Showing 45001 words to 48000 words out of 94796 words

Chapter 16 - WA ZAI FURTA Book Complete by Zainab Dahiru Wawo.pdf

12 Jul 2025

3745

da ido, matsayin abokin Bilkisu Wanda bai son kowa ya rabe ta....... Maganar ta
makale da alama ya kusa yin *subul da baka*.
Shima abokina nane kamar ka nafi sakewa dashi fiye dakai saboda bashi da fada ko kadan ni
Kuma na tsani fada rayuwata wannan abotar da kyar zatayi lasting.....
Ya zaro ido da gaske kikeyi ko wasa?
Tayi shiru tana murmushi,
Ke!, Dago Kai ki kalleni ki Kuma maimaita abinda Kika ce Ni da Suleiman duk matsayin mu
daya?.......
Ta Dora hannu bisa Kai *wallahi idan akwai abinda ya fi shiga uku a yau to cikin sa nake*....
Dan Allah Anwar kabar ni haka nan na gaji yunwa nakeji har an kusa Kiran sallah.......
Zan dawo anjima.....
Basai ka dawo ba zamuyi magana ko ta waya ne....... Zan dawo da karfe 8 idan Baki fito ba Zan
shiga har ciki in fiddo ki.....
Ta bude Baki, sannan ta tsuke fuska, nifa bana fitowa da dare na Kuma fada maka tun last
semester.
Na fi kowa sanin haka sai nidin Anwar ne dole ki fito saboda....... Maganar ta makale. Ita Kuma
ta tattara hankalinta kaf akansa......
Yayi murmushi, kije ciki sai na dawo anjima.......
***************
*KADUNA RIGASA*
Tayi turus, duk sukayi tsuru tsuru ba kamar Shi guiltiness ya kamashi........ Ta kakaro murmushi
Wanda yafi kuka ciwo kafin tace .... Ohhh sorry ta juya yayi Kiran duniya amma Bata dawo ba,
Ya saki Amira da sauri yabi bayanta Nan da Nan kishi ya turnuke ta itama.....hawaye suka
shatato Mata sharrrr.…...✍✍
*Zainab Dahiru wowo* ce�



Ayi hakuri da kadan
[3/23, 8:00 AM] +234 706 188 4461: *WA ZAI FURTA?*
1⃣5⃣

*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya
shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*

*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*

*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*

*****************
*Federal University dutsinma*

Anwar din nan ya mayar dani sakarai. Shi girman Kai ya hana ya fito yace Yana Sona shine
yake ta gewaye gewaye, bai San halina ba, a dole yanda banzayen Yan matansa ke zubda
class suna crushing din sa nima haka yakeso nayi..... Ba dai Bilkisu ba, ko Zan mutu bazan ce
Ina son sa ba. Zan daure na cije na nuna mishi ban San inda ya dosa ba inaga idan yaji uwar Bari *Zai furta*.
Ya fada bisa gado...... Ya kalli sama .
Sadeeq ya kalleshi an dawo fa!
Baka ga missed calls Dina ba?
Ina so ince ka amso Mana abinci *M&M*...... Abdul din fa ya daina dafa indomie ne?
Kai ubanka da indomie din Nan, Wai me yasa kake son gana Mana azaba?......
Ya kyalkyace da dariya azabace cin indomie?
Nifa bazanje wani *M&M* ba kawai muyi normal life na student kada mu banbanta...... Ubanwa
yace to baka sai Mana gida ba ka kawo mu hostel?
Ya Kara murmushi....ba za ka gane ba..
Ban ganewa wallahi....
Ranar da aka ganoka tabbas ka shiga uku.....in shaa Allah har na gama babu wanda zai sani,
Ya bude ledar da Bilkisu ta bashi kamshi ya doki hancin sa, rantsattsen agogo ne Mai tsada
cikin cover....... Kai ya tashi zaune.
Menene?
Bilkisu ta siya mun agogo wallahi.
Ya fada Yana daga Shi sama.......
Hmmm, wannan babbar kyauta ce, ka daina cinyewa Yar mutane kudi fa.
Yayi murmushi ya cire na hannunsa ya mayar da nata.......
Anwar a fidda maganar wasa ka dubi girman Allah ka sai Mana gida ko ka Kama Mana haya
mubar wannan kwamachalar......
So kakeyi nayi ma wata ciki..... Ya zaro ido.
Yes! Bari na fito maka a mutum sak!
Dan ubanka yanda Yan matan nan ke kawo man hari kana tunanin idan na ware baxasu bini
daki ba? Ko ni katako ne da Zan ga mace daga ni sai ita na....... Shikenan, ai shikenan next
year by now mun Fara bankwana ma.
Wayarsa tayi Kara ya dauka....... Ya Dan kalli sadeeq buga mun sixteen million times 42
please..........
Bayan ya ajiye sadeeq ya hado musu oat suka Sha sannan suka tafi masallaci.
Akan hanyar su ta dawowa yace sadeeq Ina son ka Sami Suleiman kace kada na Kara ganin
sa da Bilkisu....... Dalili?
Ya katseshi.

