Showing 66001 words to 69000 words out of 94796 words
Chapter 23 - WA ZAI FURTA Book Complete by Zainab Dahiru Wawo.pdf
da ita da sauri, kafin ki gudu Dan Allah gobe kada ki Sanya
mun hijab din nan kuma kiyi mun girki da kanki Zan zo around 10:00am kinji ko?
Ki ce b lefe na kawo ba, hasafi ne saboda Ina son ki.... Ta zame yayi saurin rike hannun ta ki
jira na Baki kudin dinki Mana ..... Ka barshi nidai... Bakya so?
Ta daga Kai..... Da gaske bakya so?
Um, tace a hankali.
Yayi Yar dariya kudin ke Baki so ko Ni?
Kudin ta fada tana sim sim da Kai.
Yayi murmushi Ni kina Sona Kenan?
Ta yi alamar fizge hannunta.... Ya rike gamm. Kice inji Mana kina Sona?
Ta yi kasa da Kai ji takeyi kamar ta bude kasa ta shige ta huta.. ...ya Kara dariya sosai ohh ni
Anwar Ashe akwai ranar da bakin nan zai mutu?
Ai Dana San wannan kalmar ce zata sa in Sami saukin tsiwa da tuni na Gaya Miki saboda na
Dade Ina dakonta.......
Idan daddy ya Baki zabin auren mu kice kinfi so ayi kafin mu Gama school....... Lokacin ne ta
banka mishi harara da sauri ta kawar da Kai.
Ya Kama dariya ya figi hannunta zo kiyi mun rakiya naga alamar nema kikeyi ki gudu ciki ko?
Ta biyoshi a hankali yasa hannu ya fiddo rafar kudi ya ajiye hannun kujera idan kin shigo ki
wuce dasu na dinki ne....na gode. Ta fada a hankali. Tayi murmushi ya ce my pleasure dear.
Ta Dan harareshi ya tuntsure da dariya shin na Riga na *FURTA* ai to boye boye name?.
Suka fito tayi saurin fizge hannunta ya Kama murmushi Yana fadin ke dai Yar kauye ce......
Allah yayi?
Sadeeq ya taresu.
Allah yayi sadeeq yau kwana ta saka ni sai da na *FURTA* Ina son ta...... Sadeeq ya you
firgigi ya ce waoooh *Anzo wurin kenan*.... Duk suka bushe da dariya ita ko sai murmushi
takeyi kasa kasa...... Munafuki ai duk Kaine tun farko kayi ta wahalar da ita... Shin ai nadai
FURTA gobe Zan dawo *Zance* ya bangajeta da kafada ko Bilkisu??? Ta galla mishi harara suka kwashe da dariya.....
Kiyi mun tuwo goben.... Ya shiga mota tana tsaye har suka fice gate din....
Wai da gaske ka furta kana sonta?
Wallahi kuwa, sadeeq rigimar Bilkisu bana iya daukar ta, ta tsareni lallai sai tasan wanene
Ni...... Saboda me zaka boye Mata Wai?
Ai na fada.... Amma fadar sai ta tsorata Kuma. Na rasa me take so, Kuma Wai ita ya zata fada a
gida wace amsa zata bawa su daddy....na ce kice *Ina son ki* saura kadan tayi penting .....suka
bushe da dariya...... Amma ka Mata gatsal! To ya zanyi da ita? Kaga yanda ta nemi ta firgice
mun? Banza finally ka furta dai.
Yayi dariya *Anwar ya furta* naji tsoro yarinyar Ina son ta saboda class wallahi.....gidan sa dake
*Minister's hill* suka nufa.
Mommy..... Mommy ta Fara kwada Mata Kira tana Hawa sama.
Tana faman shirya jaka ta shigo dakin, mommy Anwar fa ya kawo Kaya da yawa ..... Wane irin
Kaya?
Ina daddy?
Sunje sallah kasa.
Wane irin Kaya ne ya kawo.
Jikunkuna ne set hudu.... Ta kalleta da sauri jakunkuna? Na menene????
Ta sunkuyar da Kai ta sunga Mata kudi Kinga Wai su Kuma nayi dinki...... Duk Akan me?
