Showing 81001 words to 84000 words out of 94796 words
Chapter 28 - WA ZAI FURTA Book Complete by Zainab Dahiru Wawo.pdf
Mata hijab ya figi hannunta suka fito....
Sadeeq shida Aisha kadai a Falon Maryam tayi ciki abinta..... Ta kalleshi idan ka Gama muna
waje.....
Kanta a kasa ta kasa dagowa ta sanyata jikin mota ya matso kusa da ita sosai kamar zasu
hada jiki ya Fara Mata magana a hankali.... Ina so ki sani ni ba katako bane,in shaa Allah bazan
kasa ba daddy mamaki ba Amma da sharadin sai kin daina wannan kunyar kin sakemun
jikinki..... Ta runtse ido ya sunkuya Yana lekenta..... Wannan kunyar taki wallahi tana Sanya
mun sha'awar ki Bilkisu tabbas idan Baki saki jiki Dani ba to I have no choice but to sleep with
you..... Ta juya ta kife Kai ga mota *na shiga uku ni Bilkisu*..... Ya juyo da ita, matsalar bani da
kunya ko a gaban waye Zan iya taba ki don haka kina da aiki ja don duk ranar da na bukaci
taba ki Kika Hana kamar yau to ki sani Zan...... Anwar please.... Ta fada tare da runtse ido. Ya
kyalkyace da dariya... Sadeeq ne ya fito Shi kadai ba Aisha .... Ya kallesu to pigeon muje ko?
..... Sadeeq yarinyar nan ta fiye kunya fa tana takurani da yawa...
Tayi sukutiiiii, Sade yayi murmushi Bilkisu ya da kunyar miji Kuma?
Ya zagaya ya shige mota.....Yana fadin kasan baka Gama ba ka fiddoni..?
Ya kalleta sadeeq bai gaji ba ko mu koma?.... A'a kuje Dan Allah...ya Kyalkyace da dariya
matsoraciya kizo mun da dumamen school gobe zanci a mota kinji ko?
Ta Dan saki ajiyar zuciya ta ce toh.
Ya langwabar da Kai Bilkisu bana son tafiya wallahi.... Ta ce ya Salam! Amma a zuci...
Zan say kawo Miki irin pad din kamfanina kiyi amfani da ita ance tana da kyau sosai idan Bata
Miki ba Kinga Dole a canza sabuwa..
Ta mishi banza.
Yayi murmushi kinji?
Um, ta ce.
Ko Zaki bini..
Ta ingijeshi ta kwala. da gudu ya tuntsure da dariya ya fada mota...... Sadeeq anya Zan iya
zuba ma yarinyar can ido?
Ka rufa Mata asiri Dan Allah... Ya fada Yana Yar dariya.
Amma fa tana da tarbiyya sosai could you imagine ta tsorata simply don na yi hugging dinta?
.....wallahi Anwar Bilkisu na bani mamaki ta fita daban daga cikin Mata maganar gaskiya
wannan lokacin kafin ka sami yarinya Mai kamun Kai irin ta Yana da wahala kasan abinda ke
bani mamaki?
Ya girgiza Kai..
Yanda she's fully hijabite wallahi kaga fa tun zuwan ta school din nan Bata taba Sanya gyale ba
Bata shigar banza ga addini sallah Bata wuce ta cikin jam'i naji ana rade radin ita za a ba
Amira....
Ya danyi murmushi, wallahi har tausayi ta bani Yanzu duk jikinta ya tsinke da rawa sadeeq ta
tsorata da nace zanyi kissing din ta wallahi hada kuka....
Ya kyalkyace da dariya ya ce baiwar Allah.
Sai ka lallaba ta ka Kara daurewa kada ka janyo ma kanka jangwam ta rikice maka Kuma......
Naga alama fa akwai rikici .
Kasan Aisha ta nuna tana da interest akaina?
Ya kalleshi haba???
Ya Dan Bata rai, no Bata mun ba, Ina son mace mai Jan aji nafi so na Sami mace wacce Ni ke
binta tana ban wahala ba ita ce zata ringa zakewa ba..... Kamar Bilkisu kenan? Ya katseshi
Yana dariya... Yayi murmushi Anya Zan Sami kamar ta at least ma ko wacce bata kaita ba.. da
tana da kanwa ko Yar shekara biyar ce Allah da Zan jira..
