Showing 1 words to 3000 words out of 94796 words

Chapter 1 - WA ZAI FURTA Book Complete by Zainab Dahiru Wawo.pdf

12 Jul 2025

3734

[3/23, 8:00 AM] +234 706 188 4461: WA ZAI FURTA??
0⃣1⃣

*Gaba daya labarin tukuici ne ga Hajiya Rabi badawi ( maman Ibrahim ) Allah ya shirya Miki
zuri'a ya Kara arziki Aunty Rabi tawa*

*KINA RAINA MAMAN WEEDAD MARUBUCIYAR ALJAZEERA DA DR. JUNAID.*

*FARKO*

*Federal University dutsinma*

Gudu-gudu, sauri-sauri take tafiya Babu abinda kirjinta keyi sai dukan tara-tara, dodazon
mutanen dake chunkushe bakin gate wadanda security suka dakatar don bincike saboda Babu
dalibin dake wucewa wurin sai ya gwada I D card, takaici da karuwar faduwar gaban suka Hana
ta sukuni, sakamakon yaune ranar farko da zata Fara shiga aji a makarantar. Tana cikiniyar wucewa taji an janyo hijabinta alamar an mayar da ita baya Shi Kuma ya wuce
da sauri Yana faman daga ID card din nasa, ta bishi da kallo saurayi ne matashi dogo.....
*Anwar! Anwar !!* Wani ya bi bayansa da gudu, dai dai ta nuna nata ID card din ta wuce Shi
Kuma ya juyo don ganin Mai kiransa har lokacin bai tsaya daga saurin da yake faman yi ba. Ta kalleshi sosai tare da samun tabbacin fuskar bazata taba guje mata ba, tayi guntun tsaki
tabi wata hanya.
Da tambaya ta gano ajin, da Shi ta Fara tozali lokacin da ta kunno Kai, ta hade fuska gabas
da yamma ya bita da kallo har ta zauna ....kallon ta yakeyi Yana karanta karancin shekarun ta
yanda har ta shigo jami'a wannan yar ficiciyar diyar...... Ya Dan tabe baki, may be giyar kudi taja
iyayenta mata jumping.....shigowar lecturer din yasa Shi watsar da zancen. Sakamakon sune Yan alfarma list din karshe na admission yasa lectures duk sunyi nisa har
wasu sun kusa karewa, da alama ajin ita kadaice musulma domin duk matan ajin arnaku ne
babu Mai alamar ko gyale ko wace ka gani gashi hirtsi-hirtsi.
Yawancin su ko *zo in kashe ka* basa ji da hausa, a gurguje malamin ya raba script na test
din da yayi, yace class rep. Ya raba ma kowa, layi-layi yake bi. Zuwa can malamin idon sa yakai
gareta, ya tako zuwa inda take tare da Fara jefo mata tambayoyi.
Gaba daya hankalin Yan ajin ya dawo kanta ana jiran aji idan zata iya bada amsa da turancin
kamar yanda yake magana wasu nata sumke dariya cikin su harda Anwar saboda kowa yasan
yaran hausawa da kwabar turanci.
Ta Sha *mur* kawai yayi maganar duniya taki bashi amsa. Kowa mamaki yakeyi *Anwar* ya
Kara binta da kallo duk miskilancin sa yau ga kakar sa ya samu. Hankalinta a kwance ko motsi
takiyi haka malamin ya gaji ya kyaleta tare da Shan alwashin idan tasan wata ai Bata San wata
ba. Dai dai lokacin da class rep ya gama raba takardun. Lecturer din ya ce Wanda baiga nashi
ba ya fito, mutum biyu suka fita duk Mata sunfi mintuna shidda a tsaye kafin yace su kadai ne?
Duk akayi shiru yayi ta maimaitawa Amma ba Wanda yayi magana, ya fiddo takardu uku yace
*Hamza Yusuf* ya Kira sunan yafi sau goma Amma da alama baya ajin yace shine highest he
scored 9/10 ya kalli biyun yace kune second highest kunci 8/10 ya Mika wa kowace takardar ta