Ta Kara kasa da Kai, ya ce tsaraba ce ya kawo mun.... Saboda???...... Ta Kara katseta da
sauri.
Ya ce Yana Sona ne???
Muje naga kayan, bazaki ce mishi daddyn ki ya hana karbar kaya ba?
Wallahi duk abinda na kokari in sanar dashi bai yarda mommy.
Wohohoho ta fada tare da rabka salati...... Amma kin San daddyn ki zaiyi fada ko?
Mommy Anwar Shi ne *Hamza bushara*..... Mun sani. Ta ce a takaice ta zaro ido Kun sani
mommy?
Yes, ta fada tare da wucewa tana fadin jekiyi sallah nasan fada ne yau duk sai mun Sha ni da
ke.....
Ta falon ya shigo Yana ganin kayan ya kwala ma Bilkisu Kira.
Ta fito da gudu gudu.....
Wadannan kayan fa? Ta sunkuyar da Kai, Anwar ne ya kawo su daddy.
Na menene?
Ya ce tsaraba ce kada yazo hannu biyu....
Saboda me?
Tayi jimmmmm kafin ta ce *Wai Yana Sona ne* yanayin yanda ta Fadi maganar kamar Yar koyo
mommy ta shigo ya kalleta Kinga Kaya?
Hada kudi....
Ya kalli Bilkisu ke kina sonsa?
Tayi shiruuuu kinji mamana kina son sa?
Tayi kasa da Kai kawai.... Yayi murmushi kina son sa kenan.
Ki mayar mishi da su kice bana karbar irin wannan kyautar idan har da gaske yakeyi ya turo
iyayensa.... Ta dora hannu saman Kai.... Daddy bayar Dani zakayi haka da wuri ta kurma ihu
tana kuka.
Ya yi Yar dariya, to tunda kin Sami Wanda kike so me ake jira..... Nidai kada a turo...ke bama
son rashin wayo.
Turowar an fada Miki Yana nufin za'ayi Aure?
Hakan zai nuna idan da gaske yakeyi sai a ajiye magana.
Ta danyi shiru alamar ta gamsu.
Ya wuce Yana girgiza Kai Yana murmushi,
Mommy ta kalleta tana hararar ta, wannan koke koken ba komai zai janyo Miki ba sai raini
wurin Miji. Komai ke sai ki bare Baki saboda kina ruwa ruwa.... Mtsew ta ja tsoki.
Wannan rawar Kan da Anwar keyi inba auren ba meye zai kamance ku?.... Mommy..
Yi min shiru, Ina ce Nan Kika diririce Kika firgice saboda yayi fushi da ke ko?
Ta zumburo Baki kaiii mommy....... Ke arrr kilibabba.
Ta wuce , ta Mike ta bita da gudu mommy yace zai zo gobe by 10... Sai kije ki fadawa su
Rahina don su shirya mishi kin dai San ba Mai sauko Dani da safe ko?
Mommy cewa yayi ni Zan girka baya son nashi...... Sai kawai tayi dariya tace yaron nan hooo.
To ya kyauta ma kansa sai kiyi asubanci saboda na sanki da shegiyar nawa da duminiya,
Bilkisu za a Fara wa miji hidima..... Kai mommy ta bita tana shagwaba....
Ta kyalkyace da dariya. Ai munji dadin zuwan sa saboda kullum daddynki cikin waya yakeyi
Yana jiyo labarin badakalar ku.....kamar ya mommy??
Tayi Yar dariya akwai wadanda kebin movement dinku kullum...... Ta zaro ido yasan Anwar na
zuwa gurina mommy???
Tayi murmushi har ciwon cikin da kikayi ya je har cikin dakin ki,sannan ya balla Miki kofa.... Ta
zare ido na shiga uku na... Ke dakata, tunda bai nuna Miki ba wallahi kada ki nuna kin sani
Babu ruwana.... Cikinta yayi kulululu ta hadiye miyau kut!.
Mommy Dan Allah laifina ne? An fada mishi Nima bana son haka ko?
Ina Jin abinda yayi saving din ki kenan....
Ta saki ajiyar zuciya kaiii Anwar case ne.
Ko bude kayan basuyi ba yanda suka ajiye haka aka barsu a wurin.
