Showing 27001 words to 30000 words out of 94796 words
Chapter 10 - WA ZAI FURTA Book Complete by Zainab Dahiru Wawo.pdf
kukan da biyu takeyin sa, kasa ta sauko ta Fara magana a hankali,
Aunty Amira kiyi hakuri Dan Allah Akan abubuwan da suka faru sharrin shaidan ne, in shaa
Allah hakan bazai Kuma faruwa ba......Ayya Ummi ba komai ya wuce.
Ta fizge hannun ta bari in zubo Miki abinci......um um na gode ta mike.
Ina zakije toh? Ki zauna muyi fira.......ya Kara hade fuska ya tsuke.
Ta Dan tabe baki , a'a barci nakeji da wuri sai ko zuwa gobe haka.
Har kofa ta taraka, kafin taja kofar.
......... Gaskiya abinda kakeyi ko kayi Abban Ahmad wallahi baka kyauta ba, Shi ido ba mudu ba
yasan kima.
Ka rikeni gaban Ummi ai wannan cin fuska ne.
Ya kalleta sosai.......makaho idan Yana Kashi in har ba'a zungureshi ba to bazai gane ana
kallonsa ba.
Yarinyar can abinda take nuna mun tun kafin in aureta dole in bita in Mata yanda takeso ita
bazata bi ra'ayi na ba.
To Ni da ita wake auren wani?......duk da haka Yanzu kaga.....kiranta mukayi?.
Inba kilibibi da tsugudidi ba me ya kawota Yanzu?
Ba a haka......ke naji.
Tayi murmushi.... Ita Amarya ai Bata laifi.
To wannan dai tanayi.
Naji dadin zuwan ta yau din wata kilan ta Dan Sami darasin kula da miji idan ita din Mai hankali
ce.
Ya Mike idan kin Gama sallamar Yara Ina jiranki.
*Ummi* taci kuka kamar ranta zai fita, tabbas ya kamata tayiwa kanta karatun ta natsu. Ashe ita
sunan tana Aure Amma har Yanzu Bata San meye Jin dadin Aure ba, ta goge hawayen da ke
shatatowa, dole in kwantar da kaina inci arziki in barshi inda yake saboda tabbas idan naki
abinda yake so nice Masha wuya.............
******************
*Federal University dutsinma*
Shigowar su Aisha ya bata damar neman mafita.
Ita kanta ma tana son ya zo su gaisa amma bazata iya kiransa ba.
Text ta tura mishi.
_Kaxo ku gaisa da su daddy yanzu_.
Wayar na hannun sa Yana kallon film.
Zaune ya tashi zumbur.
Sadeeq ya kalleshi lafiya?
Ya jefa mishi wayar.
Anzo wurin Dan ubanka sai kaje ka gabatar da kanka.
Munafukan banza Kun tsaya sai ba juna wahala kukeyi.....mtsew malam ban wayata.
Ya jefa mishi.
Wani text din ya Kara shigowa ... _zasu tafi in d next 30 minutes so hurry up and come_
Kara jefa ma sadeeq wayar yayi.
Kai seriously fa ...ya fada Yana zaro ido.
Ya tuntsire da dariya sai ka tashi ka tafi.
Ku dai tashi mu tafi wallahi bazanje Ni kadai ba. Kasan dai rashin zuwan Nan kuma wani
problem din ne.
Anas ya Mike zumbur Tabb ku tashi mu tafi rigima dame ta cimma kurege.
........ Ya kallesu sai faman canza Kaya sukeyi, yayi murmushi wallahi Yan iska ne ku.
Kaman zakuje biki?
Sadeeq ya jefo mishi wani farin boyal malam saka mu tafi...
Ya Mike idan Kun Gama mu je banson shirme.
Duk sukayo mishi chaaaaaa wallahi sai ka canza Kaya Dan ubanka da wannan hug din zaka
je?
To meye aciki?
Kana hauka ne?
Ku daine mahaukata, Kun zauna Kuna ta faman wata kwalliya kamar zakuje daurin Aure.
Yayi hanyar waje.
Anas ya finciko Shi, kasa manyan kayan nan kada muci ubanka.....kici kici suka Fara kokawar
cire mishi riga. Ba arziki ya cire su.
Sukayi juyin duniya yasa hula kube yakiya dole suka hakura sai dariya yakeyi masu duk sun
Sha huluna.
