidau
ta kalleshi na sakonni ta jinjina kai batare da ta furta kalmar ba ta matsa gaban Kabarin Sadauki
Gauɗu ta russuna gabansa ta miƙa hannunnta na dama ta ɗora saman Kabarin kanta sunkuye,
ganin haka sai shima Hadimi Tsidau ya taho da sarsarfa ya russuna a bayan Lina tare da sauke
kansa ƙasa, ta sami mintoci goma sha biyar a haka sannan ta mike tsaye shi kuma Hadimi
Tsidau na nan sunkuye cikin girmamawa. Murmushi ta yi kana ta soma magana cikin tsantsar
isa da mulki inda kallaman ke fita É—aya bayan É—aya.
"Tsidau zanyi aikin da kaina domin ina tare da Zobben sihiri na Sadauki GauÉ—u duk da saka
Zoben tamkar na yafa mayafin mutuwana ce ga rayuwata amma akan cikan burina zanyi
wannan kasadan saboda da in mutu a hannun Lima gara na ƙare rayuwa a matsayin baiwa a
masarautar Sarki Gamji ko ba komi shi É—in mahaifi ne ga shugabana Sadauki Gaud'u."
"A'a Uwar gajiyana banayi miki fatar shiga hannun azzalimin Sarkin nan wanda har 'Æ´a'Æ´an
cikinsa bai bari ba saidai kafin ina baki labarin hatsarinsa zanso sanin sirrin da Zoben ke tare da
shi da na kasa ganowa tun sadda mai gidana Gaud'u ke sanye da shi."
"Tsidau bana buƙatar jin komi daga masarautar Sarki Gamji domin Sadauki ya sanarmin da
komai sannan Zoben da zan fito da shi yana ƙasan Tekun Kabobo sirrinshi mai faɗi ne domin
duk wanda ke tare da shi a cikin yatsarshi yafi ƙarfin duk wani matsafi haka duk abin da ya
tunk'ara sai ya samu nasara komin wuyar lamarin, in barka haka."
"Tafdijan amma Shugabana yana da wannan Zoben ya yi sake mugun nufin mahaifinsa ya yi
nasara akanshi?"
"Ya sanarmin ya wuce shekaru bakwai da cire ainihin Zoben a yatsarshi jabun ke sanye da shi
tare da boyewa mahara Zoben gano jabun ne ke yatsarsni cikinsu har da mahaifinsa domin
burinsa ya mallakamin."
"Shugaba ya sanki da jimawa kenan?"
Jim ta yi domin bata son ambatar ƙaddarar da ya taɓa afka mata wanda ya kasa b'acewa a
ranta haka ta kasa maida hankali akan gano dalilin faruwar lamarin kamar yarda tak'i amincewa
ruhinta a hukunta mai laifin duk da tarin damar da take da shi na aikata masa komeye da ta so
amma ganin Tsidau na dakon amsarta sai ta amsa a takaictda " Eh."
"Affuwan Uwar gijiyana, ban gamsu da amsar nan ba a matsayinsa na sirrintaccen Hadiminki
bai kamata ki riƙa bani bayani a dunkele ba dukda ina aljani zan iya gano kome kika boye saidai
alkawari nayiwa Shugabana cewa bazan taɓa binciko sirrinki ba kamar yarda ban taɓa gigin
binciko nashi ba bisa alkawarin da na daukan masa wanda wannan lamarin yasa aka kawo
masa hari batare da na nasan meke faruwa ba dan haka a yau ina neman alfarman ki amince
alkawarin da na ɗaukawa Shugabana ya zamo tarihi inda zan riƙa sanin abin da zai sameki na
kangin rayuwa kafin ya iso na tareshi na maidawa wanda yayo aiken."
"Godiya nake ya kai Tsidau amma ban amince ka zamo cikin marasa cika alkawari ba, ina son
ka yarda komi nawa kada ka binciko sai wanda na baka dama, ka dauwamma a aikinka na É—an
aike tare da rakiya zuwa inda nake da muradin tafiya da kai."
"Angama ya ke Uwar gijiyana, Gimbiyan gobe bisa amincin mahaliccin tsuntsaye da tsirrai."
"Tsidau ina yawan jin kalaman nan a bakin Sadauki GauÉ—u sannan duk in ya furta na kanji kaina
ya yi girma basirana ya toshe inda nake hango kaina cikin wani duhu tare da haske daga nesa
can, shin me hakan ke nufi?
"Uwar gijiyata rayuwar Shugaba na tarin ababen al'ajabi domin duk nacina akan ya bayyamin
sirrin da ke cikin kalaman nan ya k'i dan haka ban san komi akai ba domin harshesa nake
kwaikwayo har na ambata miki hakan sai dai ina ta tabbacin wani abin bautane mai girma da
ƙarfin mulkin da ya doke wanda su Sarki Gamji ke bautamawa."
"Zanzo sanin shi ko da kuwa hakan zai iya zamowa ajalina ne."