da one thousand naira, yace class rep ya turo mishi *Hamza yusuf* office domin ya amshi
kyautar sa da Kuma script din nasa.
Har ya kai bakin kofa ya juyo what is your name? Kanta a kasa sai da ta kusa da ita ta
zungurota sannan ta dago har lokacin fuskarta a murtuk, da kyar ta iya bude baki tace *Bilkisu
Abdullahi gada* ya kada Kai *Discuss the macro objectives of ERGP In Nigeria* you'll present it
next week in front of everybody as your make up of this test.....ya na gama fadar haka ya fi ce
abunsa, ta sunkuyar da Kai kawai tana rubuta question din a bayan littafin ta .......kowa ajin ita
yake kallo ganin ba wani alamun damuwa a gareta .....Anwar ya kalli abokin sa yace waccen
yarinyar gadararriya ce yayi murmushi ta kaika?.
Ganin an Fara mikewa yasa tayi zumbur ta Mike Babu inda tayi ma tsinke sai sit din Anwar
Yana ta kokarin tattara takardu zai Mike ta tsaya kansa, agidan ku ba'a koya maka tarbiyyar
daratta mace ba? Ta fada Kai tsaye gaba daya shock ya Kama Yan ajin masu niyyar fita duk
suka dakata, da sauri ya kalleta..... Ta jefe Shi da wani mugun kallo na wulakanci kafin ta ce
kawai don ka dauki mutane banzaye Ina tafiya zaka Kama mun hijab ka mayar dani baya
.......ke! Ya daka mata tsawa tare da mikewa tsaye .....itama ta daka mishi tsawa, zaka dakenine
marar tarbiyya? Tare da zaro mishi ido idan hannunka ya Kara gigin taba mun hijab wallahi duk
Wanda ya tsaya maka a school din nan sai na ganshi mtseww....ta buga tsoki sannan ta nuna
Shi do yatsa, ka kiyaye ni banzo Nan don inyi wasa ba kasa hakan a ranka ta watsar da
takardun kasa ta koma ta zauna, wani uban tsalle yayi wallahi sai ya daketa aka rike Shi yana
ta faman ihu kamar mahaukaci , ko ajikin Bilkisu taci gaba da rubutun ta kawai da kyar aka fitar
dashi ajin.
Mutane sunfi ashirin bisa kansa suna bashi hakuri hada Yan aji uku da hudu akan kada ya
biye Mata yarinya ce. Da kyar aka shawo kansa.
Ya fakaici idon kowa ya tafi amsar script dinsa domin baya so a gane Yana da kokari
cewarshi Shi baizo don nuna shidin wani ne ba, yayi wa malamin karyar baya aji ne kawai.
Yana komawa hostel ya Fara karatun presentation din Bilkisu domin yi mata tambayoyi, ita
kuwa da yake wani gida take na haya dakuna shidda ne a gidan kowa ne daki sai mutum hudu
ko biyar su Kama Amma ita nata Bata Kama da kowa ba iyayenta ita kadai suka Kama wa daki
daya sakamakon dakunan suna da tsada ko wane da kitchen da toilet akan dubu dari da ashirin
120k. Notes din da aka wuce ta tabi wadannan Yan matan biyu dasuka ci gift ta karbi nasu tayi
photo copy ganin sune masu kokarin ajin. Karfe biyu suka koma wata lecture din Bata yarda ta
makara ba, taki sakar ma kowa fuska saboda tana son sanin halin kowa don tasan dawa zatayi
abota.
Karatun hauka Anwar keyi saboda Bilkisu ya gama tsanar yarinyar kamar yanda itama Bata
kaunarsa, kullum tunanin sa yanda zai rama wulakancin da tayi mishi yayin da ita Sam ta shafe
babin sa ta manta da al'amarain shi daga masallaci sai daki tayi kwanciyar ta tana duba
litattafai abinda ya shige mata Kuma sai tayi goggling. Ranar presentation ta zagayo kasancewar ajin sunfi dari yasa malamin zuwa da microphone
tana cikin tashin hankali da firgici Amma miskilancin Bilkisu yasa ba Wanda ke gane hakan.
Abinda kawai ya kawo malamin shine don tayi presentation din kusan Shi da Anwar Abu daya
suke sakawa a zuciya watan sai sun kunyatata. Fuskar ta tamau ta Mike ta isa gaban Allon yayin da ya Miko mata abun maganar jikinta ya
tsinke da kyarma anan ya fahimci hakan wurin amsar abin maganar yanda hannun ta ke

