Showing 1 words to 3000 words out of 44631 words

Chapter 1 - KUNDIN QADDARA BOOK COMPLETE By MJay.pdf

[12/15/2016, 10:48 PM] Mss Mjay: *WRITTEN BY MSS MJAY*
In dedication to *Sembyy luff(TWEA)*


*01*
Sauri sauri gudu gudu take tafiya,tanayi tana waigen bayanta domin ta tabbatar in bai biyo ta
ba,ta riga ta gama tsorata da halin mahaifinta,ace ka haifi mutum amma ka nuna kashi ya fishi
matsayi a wurinka.Wannan dame yayi kama,da ana chanja mahaifi data dade da chanja nata
tunda baya sonsu daga ita har kannenta da mammyn su.Tana cikin tunanin nr harta qaraso
makarantar tasu mai suna COLLEGE OF ARABIC AND ISLAMIC STUDIES, tana zuwa bakin
gate ta hadu da kawarta mai suna hafsah a tsaye tana jiranta.Suka rungume juna cikin farin ciki
tare da karasawa cikin makarantar.
Karfe 3:00 daidai aka tada su,suka jero suna tafiyan su itada hafsah.Da hafsah taga shirun yayi
yawa kuma kaman yau ran qawar tata a bace yake.
A hankali tace"taybah lfya kike kuwa yau,you seem lost in thought,ko abbu ne kuma?"
Taybah ta juyo a hankali ya kalli kawar tata tare da qoqarin goge kwallan daya taru a idonta
tace"ki bari kawai hafsah,abbu nada matsala ni banma san ya zanje in samu su mammy ba
yau"ta fada cikin kasallaliyar murya".
"Kiyi hakuri taybah,Allah yana tare daku,ungo wannan inkin koma gida ko gari ki siya muku
kusha" ta fadi haka tare da miqa mata 100.
Taybah tayi dariyan farin ciki tare da runguma kawar tata cikin farin ciki"i love you bestiee
na,nagode sosai".Daidai nan suka qaraso kofan gidansu hafsah ta shiga ciki tare da ma qawar
tata sallama.
Taybah taci gaba da tafiya cikin sauri ta qarasa shagon tanimu ta siyo musu garin 70 sugarn
30 ta qarasa gida cikin farin ciki.
Koda ta shiga ta samu mammy zaune tayi tagumi su kuma su yasmeen na zaune kusa da
ita,daga gani sunci kuka harsun gaji.Suna ganinta suka ruga da gudu suka rungumeta"Oyoyo
addah taybah,kin siyo mana wani abune?"salimah ta fada tana qoqarin karban ledan hannun
yayar tata. Taybah tayi murmushi tare da miqa mata ledar garin ta qarasa wurin mammyn tasu tana gaida
ita.suna cikin gaisawa ne yasmeen ta dawo ta roba ta zubo garin tare da spoons.Suka fara sha
har mammyn tasu amma ita spoon 3 kawai tayi ta bar musu saura.
"Mammy kisha mana"taybah ta fada cikin tausayi."karki damu taybah cikin nawa ne banajin
dadin shi,kusha kawai"ta fada cikin murmushi.
Taybah ma bata sha garin sosai ba ta tashi ta shiga daki.ta tube kayan jikinta tana neman na
sawa idonta yakai kan wata takarda da mammyn tasu taketa boyewa tuntuni.



©Mss Mjay
[12/15/2016, 10:48 PM] Mss Mjay: WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG
WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG
*KUNDIN KADDARA*

WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NGWWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG

Written by
*MSS MJAY❤*

In dedication to
*sembyy luff*


WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG
*02*


Daukan takardan tayi a hankali tare da boyewa a cikin kayan da zata sa.

Ta fito daga dakin ta zauna kusa da mammy sannan tace "mammy inaso inje gidansu hafsah na
manta government note book dina a hannun ta gashi gobe munada test".

"Toh shykenan taybah, karki dade dan Allah dan inaso inje gidan hajiya hussai kozan samu
wanki inyi".
"Karki damu mammy, yanxu zan dawo in shaa Allah".

