Showing 33001 words to 36000 words out of 94796 words

Chapter 12 - WA ZAI FURTA Book Complete by Zainab Dahiru Wawo.pdf

12 Jul 2025

3758

dauko key din.
Ta Mike.
Ya Kura Mata ido, Yana son tayi shigar doguwar Riga, wannan kamshin zuwa akayi ayi mun
kwalele?
Good and fine, ta ce cikin zuciya, sannan tayi murmushi ta ce hmm kawai.
Kinji?
Gobe zanje kasuwa Dan Allah da safe ba dadewa zanyi ba, Zan biya gidan Salma.....me akeyi
gidan salmar?
Ta dan mishi warrrr da ido, zumunci......duk sai ya diririce, Ni Zan kaiki ko?
Ta Dan Kara farrr da ido tare da Yar dariya, lokacin da Zan fita bana tunanin ka tashi cos by 8
nake son zuwa kasuwa Kuma Kai ba ma'abocin son zuwa kasuwa bane.....Zan biki please.
Saura kadan ta tuntsure da dariya yanayin yanda yayi maganar. Ta danyi murmushi.....Ummi ce
ta fito da key.
Ta mike Bari na dauko book na.
Ya bita da ido Ummi ta dankara mishi harara Amma Sam bai lura ba.
Bude tabar kofar tana dawowa Bata shigo ba ta tsaya bakin kofa....ga key din Ummi, ....wuf ya
Mike Bari na karbo.
Tana daga waje ya hada da key din da hannun ya rike in fito goben muje?
Nooo, kaga Ummi zata ji haushi kayi hakuri ka bata full time dinta don nima turn Dina.....ya
murza hannun da karfi.
Tayi Yar Kara, ya dawo Yana dariya...... Ummi kamar zata fashe amma ta daure ta cije duk da
haka sai da ya danga chanji amma sai kawai ya share.
Butique ta tafi, ta siyo rantsattsun English wear sabbi hada three quarters wando da skirt da
crazy jeans.
Har ta dawo wajen Sha daya bai fito ba.

Ta fada wanka Yara sun tafi islamiya tahfeez, ta kulle kofar ciki tabar Mai aikin ta kitchen tana
fita ta kofar baya.
Amira nada gashi sosai, kanta kananan kalaba ne duk sun zuba bisa bayanta wani sky blue
crazy ta saka da wata crazy riga Mai hannu daya nononta kawai rigar ta rufe kasan ta Kuma
bazace, ta cikin Bazar kana hango cibinta.
Kamshi kawai ke tashi gidan.
Sha biyu saura ya fito, motar ta kawai ya gani yasan ta dawo.
Ya nufi bangaren nata don agaisa.
Tana Jin motsin sa ta ruga daki ta dawo rike da littafi kamar me karatu ita a dole bataji shigowar
sa ba.
Mutuwar tsaye yayi ya kusa sarkewa da miyau sai kawai taji Yana tari.....ta dago Kai da sauri
irin ta razana din nan.......

*****************
*Federal University dutsinma*

.....Ta kasa dagowa ta amsa, jikinta ya Fara Yar kyarma.
Helen ta kalleta, Anwar na Miki magana...
A hankali ta juya kamar Mai ciwon wuya , idanun sa cikin glass Yana Dan murmushi........ Minti
biyu. Ya fada kafin ya juya ya Fara tafiya can nesa wurin parking motoci.
Ta Mike jikinta duk ya mutu tabi bayansa.
Jingina yayi da mota hannuwan sa duka cikin aljihu ya kura Mata ido.
Kanta a kasa ta karaso fuskar ta babu yabo ba fallasa. Ta kasa magana.... Ya Kara nutsar da
idanun sa gareta yace: Ranki ya dade ya exam din?
Ta danyi murmushi kadan Alhamdulillah...Ina kwana.
Lafiya Lau, na Aiko a Baki hakuri kina ta ba mutane wahala kince dole sai nazo da kaina to gani
nazo.
Ta Kara kasa da Kai tana murmushi...... ban taba tunanin zakiyi fushi haka dani ba ko kadan.
Tayi shiru dai,
Har kiranki nayi da sallah without knowing u deleted my number....... Shikenan dai ya wuce. Ta
fada a hankali.
Kin tabbatar ya wuce?
Eh,
Mun shirya?
Sai kawai tayi Yar dariya saboda yanda yayi tambayar kamar wani karamin yaro.
Yabi fuskar da kallo...... Ji yakeyi kamar ya kamota ya rungume... Yayi murmushi kinji mun
shirya Yanzu ko?
Eh,
To na gode, Zan kiyaye daga yau Allah ya Kara Baki hakuri shikenan ko?
Um, tace a takaice.
Ina zakije yanzu?
Gida Zan tafi.
To muje na rakaki ..... A'a barshi kawai na gode, ta katse shi tare da yin gaba abinta.

