Showing 3001 words to 6000 words out of 94796 words
Chapter 2 - WA ZAI FURTA Book Complete by Zainab Dahiru Wawo.pdf
Yana
son kulla mu'amula da ita Amma Yana ganin hakan a gareshi zai zubda mishi aji. Ita kuwa a
gareta Sam bai ma gabanta ko kadan idan an hadu a gaisa idan ba a hadu ba Bata ko tunanin
sa. Shine ma sau da yawa take Dan takura tunanin sa kadan kadan. Ta Dan Fara sakewa da su chinyere saboda ta lura sune masu kokarin ajin, takan zauna tayi
tunanin akwai department din da yakai Economics barin wuta duk makarantar? Sau da yawa
tana tunanin Anya ba hausa ko Islamic zata koma ba?
Ta gama tsorata da makarantar musamman yanda taji ana bada carry over, probation da
Kuma withdraw. Takan yi tunanin ai ita abun kunya ne gareta ta sami Koda carry over din ne ma
hakan yasa ta Kara dagewa tana Kara naci cikin karatun ta musamman da jarabawa ta karato
kullum tana library ko Kuma tare da su chinyere tana Kara koyon karatu.
Saura kwana hudu su Fara jarabawa misalin karfe hudu na marece tana zaune wani class
tana faman karatu yazo wucewa kunnensa like da air piece har ya gitta said yaga kamar ita,
yayi jimmm Yana tunanin ita ce ko gizo idanun sa keyi Masa kamar kullum?
Kamar kada ya dawo sai Kuma dai ya koma don tabbatarwa .....ita din daice tana ta faman
Mimi da baki ya kyalkyace da dariya lokacin daya kunna Kai ajin hankalinta naga littafi har yazo
ya zauna kusa da ita....tayi firgigi cike da tsoro ko da taga shine bata San lokacin da ta balla
mishi harara ba.....yayi murmushi afuwan matsoraciya duk wadannan mutanen meye zai kamaki
da rana gatse gatse haka? Ya karasa maganar Yana janyo littafin ta gaban sa, meye kike
karantawa ayi mun bayani.
Haushi ya turnuketa domin karatun ya Fara shigar ta sosai gashi yazo zai rikita ta, Tasha mur
tare da janyo littafin Dan Allah karatu nake zaka rikitani ka tashi ka bani wuri.....bazaki koya
mun ba?
Nima Yanzu ai nake karantawa ta fada cikin fada fada, yayi murmushi it's alright go ahead and
read ya sunkuyar dakai kawai bisa desk din. Ta ci gaba da karatun ta ba tare da ta Kara bi ta
kansa ba.
Idan ta karanta sai that bude can karshen littafin ta rubuta haka haka Yana ta lura da ita duk ta
dage bakin Rai bakin fama Nan da nan ya gane hadda ce takeyi. Yana so ya mata bayani
Amma ya rasa ta inda zai Fara......
Tana son kamshin turaren sa ainun Anwar Dan gayu ne matuka Yana daukar wanka gashi
kyakkyawa. Kamar ta karanci zuciyar say ta Dan karkato Dan Alalh wannan kalmar me take
nufi? Ta sungo mishi littafin a gaban sa. Daman tun zaman sa kusa da ita ya kashe music din
hakanan wayar ke jikin kunnen sa.........yayi kamar baiji me tace ba har sai da ta kalleshi
sannan ya Dan zare wayar daga kunne Shi ala dole baiji me tace ba ya dan kalleta Shima kina
magana ne?