kakkarwa. Idanun ta suka kawo ruwa tayi saurin cewa *innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Ta tsaye
tare da sunkuyar da Kai kasa ta Fara magana a hankali cikin taushin murya wacce ke cike da
tashin hankali.......
My name is Bilkisu Abdullahi gada and I'm here to present the macro Economic objectives of
Economic recovery and growth.......yanayin fitar turancin nata yasa ajin natsuwa tare da Kara
zura mata ido lecturer din ya Goya hannuwa biyu kawai Yana kallonta Shima .....
Bayani take karantowa cikin natsuwa tana Kara lankwasa turancin nata cikin kalmomin
kwarewa da birgewa hakan ya Kara tarwatsa zukatan kowa ciki harda Anwar ta share kusan
mintuna hamsin tana magana har sai da malamin ya dakatar da ita Shi kansa jikinsa yayi sanyi.
Ta saki ajiyar zuciya a hankali har lokacin kansa na sunkuye ....ya kalli Yan class din *Any
question*? Duk akayi tsit! Amma wasu idanun su Yana ga Anwar kallonta kawai yakeyi ya rasa
ma mezai fassara tunanin sa. Malamin ya watsa hannu tunda ba tambaya ni ina da ita, ya jefa
mata daya.....tayi jimmmmm kamar bazata iya amsawa ba kafin ta Dan motsa kadan ta Fara
zakulo bayani, gaban ta yazo ya tsaya Yana kallonta har ta Gama, sannan tayi shiru.
Yafi mintuna shidda baiyi magana ba kafin ya kalli Yan class yace please will you help me give
her a roundplus? Duka ajin yadau tafi.......raf raf raf abun mamaki ciki hada Anwar.....ya fiddo
five thousand ya Mika mata congratulations you score 10/10 wallahi......ajin ya dauki ihu da
sowa.... Ta danyi murmushi kadan kafin ta karba ta wuce abinta har lokacin jikinta na
karkarawa.
Duk ajin ya rikice da hayaniya kowa na fadin albarkacin bakinsa, haka malamin ya fita kamar
jira Anwar keyi ya Mike ya Isa wurin ta, congratulations sai a bamu ladar ganin ido......Ibrahim
da sauran Yan aji kowa ya zaro ido domin kowa yasan Anwar da gadara, rainin saying da Kuma
girman Kai. Kowa na jiran abinda zatayi sai kawai ta dago tana Yar dariya ( domin Bilkisu Bata da riko ko
kadan da anyi mata zata rama Kuma ya wuce har abada wurinta).
Ta tura mishi kudin to gashi ai ba nisa sukayi ba ta fada tana Kara Yar dariya, tadanji kunya
matuka domin neman fada yazo, ya danyi murmushi kya turan kudi? Kiban kaso na kawai ko
rabawa zamuyi? Ta Dan kalleshi kadan.......gabansa ya Fadi kwarai a karo na farko. To mu raba
Mana ta fada tana maida kanta bisa littafi.... Okay ya Mika hannu bani nawa toh, ta nuna kudin
da baki gasu nan ka dauki naka kabar mun nawa..
Yayi Yar dariya kafin yasa hannu ya dauki 2500 yabar mata 2500.
Amma Kuma ya kasa tafiya sai juya kudin yake da hannu Yana murmushi. Ta dago Kai ta
juya mishi ido alamar tsayuwar ta mecece tunda ta sallameshi? Sai kawai ya bushe da dariya
yace okay thanks. Ya fice class din abikansa da wasu Yan ajin suka bi bayansa, ta kwashi Yan
takardunta tayi daki domin sai 2 zasu dawo wata. Yana tsaye duk an rufeshi ana mishi surutai
sai dariya kawai yakeyi tazo ta raba ta wuce ya ringa satar kallon ta har ta kule.....
*****************
*KADUNA RIGASA*