Suka kyalkyace da dariya.
Ya zuki iska ya fesar.... Gaskiya Ina bukatar matata .....ka rufa mata asiri Anwar Dan Allah
kaifa da kanka kace zaka bada mamaki...... Kai nifa ba katako bane ko?.
Eh,but at least ka duba yanayin idan ta Sami ciki fa?
Shine me? Ya harareshi, Ina nufin kaga na farko tun a laulayi idan Mai Shan wahala ce an Sami
matsala musamman ga karatunta, kaga automatic spill over, na biyu bazata taba fita zargin
mahaifan ta ba cewar ita ta sanar da Kai akwai Aure bayan an gargadeta da tayi shiru,na uku
karatu da goyo Anwar is not easy akalla.... enough jor.... Ya daga mishi hannu... Amma Zan
ringa Dan romancing dinta gaskiya ban iya daurewa..... Romance din zai ringa Sanya maka
sha'awa akwai ranar da wallahi zaka kasa controlling kanka tunda kamar yanda ka fada din Kai
ba katako bane...... Ya Allah !!! ya fada tare da maida Kai ya kwantar bisa sit, sadeeq meye
dabara?
Ina ga mu rage ziyarar su gida , ka ringa tsareta school duk maganar da zakuyi nasan idan
kana ganin jama'a bama zaka kawo komai a ranka ba..... Nawaoooo,!!! Ya fada tare da tashi
zaune.. gaskiya nidai an kwareni ....
Sadeeq ya kyalkyace da dariya rawar kanka ta janyo maka....... Ya Kai mishi duka, naje nayi.
Yanzu dai ai daga wannan semester din saura daya ko?
Biyu dai....
Ya katseshi ...ya ja dogon tsoki kawai ya kwanta tare da runtse ido. Sadeeq ya bishi da kallo
Yana murmushi......
Wai ya mufeeda ta hakura ko?
Ya yatsuna fuska, ance har yau ta kasa shigowa school saboda kunya..... Maganin ta kenan...
Ya tashi zaune Yana Yar dariya kasan ni duk wake bani dariya?
Ya ce sai ka fada.
Helen, tunda akayi case din nan Yanzu ko layin da nake zaune Bata bi kasan arna da shegen
tsoro....... Suka kyalkyace da dariya.
Bilkisu ta zabga uban tagumi har lokacin jikin ta bai daina rawa ba, kirjinta kuwa sai dakan
uku uku yakeyi, *Na shiga uku ni Bilkisu Wai kiss* .... Nikam dama na hakura da Abujan da
Yanzu Ina can zamana qalau..
Ta runtse ido lokacin data tuna ya zagayo da hannayen sa bisa kirjinta ya kwanto jikin ta......
Tsikar jikinta tashi Yarrrr lallai akwai damuwa .... Ta bude ido su maza basa da kunya ko
kadan....
Haka ta kwanta tana ta juye juye da ta tuno Shi da yanda ya ringa Mata sai ta kudundune jikinta
ta boye kanta cikin filo.....
Murjanatu cikin masu aikin gidan ta Kira da sauri ta ce maza ta dumama tuwon jiyan kafin ta
fito wanka.....
Yau taga amfanin nikaf, saboda da Babu ita tasan bazata iya kallon Anwar ba.....
Tana shiga ajin anata raba test din da Richard munafuki yayi. Two over ten, three mutum biyu
keda 5 su chinayye...... Itama two taci, Anwar ya saka tashi aljihu kawai lokacin da ya buda
yaga yaci nine....
Ya kame Baki na shiga uku.... Mutumen nan wallahi mugu ne daman yafi so mu fadi.... Sadeeq
na bayanta ya ce nawa Kika ci Bilkisu?
Ta mika mishi 2 ce shegen kaifa? Yayi murmushi three..... Anwar yayi fit ya fizge takardar ya na
zagayo ya kalli root dake kusa da ita yace ban wuri.... Ta kwashi takardun ta ta koma sit din da
ya taso.... Basai ka fizge ba two ce kai nasan nine kaci don ma baya bada cikon da tabbas ten
zaka ci....... Inji waye ya fada Yana murmushi....ta zumburo Baki nidai fiddo naga Ni...... Ya Mika
Mata Yana murmushi.... Kamar jira ake taje hannun Bilkisu aka Fara rokonta ta bada ayi
snapping.... Ta Mika musu.