Tana cikin tafiya kawai saita tuno takardan data tsinta a daki daxu. Tayi sauri ta lalubo cikin
zanen ta tare da fito da takardar. tana budewa taga an rubuta

"Ni usman bada yawuna ba in kika..........."
Tana cikin karantawa ba tare data lura cewa ta karaso bakin titi ba kawai taji mota tayi sama da
ita!.

WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG
8
Matuqin motar ya fito cikin sauri tare da tabata amma ko motsi kadan batayi ba. Yana cikin
dubata ne takardar da take karantawa ta fado daga hanunta.
Ya dauka tare da sawa cikin aljihun shi sannan ya juya a fusace yana kallon dan nashi dake
tsaye kawai yana kallon su.

"Zaka dauke ta ne kasata a motar kosai ranka ya baci".

Cikin hanzari matashin saurayin ya duqa tare sa daukan ta sannan ya nufi motar da sauri. Ba
bata lokaci suka nufi asibiti "JOS UNIVERSITY TEACHING HOSPITAL" (JUTH) dake hanyar
lamingo.

Suna isa aka wuce da ita emergency cikin sauri.

Alhaji usman ya dubi dan nashi cikin bacin rai yace....
"Bansan randa zakayi hankali ba faysal, kana tuqi amma bazaka lura da abunda kakeyi ba?

Faysal ya duqar da kanshi sannan yayi magana a hankali "Kayi hakuri daddy, fadan daka mun
ne duk ya gigita ni wallahi".

Saboda takaici kasa cemai komai dad din nashi yayi.

Sun kusa 40mins a zaune sannan likitan dayake dubata ya fito.
"Are you her father?" Ya furta yayin dayake kallon alhaji usman.

Alhaji usman yayi sauri amsawa "yes i am.....i hope everything is alright doctor".

"Come with me".......likitan ya fada sannan yayi gaba.
Alhaji ya bishi da sauri tare da addu'an Allah yasa komai lafiya.


©Mss Mjay
[12/15/2016, 10:48 PM] Mss Mjay:
WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NGWWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG
*KUNDIN KADDARA*
WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG

Written by
*MSS MJAY❤*

In dedication to
*sembyy luff*

WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG
*03*


Suna shiga office din likita ya dubi alhaji usman tare da cewa."mr?".

"Usman please", ya fada cikin sauri.

"You look tensed mr.usman, don't worry your daughter is perfectly alright" likitan ya fada cikin
murmushi.

Ajiyan xuciya alhaji usman yayi tare da hamdala.
"Can we see her please?".

"Sure you can, we can discharge her as soon as she is awake". Likitan ya fada.
"Thank you doctor". Alhaji usman yayi gaba faysal na binshi a baya Suka shiga dakin da take
ciki. Tana kwance tana bacci cikin nitsuwa ba tare da wata damuwa ba.
Alhaji usman ya dubi faysal tare da fadin
"Zanje gida,ka zauna da ita in an sallameku da wuri ka kaita gida kama iyyayenta bayani".
"Toh shyknn dad".

WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG

*4hrs later*

"Yasmeen, nikam ko zakije gidansu hafsah ki dubu addahn ku, tun dazu ya kamata ace ta dawo
amma har yanxu shiru kakeji". Mammy ta fada cikin bacin rai.
"Kila wani abu ta tsaya yi mammy amma bari inje in gani"

Tana cikin tafiya ta hadu da hafsah a hanya. Da sauri ta qarasa tare da tambayanta addahn ta.
Hafsah ta dubeta cikin mamaki sannan tace
"Dama tace wurina zataje ne?".
"Ea addah hafsah, kuma yanxu kusan 4hrs kenan bata dawo ba shine mammy tace inje in
dubota". Yasmeen ta fada cikin sauri.
" Toh aii yanxu gidan naku zanje in kai mata notebook dinta". Itama hafsah ta fada. "Muje wurin
mammy kawai". Ta sake fada sannan suka juya suka nufi gida.