*WASHE GARI*
Karfe bakwai tana kitchen, daddy ya fito zai je office ya leka... Bilkisu a bani abinda ya sauka
na jiyo kamshi ko Anwar din kawai keda shagalin?... Ya karasa maganar Yana murmushi.
Kaiii daddy ta fada cikin Jin kunya....
Har ciki ya shiga Rahina nata fere dankali, saratu na grating kwakwa, ya kallesu yau aiki ya
karu ko?
Iyye hada kaza haka?
Ya bude oven.... Ta rufe fuska lallai yarinyar ashe catering school din bai tashi a banza ba...
Menene can?
Wipping cream daddy... Zakiyi cake ne?
Na Gama gashi can ma.... Ya sa hannu ya dauki daya ya Kai Baki..... Um um..ya naji wannan
kamar ba irin Wanda ake Mana ba?...... Kai daddy ta Kara fada yayi dariya....
Mommy ta shigo ga break din can fa.... Zo kiga sonkai Bilkisu na hadawa Anwar gara ba irin
..... Kai daddy... Eh Mana.
Ta matso iyyeh lallai Shi yasa baji gida ya Fara daukar harami.... Ta bude tukunya.. hada Kan
rago?......
Kai Kai Kai daukon kwano Shi zata zuba mun ja'ira..... Duk suka kama dariya.
Rayuwa irin ta gidan su Bilkisu tana da ban sha'awa......mommy ta kalli Rahina, yau taku ta
sameku ko?.... Abinda na fada Yanzu kenan.... Daddy ku je falo Zan kawo muku nidai... Duk
suka kwashe da dariya... Mommy tace komai Zaki debo Mana ko sai ankai wa Anwar din nazo
na ce Zan Dauka..... Kaiii mommy Wai ya Zan ce baza ku ci ba ???? Suka fita suna dariya hannun daddy rike da cup cake Yana gutsira...
Ya kalli mommy in shaa Allah tarbiyyar da muka ba Bilkisu bazai taba Sanya muyi Dana sani
ba.... In shaa Allah.
Ina ta fada akan catering school din nan Kika dage Kinga Yanzu amfanin yazo ko?
Ai na fada ma Kuma wallahi cewa yayi nata yakeso baya son na Yan aiki kaga Idan Bata iya ba
zai aureta Yana sonta Amma can gaba matsalar dole ta taso.... Yaron Yana da rawar Kai akan
Bilkisu hakan na bani tsoro, ya kasa danne feelings dinsa kin lura ko?
Hada yarinta ke damunsa..... Yes da giyar kudi.
Yama arzikin sa kankanta kawai hankali da natsuwa yaron ke bani sha'awa...da kunya
Kuma....yes Yana da kunya of course.
Bilkisu ta shiryo musu komai a tray ta kawo Yana Shan Lipton da biscuit....daddy biscuit
Kuma???
To wancen kwalayen biscuits idan bama ci ya zamuyi dashi na ce ku rabar Kun jibgesu.... Dasu
mommy zata tafi sokoto ne na dibar Mana namu Yana store... Ohhh ban sani ba ... Ta ajiye ta
koma.
Ya bita da ido, abinda ke tayar mun da hankali shine yanda yake son ringa nuna Mata komai
da karfin tsiya..... Gaskiya fa.
Yanzu idan ya turo iyayen zuwa taushe zaka ce su kawo kayan baiko?
Eh, ki Bari zuwa dare zamu maganar kiji yanda na tsara lamarin.....
Karfe takwas ya fita office mommy Kuma ta Haye sama domin komawa barci.
Sauri sauri suka karasa aikin , goma saura kwata an shirya komai ta fada wanka.
Ta fiddo Kaya sunfi ashirin ta rasa wane zata saka?
Tabbas Bata son ta saka matsattsu tunda ya tilasta gyale zata saka.
Da kyar ta dauko wata doguwar riga bubu na boyel peach an mishi kwalliya da *Stones* blue.
Dinkin ya bude sosai, ta yi simple kwalliya ta shafa light pink na lipstick..... Rahina ta
kwankwasa Mata kofa... Aunty kizo.
Inji waye? Ta fada tana gyara lagen gyalen... Uncle Anwar ne gashi can na bude mishi falo....