Daddy ya Fara mikewa Zan jiraku waje ku karasa kada muyi dare....... Tuni su Aisha sun rufo
mishi baya don barin Bilkisu ta gana da mommy.
Mashin din muhseen roba roba suka amso.
Sadeeq ne driver, Anas tsakiya Anwar karshe.
Suna shawo kwana sadeeq ya kurma zagi ashar, wancen muguwar motar fa?
Dai dai su daddy na kunno Kai sai dai ji sukayi Anwar ya dire da yake ba gudu sukeyi ba.
Ga Anwar nan kuwa inji Aisha.
Murmushi daddy yayi, nesa kadan sukayi parking.
Tare suka jero su uku.
Wata irin faduwar gaba yakeji wacce bai taba Jin irinta ba, duk suna durkushe lokacin da suka
karaso.....Barka da rana.
Idanu su Aisha suka bude duk girman Kan su?
Ya fadada fara'ar sa ya Mika musu hannu, Assalamu alaikum duk Wanda suka gaisa sai ya
dago hannun alamar ya Mike tsaye har yakai ga Anwar,
Wani shocking yaji duk illahirin jikinsa ya dauka dai dai lokacin ne Kuma Bilkisu da mommy
suka fito.
Ta danyi dariya to mommy ga Anwar can .
Da sauri ta Fara waige waige Yana Ina?
Gashi can daddy ya rike hannun sa.
Tunda ya dago daddy bai saki hannun sa ba, ya rikeshi gamm suna Yar tafiya hakan yasan su
sadeeq da Aisha stepping back kadan suna bin bayan su.
Sai murmushi yakeyi Yana sunsunne Kai.
Daddy ya kula dashi tsaf!, ( Abinda bai sani ba yasa an kishi bincike kaf akansa tun lokacin da
Bilkisu tace wurin Shi take daukar karatu ).
Ya karatu?
Alhamdulillah! Ya fada,
Kana fama da rigimar Bilkisu ko?
Yar dariya kawai yayi, har lokacin yaki yarda su hada ido dashi.
Ai kullum labarinta Anwar, ko an Kara wani fadan ne?
A'a ya fada Yana murmushi.
Ta ce Kai Dan Kano ne ko?
Eh, ya ce har lokacin fuskarsa ta kasa daina murmushi.
Me yasa baka jituwa da malamai?
Lokacin ne ya Dan saci kallon daddyn ta gefen fuska....
Ya kasa amsa tambayar.
Ganin haka yasa yaci gaba da cewa, mutunta malamai akeyi ana gaishesu, wasu akasin hakan
duk kokarin ka sai sunyi maka mugunta.
Haka ne!, Anwar din ya fada a hankali.
Sai a kiyaye kaji ko?
In shaa Allah. Yace.
A bakin mota suka tsaya.
..........ga Anwar ga Anwar , tun daga nesa mommy ke fada tana dariya.
( Na shiga uku ni Hamza ). Ya fada cikin zuciya.
Duk su sadeeq suka gaisheta Bilkisu na gabatar dasu.
Ya yunkura zai zukunna don gaisheta daddy ya rikeshi, ku gaisa a tsaye kamar yanda sunna ta
koyar.
......ya akayi Kika gane shine Anwar? Daddy ya tambayeta Yana murmushi.
Balky ta nuno min Shi lokacin da mun fitto.
Idanun ta na kansa Shima Yana son kallonta Amma ya kasa.
Su Aisha sukayi bankwana suka juya, Shima ya saci kallon su Anas alamarr su ware lokacin
dasu daddyn kema su Aishar bankwana da nasiha.
Sai dariya sukeyi mishi daga nesa. Daman tun da suka taho da daddy din suke mishi dariya
ganin duk yanda ya dabarbarce.
Anas yace munafuki kaga duk rashin kunyarsa yaki sakewa Kuma don sun dauki mutane Yan
iska Basu so a gane suna son juna.
Anas ne ya matso ya Dan rusuna zamu koma hostel Allah ya tsare hanya...... Amin Amin ya
zaro envelope ya Mika musu. Har lokacin hannun daddy na cikin na Anwar.
Ya kalli Anwar tafiyar ku daban ko?
Ya Dan sunkuyar da Kai tare muka zo.
Ohhh, to su tafi sai mu ajiyeka...... Ba Anwar din ba ita kanta Bilkisu tayi mamakin hakan.