Hankalin mammy ya tashi sosai jin wannan labari. Har bayan wasu 2hrs ba taybah ba dalilinta
gashi kuma abbansu ya kusa dawowa, hafsah harta gaji da jira ta tafi gida.

Tana cikin tunanin ne tajiyo sallamarshi yana shigowa gidan. Da sauri ta miqe tana jiranshi ya
qaraso.
Ya shigo gidan da ledarshi a hannu. Su yasmeen duk suka gaishe shi. Ko kulasu baiyiba balle
mammy ta take qoqarin karban ledan hannunshi.
Yayi saurin ture hannun nata tare da fara fada "bance ki dinga boye yaranki a daki ba daga na
shigo?kin kama kin haifo yara mata kawai, me zasu mjn inba qarin wahala ba. Ina yar iskar
yarki take, tazo ta dafamun indomien nan ta soyamun kwai ta kayo mun daki ina jira.
"Taybah! Taybah!! Taybah!!!, ya kira a fusace.

"Malam tun dazu ta fita amma har yanxu bata dawoba, dama in jira ka dawo ne ko zaka dubo
mana ita". Mammy ta fada a tsorace.

"Kice kawai kin turata yawon iskanci"
Ya wurgo mata ledan hanunshi tare da fadin
"Gashinan kije ki dafa ki kawo mun, wannan matsalar kuce".
Yayi gaba abunshi ya barsu tsaye suna sharan kwalla.

WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG

*10:00pm*

A hankali ta bude idonta tana tunanin abunda ya faru, da sauri ta miqe tana dube -dube
idanunta ya sauka akan faysal yana gyangyadi.
A hankali ta ce "bawan Allah".
Ya juyo a hankali tare da mata murmushi "kin tashi?"
Ya furta a hankali. "Bari in kira likita ya sallamemu koh".


©Mss Mjay
[12/15/2016, 10:48 PM] Mss Mjay: WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG
*KUDDIN KADDARA*
WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG

Written by
*MSS MJAY❤*

In dedication to
*sembyy luff*

WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG

*04*


Cikin yan mintuna ya daeo tareda wata nurse,ta duddubata sannan ta basu sallama.

Faysal ya matso kusa da ita tareda kallonta,sai yanxu ya kare mata kallo dakyau.

Taybah doguwar yarinya ce,baqa amma irin baqin nan mai sheqi, tanada manyan idanuwa
masu kaman an diga musu zaiba(sexy eyes)with long eyelashes a pointed nose da bakinta dan
qarami(kaman na hafsy�).

Tanada dire sosai ga baqin gashinta dan daidai.

Jin shiru yayi yawa yasa taybah dago idonta domin taga meke faruwa, Dago idon dazatayi ta
sauke su akan kyakyawar fuskar shi mai cike da kamala da haiba.

Dogo ne wankan tarwada. Awwn he's damn handsome (mummy ki rufe baki hakanan plzz).

Kawar da fuskarshi yayi sannan ya qara juyowa ya kalleta yaga she's lost in thought staring at

him. Yana daga cikin abubuwan daya tsana kallo dayawa.

Nan da nan yaji ranshi ya baci har baisan lokacin daya mata magana a fusace ba
"Ki tashi mu tafi kin tsaya kallona, ko yau kika fara ganin kyakyawan saurayi ne?"
Ya fada raising one of his eyebrows and feeling a little bit irritated.

Taybah taji wata kunya ta rufe ta, tayi saurin dauke kanta tareda sa hijabin ta. Tayi tsaye tana
jiran mai zai ce kima.

"Ki wucr mu tafi mana"
Ya fada cikin fada.

Tayi gaba da sauri har tana tuntube ya biyo ta a baya suka qaraso harabar asibitin.

Suna isa gaban motar wayan faysal yayi kara, ya ciro wayan tareda da duba me kiran sai yaga
dad dinshi ne.

"Salamu alaykum dad, yanxu aka sallamemu zan kaita gida ne"

*No son,ku jirani gani nan xuwa nida umman ka, don't go anywhere".
"Lfya dai koh dad?" Faysal ya tambaya adan tsorace.