Ya bita da kallo baya so ta tafi ko kadan.
Ya hura iska.... nawaoooo yarinyar nan miskila ce ta karshe.
Wani sanyi zuciyar ta keyi mata, tana zuwa daki ta fada bisa katifa ta rungume filo ta maida
idanu ta rufe a hankali.
Su Anas suka bushe da dariya, ya cire glass Yana hararar su , Helen na bayansu, tana so taji
yanda akayi.
Munafuki sai kace yau neman shiri zakayi Shi yasa tun karfe biyar ka yo wanka kana faman
shiri.
Mtsew yaja guntun tsaki, suka jera suna tafiya.
Ya kalli Helen din dake kokarin jerawa da su yace ke kuma lafiya kike faman binmu?
Kamar za ta nutse dan kunya, ta juya kawai ta koma...... Sadeeq ya harareshi wallahi ka daina
dizga mutane haka Anwar.
Ya maida glass din a idon sa, inba gulma ba ubanwa zatayi cikin mu?
Kasan tun dazun ina tsaye da Bilkisu hankalin ta na nan?
Kayi mamaki ne? Inji Anas.
Waye bai San ta mutu kanka ba...... Ban san abinda kuka mayar dani school din nan ba. Ko
wace jik and jak Sona takeyi? Mtseww kada kusanya inci ubanta da kyau fa. Mufeeda ma ta
gama haukanta ta shafan lafiya bare wata arniya....... Kada ka taba yarinyar mutane arnan can
sun fika hauka..... Ko in gwada? Muga cikin mu wa ya darar ma wani? .......Anas ya zaburo Kar ka Soma wallahi. Babu ruwanka da ita baka San tana yi ba kawai ka
ci gaba da nuna Mata baka ganeba.
Naji! Ya fada a takaice.
Yaushe zaka Mana bayanin Economic of production?
4, yace a takaice.
4, Kuma?
Eh, saboda zanje wani wuri da daddare.......duk suka kalleshi.
Yanzu barci zanyi, 4 Kuma sai muyi zuwa magrib ko bai muku ba?
Amma ai yau ba ball ina zakaje ne?.... Murmushi kawai yayi.
Suka Kara binsa da ido.
Wai lafiya? Ya bukata Yana Yar dariya.
Ina zaka je muka ce?
Wanda zai bini ya shirya ban hanaku ba.....
Duk sukayi shiru, suna kallon kallo.
Ya kyalkyace da dariya wallahi ku munafukai ne...... sadeeq ya Kai mishi duka wallahi baka da
gaskiya.
Ya kyalkyace da dariya.
Mashin daya suka hau.
Dakin acike bai samu ya yi barcin ba daga wannan sai wannan, ya gaji matuka. Shi ba koyawa
ko bayani ke baya son yi ba, cin lokacin sa da akeyi ke sanya Shi kosawa.
Sai da yayi wanka sannan ya Fara shiri cikin farin boyel ya dauko hudaddun takalma ya saka
na fata *masarati*, yana cikin sharce gashi suka shigo.
Duk suka zaro ido..... Ya fiddo turaruka ya shiga fesawa kusurwa kusurwa, lungu lungu.
Sadeeq ya kalleshi *Anwar Ina zaka je?*