Ki ce Ina zuwa..
Ta Kara feffesa turaruka a jiki.... Ta juya ta Kara juyawa a madubi sai Kuma ta danji kunya tayi
murmushi ta fita tana takawa dai dai cikin plat shoe light blue kalar gyalen.
Tana bude kofa sai kawai ta kwashe da dariya ganin sa bisa dining table Ya Fara cin abinci....
Na shiga uku Kai baka bakunta ne Wai??????
Ya kyalkyace da dariya inayi Mana gashi ni nake zubawa kaina? Idan bana bakunta ai zanje
ciki na Kira ki zuban ..... Ta galla mishi harara Kai baka da aiki sai ci..... To ai yunwa ba kanwar
ubana bace ko?
Ta kyalkyace da dariya ya akayi Kika San Ina son kan rago?
Ta ce hmm, ya lunkuma harshe a Baki Yana um...um...um please budan can menene?
...... Wai Kai baka ko irin Jan ajin Nan?
Ya kyalkyace da dariya kaiii Ni Zaki Sanya na kware wallahi.
Daukon lemu Mai sanyi ni bana Shan tea wannan sai ku Yan gayu..... Ta Kara hararar sa....
Ya kamata na Sanya wa hararar nan doka duk lokacin da kikayi ta ......
Ta Mike kawai ta Isa inda fridge ta bude wane kala Zan kawo maka?.... Peach daukon peach
dinnan Amma fa roba biyu Ni daya bata Isa ta.... Ta Kara dariya ohh Allah gamu gareka....
Ya Miko Mata chips da egg Fara ci Nim zanci irinsa..... Kana da cikin Zane ne?
Yayi murmushi Amma kajin nan dasu Zan tafi fa don sai dare Zan dawo.... Zaka dawo Ina?
Anan.... Ya fada Yana kallonta.. ke na dawo Abuja fa sai an koma school nida Kano......ta zaro
ido duk kana me?
Ya nutsar da idonsa cikin nata yace duk Ina zuwa Ina ganin ki... Tayi kasa da Kai tana
murmushi.....
Kill babba abinda kike son ji kenan ko?
Tun karfe nawa Kika tashi yau?
Ta Dan zumburo Baki ban koma barci ba tun asubah..... Nima haka ya fada Yana murmushi. Ta
harareshi kana meye?
Ina kallon agogo na kagara 10 tayi kamar na Miki waya na ce na mayar dashi eight..... Ta yi Yar
dariya yabi kuncinta da kallo..... Kinyi kyau sosai fa.
Ta ce hmmm.
Ni na yi kyau? Sabbin Kaya na dunka saboda zuwa Nan fa.... Ta kyalkyace da dariya Kai na
bani yau to me nace?
Ya Dan Sha mur naga kamar Baki fahimci hakan ba.... mtsew ta ja guntun tsoki.
Yayi Yar dariya ya Mike Yana goge baki da tissue taso idan bazakiji ba muyi magana ba
dadewa zanyi ba Zan barki kiyi barci sai na dawo da dare ko? Ya na maganar Yana tafiya tare
da janyo hannunta..... Ohh Shi baya Jin komai ya Kai hannu ya tabani ni Bilkisu??.
Ya zaunar da ita sannan ya zauna kusa da ita.... Ya akayi Kika bar kayan can anan? Daddy
yace ki mayar mun?
Ta daga Kai alamar eh,
Kin fada mishi in sonki?
Nan ma ta daga Kai?
Duk da haka bai karbi kyautar ba?
Ta ce eh,
Sunyi yawa?
Eh,
Yayi murmushi to Yanzu me yace?
Ta yi kasa da Kai yace ka turo iyayen ayi magana.... Ihu ya daka kawai sai ya Mike tsaye ya
janyota ya Bata wani hot hug.
Ta zame ahankali ta zauna tana murmushi....... Dan Allah kizo na you hugging dinki...
Ta galla mishi harara ya zauna Yana dariya *Amma fa nazo da sa'a* .......kawai ta jiyo motar
daddy alamar ya dawo.... Gama daddy Nan ya dawo.... Gooood ya fada tashi kije kice Ina son
magana dashi.....
Ta zaro ido.... Meye zaka fada mishi?
