Showing 9001 words to 12000 words out of 94796 words

Chapter 4 - WA ZAI FURTA Book Complete by Zainab Dahiru Wawo.pdf

12 Jul 2025

3754

naga
30marks ne.
Ya dan gyara zaman sa kadan tare da kango mata booklet din sa yace kiyi sauri ki kwasa.
Habaaaaa.....ga bilkiyda saurin rubutu gata very smart. Duba daya sai ta kwaso layi biyu. Cikin
sauri ta gama shafin tace juya....Shi kansa yayi mamaki yace ke duba da kyaufa kada kiyi
shirme. Wallahi na gama ka juya kawai.
Haka ya bata dukan sauran question hudun da bata iya ba.
Sai da ya tabbatar ta Gama tsaf sannan yaci gaba da amsa Shima question 4 din da tace tayi.
Ta Dan waiga ta hango Suleiman can baya an cillashi sai zare ido yakeyi.
Duk Wanda ka kallo zakaga ko Yana zufa ko Yana ta raba ido.

Kije kiyi submitting...ya fada kasa kasa ta ce toh.
Kowa sai kallonta yakeyi Yana mamakin yanda zata bayar da wuri haka, Wasu na tunanin
kawai ta gaji ne da zama kamar yanda Suma suke zaune, tafi mintuna talatin kafin wasu tsirara
suka Fara fitowa duk Wanda ya fito idanu jawur ana tsinar malamin kusan kowa ya sadakas da
kawai faduwa zaiyi course din saboda rashin iya amsawa. Suleiman kawai take jira ya fito sai
kuwa gashi Yana ganinta yace, Bilkisuuu..... Yau naji wuta wallahi Allah dai ya kyauta Amma
question biyu kawai nake da tabbaci cikin sauran.
Tabbb....wallahi ni Allah ya taimakeni Anwar ya bani duka Wanda ban sani ba....hada question
one?
Eh Mana.
Wai da gaske kike?
Wallahi kuwa.
To Ina Jin keda shine kawai kuka amsa ta don ko su chinyere gasu can suna cewa Basu gane
ba.......Allah dai ya kyauta ta fada tare da cewa sai gobe ta ruga hango Anwar yayi hanyar
*Gate* Yana ta faman sauri.
Anwar.. ta kwada mishi Kira, yasan za a rina Shi yasa yaso ma kada su hadu.
Ya Dan tsaya Yana murmushi , ya jarabawar Bilkisu ya fada Yana latsa waya.
Hmmm jarabawa yau Allah ya rufa man asiri bacin Kai ai Dana shiga uku. Na gode na gode
Allah ya Kara ilimi......Daman ka iya course din sosai haka? Naga yanda ake ta kuka dashi Kai
komai ka amsa.....hatta jamilu ma naga naka yake kwafa ( copying ).
Murmushi kawai yayi yace ba damuwa.
Ya wuce kawai. Ta bishi da ido. Anwar...ta Kara kwada mishi Kira.....ya juyo wallahi na gode
kaji?
Sai kawai ya kyalkyace da dariya ya juya abinsa.
Taji dadi sosai da sosai a Ranar domin course din kadai kowa ke kuka dashi wannan
semester din.
Hutun ya kasance dogo akalle ankwashe watanni biyu a gida kafin a dawo aji biyu.( Su Bilkisu
an Fara manyanta ) wannan karon suna gida result ya fita inda take da 4.22 ta Dan sauko
kadan saboda ansha wahala matuka Shi Kuma Suleiman Yana da 2.72 Amma ya Sami carry
over daya. Sun koma da makaranta da sati biyu akayi *convocation* tare da bayar da kyaututta ga first
class da over all.
Bata halarci wurin ba. Saboda ba kowa ya maida hankali ga taron ba. Hakan yasa Anwar
zuwa tare da karbar five pointer award da Kuma overall student na aji daya da suka gama.
Kamar munafuki ya karba sim sim sim yayi saurin barin hall din ganin babu alamun Yan ajin
su ko wani Wanda ya sanshi. Ashe Suleiman yana wurin.
Ba karamin mamaki yayi ba watan Anwar shine *Hamza Yusuf* din da ake nema cikin class
Amma wallahi sai ya fadawa Bilkisu.................
*************
*KADUNA RIGASA*
Yana ta mamakin yanda ummi ta mishi text tana son ganin sa alhalin bata taba hakan ba.
Yana zaune babban falon gidan nasu an cika gaban sa da kayan ciye ciye da lemuka kamar
kullum ta shigo tana ta faman Bata rai .