Mutumen can na daga mun hankali bana kaunar Dan iska.... Yayi dariya Kuma duk da Haka
Baki taba faduwa course dinsa ba ko?
Ta harareshi Amma da yake akwai nikaf bai gani ba tace da hawan jini, da na ruwa ko?,ya
kyalkyace da dariya, toh eh Mana,duk sai ya gama tayar Mana da hankali tukun Kuma *E* din
nan dai ce ko *D* ..... Ina laifi ai yafi carry over ko?...... Zatayi magana malamin ya shigo..... Ya
fiddo waya ya dan Mata magana a hankali..... Shiga WhatsApp... ```kinyi barci jiya?```
Ta maida mishi da ```me zai hana?```
```ni kuwa kasawa nayi saboda tunanin ki```
Ta kasa cewa komai
```kinji```
Ta ce ```Hmmm```
```smiles kin zo mun da tuwon?```
```yana mota```
```ina zamuje naci```?
```ina fa, anan waje ko?```
```Bana son waje is too open let's go to the field or new lecture rooms side I need quite place
okay?```
Tayi shiru.
``` kinji ko?```
Ta maida hankali gun lecture.... Ya zunguro ta da hannu ....dole ta rubuta mishi
```naji```
Yayi murmushi.
``` sai Anja mun aji?```
```Ka bar mu muji lecture Anwar```
.....```ke ni ban wani ganewa ki Bari kawai zamuyi tutorial```
```Hmmm```
Malamin na lura dasu,
Yana gamawa ya ce tear a sheet of paper write your number only......
*Mun shiga uku ka ga abinda nake gudu ko?*
Ya sumke Yana Mata dariya.
Kina da black biro?.....
Banda Shi ta fada cikin tsiwa.
To kiyi sauri ki wanka ko na rubuta miki,?
Kawai kayi na kwafa idan Kuma ya tayar Dani shikenan.....
Yayi murmushi....
Ya Fara dictating questions based on what he discussed.
Ta Kara tsure Mata tana magana kasa kasa ... Wallahi kana ja mun wannan semester din.....
Yayi shiru Yana murmushi Yana rubutu.
Tana kokarin Jan layi ya turo Mata takarda har ya Gama Daman two questions ne. Ya ci gaba
da rubuta nashi Yana layin karshe kawai malamin ya ce hands up...... Amma sai da ya karasa
Kai Anwar karshe ne......ta galla mishi harara cewa zakayi kasan abinda ka taka, yayi dariya to
meye acikin nan cubweb theory din ke da wahala?
Ta ce hmm, duk ya Gama birgeta, gunguni kawai ke tashi cikin ajin.
Yana zuwa layin ya karba ya dan harari Anwar din ya wuce ....
Yana fita sadeeq ya taso kaga mutumen Nan ko?
Yayi murmushi bana fada ma ba, gaskiya naji dadin bayanin jiya... Ta kalleshi da sauri au
Daman kunyi wannan din?
Sadeeq ya ce wallahi jiya kamar wasa ya koyan Kinga da yau naci kaniya ta...... Ta ce hmmm
kawai,
Anwar ya kalleta kema yau zamu Fara karatu kiyi hakuri..... Na fito karfe hudu kenan?
A'a ki Bari sai after Isha zanzo gidan....
Gabanta ya Fadi, na marecen nake ga zaifi ko kuwa?
No!, Bana son yawan fita inba lecture akeyi ba, kawai ki jira zanzo kinji ko?
Toh, ta ce a hankali.
Ya Mike muje....
Ka Kira sadeeq muje yaci..... Zan rage mishi ..
Anwar meye Haka? Wasa tare ci banban.... Ya danyi dariya yarinya kawai kice kina son wani
kusa kada muje na cinyeki Ni kadai.... Laaaa ni ba Haka nake nufi ba..... Sadeeq!!! Ya kwala
mishi Kira....
Ya karaso Yana murmushi ya akayi?