Amira kiyi hakuri wannan auren da zanyi ki daukeshi amatsayin kaddara wallahi wallahi bazan
taba wulakanta ki ba don girman Allah kiyi hakuri ki daina wannan kukan......baban Ahmad Dan
Allah ka fita ka bani wuri wallahi ko ganin ka bana sonyi na tsaneka da dukkan wannan
rayuwar.....ya zukunna na tuba na rantse Miki da Allah ba zanyi auren nan don in wulakanta ki

ba mu daukeshi matsayin kaddara Amira kiyi hakuri nasan ban kyauta Miki ba, ta Mike tsaye
yaudarar maza wacece ban sani ba? Haka kuke cewa Amma wallahi ka zalunceni ka cuceni
kaci amanar kauna.....kada kice haka na rantse da Allah har gobe Ina kaunar ki.....karya kakeyi
baka kaunata da baka ga wata har ta birgeka kake kokarin kawo ta gidan nan ba. Shima
mikewar yayi bacin Rai zaisa ki Fadi haka Amma Ni nasan wallahi ba haka bane Amira kiyi
hakuri laifi ne na riga nayi na tuba Dan Allah kiyi hakuri.....mtsew ta wuce nabar maka dakin
tunda Kai bazaka tafi ba. Tabar Shi Nan tsaye.
Ya dafe Kai kwalla suka zubo mishi Shi kansa yasan Yana kaunar Amira Kuma baida niyyar
Kara aure, matsalar kanwar abokin sa ce yasan kaunar da yarinyar keyi mishi tun Yana saurayi
da farko Yana ba yarinyar fuska ba tare da Yana tunanin zata iya like mishi haka ba, kowa
yasan suna tare Yanzu idan yace bazai aure ta ba kamar yanda abokin nasa ya bukata lallai
zasu Bata.
Ya zauna bisa gefen gado ya dafe Kai dole in lallaba Amira har ta sauko tabbas bazan yi auren
Nan ba matukar Bata cikin kwanciyar hankali.
Ya kwashe kusan kwana biyar Yana faman lallashi kafin ya shawo kanta hakan yasa Shima ya
Sami sukuni da kwanciyar hankali. Nan da Nan suka Fara hidimar aure shida ita . Ya dauketa
suka tafi Kano hado lefe, ya zauna gefe yace to ki Fara zabar lesuka , tayi jimmmmm kamar
zata ce dauko mun Yan dubu uku da dari biyar sai Kuma wata zuciyar ta kwabe ta da cewar
kisa tsoron Allah ga wannan lamarin bazaki taba tozarta da wulakanta ba.
Ta Fara ma lesussukan kallo tana tambayar farashi har aka kawo na karshen masu kudin
daga dari suka Fara, ta ce nawa za a Sanya ne? Yace yanda duk kike ganin ya Isa ni Dan kallo
ne, ta dunga darzo manya manyan lesussuka tana warewa idan ta dauki red Shi sai ya dauki
pink ko maroon, haka sukayi tayi har aka Gama da suturu aka koma kayan shafa da kalmomi. Sun kashe kudi yafi miliyan uku sannan suka je gurun jakun Kuna da akwattai nan ma aka
darje kusan set takwas ta daukar ma Amarya pink shi Kuma ya dauki sky blue.
Bata kawo komai cikin ranta ba, tana ta addu'o'i na Kara karfin guiywa kamar yanda
mahaifiyarta ta Bata shawara.
Ita dashi aka Kai lefe, gidansu yayi wa Amarya sabon gini kusa da nata, sai dai yafi nata kyau
nesa ba kusa ba saboda tsarin yabanbanta.
Sati daya saura bikin ta dawo gidansu da maraice ta tarar an fitar da kayanta duka anata fenti
tayi tsaye turus, sai gashi ya fito daga gidan amaryar yace shigo kiga anyi wa Amarya jere
Amira. Gabanta ya bada Ras! Da karfi ta daure tana yake tabi bayansa, na mutu.....kawai na
mutu...abinda take nanatawa kenan cikin Rai ganin dukiyar da aka lafta gidan. Sai dai kwalla su
cika idanunta tayi saurin mayarwa ganin yanda yake ta zakwadin nuna mata ko'ina. Jikinta yayi
mugun sanyi ya kamota suka zauna babban falon Wanda suka Fara wucewa, Amira ya naga
jikinki kamar yayi sanyi? Ta Dan kakaro murmushi ba komi tana faman sunkuyar da kai, yayi
kasa da murya ki aminta Dani Amira tunda Kika kwantar da hankalinki tare da kwantar mun da
nawa wallahi na Miki alkawarin bazan taba watsa Miki kasa a ido ba, yanda mutane suka zuba
Ido suga wata baraka Basu gani ba Yanzu daga wurin ki ba wallahi bazan taba bari su gani ba.
*Wannan gidan naki ne bana amarya ba* ita gashi can ana mata fenti kayanki gasu can ana
sakawa mota za a Kai wa su *Umma* ( mamar ta ).
Tayi saurin dago Kai Amma suna hada Ido sai ta rushe da kuka.....ya rungumota kiyi hakuri na
Miki laifi I knew!