Ya kalleta tana ta faman karairaye karairaye......Amarya bakya laifi ko kin kashe Ahmad (
Babban yaron sa ) ya fada cikin zolaya Yana Yar dariya hannun sa rike da samosa mutumen shi
Yana ci.
Banga alama ba, ta fada tana taunar cingam.
Ya kalleta jin maganar ta fito gatsal....
Kamar Yaya?, Ya bukata.
Kamar yanda kaji.
Kamar yanda naji?
Ya maimaita cike da mamaki kafin ya ajiye guntun samosan bisa plate ya tattara hankalin sa
duka wurin ta.....me ke faruwa ne ummi?
Tayi shiru!
Dake nake magana...me ya faru?
Ta gyara Zama, Ina ce apartment din da kayi sabo Ni ka gina mawa Amma labari yazo cewa
Aunty Amira ta koma....... Ke ya daka mata tsawa.
Nan da nan ya harzuka, Ni na fada Miki Ina Miki gini?
Gabanta ya fadi tayi tsuru tsuru, kinji? Munyi dake Ina Miki gini?
Okay ita da Zaki aure Mata miji Bata kawo mun matsala ba sai kece Zaki fara kawo mun tsirfa?
Saurara da kyau ya Mike tsaye Yana nuna ta yatsa wallahi matukar kina son Zama dani tare da
Jin dadi sai kin daratta Amira kin mun biyayya kin Mata bazan dauki sakarci ko kadan ba.
Dukkan ku Ina sonku to dole kowace tabi ra'ayi na, idan Kika saki na gane kina da matsala to
wallahi zakiji ba dadi.
Mtsew ya buga tsaki ya wuce.......ta yi zuruuuuu tana zare ido lallai ta gwada Bata ji dadi ba.
Kwallah suka zubo Mata. Ta buga ma babbar yayar su waya domin ita ce abokiyar shawarar ta
.....salati ta kamayi ubanwa ya aike ki? Ai kinyi sauri bari zakiyi sai kinje gidan yasan dadin ki
lokacin yazo hannu tukun Amma Yanzu ai lallaba matar sa yakeyi tunda ya Mata laifi.
Ki bari Zan baki ahawarwari idan na shigo gobe.
Tun daga ranar Bata Kara Sanya Shi a ido ba. Tuni a Mata hudubar kada ta saki ta dauki raini
ga matar sa Kuma idan ta a gidan ta Sami damar juya Shi yanda zata amshe ragamar komai.
Babu yanda ba a yi dashi ba ko kamu ayi yace bai son bidi'a ba Dan komai ba kada ma akirkiri
partyn Amira taji ba dadi.
Ranar walima akayi mashi Sha Tara ta arziki hada mota.
Yana falon sa zaune yaji marokiya na sanarwa. Shima ya Mike ya kirawo marokiyar ya bada
makullin mota kirar *GLK* baka 2019 model ta kusan miliyan Tara yace yaba Amira ayi
sanarwa.
Nan dangin Amarya kuwa suka Fara surutai............
Ko ajikin sa. Dangin ango dana Amirai kuwa suka Fara rangada guda suna tayata Murna.
Hakan ba karamin harzuka Amarya da danginta yayi ba. Nan suka Kara hure Mata kunnen
wallahi sai ta tashi tsaye Dan kwato ma kanta yanci.
Kuka takeyi wuiwui.
Kafin karfe shida gida ba kowa duk an tafi.
Ana gama sallar isha'i ya ja Amarya zuwa sashen Amira don yi masu huduba.......