Tuwo aka kawon Wai bazan ci ni kadai ba sai tare da Kai... Yawwa Bilkisu Allah dai ya biya kin
San kuwa yunwa nakeji wallahi.... Ya banka mishi harara Kuma Kai baka wuce tayi ko?
Ban wucewa kin ganshi Nan ko ruwan zafi bai iya dafawa .... Duk suka kwashe da dariya.
Ina zamuci tuwon?
Field... Anwar ya bashi amsa.
Okay kuyi gaba Zan biyo ku da mashin.
Ungo nidai kaja motar Dan Allah..... Ya wurga mata harara ya fada gaba ya zauna kawai.
Dole ta shiga ta ja motar a hankali.... Duk inda suka gitta sai an bisu da kallo.. ba karamin kashe
zuciyoyi sukeyi ba a school din suna bada *Plus*
Sadeeq na gama ci yabar wurin yace zaije aski.
....me Zaki dafa mun da dare?
Abinda kake so, ta fada..... Ke daga nikaf din nan na ringa ganin idonki.... Ya karasa maganar
Yana yakice Shi .... Ta yi kasa da Kai tana murmushi..... Ya shafa gefen fuskar ta Yana fadin
```lemme see this baby face``` ... Ta to dariya ta ce kaiiiiiii.....
Yes, ya fada Yana Kara kallonta,
Me Zaki dafan?
Abinda kake so, ta Kara maimaitawa.
Kiyi mun chips mana.
Toh, ta fada a hankali.
Babban fridge din nan Kinga akwai kaji da naman rago da kawuna ko?
Um, ta ce.
Idan kina bukatar kifi kiyi mun magana a kawo Miki Shi kinsan baya da dadin ajiya saboda karni
ko?
Gaskiya fa.
Me yasa baki taba rokona wani Abu ba?
Ta kyalkyace da dariya kaiii Anwar... Yabi fuskar da kallo..... Yana murmushi.
```Bilkisu kin San cewa ke din ta daban ce kuwa?```
Na sani Mana... Ta fada tana murmushi.
Ya akayi kika sani.....
Tayi dariya saboda *Bushara na Sona*..... Ya kyalkyace da dariya for the first time kin kirani
*Bushara* Dole na Miki kyauta yau Zan canza Miki motar Nan...... Dan Allah ka barta Ina
sonta....... Karki damu ai ba rokona kikai ba, Ina son ki bar tarihi FUDMA a ringa kwatancen
mu..
.. Yanzu ma anayi.
In tambayeki???
Ta ce um,
Yaushe Kika Fara Jin kina Sona?
Ta yi kasa da Kai tana dariya.....
Kunya kike ji?
Ta Kara murmusawa..... Okay rubuta mun ta WhatsApp..... Ka Bari Zan fada maka..... Yaushe?.
Tayi shiru tana murmushi.
Kunyar ki tayi yawa Bilkisu....
Muje ki ajiyeni gida .
Ta tayar da mota,
Har ciki ta shiga yau, ya ki fita ya tsareta da ido sai kuma ya ce affff.... Ki jirani Ina zuwa please
ya shiga gidan da gudu.....
Ta bishi da kallo tare da sakin ajiyar zuciya a hankali....
Ya dawo dauke da Yar leda Mai kyau a hannunsa, ya leko ta taga, it might be Baki zo da
English wears ba ko?
Kisa wannan anjima.... Ta zaro ido...
Ya Kara sunkuyawa ba abinda Zan Miki Allah kuwa kawai Ina son ganinki cikin su matsala daya
za a Samu idan kika Fara wannan kunyar taki lallai Zaki janyo ma kanki na taba ki.... Ban Baki a
boye ba, just wear it and feel free okay????
Ta daga Kai a hankali.... Yayi murmushi that's my babe...... Tayi baya da motar ta fita a hankali
duk jikinta yayi sanyi duk da bata ga kalar kayan ba.....
Yabi motar Yana murmushi... Ya ce tsoron ta yayi yawa gaskiya. Ya zuki iska ya fesar ya wuce
ciki.