Ya kalli Bilkisu ba abinda kike bukata Kuma?
Tace eh. Okay muje kada dare yayi suka bude mota.
Lokacin ne ya Sami hada ido da ita.
Ya sakar mata murmushi sai kawai ta harareshi ta juya.
Gaba ya shiga Yana nuna hanya.
Allah dai ya baku sa'ar karatu ya kareku daga dukkan sharri.
Yace Amin
Dan Allah kusa tsoron Allah ga dukkan al'amuran ku Anwar kada kuci amanar iyayenku, kaji ko
?
In shaa Allah mommy. Ya fada.
Yayi matukar godiya lokacin da suka ajiye Shi daddy ya umurci driver ya sauke mishi sauran
kayan dake boot , sannan ya Mika mishi envelope Mai kauri.
Yayi godiya sosai. Aka Fara sauke Kaya, cartons din lemuka , ruwan roba, carton din indomie,
oat,Madara family size 3, corn flakes, biscuits kala kala,Dan kalin turawa cikin buhu, plaintain,
kwai Crete hudu,fresh milki, gasassun kaji, kilishi, soyayyar miyar naman rago, dambun
Daman kaji, fanka Mai chargy ( Daman Yana da ita ), sabon carpet kato Mai laushi da turaruka. Cikin kwalaye aka jero kayan.
Yabi kayan da kallo kafin ya Kara komawa bakin tagar motar yadan rusuna, Angode Allah ya
Kara arziki Mai albarka ya bada lafiya da tsawancin kwana. Duk suka amsa Amin Amin.
Ya daga musu hannu Allah ya kiyaye lokacin da driver yaja mota, gaban hostel din cike da
mutane Shi kawai ake kallo saboda motar da ta janyo hankalin kowa.
Da gudu su sadeeq suka karaso.
Ya kallesu ku shiga da kayan Nan zanje in ga Bilkisu......kawai ya tsaida mashin ya
koma..............Tana ta faman shirya kayan Jennifer ta shigo, Bilkisu Anwar want you......ta
kalleta da sauri Anwar?
Yah, he's out side...... Tana fadar haka ta fice abinta.
Ikon Allah, lallai ni ta bance , duk FUDMA kuwa akwai macen dake juya Anwar kamar Ni?.
Wallahi Bata taba tunanin zaizo ba lokacin da tayi mishi text despite fushi da rashin daukar
wayarsa, Wai me yasa Baya mata fushi da gadara da Kuma wulakanci kamar yanda ya Raina
kowa?.
Hijabi ta saka ta janyo dakin.
Yana tsaye ya harde hannu duka biyu a kirji.
Manyan Kaya na mishi kyau matuka, ya Kura Mata ido kamar zai cinyeta.
Ta karaso kanta kasa, Ina wuni.....ban amsawa.
Wai Bilkisu me kike nufi ne?
Me Kika fadawa su daddy akaina?
Ta dago Kai me fa, wani abu ya faru?
Komai ma ya faru gashi kince dole nazo mu gaisa ya Mika Mata kudi Kinga bayan Wanda aka
ba su sadeeq ga nawa Kaya Kuma nacan an ajiye mun kamar.....to meye ne ba kyauta bace?
Ya kalleta, Kuma only me?
Ta daure fuska Ni ban gane abinda kake nufi ba...... Meye Kika fada ma iyayenki a kaina?
Simple question.
Ta gyara tsayuwa, sun San cewa Kaine kake koya mun karatu Kuma Koda yaushe Ina Basu
labarin karatun da mukayi.....ya akayi daddy yasan bana shiri da malamai?
Ta zaro ido wallahi bamuyi wannan maganar ba.
Kin tabbatar?
Ta balla mishi harara na maka ta kudin ka.
Ya kyalkyace da dariya, to ai abun ne ya bani tsoro,
Mtsew ....tayi tsoki.
Mun shirya ko? Tunda na amsa Kira na Kuma bada hakuri Nima ayi hakuri na gaji da fadan Nan
wallahi.
Mun shirya ko? Ya Kara maimaitawa Yana murmushi,
Ta yi Yar dariya eh,
Good, Dan Allah kiyi mun godiya sosai na gode.
Ba komai. Sai gobe.
Korata kikeyi?
A'a bana son dai a Kira magriba kana Nan ko?