*Ayi hakuri da typing error please yanayin typing din ne saboda kawai ta WhatsApp nake yi

Kuma gaskiya bana bi idan na Gama kawai nake turawa.
*Daga zainab wowo*��✍
[3/23, 8:00 AM] +234 706 188 4461: *WA ZAI FURTA?*
0⃣3⃣


*TUKUICI NE GA AUNTY RABI ALLAH YA KARA ARZIKI DA RUFIN ASIRI*

*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*

*Domin ki.... blood sister khadija Dahiru wowo miji na gari I pray my besty*

*DAYA TAMKAR DUBU AL'AMEEN ZUBAIRU* TANNY ALLAH YA RAYA MIKI YARON NAN YA
KARA MISHI KYAU DA KWARJINI�

*Federal University dutsinma*

Tunda aka dawo bai yarda sun hadu da Bilkisu ba har suyi wata magana. Tana ta kokarin su
hadu Amma yaki yarda.
Suna tsaye ita da su favour bakin ajin da zasuyi darasi ta hango Suleiman na taho wa, tun
daga nesa suke ma juna dariya saboda Yanzu sun Zama tamkar *Wa da kanwa*, Anwar har
yazo ya wuce ta gaban ta bata ganshi ba amma Shi Suleiman man din ya hango shi.
Yana karasowa malamin Shima ya iso haka suka rankaya zuwa aji.
Ko Zama Yanzu kusan tare sukeyi.
Har Yan class din sun Fara lura da shakuwar su.
Ya fakaici idon malamin ya Fara mata magana kasa kasa.
Wai Bilkisu kinsan Hamza Yusuf din say ake nema ajin nan Anwar ne?
Ta zaro ido *Anwar*?
Eh wallahi. Jiya gaba na ya amshi award din first class da Kuma overall award ina kallon sa yayi
saurin boyewa ya bar hall din da sauri.
Ta rike baki. Innalillahi, wallahi sai na mishi magana naga wannan semester din ma tunda
muka dawo sai wani shareni yakeyi.
Hmmm, ai da yake kece, Amma Anwar inba ke ba waye ke mishi shigar kawara duk
makarantar Nan. Kinsan girman kansa, jiji da Kai da kuwa maida kowa banza yasa aka tsane
Shi wallahi ya cika gadara....... Duk yaji dashi nikam daga yau wallahi ya shiga uku dani.
Ba abinda nake nema wurin sa inba karatun ba.....ta katse shi.
Hmmm Hana wallahi nayi mamakin *Business finance* din last semester, bana fada maka cikin
mintuna da Basu wuce talatin ba ya gama kusan questions 4 kowa na kuka da question one
amma Shi duka yayi. *B* fa gareni course din Kuma wallahi C A da 22 na shiga......ohh ni
*Balky* ai wallahi ya shiga uku dani. Suleiman man dai sai dariya yakeyi yace idan kin kwaso wurin sa Kya ringa koya mun....tabbbb
tare zamu je kyaleshi ai wallahi sai na fitine Shi ga wannan semester din kurar ta tafi ta aji daya.
Daya ke Anwar din Yana ta gefenta sai kawai ta yi ta kallon sa.