Haka Nan.....
Zancen banza kenan, haka kawai sai ka raba su babu dalili?
Yaron banza ne bana son sa.....kada ka tsani Dan mutane. Kowa yasan Shi mutumen arziki ne
idan kana da wata hujja ka fiddo kafin ka yanke zumunci.
Kana ganin wasa nake ko?
Wallahi semester din nan takunkumi Zan sakawa Bilkisu akan Shi saboda Shi kadai take kulawa
yaron Yana da mugun shisshigi.
Anwar! Anwar!! ..... Idan son yarinyar nan kakeyi........ Wai Kai me yasa baka ganewa? Dole sai
Ina son ta Zan Sanya doka akanta????
Ni Sona takeyi da take Sanya mun doka inabi?
Ko kasan yarinyar nan juyani takeyi kamar waina?( Masa ).
Kuna dai juya juna.
Kuma duk laifinka ne, ka zauna wurin kallon ruwa kwado yayi ma.....
Sadeeq Banda wani personal business da yarinyar nan da ya wuce friend, kawai bana son tana
kula Suleiman period.
Mtseew to ka jaraba ai Bilkisun ba bakuwar ka bace na tabbatar akan Suleiman tana iya
kyaleka kwata kwata...... Da gaske? Ya zaro ido.
Lallai dole naci uban yaron nan.
Sadeeq ya tuntsure da dariya, Allah gamu fareka.... Sai ka maida hankali toh.
Kai da Bilkisun duk munafukai ne kowa Yana fama da ciwo ya gwammace ya mutu da ya fitar
da cutar......
Kamar ya?
Kai ba bahaushe bane?
Ya doka tsoki....... inyamiri ne ni.
Yaushe Anas yace zai dawo?
Sunday.
Ai Kaine ka kwaso mu badon na shirya ba wlhi.
To ya zanyi?
Ya kalleshi ya zakayi? Wani ya tilasta maka?
Ya kada kafada tare da watsa hannu yace ko daya.
Zaku kaisu idan Kaya ne.
Ina tausaya maka ranar da wani zai maka shigar kutse......
Ku bakwa ganewa, yarinyar nan tana Sona fiye da duk wata yarinya da ke hauka a school din
nan, na rasa girman Kan da ya ke hanata *FURTAWA*....... Kai ba sai ka *FURTA* ba?
Mtsew....your are not well.
Ya kwanta bisa gado, ka dafa Mana shinkafa muci da miyar can Mana.yayi murmushi ka
canza maganar Kuma? Toh
Yanzu kuwa ya Fara Shirin aiki.

Ya janyo waya ya Kira Bilkisu,
Tana kokarin fere doya Aisha na warming Miya daga gefe Kiran ya shigo,
Ta ce hmm sannan ta daga .....
Hello, Ina wuni......