Zan rokeshi yabar Miki kyautar nan bazan koma da ita ba.... Kai Anwar daddy fa baya son
gardama.... Haba?
Allah.
Yayi murmushi jeki ce Ina magana...... Tashi kada ya shiga ciki please.... Ya mikar da ita...
Yana kokarin shiga ta fito daddy ka Kuma dawo? ..... Bilkisu kice ma Anwar securities din nan
ya Basu damar Zama Mana tsayuwa ai babu dadi ko?...... Shine yace Wai zaiyi magana da
Kai.... Ya kalleta da sauri Yanzu?
Eh, okay Zan biyo ta Nan Ina sauri ne nayi mantuwa.....
Police din da suka rako Shi suka bude mishi kofa ya shiga ta dayar kofar.
Ta dawo, yace na fito?
No. Zai biyo ta.... Ya banko kofa Anwar lafiya dai ko? Ana jirana office.... Da sauri ya sauka
kujera ya zukunna.... Yayi saurin Mika mishi hannu taso inji menene???? Ya rike hannun sukayi
hanyar fita.... Ya Kara kallonsa menene?
Ya kasa magana kunya duk ta kamashi.... Ya tsaya chak ya fuskance Shi...Anwar!
Ya Dan rusuna daddy Dan Allah abar Mata kayan bana son na koma dasu..... Ya kura mishi
ido... Amma kasan sunyi yawa ko?
Ayi hakuri Zan kiyaye next time Amma now abar Mata don Allah.
Ya Kara kallonsa sosai sai Kuma yayi murmushi... Shikenan Amma bana so ka daina kaji ko?
Ya rusuna na gode Allah ya Kara lafiya da shekaru masu albarka...... Aminnnmm ya Rabbi.
Ta fada maka nace ka Aiko?
Ya Kara sunkuyar da Kai In shaa Allah zasu zo gobe... Yayi dariya
gobe yayi sauri zuwa asabar dai ko?
Ya noke Yana murmushi.... Shikenan sai na dawo ana jirana ......
Ya dawo Yana murmushi tana zaune.....ya karasa Yana fadin yace ki dauki kayan shikenan
ko?
Ta kalleshi da sauri.
Yayi dariya rokonsa nayi, ya Kuma amince ... Ta ce hmmm.
Na ce mishi Zan turo gobe yace sai zuwa asabar....
Ta ce hmmm kawai... Yanzu Kinga Ina da hujjar cin uban Suleiman ko?
Ta zaro ido.... Dan Allah ka bar maganar sa, Zan fada mishi an Mana baiko...... Ban yafe ba
Kika Kuma magana dashi ..... Ta zaro ido..lallai idan aka koma school akwai chakwakiya.
Ya Mike Zan tafi sai na dawo anjima kinji ko?
Ta ce toh itama ta mike, daukon kazar da wancen cake din dasu Zan tafi.
Ta sungumo mishi suka jera ya fizge gyalen tare da shafa gashin ta yaja.... Nayi sa'a fa domin
Ina son yalo yalon gashi..... Rufen gashi ko na saki kayan Nan su zube... Da kin sake wasu
wallahi.
Ya Kara shafa gashin Yana murmushi sannan ya mayar Mata da gyalen... Ta banka mishi
harara... Kana da matsala wallahi hakan haramun ne... Astagfirullah na daina.
Ya fada Yana dariya...
Yana tafiya ta saki ajiyar zuciya tace kaiii Anwar case ne.
Ita da mommy suka bude jakunan.... Tsoro yasa suka mayar suka rufe..... Ta kalli Bilkisu yaron
nan sai ya kusa haukata ki idan kukayi Aure...
Tayi jimmm... Kawai.
Tare da Sadeeq ya dawo..... Tana shigowa yace koma ki sako hijab........
Ikon Allah sadeeq ya fada tayi saurin juyawa.... Banza wallahi kwakwa ke kawo ka marar
zuciya..... Naji kome zaka ce kai ne ka jawo ni dole na biyoka kuma na gama zaman zuruu......
Ya yi murmushi.
Abinda Zan Rama?? Kai kishin naka ma da bashi da aji..... Ya Kara kyalkyace wa da dariya,
kishin