Hmmm, kawai kin koreni sai anjima ya Dan juya kamar yayi fushi.
Allah ya baka hakuri ka dawo ban koreka ba.....ya juyo Yana murmushi tunda kin bada hakuri
kin tsira.
Zan kiraki please.
Ta juya.
Kinji?
Na ce toh.
Tuni magana ta Game ko'ina akan zuwan iyayen Bilkisu Kuma anga Anwar a wurin.
Hankalin mufeeda yayi mugun tashi ta dunga bala'i a daki. Tare da Shan alwashin dole ta
gyarawa Bilkisu Zama ta Kuma ja mata kunne akan Anwar.
Sha daya da kwata na dare ya kirata. Labarin kayan da aka kawo mishi da makudan kudin da
aka bashi yake lissafa Mata sanannan yadanyi Mata bayanin course din da zasuyi gobe.
Sha biyu ta wuce suka ajiye.
Su sadeeq sunyi sunyi yayi confessing akan Bilkisu Amma amsar kamar kullum itace, *baku
da hankali*
Kowa yayi mamakin ganin su rumi rumi.
Sai karfe hudu suka gama lecture.
Duk ta gaji tana tafiya da kyar kawai taji anfinciko hijabin ta.......jira karamar Yar iska.
Kafin ta Ankara sun Mata zobe.
Ta kallesu daya bayan daya tace *Anzo wurin* cikin zuciya.
Lafiya?
Ta bukata tana musu kallon up and down.
Ko zamuji na jaki ne tukun?
Ko Kuma Ni ko?
Wallahi tallahi duk Yar iskar da ta Kara ja mun jiba sai naci kutumar........ke banza...mufeeda ta
katseta.
Wani kallo ta wurga Mata nice banza?
Eh kece banza ko Zaki Rama ne?
Akan meye Zaki kirani banza?
Saboda Anwar..!
Wallahi idan Baki fita harkar sa ba Zaki......Zaki fiddani karatu FUDMA?
Ta bukata.
Amma ke a matan ma rakiya kikayo, ai mace idan ta cika mace namiji binta yakeyi ba itace ke
bin sa ba. Kije ki tambaya Dani da Anwar waye ke bin wani?
Ko an fada Miki dashi da Babu suna da banbanci a wurina?
Karatu ma da mukeyi Shi ke rokona da inzo ba Ni ce ke makalewa ba. Ta fiddo waya ta latso
missed calls.....ta nuna Mata fuskar wayar kalla ki gani.....don haka wallahi tallahi sai kinyi Dana
sanin kirana banza......ta ingijeta ta wuce , gigin yasa jamcy ta Kai hannu zata rikota ji kake
faaass.... Ta wanka Mata Mari , Marin da ya janyo duk illahirin masu wucewa da wadanda ke
zaune sannan ta daga murya....duk wacce Kuma take ganin ita Yar Tasha ce tazo ta yi gigin
kwatanta abinda tayi ko a nemi wata ta Rama Mata...... Bilkisu lafiya meke faruwa?
Suleiman ta gani.
Tayi murmushi cike da takaici duka na suka zo yi saboda inji tsoro in daina karatu da kula
Anwar .
Duka?
To bisimillah kuzo ku dake ta wallahi summa tallahi da na karya hannun yarinya ko waye
ubanta....duk suka juya suna gunguni, yace:, Yan iskan karya.
Muje kyalesu. Suka jera.....
Haushi ya kamata lokacin da ya Kira taki daukar wayar.
Tasan akan maganar test din *GST* ne. Yasan cewa ta tsani CBT,
Ya buga tsoki, duk duniya Babu Mai Sanya mishi ciwon Kai irin Bilkisu.
Bakin Auditorium din cike da dalibai abinka ga general course. Tana can gefe ta makure sai
faman karatun past question takeyi, Shi kuwa sai wurge wurgen ido yake ta inda zai hangota,
Mufeeda na can jikin bedi sun Kura mishi ido.
.......Wai Daman kina Nan? Yanzu naga Anwar Yana nemanki nace bamu hadu ba, Aisha ce ta
karaso rike da past Q din itama.
Yana Ina?
Gashi can....
Ta Mike , okay jirani Ina zuwa.
Yana hangota ya nufo ta.
Tayi kamar Bata ganshi ba ta nufi inda su mufeeda.