Cewa nayi me wannan kalmar ke nufi? Ta nuna mishi da yatsa ....yabi hannun nata da kallo
Yana kallon Zara zaran yatsun ta ya ce bari muji sentence din, Ya fada mata ma'anar kafin yace
kin gane course din nan ne? Ta Dan bata rai to gashi dai Ina karantawa...... Ya Kara janyo
littafin gaban sa ya budo shafin farko...... Kin San fa abun duk labari ne Kinga.......ya Fara mata
bayani a hankali ahankali Nan da nan ta Fara fahimta sosai saboda bayanin nasa duk da hausa
yake mata. Haka haka har ya gama mata littafin. Taji dadi sosai da sosai ta fadada fara'ar ta
ohhhhh Ashe ka Gama covering komai ko???.......a'a fa nima kawai na gane darasin ne lokacin
da yake bayani a class.....Amma wallahi ka iya bayani saboda har kafi malamin ma iyawa....ya
danyi dariya tinda na Miki bayani da hausa ko? Ta kyalkyace da dariya yabi fuskar ta ta Yana
Kara kallo ta bude jakar ta to Dan Allah ka gane wannan math din? Ta fiddo littafin. Dariya
kawai yake cikin Rai Amma a zahiri yadan basar.......ya kalli littafin, gaskiya ban iya Shi ba
Amma ki bari yau sanje dakin wani dan aji hudu ya koya mun gobe sai mu hadu in nuna
Miki......da karfe nawa? Ta katse shi, Yayi murmushi duk lokacin da kike so goben....... 8:00am
Zan jiraka anan.
Ya zaro ido 8? Gaskiya sai dai 4 saboda barci bazai barni na fito da wuri ba.
Kamar zatayi magana sai Kuma ta fasa ta ce Allah ya kaimu lafiya tare da janye littafin yabi
Dan karamin bakin ta da kallo har ta sunkuya.
Ta Mike tana kokarin sagala jaka ta kalleshi tana murmushi Dan Allah ka koya da kyau Zan
jiraka anan din goben in shaa Allah.
Yace ba damuwa.....see you then. Ta wuce.
Yabi ta da kallo kamar ya rufa mata baya amma Shi kansa yasan bazai iya hakan ba ( saboda
gadara ).
Zuciyarta Fara fes! Ta isa daki taji dadin bayanin Anwar matuka.
Washe gari tana fitowa masallaci ta wuce class din kamar yanda sukayi alkawari, ta fiddo
wani course theory ta Fara karantawa kafin ya iso. Ta nayi tana Dan kallon taga tare da duba
agogon wayarta har kusan hudu da arba'in.
*Anwar* kuwa Yana can Yana shakar barci abinsa sammm ya manta da maganar su.
Allah ya taimaketa kawai sai ga su chinyere sun shigo karatu Suma Kuma cikin sa'a statistics
din zasuyi solving sai kawai tayi joining suka Fara.
Tana yi tana tunanin watakila Anwar bai iya bane Yana Jin kunyar zuwa....ta tabe baki to meye
na karyar zaije ya koya bayan yasan bashi da wani kokari....mtsew taja guntun tsoki.
Bai farka ba sai shidda saura ya tashi a hargitse ga takaicin lokacin sallah ya shige ga Kuma
tunanin sabawa Bilkisu alkawari da yayi.
A gurguje ya watsa ruwa yayi sallah ya fito da sauri.
Ya shawo kwana ita Kuma ta fito ajin zata tafi. Tana hango Shi tayi sauri bi ta dayan side din
tabayan azuzuwa tayi hanyar fita gate sauri sauri.....tana tunanin watakila Yana can Yana faman
koyo don yazo ya birgeta..tayi tsoki to karya tame ne?
A hargitse ya shiga ajin sai wurge wurgen ido yakeyi girman Kai da nuna Isa sun Hana ya
tambayi su chinyere ko sun ganta. Rai bace ya fita Nan ya Fara bin azuzuwa neman ta.
Helen ta tabe baki I don't like this Anwar honestly.... Mtsew don't mind idiot abeg inji chinyere
Nan gulma ta tashi.
Ya cika girman Kai da nuna Shi wani ne, baya yi ma kowa magana sai abokansa uku. Surutai
kala kala saboda Shi din Daman baida farin jini a class din tun zuwansu Wai ya cika fadin Rai
da gadara.