"Uwar Gijiyata kidaina ambatar mutuwa baki zamo Shugaban Tsibiri ba wacce adalcinta zai
kewaye Duniya."
Murmushi ya kubce mata sannan ta fuskanci Tsidau tana mai cewa "Ya kai amintaccen
Hadimina hakika mun kusa rabuwa domin da zarar na sanya Zoben, zan bacewa ganinka na
har abada kai kuma zaka tsinci kanka cikin jinsinka cike da yanci daga nan kazamo yantacce
daga bawa ni kuma zan mallaki Tulun ruwan albarka saidai ba zan jima ba akan karagar mulki
Tsibiri Sarki Gamji sai aikomin da sako walau irin wanda ya aikowa Sadauki GauÉ—u ya halaka
ko ya ɗaukeni daga yankin zuwa kurkukunsa na karkashun ƙasa na tabbata a can har zuwa
sadda mutuwa zai riskeni dan haka yanzu zan koma Tekun Kabobo in d'auko Zoben, ina
godiya da taimakon da ka riƙa bani na duk abin da nake son ci da sha tare da sutura, gaisuwata
mai yawa zuwa ga iyalenka, sai wata rana."
Momyn Haske ce í ¾íµ°
[1/13, 12:05 AM] Mrsjmoon: Hatsabiban Tsibiri
By mrsjmoon
ADABI WRITER'S ASSOCIATION.
https://arewabooks.com/book?id=63a2e3d8821822a8402d8eb1 follow me on Arewabooks.í ½í¶•
06
Tafiya na ƙara nisa inda zuwa lokacin Aliyu Malle ya tara iyali mai yawa dan ya auri bafullatanan
da ta yi makuwa mai suna Mero haka ya nemi aure a wurin wani Buzu shima da ya fito ci rani
yaga dajin Mungaye ya zama maraya sai ya zauna da iyalinsa, sannan ya koma Asalinsa ya
auro 'yar uwarshi Kanuri inda ya auro har guda biyu, a lokacin danginsa suka soma nuna masa
ƙauna tunda suka gansa cikin rufin asiri musamman sarautan da yake da shi yanzu na matsayin
Sarkin Birnin Mungaye. A wannan komawa danginsa da yayi wasu daga ciki suka biyoshi tare
da iyalansu sai Masarautan Mungaye ya sake cika da al'umma. Daga nan auratayya ya cigaba
da kulluwa tatsakanin kabilun uku wato Barebari, Fulani da Buzaye.
Wannan auratayya da ya kullu tsakaninsu sai ya tsakud'a ya fitar da wata kalan al'umma masu
kyawun sifa gami da kyawun launin fata, fuska dana sura. Kowa ka gani a cikin birnin Mungaye
mai kyawu ne musanman 'ya'yan gidan sarauta domin Sarki da matarsa masu tsan-tsar kyau
ne, wasu masu hasken, wasu mai sirki da ja da kuma masu haÉ—i da duhu kaÉ—an amma duk
wanda ka kalla mai kyau ne a Masarautan dan har akanyi masu kirari da Birnin Mungaye mai
kyawawan Mata.
Birnin ta sami wayewa bisa ziyartan turawa inda suka gina makarantun Boko tare da kawo
malamai suka riƙa koyar da su ilimin zamani duk dama can akwai masu Ilimin daidai misali
musanman Sarki Aliyu Malle tare da danginsa, sai dai hak'ar Turawa bai cimma ruwa ba na
samun nasarar rabasu da addinin da suka samesu akai wato Musulunci wanda burin sanja
masu tunani ne su koma bin addininsu ya sanya suka shigo birnin sai suka samu Sarki Aliyu
Mallae ya yi namijin kokari akan al'umman shi na ganin sun ginu akan turban gaskiya na kaÉ—aita
Allah Subbahanatu Wa Ta'alah gami da riƙo ga sunnar Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam, shi yasa har izuwa yanzu Birnin Mungaye cike ya ke da musulmai, malamai gami da
tsirarun mabiya addinin Yahudu da Nasara wanda suke zaman lafiya da juna domin tun tarihin
kafuwar Birnin babu abin tashin hankali da ya taɓa kawo matshi ziyara ko riciki a bisa
bambancin Addini ko wani tarzoma na daban sai dai su jiyoshi a makwaftansu saboda sunyi
imani da Allah É—aya ne kuma suna masu jajircewa wurin zaman addu'o'in samun kariya ga
Birnin tare da zaman lafiya tsakaninsu suma sauran k'abilun nayin irin tasu addu'ar awurin
bautarsu. Wannan tsarin ginin tubalin zaman lafiyar duk ya samune bisa jajircewar mai
Mungaye wato Malami, Sarki kuma Limamin Birnin Aliyu Malle wanda ya rasu shekaru masu
yawa sai tsa-tsonshi sukayi ta gadan Sarautar har zuwa kan sarki na yanzu Sarki Abdul Hakam.