Ta zabga uban tagumi daki ita kadai ta zuba ma kayan ido, doguwar riga ce Mai kame jiki da
hannun vest, daga kasa akwai tsaga har kusan guywa maroon ce Dana da wani katon belt
bisa kugu, da jefi jefin flowers jikin rigar red. Aisha ta taimaka Mata sukayi farfesun kaji,
sannan suka soya chips din kaskon karshe ta shiga tayo wanka tabar Aisha ta karasa ta feshe
jikin ta da turaruka masu kamshi ta gyara gashinta Amma ta mishi gammo ta nade tare da
zumbula katuwar hijab.... Tana fitowa taci karo da Aisha bakin kofa zata shigo ....Wai duk meye
kikeyi haka ga Anwar can yazo.... Gabanta ya bada ras!.... Shida sadeeq ne?
A'a Shi kadai ne gaskiya... Kin saka ma coconut juice din ice ?
Eh Yana fridge muje na Kama Miki.... Barshi baya son haka, ta katse ta.
Yana zaune kasa ya Mike kafa Yana ta latsa waya sanye da farin boyel Mai laushi kansa ba
hula.
Ta ajiye plate din chips din da cooler farfesun ta ce ... Ina wuni?
Ya Dan dago sai Shan kamshi yakeyi ya ce ... Bilkisu ya kike?... Na Sanya ki aiki ko?
Ba komi, ta fada tare da mikewa... Ya bita da kallo duk kamshin turarenta ya kashe Masa jiki.
Ta dawo da sauran kayan ta zuzzuba mishi Yana satar kallonta da wutsiyar ido, da tazo
dagowa sai ya basar.
Tana gamawa ya tura Mata Wanda ta zuba mishi ya janyo sauran da ke cooler gaban Shi ya
ce wallahi sai kin cinye duka Koda zakiyi amai.... Ta dago Kai da sauri ,.. ya hade girar sama da
kasa yasha mur ...
Dole ta dage ta Fara ci sai da tafi Rabi yaga da gaske turawa takeyi sannan ya ce mikon
dankalin na Kara bai isheni ba.... Ta tura mishi da sauri ya cinye... Peppé soup din Nan yayi
dadi fa.
Jeki Kai kayan kizo da books din da zamuyi ba dadewa zanyi ba.....
Ta mike da sauri ya bita da kallo sai kawai yayi dariya.... Tana dawowa ya Kara hade fuska....
Kina jira na ce ki cire hijab din????
A hankali tayi sama da ita.... Tsikar jikinsa ta bada Yarrrr, ya hadiye wani tsinkakken miyau sai
kawai yayi kasa da Kai ya Fara budo littafin da ta Miko....
Tunda ya Fara bayani bai dago ba ..... Tun tana Jin kunya da tsoro har ta fahimci Sam ba ta ita
yake ba gashi sai wani Shan mur yakeyi.....
Tana ganewa sama sama har sukayi course biyu.
Duk ta makure... Ya dago Kai kina ganewa kuwa?
Um, ta ce da sauri, saura kadan yayi dariya.
Yau barci nayi da Rana sosai...
Wai kin San cewa an gano nine Bushara school din Nan?
Ta danyi murmushi, nasan za a gane Kam...
Saboda me Kika ce haka?
To Anwar ko wadannan kattin da ke Bina da wadanda ke gidanka yaci asan Kai waye.... Ya
danyi dariya inji waye kawai tsabar sa ido ne.
Naji class din mu za a yi jacket da shirt na graduation Ina ga ni Zan dauki dawainiya ko?
Ya dai kamata. Ta fada kanta kasa.
Yayi murmushi, Nima Ina son yiwa yaran Nan alheri me kike ga Zan raba musu?
Kudi, ta fada.
Kudi Kuma?
Eh, Mana kudi zaifi saboda kowa yasan meye damuwan sa Kuma kudi ke maganin komai ko
kuwa?
Kuma fa, Shi yasa nake sonki wallahi saboda kina da hankali...kamar nawa Zan basu?
Yanda kayi niyya Kuma ai kafi kowa sanin iya karfin ka.
Ya kura Mata ido, ki fada mun Mana ai Yanzu shawara mukeyi nida ke ko?
Ka dai kiyasta Ni ban San nawa zance ba ko kayi shawara da sadeeq..... Da ke zanyi. Nawa
kike ga ya Dace na raba masu?.
Tayi shiru... Ka Bari zanyi tunani toh.
Okay, sai na jiki tashi ki karon