Tunda ga ranar bai Kara Sanya Bilkisu a ido ba yayi neman har ya gaji gashi baida no. Ta bai
Kuma San Wanda zai tambaya ya bashi ba haka Kuma baisan accommodation dinta ba hostel
take ko off campus. Wasa wasa abun ya Dan dameshi.
Ranar da zasu Fara jarabawa da yake ta karfe uku ce tun biyu saura yake hall din Yana so ya
ganta, ita kuwa tun 8 tana library sai biyu da Rabi ta fito bayan tayo sallah. Kansa sunkuye
baiga shigowar taba har ta zauna bayansa.
Lallai Anwar ka kyauta shine ka shanya ni rannan ko? To kayi dai dai ta fada tana faman
hararar sa .
Da sauri ya dago Kai zaiyi magana kenan invigilators suka shigo tare da fadin everybody
out..ta rigashi fita, ko da aka Fara shiga ma tayi saurin fadawa don Zama gaba gaba.
Alhamdulillah jarabawar ta mata dadi ainun domin duk abinda ta karanta suka fito.
Ita ce ta biyar din bayarwa ( submitting ) bata jira kowa ba tayi masallaci don gabatar da
la'asar saboda lokacin biyar da kusan ashirin.
G
Haka semester din ta kare ba tare da sun Kara haduwa da Anwar ba, ko kadan Bata yarda su
hadu tasan karya zai shirga mata don kare kansa.
Shi Dan garin Kano ne ita Kuma Abuja mahaifinta ke aiki Amma asalin su Yan katsina ne.
Washegarin da suka Gama jarabawa tabar garin Anwar kuwa karfe biyar na ranar yabar
dutsinma.
Hutun baida tsawo sati biyu akayi aka dawo. Sun dawo da sati daya aka saki result a *portal*
Murna tsalle ga Bilkisu saboda ta cinye ko wane Bata da carry over ko daya ga point dinta 4.33
Hakan ba karamin dadi yayiwa Yan gidan su da iyayenta ba.
Anwar kuwa 5:00 dai dai ya samu saboda duka courses din da sukayi goma Sha daya ko
wane *A* yaci. Yaja bakin sa ya tsuke.
A cikin ajin kowa nata fadin result din sa daga Mai 4 point sai masu 3 point da abubuwa. Duk
Wanda ya tambayi Bilkisu sai ta ce lafiya Lau ne ni Daman carry over ke bani so to ban samu
ba. Bata yarda ta fada ma kowa result dinta ba. Tana zaune an gama lecture din wani mugun
malami ta kura ma dan rubutun da tayi ido tana nazarin ya zata ci jarabawa da Dan wannan
rubutun? Suleiman ya mata sallama.
Suleiman matashi ne Shima a cikin ajin Mai natsuwa da son addini babancin say da Anwar
yafi Anwar saukin Kai da yarinta. Ya zauna kusa da ita bayan ta amsa sallamar Dan Allah
Hajiya Bilkisu na kasa bude portal dina ya akeyi ne?
Tayi murmushi Ina wayar taka in nuna maka?
Wallahi daki na barta ki nuna mun da taki.......hankalin Anwar na kansu haka kawai sai yaji ya
tsani Suleiman karon farko a rayuwar sa.
Ta fiddo wayar tare da tambayar sa password da matric number.
Portal din na budewa ta Mika mishi wayar kaga inda zaka Danna..... Ya danyi dariya to bude
Mana ai ba komai don kin gani. Ta kalleshi tana mamaki saboda tasan Portal sirrin dalibi ne ba
kowa kake yarda ka nuna mawa ba. Ya Kara Yar dariya ki bude ba komi. Ki gane mun Ina da
carry over? Ta ce to a sanyaye tana mamakin irin warda da yayi mata farat daya zuciyar ta cike da Jin
dadi tare da ganin kimar say da mutunci.