Ya biyota.......ke nake nema fa tun dazun kin Kuma hangoni kina neman sharewa........ Da karfi
ta finciko mufeeda tare da bankada ta kusa dashi har yayi saurin ja da baya ganin zata fado
jikinsa.
Ya zaro ido.....ita Kuma ta juyo a hasale ta Kara maida keyar ta tare da nuna ta da yatsa.......Ni
agabansa Zan Miki *warning*
Ko a Yanzu wakika ga yabi wani cikin mu?
Tuni an musu zobe ana kallon ikon Allah,
Ta daka Mata tsawa nace ubanwa Kika ga yabi wani cikin mu?
Na tabbatar tun dazun ya ganki anan Amma bai nemeki ba saboda haka kece *BANZA* Gashi
nan nabar Miki Shi duniya da lahira idan kina bukata Ni karatu ya kawoni ba shashanci da bin
maza ba don haka idan kina son sanin wacece Bilkisu please try and confront me again wallahi
you'll regret it for the rest of your life useless fool......... Kawai ta bi cikin mutane ta wuce abinta.
Zainab wowo ce dai✍
[3/23, 8:00 AM] +234 706 188 4461: *WA ZAI FURTA?*
1⃣0⃣
*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya
shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*
*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*
*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*
************
*KADUNA RIGASA*
Tun daga bakin gate yake jiyo kamshi, mamaki ya cika Shi, shin ko yayi batan lissafi ne gidan
Amira yake ba Ummi ba?
Tana tsaye cikin Riga da skirt na leshi tasha ado ya shigo.
Da gudu ta rungumeshi yaji wani tsammmmmmm...... Anya Ummi ce?
Nan danan ta Fara sabon salo. Shigowa yayi kawai ya ajiye jaka ya wuce wurin Amira sannan
ya dawo Amma inaaaa tuni hankalin ya karkata........ Bayan yayi wanka, ta zauna tana bashi
abinci kamar yaron goye tun a daki da ya motsa sai ta bashi hakuri yanzun ma tana bashi
abincin tana Kara lallashi duk ya sukukunce ya rikice. Ya kalleta wallahi Ummi Ina sonki, kawai halayenki ne suka Sanya mun ko kwanto a zuciya
Shi.......ta rufe bakin da chokaci ta debo peppé soup, sorry my love zaka ga changi I
promise...... Ai na ga changi wallahi please keep it up.......
Amira Bata Sanya Shi ido ba sai bayan isha'i ta gama kulewa ta Kai karshe.........
**************
*Federal University dutsinma*
Kowa yasan sadeeq baida fitina, murmushi kawai yayi yabarshi a wurin yana babatu.
Sai kawai ya Fara fushi dashi.
Cikin bacin rai sadeeq ya samu Anas, Yana fada mishi abinda Anwar din yayi mishi Kashi na
biyu akan Bilkisu.
Yaja guntun tsaki, kayi hakuri sadeeq wallahi *So* ke wahalar dasu duka for now ka bashi time
zai nemeka.
Tun daga ranar Bilkisu ta koma sadeeq ke nuna mata, sun kyale Anwar.
Hankalin Anwar yayi matukar tashi ga exams na karatowa, hanya ma idan ta hango shi
canzawa takeyi.
Ya rasa inda zai saka ransa.
Ko kallo bai isheta ba. Idan ta zo school amma tana komawa daki zata ci kukan ta tayi ma'ishi.
Yanzu fa kowa ya fahimci an bata Bilkisu da Anwar. Tsalle da Murna mufeeda ta ringa yi.
Tana zaune class za'a yi lecture ya shigo.
Yana ganin ta yayi saurin shiga sit din zai zauna kusa da ita...... Sai da ya karaso gaf! Daman
can karshe take sai kawai ta kwashi kayanta ta dora waya a kunne , helllooo....yes inajinki.
Tayi waje kamar me amsa wayar gaske.
Tana fita tayi jimmm sannan ta dawo tare da canza layi ma gaba daya.
Ransa ya baci, hankalin sa ya Kara tashi, kowa ya fahimci abinda tayi.
Sam ta rage fara'a in kaga tana dariya to tare take da Suleiman.
Ana gama lecture ya tsaya bakin kofa yasa hannu duk Wanda zai fita sai ya mishi magana, tana
ganin haka ta yi zamanta, Shima ya ayyana a ransa wallahi yau Kam sai dai su kwana haka.
Masu shigowa da masu