Ya lumshe ido Yana son gaisuwar ta yarinyar nan nada da'a sosai.
Lafiya, ya kike?
Qalau.
Keda waye nake Jin motsi?
Aisha,
Kuna meye?
Girki.
Me ye ne ?
Kai ai da gangan akai tamabayo......
Doya da Miya.
Zanci.....
Aikuwa baka cinsa sarkin roko....... Ya tuntsure da dariya har Yana sarkewa da miyau.... Aisha
ta kura Mata ido tana kallonta. Keda waye?
Ta bude Baki ta Mata alamar Anwar ne ba tare da sautin ya fito ba.
Rowa Zaki mun?
An maka........
Shikenan. Ki shirya anjima zamu je na siya Miki wani Abu cikin kudin Dana tara ko kuwa?
Ka dai ka siyo ka kawon ba sai munje tare ba.
Saboda me?
Haka Nan.
Karya kikeyi ba Kya son samarinki su ganki Dani........ Sadeeq ya kalleshi Kai da wa??????
Harar sa kawai yayi.
Kinji?
Ni nakeyin karya?
Eh, ko gaskiya Kika fada?
Kai Ni ban iya abinda ka iya ba..... Meye na iya Wanda Baki iya ba?
Neman magana...... Ina mamakin yanda ake cewa baka magana kana da jiji da Kai amma Ni
wallahi nace surutu gareka ga roko....... Ya Kara yin dariya.... Ke Kuma rowa gareki ko?
Rowar me?
Meye ka ce na baka na Hana?
Abinci.
Mtsew...tayi murmushi badai zance kazo kaci ba .
Muma ga sadeeq na dafa Mana shinkafa Mai dadi Ni na kawo Miki?..... Na koshi aci lafiya.
Allah kuwa..... Bana ci na gode malam .
Kai lazy baka dahuwa sai an dafa an baka ko?
Inji waye? Nafi sadeeq iya girki ko kina musu?
Eh.
In dafo in kawo Miki Zaki ci?
Noooo, ta fada da sauri. Yayi murmushi yarinyar da kinji akul.
Ta ce hmm.
Zan zo anjima kinji ko?
Okay.
Ki gaishe mun da Aishar Bari na dauki wata waya...... Ya katse Kiran.

Ta kalli Aisha Anwar case ne.
......... Gaskiya ai Yana bala'in yinki. Anwar Dan gadara Shi yake Kiran mace kinji yanda ake
surutun miskilancin sa kuwa?
Inaji amma nake ga kamar hada Sheri..... Wallahi da gaske ne.
Yan matan ne basu da zuciya. Kinga wulakancin da ya ringa yi ma khausar har kuka take
mishi.... Jakka kuwa ki Sami fareeda yarinyar nan Bata da zuciya wallahi..... Ke Aisha namiji
munafuki ne kedai baki sani ba ko Yana gewaye wa.
Last semester gab da za ayi hutu da yazo cewa yayi zance ya fito ya biyo wurina Kuma kema
kinsan kilan bai wuce mufeeda ko wannan dayar banzar Yar aji hudu.
Hmmm, kawai Aisha tace.
Salim bai dawo ba Ina Zan Sami aron mashin?
Sadeeq ya Fara maka mishi uwar harara ai taurin Kai da wulakanci ya Hana ka siya Mana sai
kaje ka hau kabu kabu......... Wohohoho..... Wai nawa mashin din yake in siya a huta?
150-200k wannan range din.
Mtsew...... Ka shirya gobe ka shiga katsina ka siyo Mana...... Ya buga ihu.
Ya shako wuyansa..... Koda wasa ka nuna inada alaka da hakan ubanka zanci..... Bazan fada
ba cika ni mugu...... Ya wuce har ya Kai bakin kofa ya waigo wane police station ne DPO ke
Zama a garin Nan??....... Ya zaro ido DPO? Lafiya meye zakayo wurin DPO?
Zan sa ya ma Dr Dan Musa warning da Suleiman akan Bilkisu.......... Wata muguwar dariya ya
saki munafuki karshen tuka tika tik... Yanzu ka *FURTA* mun abinda nake son...... Dawowa yayi
zai Kara shako Shi yayi bisa gado.... Allah ya baka hakuri.
Amma Ina baka shawara zaka tona asirinka a banza saboda zasu so sanin wanene....inji
waye?
Ba zai fada ba. *This is legal warning* ...... Ya fice da sauri Yana duba agogo.
Ya daga murya inzo in raka ka??....... Da ga can waje yajiyo Yana surfa mishi zagi.
Yana sauka achaba Aisha na zuwa zata tsallaka titi..... Aisha. Ya Kira sunan ta.
Laaa Anwar Barka da dare an dawo lafiya?
Qalau, je Kira mun Bilkisu..... Tayi jimmm sannan ta ce toh ta juya Shi Kuma yayi tsaye
maimakon yabi bayanta.
Tana tafe tana masifa, je Kira mun Bilkisu kamar wata barar sa..mtsew. Haushi na da Shi Sam
bai da manner of speaking Yana magana a gadarance da Isa na tsani wannan wulakancin
wallahi.
Tana wankin toilet ta shigo.... Kizo inji Anwar.
Ta dafe kirji...kin ban tsoro wallahi.
Ta harareta kawai zata juya..... Aisha Wai ya akayi?
....... Pad Zan jarbo Ina sauri ya ganni kawai ba wata magana Wai *je Kiran Bilkisu* irin yarinyar
nan wacce ya ajiye....
Kiyi hakuri kin dai San Hali...... Eh amma ki ringa kwatanta mishi wata rana Zan yankwana
Shi..... Kiyi hakuri dai, jira mu fita tare Dan Allah. Idan mun Gama Zan rakaki..... Wai injira ki
wurin sa?
Baki da hankali wallahi idan yamun wani dizgin inyi Yaya dashi?,
Bazaiyi ba, idan ya ganmu tare bazai...... Wallahi bazan je ba. Kina tare da Anwar seems like
you don't know him ko? Mtsew taja guntun tsoki ta fice abinta.