Kaiiii....ta fada tare da zaro ido ka Fadi accounting. Sai kawai yayi murmushi nasan za'a rina
sai wane? Ka Fadi GST English Shikenan. Nawa ne point dina? Ta duba can kasa tana
warware ido..... Okay gashi Nan 2.65. Ta kalleshi, amma Suleiman me yasa ka yarda dani
haka?......Au kin San sunana kenan? Ya fada Yana kallonta cike da mamaki, tayi murmushi eh
Mana nasan sunan ka Suleiman.
Ina fatan ke dai lafiya lau ko? Sai kawai ta budo mishi portal din ta tace kaga nawa.
Ya zaro ido kaiiiiiii...... Ta danyi murmushi Amma bana son Dan Allah ka fadawa kowa result
dina.
Ya Jin jina Kai in shaa Allah Zaki sameni Mai rike sirrin ki, amma Bilkisu kinyi wuta da yawa fa!
Ta yi Yar dariya kawai.
Allah yasa albarka. Kiban no. Ki dan Allah ko da wani Abu Yana tasowa Kuma idan bazaki
damu ba Zan ringa matsowa kina tasar Dani inda ban ganewa.
Ba matsala ga number rubuta........
A harzuke Anwar yabar class din tunda ga ranar sai kawai yayi baya da ita ko gaisuwa baya
son suyi cikin kankanin lokaci ta Saba da Suleiman ta fahimci Yana da saukin Kai bashi da
girman Kai sannan Yana da addini tare da daratta mutane.
Ko da ya gane Bilkisu nada kokari sai ya like mata ko C.A zasuyi Yana manne kusa da ita
baya yarda tayi mishi nisa.
Ko kadan Bata da mugunta duk amsar da ta kakare mishi zata bashi ya kwashe tsaf!.
Akwai wani course Mai matukar wahala gashi three credit unit ne Kuma calculation Mai
rikitarwa kowa Yana Jin course din. Anwar yayi burus da ita Yana Jin kowa na kokawa Amma ya
ki nuna ya iya. Kwana takeyi karatu da salloli, Ranar jarabawar course din ana ta jera layi kawai
malamin yace ta zauna can, hankalin ta ya tashi ganin ya cillata gaba don yau baya take son
Zama saboda ta Sami taimakon wani.
Tana Zama sai taga Anwar ne a gaban ta, ita dai kawai sai addu'a takeyi tasan yau sai Allah
da malaman gari. Tambayoyi bakwai be a amsa biyar tambaya ta farko dole ce gata da 'ya'ya
har goma.
Saura kadan ta kurma ihu saboda duka tambayoyin guda daya ne kawai ta sani itama theory ne
ba calculation ba.
Idanun ta suka kawo ruwa, taga tunda Anwar ya duke bai dago ba, hall din yayi tsit! Ta yi
zugummm, zuwa can kawai ta Fara amsa wacce ta sani.
Mafi yawancin malaman dake tsaron nasu duk sun maida hankali wurin Yan baya. Haka ta
dunga rubutu Dan Allah yasa ta Sami Koda *E* ne a course din ta wuce wurin.
Tana gamawa tayi zugummm kawai tana fargaba.
Yadan waigo kadan ganin malaman basa kusa yace kin iya question one naga tana da wahala
fa.
Tayi kasa da murya wallahi question 4 kadai na iya cikin bakwai din nan ga Shi ta farkon naga
30marks ne.
Ya dan gyara zaman sa kadan tare da kango mata booklet din sa yace kiyi sauri ki kwasa.
Habaaaaa.....ga bilkiyda saurin rubutu gata very smart. Duba daya sai ta kwaso layi biyu. Cikin
sauri ta gama shafin tace juya....Shi kansa yayi mamaki yace ke duba da kyaufa kada kiyi
shirme. Wallahi na gama ka juya kawai.
Haka ya bata dukan sauran question hudun da bata iya ba.
Sai da ya tabbatar ta Gama tsaf sannan yaci gaba da amsa Shima question 4 din da tace tayi.