A dalin jagora tamkar 'yan uwanshi da suka gabata sai dai shi ne Sarki mafi wayewa domin dan
Boko ne na gaske wanda ya taka har zuwa matakin Professor, shi yasa hawa karagar mulkinsa
ya zo da sauyi wurin shigo da abubuwan Zamani fiye da sarakunar da suka gabace shi.
Abin burgewa ga wannan ƙasaitacciyar masarauta shi ne riƙon Addininsu domin har zuwa
yanzu sarakunarsu sune Limamai kuma masu gabatar da tafsirai a lokacin Azumin Ramadan
dan haka babban masallacin Juma'a na garin a kofar Fada take kamar yarda mafi yawan
masarauta aka sani da gina Masallatai da ake sallar Juma'a a Fadar su, saidai wannan a cikinta
ake sallar Idi dan takasance mai girma tamkar wata Masarautan kaso sake ginawa haka a
gefen Masallacin wani daji ne da aka killace shi aka cika shi da shuke-shuken kayan marmari
wanda ina mutum ya shiga zai dauka a wani yanki na daban ya ke saboda yalwar bishiyoyi tare
nisan tafiya kafin a isa k'arshenta, aka ba wurin suna da Mungaye Garden.
Wannan ak'idar da Masarautar ta ginu da shi na son Musulunci da Musulmi shi yasa jama'anta
suka kasance masu karamci ga bak'i masu zuwa fatauci da zama na mundun rai. Dan ƙasar
Mungaye Allah ya hore mata kyawun fitar tsirrai (Amfanin gona) shi yasa Manoma suka cika
garin ta ko wani sassa da ke makwaftaka da ita, lamarin da ya kara daga darajar Birnin ta zamo
abar yabo ta ko ina haka duk inda É—an Masarautar ya shiga yana da alfarma.
Mai martaba Abdul Hakam na da Matan Aure biyu. Uwar gida Hajiya Hafsatu (Umma Babba) da
Amarya Hajiya Murjanatu (Mami Fulani) da yara maza da mata sai dai 'ya'ya matan ne manya
domin wasu sunyi aure tare da albarka zuri'a. A yanzu Mai martaba girma ya soma kamashi,
babban burinshi ya yi murabus ya dank'a mulkin hannun É—aya daga cikin zaratan matasan
'ya'yanshi wato Ahmad (Sardauna) da Aliyu (Saudauki) Sai dai ƙurar da ke hangowa ya sa ya
tsuke bakinsa akan ayyana wanda zai zamo magajinsa cikinsu, ya zuba masu ido yana sake
lak'antar halayyan kowa tare da wanda Jama'a sukafi nuna k'aunarsu da ya zamo jagoransu
makar yarda mahaifinsa ya yi sadda aka bashi mulkin duk da baida ra'ayi amma jama'ar gari
suka nuna shi ne zaɓinsu kuma ba jayayya 'yan uwansa sukayi masa mubaya'a sai dai a
wannan lokacin baijin shi zai sami sauk'in dank'a mulki da É—aya daga cikin 'ya'yan nasa ba
saboda kowa yana nuna mulkin ya ke so bakin rai bakin fama.
A fannin Yarimomin Mungaye kuwa duk sun can-canci hawa karagar mulkin sai dai jama'ar gari
sunfi nuna ra'ayinsu akan Sadauki sama da Sardauna duk kuwa da matsalar da ke ga Sadaukin
na auri saki domin a shekaran da ya gabata sukayi auren fari amma zuwa yanzu ya mata huÉ—u
ya aura ya saki batare da sanin laifin da suke aikata masa ba domin ya k'i yin bayanin da yasa
ke aikata sakin haka suma matayen idan an tambayesu amsar É—aya ce suke bayarwa ita ce
basuyi masa laifin komi ba ya sallamesu ba tare da ya haÉ—a shimfida da su ba.
Cikin matar na ya saka akwai ta farko 'yar kanwar Sarki mai suna Mubina wacce aka aura masa
tana da k'arancin shekaru domin kammala secondary dinta kenan a ka yi mata aure cikin
rashin son ranta inda shi kuma Sardauna aka aura masa 'yar Waziri wanda shima ya ke kani ga
sarki kuma har wayau k'anwa ce ga aminin Sadauki wato Abubakar ana yi masa alkunya da
Imam, wacce ta kasance babba mai yalwar komi na cikar halittar mace sama da Mubina,
wannan bambancin da ke tsakanin matan nasu yasa sadda Sadauki ya saki Mubina a
washegarin kaita gidanshi yasa hankali bai wani tashi ba musamman da ita Mubinar ta yi ta
murna har aka É—ora laifin akanta ganin yarda ta yi ta boren bata son auren sai ake zargin ita ce
ta nemi sakin da kanta.
Matarsa ta biyu 'yar Aminin Sarki ne wacce ta zamo mai wayewa domin ita tana da degree har
biyu amma kwanarta uku a gidanshi ya saketa hankali ya tashi a wannan karon amma Sadauki
ya nuna ko