Ikon Allah. Kai Anwar nikam tawa ta sameni........ A yanda yayi rantsuwa tabbas idan ban fita
ba shigowa zaiyi.
Ta dauraye hannun ta, Daman Riga da wando ne jikin ta, ta zumbula hijab har kasa ta Dan
fesa turare kadan ta fito.....
Bashi babu alamar sa, ta juya ta waiga ba kowa, tana niyyar komawa ciki har ta saka kafa
daya ciki kiransa ya shigo...... Ta dauka hello....... Kin fito Kuma kin koma.
Ni Banga kowa ba kana Ina?
Bakin titi..... Bakin titi Kuma?
Eh. Ki karaso.... Meye zanyi a bakin titi?
Kina da gardama ne Wai? Just come here simple and short why are you arguing?? Ya kashe
wayar.
Wai ni zai mulka? Irin yanda yake juya Yan matansa Nima haka zai juyani? Ta doka tsoki ta
wuce ciki.....
Kofar taki buduwa daman tanayin haka some times, da kyar ta bude tana saka kafa Yana saka
tashi...... Ta firgita, ta tsorata sannan ta razana ainun. Gabanta yayi mummunan faduwa ta zaro
ido tare da bude baki zatayi magana .....ya riga ta, kina daukar maganata wasa ne?
An fada Miki akwai Wanda nake tsoro ko shakka duk dutsinma?..... Babu, Dan girman Allah kayi
hakuri muje tayo hanyar fita yasa hannu ya maidata... Ban gama ba....... Sai kawai tayi kneel
down na tuba Dan girman Allah muje waje idanunta sun Fara kwal kwal alamar zata Fara
kuka...... Ya buga tsoki ya juya. Ta Mike da sauri ta janyo dakin ta datse ta bishi da gudu.
Tafiya yakeyi yaki tsayawa.....
Ta Kara sauri ta tari gabansa Wai Ina zame je ne saboda Allah?
Me yasa kika zabi bani wahala da bin yarda nake so?.
Kayi hakuri wallahi daddy ya ce baya son fitar dare Anwar kada a sanar dashi zanji Babu
dadi....... Da Yan iska yake nufi ni Kuma ba Dan iska bane...... Ikon Allah ba haka nake nufi ba.
Okay to wuce muje..... Zan siya miki sweet ne da kudin aikina...... Wallahi da wasa nakeyi maka
kawai na fada ne..... Ni Kuma da gaske na dauka saboda haka wallahi sai munje.
Shikenan, suka jera.
Tayi murmushi ko ke fa? Amma ke komai sai anyi tsiya tukun.
Me kike so?
Duk abinda ya maka.......
Kinga agogon ya mun kyau? Ya nuna Mata .
Um, kawai tace .
Na gode fa, Allah ya Kara dalili.
Amin.
Zaki ci nama suya?
A'a na gode.
Kaza fa?
Bana ci.
Shawarma...... Nifa bana bukatar komai.
Lallai yau zamu kwana a titi...... Ta kalleshi da sauri. Ya bita da ido Daman so kawai yakeyi su
hada ido..... Allah matukar Baki ce ga abinda Zan siya Miki ba haka zamu kwana...... Biscuits.