"Son just wait for us" alhaji usman ya fada tareda katse wayar.

Faysal ya juyo yana kallon taybah, daga gani ta gaji da tsayuwar da take a wurin.

Ya bude mata bayan motar tare da fadin "kizo ki shiga kafin dad ya qaraso" yayi maganar
kaman ana sashi dole.

Taybah ta tako a hankali tana dafe kanta inda ta bugu, jiri takeji kaman ta fadi a wurin.
Ji tayi jirin nata ya qaru saura qadan ta fadi taji taba kirjin mutum.

Dago kan da zatayi ta daurasu akan fuskarsu, kasa motsawa sukayi suka xubama juna ido.

Taybah tayi inhaling turaren da faysal ya fesa soo deeply.

Wannan ai saita suma, irin wannan kamshin haka damn! He's more handsome yanxu.

Shi yayi saurin dauke kanshi tare da taimaka nata ya qarasa da ita cikin motan yana fadin
"Banason ana kallon mun handsome face hake, wannan kallo aii sai kisa kyauna ya qare ya
fada ba tare daya dago kao ya kalleta ba.

Taybah ta kautar da kai cikin jin haushi, sai kace shima ba kallon nata ya tsaya yi ba.

She can't deny the fact that he's handsome, but that doesn't give him the right to be arrogant.

She was deep in her thought har batasan lokacin da alhaji usman ya qaraso ba.

Sai jin muryarshi tayi yana fadin "faysal shiga kaja tana nuna maka hanyar gidan nadu xamu
biku a baya".

Faysal ya dubi dad din nashi yanason yayi tambaya yana tsoron fadan shi.
Sai kawai ya fada motan tare da mata key ya dauki hanya.

Taybah na nuna hanya har suka qaraso anguwan nasu.

Tun daga nesa ta hango abbu yana cin wani abu a takarda.
Ta nuna ma faysal wuri tarw da cemai yayi parking anan kawai.

Kafin ta samu daman fitowa ta hango dad da sauri ya qarasa wurin abbu.
Dago kan da abbu xaiyi suka hada ido.

A firgice ya furta "ya usman"



©MssMjay
[12/15/2016, 10:48 PM] Mss Mjay: WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG
*KUDDIN KADDARA*
WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG

Written by
*MSS MJAY❤*

In dedication to
*Sembyy luff*

WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG

*05*




"Ya usman kaine?"
Abbu ya sake furtawa a firgice.

" ina samyrah?"
Shine kawai abunda Alhaji usman ya iya tambayan shi.

"Tana cikin gida,bari in kirata"

"A'a barta kawai, abunda yasa nazo yanzu dama dan kawai in tabbatar in kudin ne or akasi aka
samu. Toh amma yanzu tunda na tabbatar zan wuce gida da waccan yar taka gobe zan turo a
dauke ku da safe".
Alhaji usman yayi maganar yana nuna Taybah.

"T..to..to yaya, Allah ya kaimu goben".
Daga gani abbu a tsorace yake sai zare ido yake(kaman randa na kama maman nawal na tadi
da saurayina).

Alhaji usman ya juya tare da kallon mu mu ukun sannan yace
"Faysal, shiga mota mutafi gida".

"Wuce ki bishi ku tafi tamana"
Alhaji usman ya furta ganin Taybah batada niyan binsu.

Taybah ta daga kai tana kallon Abbun nata ya watsa mata harara tare da mata nuni da hannu
akan ta bisu.

Sum sum ta juya ta shiga motar, faysal ma ya karaso ya shiga.

Alhaji usman harya kama murfin motan zai shiga sai ya sake juyuwa yacema abbu
"Af abubakar, karka cema samyrah komai har goben".

Kada kai kawai abbu yayi su kuma su Alhaji usman sukayi gaba.

Taybah kuka kawai takeyi, meyake faruwa ne? Ta tambayi kanta, ai da sun bari ko mammy ta
gani tukunna anzo kuma an sake hadata da me shegen kallon nan.

In yanzu ya kalleshi yace ta fiye kallo. Mtsswww taja wani dogon tsaki wanda har yayi sanadin
da faysal din yaji.