Ta Dan waiga ta hango Suleiman can baya an cillashi sai zare ido yakeyi.
Duk Wanda ka kallo zakaga ko Yana zufa ko Yana ta raba ido.
Kije kiyi submitting...ya fada kasa kasa ta ce toh.
Kowa sai kallonta yakeyi Yana mamakin yanda zata bayar da wuri haka, Wasu na tunanin
kawai ta gaji ne da zama kamar yanda Suma suke zaune, tafi mintuna talatin kafin wasu tsirara
suka Fara fitowa duk Wanda ya fito idanu jawur ana tsinar malamin kusan kowa ya sadakas da
kawai faduwa zaiyi course din saboda rashin iya amsawa. Suleiman kawai take jira ya fito sai
kuwa gashi Yana ganinta yace, Bilkisuuu..... Yau naji wuta wallahi Allah dai ya kyauta Amma
question biyu kawai nake da tabbaci cikin sauran.
Tabbb....wallahi ni Allah ya taimakeni Anwar ya bani duka Wanda ban sani ba....hada question
one?
Eh Mana.
Wai da gaske kike?
Wallahi kuwa.
To Ina Jin keda shine kawai kuka amsa ta don ko su chinyere gasu can suna cewa Basu gane
ba.......Allah dai ya kyauta ta fada tare da cewa sai gobe ta ruga hango Anwar yayi hanyar
*Gate* Yana ta faman sauri.
Anwar.. ta kwada mishi Kira, yasan za a rina Shi yasa yaso ma kada su hadu.
Ya Dan tsaya Yana murmushi , ya jarabawar Bilkisu ya fada Yana latsa waya.
Hmmm jarabawa yau Allah ya rufa man asiri bacin Kai ai Dana shiga uku. Na gode na gode
Allah ya Kara ilimi......Daman ka iya course din sosai haka? Naga yanda ake ta kuka dashi Kai
komai ka amsa.....hatta jamilu ma naga naka yake kwafa ( copying ).
Murmushi kawai yayi yace ba damuwa.
Ya wuce kawai. Ta bishi da ido. Anwar...ta Kara kwada mishi Kira.....ya juyo wallahi na gode
kaji?
Sai kawai ya kyalkyace da dariya ya juya abinsa.
Taji dadi sosai da sosai a Ranar domin course din kadai kowa ke kuka dashi wannan
semester din.
Hutun ya kasance dogo akalle ankwashe watanni biyu a gida kafin a dawo aji biyu.( Su Bilkisu
an Fara manyanta ) wannan karon suna gida result ya fita inda take da 4.22 ta Dan sauko
kadan saboda ansha wahala matuka Shi Kuma Suleiman Yana da 2.72 Amma ya Sami carry
over daya. Sun koma da makaranta da sati biyu akayi *convocation* tare da bayar da kyaututta ga first
class da over all.
Bata halarci wurin ba. Saboda ba kowa ya maida hankali ga taron ba. Hakan yasa Anwar
zuwa tare da karbar five pointer award da Kuma overall student na aji daya da suka gama.
Kamar munafuki ya karba sim sim sim yayi saurin barin hall din ganin babu alamun Yan ajin
su ko wani Wanda ya sanshi. Ashe Suleiman yana wurin.
Ba karamin mamaki yayi ba watan Anwar shine *Hamza Yusuf* din da ake nema cikin class
Amma wallahi sai ya fadawa Bilkisu.................
*************
*KADUNA RIGASA*
Yana ta mamakin yanda ummi ta mishi text tana son ganin sa alhalin bata taba hakan ba.
Yana zaune babban falon gidan nasu an cika gaban sa da kayan ciye ciye da lemuka kamar
kullum ta shigo tana ta faman Bata rai .
Ya kalleta tana ta faman karairaye karairaye......Amarya bakya laifi ko kin kashe Ahmad (
Babban yaron sa ) ya fada cikin zolaya Yana Yar dariya hannun sa rike da samosa mutumen shi
Yana ci.
Banga alama