Tun bai lura har ya fahimci tana kallon sa. Ya Dan juyo suka hada ido ta balla mishi harara Shi
Kuma sai ya kawar da Kai Yana murmushi kawai. Haka sukayi tayi da sun hada ido sai yayi
murmushi ita Kuma ta harareshi.
Yana ta sake sake cikin Rai *Kuma yau me nayi Ni Hamza* bana iyawa rigima da fitinar
Yarinyar can. Ya kawar da Kai bai yarda sun Kara hada ido ba har aka gama.
Hankalin ta na kansa yana mikewa itama ta Mike.
Abinka ga namiji kafin ta sunkuya ta dauki jaka har yabar ajin. Da gudu tabi ta kofar baya kawai
sai dai ya ganta gaban sa.
Gaban sa yayi mummunan faduwa Amma miskilancin Anwar bai yarda ta gane hakan ko a
fuska ba hasali ma sai yayi Yar dariya *Hajia Bilkisu an tashi lafiy?*
Ta rike kugu To yau Allah ya Kama ka, Ashe Kai ne *Hamza Yusuf*........ Har ga Allah ya Dan
razana. Amma a zahiri sai kawai yayi dariya duka kumatunsa suka lo6a ....inji wane
makaryacin? Ya fada Yana dan waige waige kada sauran Yan aji masu fitowa suji,
Wallahi Kaine *Hamza Yusuf*.... Ta fada tana hararar sa. Tana matukar bashi dariya saboda ko
gida bai taba samun Wanda ke mishi magana Kai tsaye Babu shakka ba irin Bilkisu.
Yadan Sha mur Yana Dan zare mata ido ke ni bani bane ya gitta zai wuce .....Tasha gaban sa
da sauri tare da ware hannuwa ba inda zakaje sai ka fada mun wanene jiya aka bashi kyauta ya
boye ya gudu?......tuni hankalin mutane ya dawo kansu an Fara fahimtar meke faruwa.
Ya zaro ido..... Ke ni bani bane..... Wallahi Kaine.
Naji nine yanzu meye kike so? Ya fada Yana Yan waige waige kamar marar gaskiya. Zaka
ringa koya mun karatu wallahi don bazan kyaleka ba....shine damuwar? Ya fada cikin kosawa,
shikenan duk lokacin da kika shirya Zan nuna Miki. Ya wuce da sauri ya barta tsaye.
Suleiman ya karaso kin dai gani ko?
Kyaleshi ai wallahi na daina wahala daga yau addabar sa zanyi.
Nan wuri ya rikice da surutai kowa na mamaki.
Tun daga lokacin kimar Anwar ta Kara karuwa duk masu Jin haushin sa suka daina. Matsala
daya ce Babu Mai iya tunkarar sa da maganar koyo duk ana Jin tsoro da shakkar sa.
Tun daga lokacin Bilkisu ta dami Anwar ya rasa yanda zaiyi da ita ba abinda takeyi mishi sai
terere kowa Yanzu yasan wanene Shi , ya rasa dalilin da baya son mata wulakanci kamar
yanda yake ma kowa.
Ko lecture za ayi Mafi yawan lokuta sai ta zauna kusa da Shi sai dai yayi ta dariya.
Na kusa dashi mamaki kawai sukeyi yanda baya hantarar Bilkisu ko kadan don ko su din
lallabashi sukeyi.
Satin da ya kasance daga Shi sai na yin first C.A sun fito lecture seven to nine ( 7-9 ), Yana
tsaye ta fito da sauri don kada ya gudu sakamakon daya ce kawai garesu a Ranar.
Anwar muje ka koya mun *Math for Economic* din nan ban gane komai ba gashi jibi yace Shi
zaiyi nashi test din.
Duk Wanda ke wurin sai da ya kalli Bilkisu cike da mamaki yanda take mishi magana Kai
tsaye haka, Sam bashi ma take kallo ba ko lokacin da takeyin maganar hankalin ta naga jakarta
tana saka littafin da suka gama, yayi Dan murmushi ba dai Yanzu ba ko? Saboda ko break
banyi ba yunwa...... Ta dago Kai da sauri Nima banyi ba ai idan mun gama duk ma tafi muje
muyi.
Ta nuna mishi hanya wuce muje wallahi yau ba inda zaka je......bai San lokacin da ya kwashe