"Keh, ince dai badani kike tsakin nan ba?"
Ya tambaya angrily dan tsaki in one of thd things he hate soo much.

"To ni ko kallonka nayi ne? Ina ruwanka dani wai?".
Ta fada tana turo baki.

Amma wannan yarinyar akwai yar iska ya fada cikin ranshi, zanyi maganinki amma.

Kowa da tunanin dayake har suka qaraso wani tafkeken gida dake *rayfield*.
Ma shaa Allah Taybah ta furta cikin ranta daidai lokacin da faysal ya gama parking din motar.

Ta fito tayi tsaye a wurin shi kuma faysal ya wuce ciki ya barta nan.

"Zoki wuce ciki mu tafi koh"
Mahaifiyar faysal ta fada tare da dafata.
Koda suka shiga falon sai suka sami faysal akan dining sai gwabza loma yake.

"Ya sunanki?"
Matar ta sake mata magana

"Taybah"
Ta furta a hankali tana sunkuyar da kai.

"Taybah ki saki jikinki damu, ni nan da kike gani yayan mahaifiyarki ne, wannan kuma matata
ce".
Ya fada yana nuna hajiya karimah.

Da sauri Taybah ta dago kai tana kallonshi, dama da rabon suga wani danginsu a duniya?
Take taji hawaye na zubumata ba kakkauta.

"Allah nagode maka"
Ta fadi hakan tana rungume Ammi.

"Mtswww"
Faysal yaja wani dogon tsaki tareda da barin dining din ya doshi side dinshi cikin sauri.

Binshi da kallo kawai sukayi sannan Alhaji usman ya kada kanshi kawai yayi gaba tareda
fadin......

"Ki kaita dakin rufaida nada ta kwanta ta huta, gobe duk zamu warware komai in shaa Allah".

Hajiya karimah tayi yanda yace tareda da sa Taybah tayi wanka, ta bata rigan baccin sannan ta
debo mata abinci ta mata saida safe.

Koda Taybah ta gama ta kwanta saita kasa baccin, tunanin fuskan faysal kawai takeyi tana
murmushi.

"Yeah, he's handsome, especially eyes nashi. OMG su sukafi komai kashe ta.
Ta murqusa tare da juyawa dayan bangaren taci karo da hijabinta, nan da nan kamshin turaren

faysal ya mamayeta....ta rungume hijabin inhaling the scent har qamshi yayi awon gaba da ita.

WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG

*8:24am*

"Kin shirya?"
Ammi ya tambayi Taybah bayan ta qaraso dakin.
"Ea ammi, amma rigan ta matse ni sosai"
Taybah ta fada tana qara gyara rigar tata.

Murmushi Ammi tayi taja hanunta suka nufi dining tareda fadin...
" zamuje wurin tailor gobe in shaa Allah".

Suna sauka idanunta suka sauka cikin na faysal dayayi mutuwan zaune yana kallon ta.

He's soo lost in her thought har baiyi noticing time din da suka qaraso dining din ba.

Tsinkayo muryarta mai sanyi kawai yayi tana gaida dad, sannan ta juya ta gaida shi kaman
bataso.

Ya amsa a yatsine yana wani kawar da kai.

"Laaa, yaa faysal, wannan ce budurwar taka daka cemun tazo jiya? Whoa ya she's beautiful".

Taybah ta tsinkayo wata zazakar murya tana fadin haka, sai lokacin ta lura ashe akwai yarinya
ya kimanin 10yrs old a zaune a wurin itama.

Ammi ce tace "ki gaida ita mana ummu, she's your elder sister"


"Amma zatayi iya auren ya faysal koh?"
Ta cigaba da surutun ta kaman ba cewa akayi da gaida ita ba.

Tsawa faysal ya daka mata tareda fadin "dallah ki rufema mutane baki koh"

Sum sum ta wuce cikin jikin taybah da sauri tare da boye fuskar ta ajikin ta.

Dad ne yayi gyaran murya yana fadin....
"Ya isa hakanan, kowa yaci

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login