Tayi saurin cewa. Muje ka siya mun biscuits.
Ya yi Yar dariya ko kefa?.
Napep! Ya daga murya. Shi Kuma ya tsaya. Ta kalleshi da sauri...... *Abis supper market*
zamu je Nan kadai Zaki Sami biscuits din da kike so..... Anwar, biscuits ko anan akwai Dan
Allah...... Mtsew Allah ya raba ki da gardama. Muje ko in daukeki...... Kafin ya rufe Baki har ta
tsallaka titi. Ya dunga mata dariya. Ta turbune fuska..... Gaskiya bana Jin dadin abubuwan nan Anwar
bana son abinda kakeyi mun..... Kiyi hakuri.
....Ina zakuje ne?
*Abis supper market* Anwar din ya fada Yana kallonta .
Ta harareshi kallon Kuma na menene?
Wallahi na tsani kallo rayuwata...... Na sani. Yace Yana dariya.
Ka sani Kuma bazaka daina ba?
Ya kyalkyace da dariya Nima na tsani kallo fa ta Yaya Kika San Ina kallon ki?.
Yanzu Ina amfani wani ya ganmu a Sanya Ni a bakin fudma ace har mun Fara fitar dare sai
ma a ba abun wata fassara wallahi. Mtsewww.
Fassarar me?
Ta mishi banza.....
Kinji?
Ta harareshi, ya kamata ka daina zuwa mun da dare gaskiya bana iya masifar Yan matanka
kullum sai an mun zobe kamar za a dakeni...... Basu iyawa. An fada mun tsoronki sukeyi tun
lokacin da Kika Mari kawar mufeeda...... Au ka sani ma ashe.
Yap. Yace Yana murmushi.
Dai dai sun kawo ya Mika mishi kudin suka shiga.
Ranka ya dade..... Ma'aikatan suka taso .
Ta kalleshi da alama regular costumer ne Kai.
Murmushi kawai yayi.
Kije ki zabo biscuits din da kike so.
*Short bread* daya is okay..... Ke bana son gidadanji kije ki kwashi Kaya kinji ko idan kina Jin
kunya Kuma muje na Taya ki ya zungureta da hannu.... Kamar ta bude kasa ta shiga don kunya
yanda aka Mata ratai da ido.
Sam ta kasa nuna ko daya...... Ya Kira yaron ya ce duk layin Nan sauko shi, tayi Yar dariya
tunanin ta zolaya ce yakeyi.
Da sun Kara gaba yaga wani kalar biscuits din sai yace wadannan ma duk safko dasu.......
Wasa wasa ta ga abu da gasken gaske bata San lokacin data janyo Shi baya ba *Kana
qalau* kuwa?.
Ya Kai fuskarsa daidai saitin tata kamar zai yi kissing dinta...tayi baya da sauri yayi kasa kasa
da murya *Yi kokari ki dizga ni*..... Kamar zatayi kuka ta kalleshi ka dubi girman Allah..... Me
yasa kike son yi mun irin wannan magiyar Mai tsada?
Ya katseta hannuwan sa duka a kirji.
Ka ce su mayar da biscuits din can..... Wallahi duk wadanda suka sauko bazasu koma ba, idan
Baki sa hannu kin dauki Kaya ba Zan siye duk biscuits din dake super market din Nan...... Ta
zaro ido....

Kamar me Zan Dauka?
Na bani ni Bilkisu kawai take nanatawa a zuciya...... Duk abinda kike so perfumes, cosmetics,
drinks... everything.
...... Dabara ta fado Mata, okay na amince amma kaga Yanzu duk Ina dasu ka Bari semester
tayi nisa Zan biyoka...... Yau fa sai kin dauka Kuma zamu Kara dawowa hakan ma ba laifi bane.
Kamar ta daura hannu a ka ta yi ta ihu.... Ta kalli yaron kaga zo daukon *women million din can
please*, Kuna da Apple juice? Eh hajia Mai sanyi ko marar sanyi..... Kamar ta zageshi don
takaici, ta daure tace bani marar sanyi.
Suka Kara zagayawa ta dauki robar chewing gum banana.
Ta kalleshi wadannan sun isah na gode.
Are you sure?
Um. Tace da kyar.
Biscuits din da yasa aka kwaso anata packaging a kwalaye

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login