Ita kanta Bata San ya sunan kukan da takeyi ba Yanzu. Amma Tasha almwashin zata Kara
daurewa taba maradda kunya har sai taga iya gudun ruwansa though har yau ta kasa aminta da
kalaman sa tana ganin kamar yaudara ce irin da mazan yau.
Ya sungumeta zuwa dakin da Basu shiga ba Nan taga ikon Allah duk yafi dakunan kyau da
girma yafi ko'ina Jin kayan alatu sannan taga akwatunan da ya saya jere sky blue yace kema ga
lefenki can. Kece shaida Babu abinda na banbanta sai kala.
Ahmad da Almustapha ma nasu na tafe gobe anmun waya sun zama ready.
Ta kankame Shi ta saki wani irin kukan Dadi.....kayi hakuri abinda na maka wallahi bazan taba
watsa maka kasa a ido ba.....ya Kara rike ta nasan haka Amira kiyi hakuri.
Tuni labari yakai gidan su Amarya Nan da nan maganganu suka tashi wasu na cewa ta Gama
dashi wasu na cewa tsoronta yakeyi surutai kala kala har Amarya takai ga ta
harzuka......... Turkashi a tsumayi diyar Aunty Rabi (mamn ibrahim) kada a manta a ringa
Sanya mun ita cikin addu'a Allah ya Kara mata yawancin kwana ya shirya Mata zuri'a da rufin
asiri.
Har Yanzu babana ma Yana bukatar addu'a Allah ya bashi lafiya yaba maman mu ladar jinya.
Ni din dai ce Zainab Dahiru wowo maman Abdullah
[3/23, 8:00 AM] +234 706 188 4461: WA ZAI FURTA??
0⃣2⃣

*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( maman Ibrahim) Allah ya shirya Miki zuri'a ya Kara arziki*

*KINA RAINA MAMAN WEEDAD KO DA YAUSHE*

*DOMIN KU AUREN FARI FANS ANA MUGUN TARE*

*Federal University dutsinma*
Semester tayi nisa komai yayi zafi har Yanzu Bilkisu bata Sami sakewa ba, karatun Yana
mata mugun wahala, ahankali take bin su chinyere suna nuna mata abubuwa duk Wanda ta
fahimci Yana da kokari zataje don Kara fahimtar abinda ya shige mata.
Su Anwar sune Yan baya ga komai, ya biye wa mashiririta yaki nuna ma kowa Shi din Mai
kokari ne, masu karyar suna da kokari sai ya kwantar da kanshi Yana Jin yanda suke kwabar
bayani musamman idan akazo gun lissafi.
Hankalin sa a kwance duk C.A din da akayi shine overall, Yana amsa sunan Anwar a zahiri ba
Wanda yasan Shi da Hamza Yusuf a badini.
Fahimtar halin Bilkisu na rashin girman Kai yasa Shi suke gaisawa da ita sama-sama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login