Bai ma kowa magana ba ya Mike, har ya Kai bakin kofa ya waigo ku bakwa ganin karuwa da
danta baku tambayi ubansa ba.
*Zance Zan je*....... Ya fice da sauri suka Fara surma mishi zagi.
Yana tafe Yana tunanin Yanzu kuwa Yana zuwa ya tarar tana tare da wani to ya zai yi?
Ya tofar da miyau, Wai kada abin ya Zama gaskiya.
Mashin din Salim, roba roba ya karba.
A bakin gidan yayi farking ya kafe mashin din tare da Zama saman Shi kamar kujera sannan ya
Kira wayar ta, tana kwance da Yar shimi ta barci rike da littafi tana karatu wayar tayi Kara........
Tunanin ta mommy ce.
Ta muskuta, Ba tare da ta kalli screen din ba tace.
Mommy.....
Mommy Kuma? Ya bukata.
Ta zaro ido tare da kallon fuskar wayar sai akwai ta mayar a kunne....still Baki mayar da no. Ta
ba ko?
Ya hakuri Ina wuni?
Gani waje Ina jiranki....... Waje Ina?
Kofar gidan ku.
Na shiga uku.....Bata San a fili ta fada ba sai da taji yace.....zuwan nawa ke da shiga uku?
Ta zaro ido. Duk ta diriri ce.
Ko baki maraba dani na juya?
Ina zuwa... Ta fada a hankali.
Jikinta yana ta Yar kyarma. Ohh ni Bilkisu ko lafiya?
Sauri sauri ta shirya ta zumbula hijabi har kasa ta fita.
Kallo daya tayi mishi tsikar jikinta ta tashi Yarrrr....
Anwar a manyan Kaya????
Tayi murmushi kunyar duniya ta kamata gabanta ya dunga faduwa tana zullumin me ya kawo
Shi?
Ya tsareta da ido, yaki magana.
Ta dago Kai sai ta zumbure baki ta maida Shi kasa.
Yayi murmushi, haushi kikeji nazo saboda ba Suleiman bane ko?
Kallon sa tayi da sauri , ya Sha mur!
Kin tsaya kina ja mun class kamar irin nazo zancen nan.
Dariya tayi.
Yanzu dai Ina wuni, me ya kawo ka cikin tsohon Daren nan?
Yayi murmushi, zance nazo can baya na biyo mu gaisa ko ban kyauta ba?
Gabanta ya fadi, ta dan tsuke fuska. Hmm.
Ko ban kyauta ba?
Kayi daidai.
Ke baki iya tarar bako? Ko haka kikeyi wa Suleiman idan yazo?
Suleiman again? Ta ce cikin zuciya. Wai meye kake ta fadin Suleiman...... Ba Kya so long sunan
sa na fada kada gabansa yayi ta faduwa?.
Ikon Allah ta fada.
Eh Mana. Gashi kin kasa sauraron kowa sai shine ya shirya mu....... Baka ji dadin hakan ba?

Ya Dan harareta meye tsakaninki dashi? Ki fada mun sirrin..... Anwar rigima kazo muyi ko kuwa
zuwa kayi mu gaisa da gaske?
Duka biyun nazo yi.
Karatu nakeyi. Nasan kayi covering gobe ka Fara ansar extra sheet ina page 2 ina zare ido......
Suleiman zai Baki amsa.... Na shiga uku. Ta fada tare da kallon sa. Yasha mur, ko ruwa bazaki
bani ba da gaske......juyawa tayi kawai.
Ya bita da kallo. Kwalin fresh milk ta fito da Shi da cup a hannu, gashi amma ba sanyi.
Ya karbi kofin ya Mika Mata alamar ta zubo mishi.
Ya tsareta da ido sai Yar kyakkyarwa takeyi.
Nayi kyau da manyan Kaya?
Ta tuntsure da dariya...... Yau naga ta kaina.
Shima dariyar yayi, to naji kin ki yabawa ..... Ta dalla mishi harara ita wacce kaje gurinta Bata
yaba bane?.
Ya Kai kofin bakinsa yasha kafin yace, ta yaba tayi comments kema kiyi naki.
Har zata ce ni budurwar ka ce sai Kuma tayi shiru kada yace *Eh* tafi so *YA FURTA* Da bakin
sa.
Me yasa baki WhatsApp?
Hakanan.
Bai yiwuwa , saboda duk Mai hankali baya abu babu dalili. Me yasa bakya yi?
Allah kawai bana son abun da zai daukar mun hankali daga karatun nan.
Muga wayar.......ta kalleshi.
Ya nutsar da idon sa cikin nata tayi saurin kawar da Kai.
Kada Inga text din Suleiman? Bazan shiga can ba......ta Mika mishi da sauri, yayi murmushi.
Zan dawo Miki da ita gobe ya saka aljihu. Meye password din?
Ta zaro ido, Daddy na kirana every asubah..... don't worry I'll talk to him meye password din?.
Dan Allah ka bani saboda....... Saboda Suleiman bazaiji dadi ba? Sau nawa nake ganin ta a
hannun sa?
Wai lafiyar Anwar kuwa meye Yanzu magana daya sai ya ambaci Suleiman????
Na rantse da Allah sau biyu ne, Kuma duk chargy ya kaimu ya Kuma karbo.......
Yasha mur meye password dinki?.
Gabanta ya Fadi duk ta rikice saboda ANWAR ne password din. Ya kalleta wallahi wurina wayar
Nan yau zata kwana Kuma sai kin fada mun password din..........✍