da dariya ba Yana ganin karfin halin yarinyar nan sosai, zai Kara magana ta rike kugu tare da
tafa hannu kasan Allah ba inda zakaje...... Wuce kawai.
Naji muje yayi gaba ita Kuma tabi Shi a baya. Duk illahirin wurin binsa akayi da kallo ana wani
irin mamaki.
Shi ya Fara Zama kafin ta zauna.
Yawwa ko Kai fa....ai ka gama shiga uku dani watan Kaine Mai kokarin aji shine ka mayar damu
samnoni ko?
Dariya kawai yakeyi, tana surutai tana fiddo littafi da calculator. Ta Mika mishi biro da doguwar
takarda ..ungo Fara daga farko.....
Dariya yakeyi sosai .....daga farko Kuma? Ki dai fadi abinda baki gane ba.
Ni ban gane komai ba.
Ban yarda ba Allah nasan kina son wahalar Dani ne kawai gashi yunwa nake ji walhi.
Ko me kakeji yau muna Nan sai ka koya mun kawai Fara.
Ya bude littafin to bari mu gani ko na iya.
Ta bishi da harara
Yayi murmushi yace seriously.
A hankali ya Fara mata solving dalla dalla. Dayake Bilkisu na da kokari da saurin fahimta hakan
yasa bai wahala ba nan da Nan ya fahimci lallai tana da basira saboda da yawa idan Yana koya
ma wasu sai su kusan awa hudu bisa example biyu. Akasarin Bilkisu da Mafi yawan formulas
din ma ta haddace su idan yanayi da ka take kawo mishi su. Ya kalleta hajiyar dai ashe guruwa ce ko? Ya ajiye biro gaskiya na gaji wallahi duk kin iya kina
son bani wahala ne kawai ko Bilkisu?
Ta Dan sunkuyar da Kai haka kawai taji Yar kunya ....wallahi a'a ban iya ba.
Yabi fuskar ta da kallo Yana Kara kallon yarintar da ke cike da kyakkyawar fuskar tata.
Ke ni yunwa nake ji gaskiya ya fada Yana rufe littafi.
Dan Allah ka taimaka saura fa biyu da mun gama sai mu tafi Zan siya maka break idan mun fita
waje.
Au Zaki biyani ne?
Ta zaro ido wallahi a'a naga hostel zaka koma gashi har Sha daya ta kusa, Kuma yaushe kaje
ka nemi abinci?
Ke Kuma fa?
Ni indomie zanci dana koma daki.
To Nima ita zanci. Ya fada Yana ci gaba da rubutu,
Ba damuwa Zan siya maka wurin Abdul Mai shayi na Nan waje ai nasan mutumun ka
ne.......da sauri ya kalleta waye ya fada Miki?
Tayi Yar dariya ai Ina wuce ku ta wurin Mafi yawan lokuta.
Ya Dan harareta ke kin samun ido ko?
Ta kyalkyace da dariya Wai ma.....
Eh Mana.
Rabi labari haka suka gama duk idanun sa sunyi ja....Nan da Nan ta fahimci lallai baya da
jimirin yunwa yanda har ya Fara galabaita.
Tare suka jera suna tafiya, baka da jimirin yunwa ta fada tana Yar dariya.
Ya danyi murmushi yunwa nada sabo ne?

Eh Mana Amma ga jaruman maza.
Dariya yayi sosai kafin yace naji ni ba jarumi bane ba.
Eh, ta fada tana murmushi
Ke ni sai anjima ya fada tare da yafito Dan mashin.
Ta zaro ido Ina zakaje?
Hostel.....
Indomie din fa?
Na gode....
Wallahi baka Isa ba , Dan mashin din na zuwa tace malam tafi.....ta kalleshi Allah sai na siya
maka break kafin ka tafi ko muyi rigima.
Yau ni naga ta kaina....ya fada cikin zuciya.
Ya kalleta, kiyi hakuri da wasa nakeyi na gode,
Ni ban gode ba kawai muje ta nuna mishi hanya.
Dariya ma ya kamayi.
Haka suka je indomie din akwai layi tace kaga kada mu jira zo muje.... Yace to.
Bin ta kawai yakeyi yana kallon ikon Allah sai sauri takeyi suka zagaya babban restaurant din
wurin duk yafi ko Ina kyau da tsada, tayi mishi take-away na chips and eggs aka Sanya mishi
salad da sos din hanta sannan ta siya mishi gasasshiyar kaza daya da maltina biyu da Madara.
Yana tsaye bakin kofar Daman ita kadai ta shiga. Ta fito da sauri tana ta wurga ido kafin ta
hango shi can jikin bango.......barkan ka wallahi na dauka tafiya kayi yau da kaga tsiya.
Kallonta kawai yakeyi Yana Yar dariya.
Muje ka hau mashin din zaka shigo anjima school da karfe 4? Ina son ka koya mun *Human
resources* ya danyi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login