Zainab wowo ce �

Ayi hakuri da kadan. An dameni da cigiya
[3/23, 8:00 AM] +234 706 188 4461: *WA ZAI FURTA?*
1⃣2⃣

*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya
shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*

*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*

*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*

*Godiya ta musamman ga :*
*Mowa ( maimuna Nasir )*
*Hauwa'u, ( mum khady nima Ina kaunarki matuka*
*Da masu mun waya, text da kirana direct ku sani cewa zainab wowo Bata Raina masoya wlhi
Ina kaunar ku sosai*
*Unex*�


***************
*KADUNA RIGASA*

Ta dan rike kugu tana Yar rangwada.... Mura kakeyi haka?
Wuffff.... Ya riko kugunta, kece Zaki Sanya mun ita Yanzu, Ina Kika Sami kananan Kaya haka?
Sai faman shinshinarta yakeyi ya nutsar da kansa cikin wuyanta.
Tayi wani juyi tare da mayar da fuskar ta gab da tasa saboda ya sunkuyo tayi warrrr...... Kawai
taji ya hada bakin sa da nata...... Fittt... ta fizge. Ta danyi baya tare da buga wani makirin tsalle
rigar tayi sama cikinta ya fito fili..... Kanka qalau kuwa?
Ya yunkura zai Kara chafko ta tayi baya tana Yar dariya idanunsa sun kada sunyi jawur.... Ya
kalleta kamar Mai Shirin yin kuka *Dan Allah ki tsaya bani da karfin binki ko'ina*.......
Amma kasan ba anan kake ba ko?
Ya langwabar da Kai, please one kiss.... Tabbb wlhi Haram. Ta fada tana wata karairaya.
Ya kura Mata ido duk hankalin sa ya tashi.... Amira kada ki hadu da fushin Allah ki tsaya....
To Yanzu....... Charaf! Taji ya damke ta cikin taku daya. Yana riketa ana dukan kofa da karfi.
Kafin yayi wani motsi ya jiyo muryar hajia ( mahaifiyar sa ) tana fadin Amira ko Bata ciki ne?.
Ya buga wani uban tsoki ya ingijeta ya wuce bedroom dinta da sauri.........


***************
*Federal University dutsinma*

It seems like baki da gaskiya fa!. Ya fada tare da tsareta da ido.
Ta dake ta kalleshi Yanzu dai Wayata ce zaka tafi da ita ko?
In shaa Allah, ya fada Yana murmushi.
Wai meye zakayi da wayata ne Anwar?, Bincike......., Ya fada Kai tsaye Yana kallonta, tayi
shiruuuuu.......
Naji Zan baka, kawo na goge abu daya shikenan....menene?
Wallahi dana goge Zan baka hoto ne.....hoton Suleiman?
Ta doka tsoki Wai Kai komai Suleiman??????
Eh, ai kema komai shine....mtsewww to ba nashi bane nawa ne.

Kiyi hakuri bazan Baki ba don Ina son ganin hoton.
Ta Sha mur bani da Riga ne, Shi yasa da best Aisha ta daukemu muna cin abinci akwai hotuna
da yawa nawa sai ka gaji da gani amma wannan bana son ka ganshi.......Ni Kuma naji Shi kadai
nake son gani ma .....ta zaro ido. What?
Cikin fushi ta juya gara ta nade tabarmar kunya da hauka... shikenan sai da safe ka cinye wayar
ko kaje wurin Yan gyaran waya su bude.....dawo dawo....zo ...zo..zo please. Gashi zo ki goge ya
fada da sauri Yana fiddo wayar daga aljihu.
Ta kusa sakin dariya Amma ta daure ta Mika hannu okay bani.
Ya rike wayar yaki saki.....ki rantse da Allah ba text ko hoton wani Zaki goge ba...... Wai me ka
daukeni ne?
Ya langwabar da kai hoton nawa Zaki goge?.... Ikon Allah ta fada duk ta Fara kosawa, guda
daya ne ko?
Ta sakar mishi wayar ganin baida niyyar Bata..... Ya Kara mikowa ungo amma kiji tsoron Allah
kada ki gudu da ita Kinga na rantse.
Wallahi Zan baka Yanzu.
Ya sakar Mata ta Dan ja baya ta fidda key din sannan ta shiga setting ta chanza password din,
tana dannawa zata Kara confirming yayi fit!!.... Da wayar, Wai meye kikeyi?.
Kawo na karasa please baka zanyi...... Password kike canzawa??????? Ya fada Yana Mata
wani kallo.
Tayi murmushi, Yanzu dai Kara confirming ka Sanya *Balky02* shikenan.......
Dirowa yayi bisa mashin din saura kadan ya fada Mata tayi saurin ja da baya, kawai ya Fara
binta Yana magana cikin daga murya.... password Kika chanza? Hankalin sa duk ya Fara tashi
cikin bacin Rai....... Ai ...ai ....tanayi tana ja da baya Yana binta.
Gama korar awakin na rantse da Allah sai kin sanar Dani tsohon password dinki da dalilin da ya
Sanya Kika canza....au ni Kika mayar photo?
Bayanta ya daki bango ta daga hannuwa sama Dan girman Allah ka ja baya Anwar......waye
password dinki?
Ta runtse ido...... Dan Allah kaja baya Zan fada maka...... Kina fadawa Zan koma inda nake
meye tsohon password dinki?
Dabara ta fado Mata, sunan da ake kirana gidan mu ne Kuma bana so ka ...... *Balky* shine
abinda ake kiranki saboda har daddy da mommy suka tafi banji sun kiraki da wani suna ba
bayan haka wane password ne Kika goge Wanda bakya so na sani?
Ka koma yanda kake kada wani ya ganmu a...... Suleiman kike gudu da samarinki ko? Ya Kai
hannu daya a bango.
Ta runtse ido na shiga uku.....sai kwalla sharrrr....... Ya kura Mata ido jikinsa yayi sanyi sosai, ya
sauke hannun a hankali ya Dan ja baya tare da saka hannuwan sa duka ga aljihu ya kura Mata
ido.
A hankali ta bude ido, ita kanta Bata iya fadin ga dalilin kukan, saboda wani yanayi ne ta fada
Mai rikitarwa.
Ke shagwababbiya ce?
Kamar ta shako wuyansa,
Tayi mishi banza.
Meye tsohon password dinki?......woohoho, Anwar idan maye ne ya Kama mutum tabbas sai

mutuwa.
Kina so kiga irin tawa rigimar ko?....... *Yar Fara* ta fada a hankali, kakata ce kafin ta rassu take
kirana da haka shine na saka........ta karasa maganar tana addu'a a zuciya ya Allah ya ceceta
ya yarda da hakan.
Yayi jimmm, sannan yayi murmushi me yasa baki so nasan haka?
Ta galla mishi harara ban sani ba .....Nima meye zakayi da wayata?.
.......yayi Yar dariya, bincike....ai Ni ban boye Miki ba.
Karfe nawa?
Ina ruwanki da ko karfe nawa keda kike bakin kofar gida fadawa kawai zakiyi?.
Ina binki bashin abinci Wanda aka mun kwalele lokacin da mufeeda tasa nayi laifi......ta doka
uban tsoki, kaje ta dafa maka mana.
Saboda me?
Saboda yarinyar ka ce.
A'a na kawata nake so my best friend Bilkisu.... Hmmm.
Ko ni ba babban abokin ki bane?
Shine, ta fada a gajarce.
Kika ce mun bakya fitar dare ya akayi yau Kika fito ??? Wannan karon Yar dariya tayi Wai haka
kake da masifar tambaya?
Ya bi kumatunta da kallo, yau Kika San haka?
Tayi hamma ,
Barci yazo?
Da sauri ta daga Kai.
Yayi murmushi, to jeki kwanta...... Ta juya da sauri daman kafafunta duk sunyi dayi saboda
tsayuwa.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login